Showing 30001 words to 33000 words out of 126208 words
Chapter 11 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
kwanan duniya yana jin
ana qara masa sonta ne,duk sujjadar da zaiyi saiya roqi Allah yasa shahida mallakinsa ce daga
duniya har lahira
"A ganina wannan ba wani abu bane Allah ya taimakeki,na jima ina cinsa har kawo yau gashi
ina raye ban mutu ba..." Saita mele baki cikin muryar kuka tace
"Zancan mutuwa ma kake?....." Kasa qarasawa tayi ta sake sakin masa wani kukan,kanshi ya
dafe sosai,ya tsani kukanta,idan yana ganin hawayenta ji yake kaman wani babban tashin
hankali ya sameshi
"Ya salam shahidaaah....,Allah ya baki haquri,kin manta cewa mu mutu ka raba ne?" Da
tausasan kalamanshi dake sawa rayuwarta nutsuwa yayi amfani ya lallasheta sannan suka ci
gaba da tafiya,bayan ta sa yayi mata alqawari bazai sake shan gari ba saidai da marmari.
Sanda suka isa tsaidashi tayi ta shiga gida cikin sauri,bata zarce ko ina ba sai kitchen
dinsu,tasan ba'a rasa abincin a gidan nasu,koda bamai yawa bane amma za'a dafa,foodflask
dinta ta dauka ta cika masa shi da taliya da wake sannan ta fita.
Yana tsaye harde da hannayensa a qirji,idan ka dubeshi da kyau ya zaka fahimci ya fada
zurfin tunani ne,ledar hannunta ta miqa masa baqa wadda babu ta yadda za'ayi ya iya gane
meye a ciki,saida dubeta ta masa alama da kai akan ya karba sannan yasa hannu ya amsa
"Ka tafi dashi"
"Meye wannan din?"
"Guba na baka kaci nima naci saimu mutu tare" dariya ta bashi sosai har sai daya dara,itama
sai data fada din maganar ta bata dariya
"Kinsan kuwa zai zame min abun alfahari...kuma babban labarin da zai karade
duniya...masoyiya ta baiwa masoyinta guba donsu mutu tare" murmushin daya qarawa fuskarta
daraja da kyau ta saki
"Zan iya cin guba don tunkudeka daga cinta" girarsa daya ya dage sannan ya sassauta murya
"Idan babu ke ai babu ni shahida....kina tunanin idan kika mutu kika barni zan iya qara kwana
daya a duniya" wani far tayi da ido wanda ya sanyashi yin baya da sauri
"Inni sa'im...naga alama so kike ki....." Da hanzarinta ta juya masa baya cikin shagwaba tana
dan buga qafa alamun batason ya qarasa maganar da yake
"Shikenan.....sai anjima,na gode" ya fada yana takawa don barin wajen,tana wajen tsaye harya
bacewa ganinta,saita lumshe ido ta saki hannayenta tana sakin siririn murmushi,tsakanin ita da
anwar batasan waye yafi wani son dan uwanshi ba,wannan amsar kuwa tasan cewa Allah ne
kadai masaninta.
Cikin kudinta ta cire dubu uku ta siya qaramar waya sabuwa irinta anwar,ummanta bata
hanata ba bare abbanta,sunsan cewa waya ba damun shahidan tayi ba,yanzun ma sun
tabbatar saboda anwar ta siya,wanda dukkansu zuwa wannan lokacin anwar ya zama kamar
d'a a wajensu,mutum ne da Allah yayi masa baiwar saurin shiha zukatan al'umma,hakan kuwa
baya rasa nasaba da hankali nutsuwa uwa uba tarbiyya da yake da ita,ko cikin unguwarsu
dattawan nan son anwar suke,kusan kowa zakaga yana janshi a jiki,shi kuwa ya daukesu
dukkansu tamkar mahaifansa,dalili kenan daya sanya wasu daga cikin matasan unguwar kejin
haushinsa suka kuma qwafa masa,hakanan suka daura dambar sake danqwafar dashi,hakanne
yasa duk sanda ya samu wani abu sakakke sai an haura gidan an sace,kama daga sutura zuwa
takalma ko d'an kudi,ya rasa su waye?,baisan kuma meya tsare musu ba,shi da bashi da
komai?,bai baiwa kowa ajiya ba amma ya tsone musu ido.
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*KO KUMA*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGν ½νΉν ΌνΏ½*
ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*ZAFAFA BIYAR NA
KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR
SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*KO KUMA*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da
sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGν ½νΉν ΌνΏ½*
ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½ν ½ν±ν ΌνΏ½
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*Alqawarin Allah*
0οΈβ£9οΈβ£
Tun daga lokacin ta maida abincin anwar ya zama wajibinta,duk sanda ya nuna alamun turjiya
na bazai amsa ba anan ne zasuyi fada,har hakanma ya zame masa jiki.
Gefe daya kuwa rayuwarshi sai hamdala kawai,kusan duk wani fadi tashi ya zame ma
rayuwarshi jiki,ta fannin kudin registration kuwa ba wani ci gaba da aka samu,iyakar qoqarinsa
bai hada komai ba kaman yadda ya saba,yaqi kuma sanarwa anty husaina,tun yana jin babu
komai harya soma shiga damuwa,ganin lokaci yana quracewa,sannu a hankali ya soma yanke
tsammanin samun kudin ma gaba daya,wanda hakan ya jefashi cikin damuwa mai
tsanani,damuwar da tasa anty husaina ta gane halin da ake ciki,ta kirashi tayi masa fada
sosai,ta kuma saida dan abinda ke gareta na kudi,saidai kudin basu cika ba,kaso d'aya aka
samu cikin biyu,a lokacin ya rage saura kwanaki makarantar su rufe registration.
A hankali take takowa zuwa cikin soron nasu,niyyarta ta tsoratashi kaman yadda yayi mata
shekaran jiya ya tsoratata,taji tsoro sosai ya koma gefe yana mata dariya yana fadin
"Ashe farar kura ce ke bansani ba?".
Yau da yazo kan dakalin qofar gidan nasu yaci burki,hakanan yake jin ranshi babu
dadi,wanda hakan ya bayyana har gangar jiki da fuskarshi,saidai duk sanda ya tuna yanzu
zaiga sanyin idaniyarsa sai yaji yanayin da yake ciki din ba komai bane,wayarshi dage aljihun
wandonshi ta dauki qara,ya zura hannunshi a hankali ya zaro wayar,anty husaina ce ke
kiranshi,yasan kuma kiran bai rasa nasaba da cikon kudin registration dinsa ba,zayaso
kunnuwanta su jiye masa ya samu,saidai ba mai yiwuwa bane yayi mata qarya,abokin kuka shi
ake gayawa mutuwa,sannan uwa uba bayaso wani abu ya kawowa karatunshi tsaiko,babban
burinsa a yanzu shine ya kammala karatunsa ya samu aiki,ya auri shahidansa ya kuma kula da
anty husaina,itama ta huta taji dadinsa
"Yaya dai muhammadu an samu cikon kuwa?" Ta tambayeshi bayan ya gama gaidata,cikin
nuna kasawa da sarewa yace
"Anty ina ganin saidai nayi haquri....wannan karon duk wani qoqarina na samun cikon kudin na
gaza,kudin sunqi samuwa....ina tsoron asarar karatuna..." Tausayinsa ya kama anty
husaina,tasan abune mai wuya ganin karayar anwar
"Kaci gaba da addu'a,ina nan ina nawa qoqarin mu zubawa sarautar Allah ido,in sha Allahu
yana tare da mu"
"A'ah anty.....karki takurawa kanki karki damu,nima zanci gaba da nawa qoqarin...".
A hankali ta koma da baya cikin tsananin mutuwar jiki,ba labe tayi musu ba amma ta kasa
tafiya sanda yake wayar da anty husaina,cikin mutuwar jiki da karaya take juyawa zuwa cikin
gidan,qirjinta ya quntata qwalla ta cika mata idanunta,dama akwai wani abu da anwar zai iya
boye mata game dashi?,da wannan tunanin ta isa dakinta,gefan katifarta ta samu ta zauna
tallafe da kumatunta,batasan adadin lokacin data dauka a haka ba har ya tarawa wayarta
miscal bata gani ba,saida ummanta ta daga labulen dakin
"Wanne shashanci ne kike haka shahida?,kinsan ba zaki samu fita ba kikabar anwar qofar gida
yana jiranki?" Hannayenta ta sauke tana cewa
"Yanzu zan fita umma" sakin labulen tayi ta juya ta fice tana mita
"To ke kuma ya isa haka malamar mita,tunda ta baki uzuri basai kija bakinki ki shuru ba?" Ta
jiyo abbanta yana fada
"Kaga kar kace zakamin fada,don na mata magana laifi nayi?"
"Ba laifi bane,mitar ne ni banason ji karki cikamana kunne"
"Wai yau cin mutuncin naka ne ya motsa baban shahida?" Ta saki abinda take ta zuba masa
idanu tana tambayarsa,saiyayi banza da ita ya zubda ruwan daya kurkure bakinsa ya dauki
hularsa ya fice,ajiyar zuciya shahida dake tsaye bakin window ta saki,ta godewa Alla daya
taqaita cecekucen nasu baiyi tsaho ba har yaja hankalin anwar ko yajisu.
Katifarta taje ta daga,kudaden da uncle hisham ya bata ta dauko,ta zauna ta qirgasu a nutse
sannan ta shiryasu,koda batasan nawa anwar ke buqata ba tasan cikon kudin bazaikai yawan
kudaden dake hannunta ba,don kudaden da uncle anwar din ya bata suna da yawa,don taji ma
anty amina na cewa mama su aje a karba a siyawa shahidan tukunya mai sha biyu a aje
mata,lanqwashesu tayi sannan ta miqe ta gyara mayafinta ta fice.
Sanda ta koma yana zaune kan dakalin,ya zubawa qasa idanu wanda hasken farin wata ya
haske jikinsa yake bashi hoton inuwarsa,a hankali ya dago kai idanunsu suka hadu da
juna,wani sanyi yaji har cikin rai da zuciyarsa,saiya sakar mata murmushi yana jin kaso tamanin
na quncin da zuciyarsa ke ciki ya tafi,kallon farko ana biyu ya karanci lallai akwai abinda yake
damunta,duk sai yaji wani iri,yaji babu dadi,duk wata walwala da karsashinsa ya shiga yin nashi
guri,shi ya amshi daddumar hannunta ya shimfida ya kuma yi mata nuni data zauna,batayi
musu ba ta zauna din,yana tsaye qyam a kanta yana qare mata kallo,ya samu kanshi da kasa
zama
"Mene ne yayi kutse cikin farincikin gimbiyata?"
"Kaine...." Ta fada kanta tsaye,cikin sanyin jiki ya samu dan wani dutse dake daura da ita ya
zauna samanshi
"Bana fatan kasancewar wannan ranar....wane kuskure na tafka haka harya zama tarnaqi wa
farincikin zuciyata?" Hawaye ta soma zubarwa,bana komai bane saina tausayinsa,zurfin cikinsa
yayi yawa,kara da kawaicinsa sun baci,amma ko daya bata son ya sake boye mata wani abu
daya danganceshi,tana ganin kaman hakan wani naqasu ne tattare da dangantakarsu,zai zama
tamkar bai bata muhimmancin da take tsammanin ya bata ba
"Ashe dukan inda nake tunanin nakai bankai can ba a zuciyarka?"
"Ya salam" ya furta fuskarshi na nuna tsantsar tashin hankalin daya shiga,wanda har cikin
zuciyarshi haka ne,wanda har yanajin ya zarce na rashin kudin registration da bai samu ba
"Shah......"
"Kar ka sake cemin komai....na kamaka da laifuka guda biyu kawo yanzu,ban taba boye maka
komai daya danganceni ba....amma kai ka boyemin abubuwa har biyu,ban sani ba
ko.matsayina baikai nasan wannan fannin ba...." Sanyi ya dinga ji yana ratsa qasan
zuciyarshi,duk da bai fuskanci me yayi mata ba,dubanta yake cike da qaina soyayya sa shauqi
mai yawa,ta damu da lamuransa fiye da tunanin mai tunani kamar yadda ya damu da nata,bai
tsammaci zata soshi kamar yadda yakesonta ba,ya zaci zata soshi ne irin son da baikai ya
kawo ba,kodon kyau da Allah ya bata,kodon gata data d'arashi,ko don saboda farinjini da Allah
yayi mata
"Yanzu karatunka ba nawa bane?" Ta fada maganar quruciyarta na fitowa fili,hakanan ta b'ata
rai sosai ta kuma tsareshi da ido,murmushi ya saki wanda ya bayyana fararen haqoranshi
"Nakine my shahida"
"Don me baka gayamin halin da kake ciki ba?" Dan shuru yayi yana tauna amsar da zai
bata,tsahon minti guda kafin yace
"Shahida....kin wuce duk inda kike zato kike tsammani a wajena,tunda Allah ya busan numfashi
ban taba qaunar wata d'iya mace ba saike,nine namiji,ni nake nema,kuma nine sama dake,bai
cancanci ace dukkan wata wahalata tana wuyanki ba"
"Koda bani da abun da zan taimaka dashi ai na sanyaka cikin addu'o'ina ko?" Idanunsa ya
lumshe idanunsa yayi yana sakin murmushi
"Ni na sani shahidana koda banda damuwa ba zata daina sakani a addu'arta ba"
"Ta yaya zan aminta cewar mun zama daya kana boyemin ire iren wadan nan abubuwan?"
"Shahidaa...karki sake tunanin bamu zama daya ba,kin zama muhammad anwar,na zama
rahamatulshahida" sunan ya bata dariya har sai data murmusa,tafin hannunta ta bude sannan
ta miqa masa kudin hannunta
"Ungo qirgamin" amsa yayi yana zolayarta,sannan ya soma qirgawa yana cewa
"Shahidana ta zama hajjaju" sai daya gama qirgawa sannan ya dago ya dubeta yana gaya mata
nawa ne,kai ta gyada duk da tasan nawa ne dama
"Kayi amfani dasu" sak ya tsaya yana dubanta kafin yace
"Shahida...." Idanunta ta ware masa tana dubansa itama,ya gane me take nufiSai ya saki
murmushi
"Aro na baka,amma kayi duk amfanin da kakeson yi dasu"
"Kai amma wannan yarinya kin iya bada rance....to na gode Allah ya bani ikon biya" daga haka
sukaci gaba da hirarsu,saidai rabin hankalinsa dukka yana kan halayen shahidan,yana sake
godewa Allah tabbas baiyi zaben tumun dare ba,hakanan ya tabbatar bai miqa zuciyarshi inda
bai cancanta ba.
Wannan abu da shahidan ta yiwa anwar ba qaramin qara mata qima yayi a idanun anty
husaina ba,wata qauna take mata tamkar diyar cikinta tun kafin ma ta yiwa anwar hakan,ta
yadda ta kuma yi amanna cewa anwar yayi dace da matar aure,ta kuma shiga sahun masu
masa addu'ar Allah yasa shahidan ta zama mallakinsa.
Ta gefan anwar dinma tuni ya shiga bakunan 'yan uwan shahidan musamman 'yan gidansu
da anty amina wadda sukafi dasawa da shahida duk cikin 'yan uwan mamanta,kasancewar tasu
tafi zuwa daya da mamanta,kuma ita daya ke gaya mata magana itama maman da ita take
shawara.
Cikin ikon Allah anwar yayi registration dinsa,komai yaci gaba da tafiya dai dai,rayuwarsu
da shahida kuwa ta zama abar kwatance ga duk wanda ya sansu,kowa najin jinin danuwansa
na yawo a nasa jikin,tun mutane na mamakin yadda sukeson juna har abun ma ya zame musu
jiki,su kansu yadda suke nunawa kansu qauna basusan sunayi har haka ba saidai a gaya
musu.
Sannu a hankali rayuwa taci gaba da juyawa,ta wanni fannin ana samun ci gaba yayin da
wani bangaren yake zamowa koma baya da babban naqasu wajen bawa.
Zuwa sannan shahida sun shiga ss 3 term din farko,a sannan ne Allah ya yiwa mahaifin
zunnurah rasuwa,hakan ya zama silar barinsu garin kano sukayi qaura suka koma katsina cikin
danginsu,dalilin kenan daya sanya kusancin shahida da firdausi ya sake samun tagomashi mai
yawa,ta maye mata gurbin zunnurah,yayin da ita da zunnurah ya zama sai a waya,lokaci lokaci
idan sukayi waya tana sako mata zancan fiddausin tare da sake ja mata kunne kan tayi hankali
da ita,murmushi shahida keyi yawancin lokaci,ta sake yarda Allah ne kadai.ya isa ya hada
zukatan bayinsa,har yau bata tana ganin wani abu mai kama da abinda zunnurah ke tuhumar
fiddausi dangane da ita ba.
Anwar ya samu ya kammala karatunsa cikin wahala da dagiya da kuma taimakom anty
husaina wadda ta sadaukar da dukkan wani abu nata don ci gabanshi,yayin da shahida ta zamo
mutum na biyu data sadaukar da dukkan wani abu da take ganin ta mallaka saboda anwar din.
Bayan fitowar sakamakonsa wani yayan abokinsa ya kirasu yayi musu tallar aikin d'an
sanda da za'a soma dauka,rimi rimi sukayi komai da karime karime da qarfafawar gwiwar
shahida data dage kan sai yaje,sai kuma batun tafiya training ya taso,a nan ne ya sare saboda
lissafen lissafen abubuwan da za'a buqata daga garesu,wanda kusan duka harka ce ta
kudi,koda wasa bazai doshi anty husaina da wannan batun ba saboda yasan cewa wahala ce
da nauyi kawai zai dora mata,saiya shiga neman kudi babu ji babu gani,sai lokacin da tafiyar ta
matso sannan ya shaidawa anty usaina,ta masa addu'a sosai,ranar da zaiyi sallama da shahida
ta dauko baqar ledar viva ta dire masa.
Sai daya gama kalla sannan ya dago yana dubanta,baisan ma da wanne baki zai mata
magana ba,da wanne harshe zai gaya mata yadda take a wajensa?,kaya ne da tasan cewa zai
iya buqata a ciki,wanda ko bata fada ba yasan a qalla zata kashe dubu biyar,Da hannu ta masa
nuni dole yayi shuru,tamkar ba zasu rabu ba ranar,ji yake kaman idan yaje zaiyi shekara ne bai
dawo ba.
Kwanansa uku acan shida wasu mutum biyar suna cin wuya saboda ance sam babu
sunansu cikin list din,bawai kuma babu dinba,yanayin qasarmu ne kawai,an suba wadanda
sukafi kowa rashin galihu an cire sunayensu daga list din an maida gurbinsu dana
wasu,hakanan suka tattara suka dawo gida.
Randa shahida ta ganshi ya dawo ba qaramin jin takaici tayi ba,har kuka ta kusa yi,shi ya
dinga lallabata yana bata haquri
"Duk randa Allah ya horemin abu na farko da zan fara ginawa shahida shine makaranta,zanyi
irin makarantar da yaran masu kudi suke zuwa,irin makarantar da suke karatuna zuba yaran
masu qaramin qarfi,su samu irin ilimin da yaran masu hannu da shuni suke samu,su samu gata
da kulawa irin na yaran masu dashi"shuru shahida tayi tana karantarsa,har cikin zuciyarsa
maganar take fitowa saboda yadda hakan ya bayyana saman fuskarsa
"Yaran marasa shi suna shan wahala,suna shan wahala matuqa wajen neman ilimi,bayan sun
samu karatun da qyar ya zamana karatun ya kusa zama na banza,sakamakon yadda aiki ke
musu wahala,wanda wasunsu daga qarshe sakamakon karatun nasu kusan dai dai yake da
takardar tsire" nan ma dan shuru yayi yana hadiyar yawu,sosai lamarin ke sukar zuciyarshi,sun
jima suna tattaunawa game da halin rayuwa sannan daga bisani sukayi sallama.
Anwar bai gajiya ba bai kuma sare ba yaci gaba da neman aiki baji ba gani,burikansa din
nan guda biyu su yake fafutukar ganin ya cimmawa,yana tsoron shahida ta kammala secondry
ba tare daya samu aiki ba,babban burinsa a duniya suyi aure sanda zata kammala
makaranta,ya kuma tsaya mata tayi karatu kaman yadda takeso harsai tace ya isheta,yana da
burin yi mata halacci kwatankwaci koma fiye da yadda tayi masa.
*BAYAN WATA HUDU*
Kallonshi take tamkar ta zabga masa mari haka takeji,saidai hakan ba maiyuwuwa bane
tunda ba tarbiyyarta bace,dawowarta kenan daga gidan anty amina ya tsaidata,sam batasan
yana biye da ita tun daga qofar gidan anty amina ba cikin motarsa saida ta iso layin nasu,ta
shiga gida da niyyar ba zata saurareshi ba yadda yaketa zabga aike yasa umma tace ta fita ta
saurareshi.
Hakanan cikin jikinta takeji kamar akwai wanda yake kallonta,kamar anwar na wajen tare
dasu,a hankali ta kalli damanta,shine kuwa sanye cikin jibgegiyar rigar sanyi da wandon
jeans,kasancewar ana cikin yanayin sanyi,yayi kyau matuqa,kai kace wani ne ko dan gidan
wani,kyansa ya sake fitowa,fitilun motar daya bari