Showing 87001 words to 90000 words out of 126208 words
Chapter 30 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
dake sama tana juyawa ta sake
dawowa ta kwanta a riginginen dai,haka kawai zuciyarta tayi wani rauni,hawaye ya soma bin
kumatunta yana zirarowa gefan fuskarta,ta dinga shareshi akai akai,duk sanda ta tuna anwar
zata aura sai taji zuciyarta ta quntata,a ganinta bata dace dashi ba,bata cancanci mutum
kamarsa ba,tunda a baya ya iya guje mata a gaba babu abinda zai hanashi aikata hakan,bugu
da qarima gaba daya auren manufa zaiyi da ita,yayi ne don kawai ya rusa walwalarta ya rabata
da nuradden.
Umman ta dan jima tana kallonta ba tare data sani ba kafin tatako zuwa cikin falon,ta samu
kujera daya ta zauna sai a sannan shahidan ta ganta,miqewa tayi daga kwanciyar kuka na balle
mata sosai,baki ta sake umman tana dubanta sannan tace
"Saikace qanqanuwar yarinya zaki tasani gaba kina kuka?,meye hakan?" Zamowa tayi daga
saman kujerar da take kai tayin kneeldown a gaban umman ta kama hannayenta
"Don girman Allah umma ki dakatar dasu,ke daya ce burina na qarshe,wallahi umma bana
sonshi shima baya sona,ku aura min koma waye umma amma banda anwar?" Idanu ta saka
tana kallonta,a iya saninta abinda ya faru tsakaninta da anwar ma laifi nata ne,iya abinda ta
saninma baiyi zafin da zata rikice hakan ba harta rasa sukuni da walwala ba,Yayin da khadija
wadda shigowarta kenan ta tsinci xancan ta dafe baki gami da zare ido cikin mamaki,har
batasan sanda tayi subutar bakin cewa
"Yaaya?,ya anwar ne fa?" Daga kai umma tayi tayi mata nuni data fice,haka ta fita cikin dimbin
mamaki,ta zaci antyn tata zatayi farinciki da dawowar anwar rayuwarsu fiye da yadda su
sukayi,amma ga sabanin hankalinta sai taga ba haka bane sam.
A nutse umma ta zuba mata idanu,cikin sanyin murya wanda ke nuna har jikinta ma a
sanyaye yake tace
"Ashe so kike ki tona mana asiri shahida bayan lullubin sutura da Allah yayi mana?" Ta qarasa
maganar wani abu na taba zuciyarta wanda ya bayyana har a muryarta
"Shahida ashe baki qaunata?,ashe ba rufin asiri Allah yayi miki ba damu kanmu daya dawo miki
da anwar?,meye a zuciyarki shahida?,bakison farincikina ashe da walwalata?"kai shahida ke
girgizawa kuka na qwace mata
"ba haka bane umma,umma bana sonshi kiyi haquri umma,wallahi banajin sonshi kwata kwata"
"Shahida indai nice na haifeki ina....."
"A'ah,karki qarasa don Allah umma" sukaji wata murya da sako kanta kenan dakin ta tsinci
zancan shahida na qarshe da lafazin umman ta fada,dukkansu suka juya suna kallonta,anty
usaina ce,ta qarso inda suke zaune,wajen shahida ta nufa kai tsaye ta kama hannayenta
sannan ta zauna gab da ita,hankalin umma yadan tashi kadan don ba zataso shahida tacigaba
da magana kan anwar ba,don tana da tabbacin batasan wace ita a wajenshi ba
"Idan kika fadi haka kamar kin mata qarfa qarfa ne ai" tana kallon umman tayi maganar,wani
sanyi shahida taji cikin ranta,tana fatan Allah yasa zuwan matar ya zame mata haske
"Idan kuma tana da hujjarta fa wadda tafi taku qarfi?,ki barta aji hujjarta da dalilanta tukunna".
Miqewa umma tayi
" bata da wata hujja ko dalili usaina"
"A'ah bari naji ta bakinta tukunna"
"Koda kinji ta bakinta na riga na yanke matuqar nina haifeta ina bata umarnin auren anwar"
daga haka umma ta fice daga dakin tana mamakin wauta da sakarcin da shahidan takeson
tafkawa,kamar batasan meya wakana cikin rayuwarta a baya ba,bata taba tsammanin ma
anwar zai sake waiwayar shahida yace zai aureta ba sabida abunda idanunshi suka gane masa
a zahiri ba labarj,dama tazo mata tanason tayi wasa da ita?,koda taqi anwar din batajin zata
samu kamar anwar din,mutumin da tun wancan lokacin ya samu karbuwa cikin kaf danginta na
uwa da uba,badon komai ba sai kyawun halayyarsa da kyawawan dabi'un da Allah ya huwace
masa.
Maido dubanta kan shahida tayi bayan ficewar umma,suka hada idanu,hakanan shahidan taji
gabanta ya fadi,ta dauke nata idanun tana matsar qwalla,cikin taushin murya ba tare data saki
hannunta ba tace
"Shahida....inason naji meye matsalarki dashi wannan din da umma tace saikin aura,indai naji
dalilanki masu qarfi ne nayi alqawarin tsaya miki harsai an warware komai" shuru na 'yan
sakanni ya ratsa tsakaninsu,batajin zata iya furtawa wani komai,yin hakan kamar ta dabawa
cikinta wuqane,tana ji ceqa wani sirri ne agareta ga duk wanda baisan meye faru ba,a hankali ta
motsa labbanta sannan tace
"Kawai bana sonshi,shima kuma baya sona,hasalima mun rabu dashi a qalla shekara shida
kenan,ba wanda keda muradin wani" shuru anty usaina tayi tana nazarin kalamanta,ba shakka
akwai wani abu,amma dukkansu amsa kusan guda ce,jiya jiya ta titsiye anwar din kan meye
sanadin rabuwarsu da shahida amma ya kasa bata amsa daya qwaqwqwara,kowannensu
bayason fallasa asirin dan uwanshi,hakan na nufin akwai ragowar wani abu da yayi saura game
da zukatansu qarqashin zukatansu kenan koda su basusan da hakan ba?
"Amma shahida....ya akayi kikasan baya sonki?,kuma dama an taba rabuwa hakanan babu
wani dalili?"tambayar taso kaita maqura saboda rashin amsa
"Miji da mata ma kan iya rabuwa haka kawai ya saketa badon ta masa komai ba,saidon
qarewar wa'adin zamansu da Allah ya qaddara musu" saitayi shuru tana hadiyar zuciya tana
neman amsa ta biyu da zata bata wadda zata gamsar da ita,da qyar ta iya hada abun fadi
bayan anty usainan tace "Uhmmm,ya akayi kikasan baya sonki?"
"Duk wani abu na nuna kulawa ko xiyara da zai nuna saurayi yana son budurwa babu shi tattare
dashi,sau daya ya taba zuwa wajena,shima bamuyi ganawar dadi dashi ba,ta yaya zance yana
sona?" Ta qarasa maganar badon abinda ta fada ya dameta koya dadata da qasa ba,a'ah,ta
fada ne kawai donta riqeshi hujjar da anty usaina zata taimaka mata ta rana wannan auren da
take kallonsa a matsayin qarfen qafa mai wuyar kwantuwa a gareta.
Lallai ya zama dole ta shiga alaqar shahida da anwar,tana fata nan gaba dukkansu suyi
dariya,tana fatan ko meye silar shiga tsakaninsu nan gaba ya zama tarihi,rayuwarsu ta koma
kamar yadda take a baya
"Naji dadi da kika kasance yarinya mai biyayya wa iyayenta,ina mai miki kyakkyawan fatan ba
zaki toxarta ba in sha Allahu,biyayyarki zata kai miki da ixinin ubangiji" da wannan kalaman
sukayi sallama,ta fice daga gidan bayan ta samu umma ta roqeta kan karta gaya mata
dangantakarta da anwar,donta tabbatar hakan zai baiwa shahidan kunya.
Tun a kan hanya ta soma gwada number anwar din,saidai bata sami wayarshi ba akashe
take,da alama yana muhimmin wani abune,dole ta katse kiran ta isa gida,saidai lokaci lokaci
tana gwada number tashi ko xata dace ta shiga.
Tana idar da sallar magariba ta soma shirin barin gidan,umma ta dubeta
"Amma da kin dan jinkirta tafiyar tukunna,saboda garin a dinke yake da hadari ga iska ta soma
kadawa"
"Idan ya sauko bansan ranar da zai dauke ba,anty zubaida kuma zataji shurun yayi yawa,don
ban gaya mata ma ina nan ba"
"Shikenan,Allah yayi miki albarka,yasa albarka a rayuwarku"
"Ameen" ta amsa tana maida qwallar dakeson fitowa,haka ta baro gidan tana tafiya kamar
wadda batason taka qasa,wanda bai sani ba sai ya zaci salo ne ko tana sane,amma ba komai
bane sai tsabar damuwa dake cinta a rai,tana jin yadda hadarin ya taso sosai sanda takai
tsakiyar layin nasu,iska ta dinga kadawa tana ratsa jikinta,saidai sam bata damu ba,bata damu
da ruwan ya sauko ya daketa ba,hakanan bata damu data koma gida donta samu mafaka ba.
Daidai lokacin da motarsa ke tsaye qofar gidan anty usaina wadda ta buqaci ganinsa a yau
basai gobe ba,yana zaune cikin motar baikai ga yiwa mai gadi horn ba bare ya bude masa,ya
tsaya ne amsa waya,dukka gilasansa a rufe suke ruf kamar yadda al'adarsa take yawanci idan
yana cikin mota,bugu da qari kuma ma sabida iskar dayaga ta taso sosai,wanda yasan ba za'a
rasa qura ba cikinta,gefansa ya kalla kamar wanda aka fisgi hankalinsa,sai yaga kaman itace ta
wuce,yaci gaba da amsa wayar yana kallon bayanta,tabbas ita dince,amma me take har war
haka duhun magariba ya mamaye gari bata koma gida ba,idanunsa suka ci gaba da kallonta
har lokacin data dan bada tazara daga inda yake,yana shirin janye idanunsa yaga yayyafi ya
soma sauka ta gilashin motarsa,yaso ya dake yaso ya dauke kai ya saka motarsa cikin gidan
anty usaina amma saiyaji kaman umarni,a zafafe yace
"Oh god" yana zare belt din jikinsa,cikin zafin nama da kuma jin haushin kansa da kansa ya
bude murfin motar ya fice.
Yana kuzari da halittar ba daya bace,hakan ya sanya cikin qididdgaggun taku ya cimmata
"Daga ina kike haka?" A nutse ta waiwayo tana dubansa sanda take gab da qarasa bakin
titi,saita juya da niyyar ci gaba da takawa ba tare data amsa shi ba
"Wai sanda zaki fita ma kin tambayeni ne?,saboda tsabar rinton zunubi?" Kalaman sun mata
ciwo,wato tun yanzu yake nufin xai mulkata kenan?,hakan yasa ta tsaida tafiyar tata ta juyo ta
dubeshi
"Kai waye da don zan fita saina tambayeka?"
"Kinfi kowa sanin ni waye ai ba buqatar na maimaita miki,banason dogon zance wuce muje na
taimaka miki na saukeki,amma kafin sannan idan kina da niqab ki saka a fuskarki kar mutanen
unguwa su ganmu tare su zaci nima dan harka ne" ya kai qarshen zancan yana dage girarsa
duka biyun,wanda hakan ya masa kyau ainun duk da fuskarshi a murtuke take,sosai kalaman
suka fusatata wanda hakan ya sanyata ta juyo gaba daya ta watsa masa idanunta da suka sake
budewa saboda bacin rai,hakan ya tilasta masa dan qanqance nashi idanun gami da damqe
hannayensa dake zube a aljihu
"To hell with your taimako...Allah suturu buqui,har abada bana son taimakonka,sannan kuma
aikin banza kake harara a duhu,da kake gudun kar a ganmu tare me ya kaika neman dauramin
igiyarka,idan da gaske kake qyamata aiya kamata ka gujeni da gaske ta yadda ko qasa daya ba
zaka hada dani ba bare inuwa daya,indai ka cika kai anwar ne ka aikata hakan" qaramin
murmushi ya saki daya sake fitar da kyansa,ya dage dukka kafadunsa
"Ba zaki taba samun yadda kikeso ba,niba qaramin yaro bane bare kalamanki su tunzurani nayi
miki yadda kikeso,abu daya kawai na sani shine,na riga dana biya sadakinki,saboda haka ina
da power a kanki ko kinqi ko kinso...saboda haka ki wuce muje" dogon tsaki taja wanda ya ratsa
kunnuwansa,sannan ta watsa masa harara ta juya taci gaba da tafiya,bai fasa binta ba shima
har suka isa titi.
Adaidaitan farko data tsaida ya sallameshi da dubu daya yace yane abinsa,na biyu ma
haka,na uku kuwa da yame dattijone yace masa baba kaje matata ce yaji takeson yi,na bata
haquri taki haqura,nan yasa bawan Allahn ya tsaya yana mata nasiha,inda daga qarshe ya
sallameshi da dubu uku ya amsa yana godiya,ta hudu kuwa ya samu sauayi maiji da tashen
girma yaso masa gardama.kan saiya dauketa tunda itama tana son shiga
"Kana sha'awar xaman gidan kaso kenan?" Harya karkata baki zai masa diban albarka saiya
nutsu ya qarewa shigarsa kallo,tun daga takalminsa,kayan jikinsa zuwa agogonsa,aibabu shiri
yaja abun hawansa ya fece,bacin rai ya taru ya rufeta ruf sanda ta kalli titin ta ganshi fayau ba
wani sauran abun hawa na haya kuma nan kusa,ta waiwayo zata gasa masa magana ko xataji
sanyi,kadan ya rage fuskarsu ta gwaru,sam batasan yana bayanta ba a tsaye,da alama kuma
duk tsahon lokacin kallonta yake,baya yaja yana bata fuska
"Ke baki da kunya ne?,akan titi kike neman ki rungumeni?,toki maida qwalamarki,ni ba naki
bane" kawai saita fashe da kuka ba tare data shirya ba,saboda ya gama cutarta,bata ga wani
kalma da zata fada masa ba wadda zata rama abinda ya gaya mata,minti biyu kacal ruwan
sama ya soma sauka,ya kalli sama sannan ya kalleta "A karo na qarshe nake gaya miki ki wuce mu tafi" baya taja saman wasu tayoyi da masu faci
suka tashi suka barsu a wajen ta zauna,ta gwammace ruwan yayi mata koma meye data bishi
kota shiga motarshi,ganin ta zauna dafa'an ya sanyashi juyawa ya koma cikin layin don dauko
motartashi zuwa nan bakin titin dukda yadda ruwa yake dukansa.
Yana isowa wajen yaga tashinta cikin adaidaita sahu,qaramin murmushi ya sube masa,wato
dama tana da taurin kai kenan?,saiya sake baiwa motar wuta harsai daya je daya side din na
adaidaitan,ya tabbatar ta ganshi sannan ya barsu suka wuceshi,a baya yaci gaba da binsu har
xuwa sanda yaga shigarta gida sannan ya karya kan motar ya koma gidan anty usaina.
Sanda ta shiga gida baqinciki da takaici ya sake cikata ganin yadda gidan har baqi yadan
samu,hakanan ga kayan amsar lefe a kammale gobe kawai suke jira,hasina ma ba'a barta a
baya ba,ganun zata saka mata ciwon kai da tsokanarta yasa tayi zarcewarta daki ko tsayawa a
wajen batayi ba bare ta zauna,gaban mudubinta ta tsaya tana kallon yadda ta jiqe gaba
dayanta,haushinsa ya sake cikata,taji kaman ta sake fashewa da wani kukan,duk shi yaja
mata,da ta shiga adaidatan a lokacin daya dace da duk hakan bata faru da ita ba,haka ta ringa
cire kayanta daya bayan daya ta daura babban towel ta shige bandakinta ta hada ruwa mai zafi
tayi wanka.*AA*
3️⃣2️⃣
Sallama tayi a tsakar gidansu,khadija dake qofar kitchen tana tankadewa umma dake cikin
kitchen garin tuwo ta amsa,a matuqar kasalance kamar wadda tayi aikin shekara ta tsaya da
qofar kitchen din tana gaida umman,ta waiwayo ta dubeta sannan ta amsa tana karantar
yanayinta,khadija na gaidata ta amsa mata tana shigewa falonsu,jakarta ta aje waje daya
sannan ta cire mayafinta ta dora akai,ta samu daya daga cikin kujerun falon ta kwanta tana
sauke numfashi a hsnkali,saita tashi ta sake qaro gudun fankar dake sama tana juyawa ta sake
dawowa ta kwanta a riginginen dai,haka kawai zuciyarta tayi wani rauni,hawaye ya soma bin
kumatunta yana zirarowa gefan fuskarta,ta dinga shareshi akai akai,duk sanda ta tuna anwar
zata aura sai taji zuciyarta ta quntata,a ganinta bata dace dashi ba,bata cancanci mutum
kamarsa ba,tunda a baya ya iya guje mata a gaba babu abinda zai hanashi aikata hakan,bugu
da qarima gaba daya auren manufa zaiyi da ita,yayi ne don kawai ya rusa walwalarta ya rabata
da nuradden.
Umman ta dan jima tana kallonta ba tare data sani ba kafin tatako zuwa cikin falon,ta samu
kujera daya ta zauna sai a sannan shahidan ta ganta,miqewa tayi daga kwanciyar kuka na balle
mata sosai,baki ta sake umman tana dubanta sannan tace
"Saikace qanqanuwar yarinya zaki tasani gaba kina kuka?,meye hakan?" Zamowa tayi daga
saman kujerar da take kai tayin kneeldown a gaban umman ta kama hannayenta
"Don girman Allah umma ki dakatar dasu,ke daya ce burina na qarshe,wallahi umma bana
sonshi shima baya sona,ku aura min koma waye umma amma banda anwar?" Idanu ta saka
tana kallonta,a iya saninta abinda ya faru tsakaninta da anwar ma laifi nata ne,iya abinda ta
saninma baiyi zafin da zata rikice hakan ba harta rasa sukuni da walwala ba,Yayin da khadija
wadda shigowarta kenan ta tsinci xancan ta dafe baki gami da zare ido cikin mamaki,har
batasan sanda tayi subutar bakin cewa
"Yaaya?,ya anwar ne fa?" Daga kai umma tayi tayi mata nuni data fice,haka ta fita cikin dimbin
mamaki,ta zaci antyn tata zatayi farinciki da dawowar anwar rayuwarsu fiye da yadda su
sukayi,amma ga sabanin hankalinta sai taga ba haka bane sam.
A nutse umma ta zuba mata idanu,cikin sanyin murya wanda ke nuna har jikinta ma a
sanyaye yake tace
"Ashe so kike ki tona mana asiri shahida bayan lullubin sutura da Allah yayi mana?" Ta qarasa
maganar wani abu na taba zuciyarta wanda ya bayyana har a muryarta
"Shahida ashe baki qaunata?,ashe ba rufin asiri Allah yayi miki ba damu kanmu daya dawo miki
da anwar?,meye a zuciyarki shahida?,bakison farincikina ashe da walwalata?"kai shahida ke
girgizawa kuka na qwace mata
"ba haka bane umma,umma bana sonshi kiyi haquri umma,wallahi banajin sonshi kwata kwata"
"Shahida indai nice na haifeki ina....."
"A'ah,karki qarasa don Allah umma" sukaji wata murya da sako kanta kenan dakin ta tsinci
zancan shahida na qarshe da lafazin umman ta fada,dukkansu suka juya suna kallonta,anty
usaina ce,ta qarso inda suke zaune,wajen shahida ta nufa kai tsaye ta kama hannayenta
sannan ta zauna gab da ita,hankalin umma yadan tashi kadan don ba zataso shahida tacigaba
da magana kan anwar ba,don tana da tabbacin batasan wace ita a wajenshi ba
"Idan kika fadi haka kamar kin mata qarfa qarfa ne ai" tana kallon umman tayi maganar,wani
sanyi shahida taji cikin ranta,tana fatan Allah yasa zuwan matar ya zame mata haske
"Idan kuma tana da hujjarta fa wadda tafi taku qarfi?,ki barta aji hujjarta da dalilanta tukunna".
Miqewa umma tayi
" bata da wata hujja ko dalili usaina"
"A'ah bari naji ta bakinta tukunna"
"Koda kinji ta bakinta na riga na yanke matuqar nina haifeta ina bata umarnin auren anwar"
daga haka umma ta fice daga dakin tana mamakin wauta da sakarcin da shahidan takeson
tafkawa,kamar batasan meya wakana cikin rayuwarta a baya ba,bata taba tsammanin ma
anwar zai sake waiwayar shahida yace zai aureta ba sabida abunda idanunshi suka gane masa
a zahiri ba labarj,dama tazo mata tanason tayi wasa da ita?,koda taqi anwar din batajin zata
samu kamar anwar din,mutumin da tun wancan lokacin ya samu karbuwa cikin kaf danginta na
uwa da uba,badon komai ba sai kyawun halayyarsa da kyawawan dabi'un da Allah ya huwace
masa.
Maido dubanta kan shahida tayi bayan ficewar umma,suka hada idanu,hakanan shahidan taji
gabanta ya fadi,ta dauke nata idanun tana matsar qwalla,cikin taushin murya ba tare data saki
hannunta ba tace
"Shahida....inason naji meye matsalarki dashi wannan din da umma tace saikin aura,indai naji
dalilanki masu qarfi ne nayi alqawarin tsaya miki harsai an warware komai" shuru na 'yan
sakanni ya ratsa tsakaninsu,batajin zata iya furtawa wani komai,yin hakan kamar ta dabawa
cikinta wuqane,tana ji ceqa wani sirri ne agareta ga duk wanda baisan meye