Showing 15001 words to 18000 words out of 126208 words
Chapter 6 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
musbahu kenan,mutum daya tak daya takura rayuwarta cikin makarantar
fiye da kowacce halitta,itakam shi da nuraddeen batasan wanda yafi wani naci ba,harma gwara
nuran yakan d'aga mata qafa lokaci zuwa lokaci,tun dazun take jinta not comportable ashe
shike kallonta.
Sake duban agogon nata tayi sannan ta miqe lokaci guda,ta kuma nemi izinin tafiya kan
tana da wani uzuri,babu musu shugabannin sashen secondry dana primary suka bata izini
"Bamuso tafiyarki ba ayanzu miss shahida,saboda yanayin gudunmawar da kike badawa ta
bambanta data kowa" malam musbahu ya fada yana dubanta qasa qasa,bata amsashi ba har
sai data kammala hada takardunta sannan tace
"Ba wanda nafi a nan,kuma duk wata gudunmawa data dace na riga dana bada ita" a nutse ta
juya ta fice bayan tana yunqurin ciro wayarta daga jaka.
Sai data kira anty zubaida ta shaida mata ta wuce gidan anty amina sannan ta tsaida abun
hawa,don idan azumi ya kama bata fita ko ina sai an kammala,in bata jewa anty aminan ba
batasan lokacin zuwanta ba,hakan yasa ta daure zuciyarta ta yanke shawarar gwara taje din
kawai.
Tafiyar minti arba'in kacal daga makarantar zuwa gidan anty aminan,da sallama ta shiga
gidan,saidai hayaniyar yara bai bari anji ba saidata sake wata sallamar,hamida ita ta soma ji,ta
nufi shahida da gudu tana mata oyoyo,kafin kace meye wannan sun lullubeta,qarin tashin
hayaniyarsu shiya ankatar da anty amina dake kitchen tana shirya musu abincin rana saboda
lokacin tafiya islamiyya ya gabato,ta leqo cikin mamaki tana duban shahidan,bata taba
tsammatar ganinta ba,yadda ta saki baki ya bawa shahida dariya,saita murmusa sanda take
ciro alewa daga jakarta tana barewa qaramin yaron anty aminan faisal
"Ku qarasa ciki ina zuwa" ta fada tana komawa kitchen din,da haka suka qarasa falon anty
aminan suka zube kowa na murnan ganinta,sun kasa qarasa shiryawa ma zuwa islamiyyar.
Duk sai data raba musu abinda ta ruqo sannan sukaci gaba da hirar kowa tana biye
dashi,ta jima rabonta da walwala irin haka,tunda can maison yara ce dama ita,hakan yasa taji
wani sukuni na musamman na shiga cikin ranta.
"Yayaa,ina uncle kuwa?,yayimin alqawarin sweet har yau bai dawo ya kawomin ba" sadiq
yaron anty amina ya fada yana saka rigar islamiyyarshi,dai dai sanda anty aminan ta shigo da
plates din abinci,cak shahida taji komai ya tsaya mata,ta kasa hadiye biscuit din data farke cikin
wanda ta kawo musu ta d'an soma ci saboda hamida data takura mata cewa da dad'i,yadda ta
tsaya cak haka anty aminan ta tsaya tana dubanta,don tasan saddiq ya b'arota,yayin da sauran
yaran duk suka zuba mata idanu suna sauraren amsarta,don gaba dayansu suna da buqatar
sanin dalilin daina ganinsa dare d'aya lokaci daya kuma gaba d'aya
"Ya mutu" furucin ya fito daga bakinta kamar mai ciwon baki,idanunta kan saddiq wanda ya
kasa qarasa saka rigar tashi jin abinda shahidan ta fada,harga Allah tana daukarshi tamkar
matacce ne a ruhi da zuciyarta,duk da dama ya dade da mutuwa a cikin tata zuciyar
"Ya mutu yayaa?"saddiqa ta fada tana zaro idanu,alhini da mamaki ya bayyana qarara kan
fuskar yaran gaba daya
"Kai banason dogon surutu,ke hamida dauki abincinku ki kai muku dakinku kuci a can ku shirya
maza ku fice ku bani waje" cewar anty amina tana musu wuta wuta,don tasan tabbas ba
qaramin furuci bane wannan a wajensu,duba da yanayin sabo dake tsakaninsu dashi,c gaba fa
maganar kuma dai dai yake da hargitsa lissafin shahida da dukkan walwalar data samu cikin
gidan,hakanan yaran suka dinga fita daga dakin jikinsu a matuqar sanyaye.
Sai da suka gama fita gaba daya sannan anty amina ta qarasa kusa da shahida ta aje
kwanon abincin idanunta na kan shahida data sauke kanta qasa
"Har sai yaushe shahida zakici gaba da rayuwarki kamar kowa?,sai yaushe zaki maida abinda
ya faru kaman bai faru ba?,yaushe zaki rufe wannan tarihin daga babin rayuwarki?,me yasa
wannan lamarin yaqi fita daga ranki kamar sauran abubuwa?" Kasa bata amsa tayi sai tafukan
hannayenta data saka guda biyun ta rufe fuskarta dasu,ita kanta tana son ta koma normal,tana
son ta zama kamar kowa,tanason ta manta da komai amma ta gagara yin hakan?,me yasa
abun yafi tsaya mata fiye da komai?.
A jigace ta dawo gida bawai don tayi wata gajiya ta azo a gani ba,illa dai zuciyarta data
dahu lugub ta kuma saare tun sanda yaran suka jefa mata tambaya a kanshi,batayi dogon
zama a falon ba ta yiwa anty zubaida sallama kan cewa gobe da wuri zata tashi tana son isa
makaranta da wuri don gobene ranar hutunsu.
*1:26 pm*
Tsaye yake cikin wani makeken fili wanda ya qawatu da fareren furanni tas da jefi jefin
koraye,waje ne daya ni'imtu,ya kuma qawatu da wata irin iska mai dadi da taush take kai kawo
iya fadi da girman filin,cakude iskar take da qamshi mai sanyi wanda ke ratsa zuciya,fararen
kayane qal a jikinsa,yana tsaye gaban wata qaramar qorama mai garai garai,kana iya hangen
kifayen dake linqaya da kai kawo daga can qasanta.
Ingarman bayanshi take iya hangowa,ta zuba mishi idanu tana jin wani bugu da zuciyarta
keyi,tana jin tsoro da zumudin tunkararsa lokaci guda na mamayarta,a hankali ta dinga takawa
gareshi,iska na diban gashinta tana watsashi gaban fuskarta hagu da damanta,lokaci lokaci
tana sanya hannu tana d'aukewa.
Dab da bayanshi ta tsaya taci gaba da kallonshi gabanta na faduwa,tanajin kamar zata kira
sunanshi sai bakinta ya kasa furta komai,ta dan jima a haka sannan ta miqa hannu da niyyar
kama kafadarsa sai ya waiwayo,fuskarshi cike fal da annuri kamar yadda ta saba ganinsa,yayi
kyau ya canza kamar bashi ba,cikin sakan kad'an dukkan wani annurin fuskarsa ya gushe,ya
hade girar sama da qasa,bacin rai ya bayyana qarara a fuskarsa
"Me kike yi a nan?!" Ya fada cikin tsawa da fusata
"Ban sani ba!" Itama ta maida masa cikin tsawa da fushi,sai kuma ta juya cikin gaggawa ta
bashi baya ba tare data bar wajen ba,ta d'an jima ahaka sannan ta waiwaya,saidai wayam baya
wajen,babu shi babu alamarsa,wani tashin hankali da batasan na meye ba ya rufto
mata,musamman sanda taga duhu ya soma mamaye wajen,kiran sunanshi ta soma yi a jere
babu qaqqautawa,saidai babu alamun yana jinta bare ta saka ran zai amsa.
A firgice ta miqe daga kwanciyar da take bakinta d'auke da sunanshi kamar yadda take
kiranshi cikin mafarkin,a hankali hankalinta ya dawo jikinta ta fuskanci mafarki ne,saita sauya
sunan nashi da ambaton sunan Allah,yayin da hawaye ya soma sauka daga idanunta masu
zafin gaske,wanne wacce irin jarrabawa ce?,har a mafarkin ma bazai haqura ya barta ba,tayi
shiri hakanan ta tattara dukkan qarfinta tana yaqi dashi haiqan,saidai ta fuskanci kaman fad'an
gwaggo a kofa take.
Sai data gama kukanta son ranta sannan ta sauka a hankali don karta tashi huda da yau
take tayata kwana,ta shiga bandaki ta daura alwala,saidai yau ta kasa sallar kamar tadda ta
saba,saboda wata irin kasala da mutuwar jiki data sakar mata,abinda ya gudana a mafarkin ya
soma dawo mata tar a kwanyarta,duhun da taga ya soma mamayarta shine abu na farko daya
daga mata hankali,me hakan yake nufi kenan?,saita tuna ranar da suka ga fuskokin juna na
qarshe,komai ya soma dawo mata d'aya bayan d'aya cikin rayuwarta kamar wadda aka
kunnawa magijin film.
*_ZAN RAYU DAKE_*
Ranta a matuqar bace take kallon botikanta guda biyu dake shaqe da shinkafa da waken
sadaka wanda tuni suka hadu da qasa suka saje,botikam kuma sukayi fata fata dasu,sannan ta
sake d'aga kai ta dubi ahmadi dake tsaye gabanta shida abokanshi biyu yana kallonta cikin
gadara
"Anzubar kiyi duk abinda zaki,yarinya ba kowan kowa ba sai shegen isa da izza,don kina raba
mana sadaka saikin gindaya mana sharadi,bamu da hannun diba mu zuba da kanmu?"
"Ni kuka yiwa haka?" Ta fada tana hadiye wani qullutun bacin rai da baqinciki
"Ke aka yiwan,ki dauki duk matakin da zaki dauka"
"Xaku ga gatana" ta fada a sanyaye bayan ta duqa tana tsince abinda xai iya daukuwa a
wajen,ta fadi maganarne kawai ba don tana da gatan ko me tsaya mata ba,ta fada ne kawai
saboda bata da abun cewar
"Waye gantanki?" Ya fada bayan sun sheqe da dariya duka su ukun
"Nine gatanta!" Wata kakkausar murya ta ratsa dariyar tasu,cak suka tsaya da dariyar,basu
kadai ba har itama dagowa tayi daga tsintar da take tana laluben ina mai maganar yake da
idanunta,matashin saurayi ne wanda duka duka a qalla bazai haura shekara ashirin da biyar
ba,wankan tarwada ne dogo wanda da alama yana yin qiba zata boye tsahonsa,yana da kyan
fuska mai qayatarwa irin kyan da kama kallonshi kasan cikin yaren hausa fulani yake,kuma
tabbas sahun farko da kyawawansu,ma'abocin kwarjini da kallom farko kawai zaka yi masa
kwarjininsa ya tabaka,fuskarshi a tsuke take babu alamun annuri a tare dashi yake takowa
gabansu ahmadi,kwarjininsa ya sanyasu tsayawa cak,fargaba ta kamasu,saida yayi gab da
ahmadi kamar zai fada jikinsa don har yana dan take masa qafa yace
"Me tayi muku?" Cikin tsoro tsoro da son nuna jarumta yace
"Raina mana hankali take,kullum ta kawo abincin sadaka sai ta rainama mutane wayo" a
hankali ya waiwaya ya dubi gefanshi inda take tsaye,karon farko idanunsu suka sarqe dana
juna,wani irin nauyi taji da batabtaba jinsa ba sanadiyyar kallon idanun wani a duniya,kamar
yadda shima yaji wani yanayi da baisan na meye ba ya saukar masa harsai daya lumshe
idonsa ya kuma bude cikin sakan biyu,hakan ya sake qara kwarjininsa da kashe jikin shahida
"A'ah,wallahi ahmadi baku da mutunci" muryar wani dattijo dake xama a wajen lokaci zuwa
lokaci ta katsesu,duk suka maida hankalinsu kanshi sanda ya gama tattare buzunsa da yake
zama yana dinkin takalma,ya qaraso wajen yana nuna su ahmadi da yatsa
"Yarinyar nan tunda ta soma zuwa wajen nan kuka kafa mata qahon xuqa,da kuka fuskanci a
kintse take shine kuka tsiri takurata,kowa ya shaidi yarinyar nan tunda take zuwa wajen nan
bata da abokin fada,hasalima taimakonmu take,bamu da abin ce mata sai godiya,kullum daga
kwanonta muke ci mu qoshi,bata taba bude baki ta kula wani ba bare rashin kunya ta biyo
baya,dama yau tun dazu na kula da take takenku shi yasa naqi tafiya gida da wuri har sai ta
tashi,ashe kuwa tsiya kuka shirya" a hankali ya dauke kyawawan idanunsa daga kan dattijon ya
maidasu kansu ahmadi da duka gama tsurewa saboda bayanin da baba isuhu ya kwararo,sosai
ya kafesu da ido wanda har sai da sukaji kallon har cikin lakarsu
"Kubar nan,daga rana irinta yau kada na sake ganinku a nan arean,koda kuna da abunyi har sai
ta gama raba abincinta ta tafi"
"Barema basu da abinyi sai zaman kashe wando" baba isuhu ya dora sharhinsa,da hanzari
suka juya suka soma tafiya,saida suka bada 'yar tazara a tsakaninsu sannan suka fara gunguni
"Ba wani shege Allah,ke kuma zamu gamu,mu dake ne wallahi......ba wani waye waye" da kallo
ya bisu hannayensa xube a aljuhun wandonshi,idan ka tsirawa fuskarshi ido sosai qaramin
murmushi yake can qasan ranshi,saboda yadda suka nuna raki muraran da basu tsaya sunyi
zage zagen daura dashi ba,ya tabbata da sai sun gane kurensu.
"Allah ya saka maka da alkhairi kaji yaro....kubura maza hada kayanki ki wuce gida" baba
isuhu ya fada yana juyawa wajensa shima yana ci gaba da hada nashi kayan.
Cikin wani irin nauyi da taji jikinta yayi mata ta duqa tana ci gaba da tsince abinda zata
iya,saiya duqa shima a hankali yana tayata laluben farantai da cokulanta da suka nutse cikin
qasa.
Kusan ma ya fita lalubowa da yawa,hannunshi yayi futu futu da qasa fiye da nata,baice
komai ba ya taka wajen wata roba tata ya zuba cokulan ya ciro d'an tsumma daga aljihunsa
dayafi kama da handkherchief ya goge hannunshi sannan ya dauki botikin daya rage a wajen
ya saka robar a ciki ya rufe ya dauki botikin yayi gaba,bata gane me yake nufi ba amma saita
gaza tambayarsa saboda kwarjinin da yayi mata,binsa tqci gaba dayi wanda suna kaiwa
qarshen titin yadan ja ya tsaya,saita wuceshi tayi gaba,takunshi ta dinga ji alamun yana biye da
ita ne,saidai idan ba kaga sanda suka taho taren ba ba zaka ce tare suke ba.
Suna karyowa layinsu taji gabanta ya fadi sanda ta kalli gidansu
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta furta cikin zuciyarta,saboda tuna kalaman da ummanta ta
dinga fada kam mahaifinsu kafin fitarta da abincin sadaka,fatanta d'aya,Allah yasa zuciyar
umman ta sanyaya kafin dawowar mahaifinsu,matuqar bata sanyaya din ba Allah ne kawai
yasan iyakacin abinda zai faru yau a gidan nasu.
Wannan tunanin da kuma tunanin wanda ke biye da ita baquwar fuska ne a unguwar yasa
saura gida biyu ta qarasa qofar gidan nasu taja tunga ta tsaya ba tare data juya ba,tana jin
sanda ya qaraso gefanta ya aje mata botikin
"Duk sanda zaki taho ki dinga samun d'an rakiya namiji babba yana rakoki ya dawo dake" ya
furta cikin wata kwantacciyar murya data tafi da tunaninta cikin lokaci guda,ta lumshe ido tana
jin zuciyarta na qara yawan bugunta,bata motsa ba har sai data tabbatar ya bace daga layin
gana daya sannan ta sanya hannu ta dauki botikin nata,sai kuma taji haushin kanta ya
kamata,ko banza ya cancanci ta bude baki tayi masa godiya saboda taimakon da yayi mata ba
tare daya santa ko yasan daga ina ta fito ba,yanzun haka babu lallai ta sake ganinsa bare tayi
masa godiya,da wannan tunanin ta qarasa qofar gidansu,sai kuma fargabarta ta dawo sabuwa
sanda ta soma jiyo tashin murya daga cikin gidan nasu,dai dai sanda qanwarta mubina ta fito
hannunta dauke da 'yar tsana da kayan wasa na qasa wanda suka sha fentin pink da green,har
zata wuce abinta da gudu shahida ta cafko rigarta,saita tsaya tana duban shahidan
"Baba ya dawo?" Ta tambayeta tana fatan tace mata a'a,amma saita amsa mata da
"Eh ya dawo,yana qofar dakinsa ma suna fada da umma" ta bata amsa tana zame rigarta ta
sake sheqawa da gudu ta shige cikin yara 'yan uwanta ko a jikinta.
Jingina bayanta tayi a soron gidan nasu tana jin munanan lafuzan dake fitowa daga bakin
mahaifinta da mahaifiyarta suna jifan junansu dashi,wani qataton tashin hankali da take tsintar
kanta a ciki duk sanda ta riskesu a wannan halin ya rufto mata,saita sulale ta duqa a soron
tanajin ruwan bala'in dake tashi cikin gidan,wanda ta tabbatar zuwa yanzu dukka maqota kowa
ya kasa kunne ya diban rahoto,ta rasa wannan wacce irin masifa ce?,ta rasa meke haifar da irin
wannan gagarumin yaqi kulli yaumin tsakamin mahaifanta,basa kwana uku cur cikin jituwa da
juna,basa sati cikin salama da walwala,tunda ta taso tayi hankali haka ta rsiki rayuwarsu,babu
ragayya ko kad'an ga junansu,ba wanda ke ganin wani da gashi a tsakaninsu.
A qalla sun kusa awa guda suna wannan dauki ba dadin a tsakaninsu,wanda har zuwa
sannan hawaye baibar zuba a idanun shahida ba,tilas ta miqe da niyyar shiga ciki ko Allah
zaisa tayi nasarar dakatar dasu,duk da tasan cewa da wuya wai gurguwa da auren nesa,don
idan irin hakan ta faru dukkansu idanunsu rufewa yake basa ji basa gani.
Ilai kuwa yana zaune bakin rijiya yayin da da umman tata ke cikin kitchen,har ta qaraci
sallamarta babu wanda ya jita a cikinsu,hakan ya sanya ta dirr botikin ta durfafi dakinta ta bude
ta shige sannannta rufe qofar ruf waiko zata daina jin tashin munanan furucinsu,saidai bata
sauya zani ba,haka tq zame ta zquna gefan katifarta ta hade gwiwarta ta qanqame tana ci gaba
da kukanta.
Basu saurara ba har sai da khadija qanwar shahida ta biyu ta dawo daga gidan kitson da
umman ta turata da yunwa,tace umma yunwa amma bata bi ta kanta ba,hakam yasa ta watsar
da takalmanta ta zube dirshan wajen tahau ihun kuka,katsam sai farouq mai binta ya farka daga
baccin da yake shima ya hau tsala nashi kukan jin ba'a daukeshi ba akan kari,tilas baban nasu
ya suri takalminsa ya fice fuu badon sun gama ba,ita kuma tahau hidimar yaran tana yi tana
mita da alamun itama bata huce ba.
"Au,ita kuma wannan yaushe ta shigo tazo ta yasarwa da mutane botiki kan hanya salon
wani yaci karo dashi ya fadi,inama sauran botikan?" Jin hakan ya sanya shahida komawa
saman katifa ta kwanta luf tamkar mai bacci tana sauke ajiyar zuciya,hakan ya sanya koda
khadija da umman ta aikota tazo ta dubo shahidan tazo saita koma tace mata umma bacci take "Bacci?,bacci kuma da wannan yammacin?,k'nnnnn,to Allah yasa ba zazzabinne kuma ya dawo
ba" ta fada tana ci gaba da baiwa faruqu nono.
Takunta ne kawai ke kai kawo a idanunsa sanda yake komawa daga inda ya
rakota,idanunsa ya dinga lumshewa hakanan yanayinta da yanayin tafiyarta yaji ya
burgeshi,sanyinta,yanayin maganarta,da haka har ya qarasa wajen da suka baro dazun,yanzun
babu kowa,har malam isuhu ma ya wuce,kai tsaye ya wuce shagon balarabe mai saida kayan
provision,wanda dama tun asali wajensa yazo.
Hannu ya bawa bala sukayi musabaha,sannan ya zauna kan bencin dake aje daga cikin
shagon saboda custumers daya tarar yana sallama
"Ai na hangoka kaida wadan can yaran marasa kunya,yarinyar da babu sawa ba fitarwa,ina
Allah Allah naje na musu magana naga kaje,ai yarinyar kirkir ce,ba qaramin taimakon masu