Showing 69001 words to 72000 words out of 126208 words
Chapter 24 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
tsaye,tasan akan wa yake tambaya saita saki murmushi
"Abokin aiki,aiki muka gama dashi yanxu" dan shuru yayi kishi na cinsa,ji yayi kaman ya maqure
saddam din sabida ya karanci irin kallon da yakewa saddam din shima irinsa yake masa,kansa
kawai ya jinjina yana qarasowa
"Kin kashe wayarki kin tsammaci bazan iya laluboki ba duk inda kika shiga ko?" Boye dariyarta
tayi,batasan ya dagota ba
"A'ah,kasan idan ina aiki banason yawan amsa waya,dalili kenan daya sanyani na kashe" inda
ta tashi ya koma ya zauna yana kallon office din nata,kaman yadda ya saba burge jama'a shima
ya burgeshi sosai
"Sannunka da zuwa" saiya kalleta
"Allah yasa har zuci" qaramar dariya ta saki
"Da ba har zuci ba da tunu na koreka ai" maimakon ya amsa saiya jefo mata wata tambayar
"Wanne babban baqo haka kukayi a companynku yau?" Dan tunani tayi kadan sannan tace
"Gaskiya ban sani ba,saboda ba bangarena bane" kishi yakeji sosai da fargabar kar shahidan ta
subuce masa saiya sanya idanunsa cikin nata sanda take za a wata kujerar da take kallon tashi
"Haka manyan mutane ke zuwa wajenku?" Kafada ta dage
"Wajensu dai,abune mawuyaci ni nasan zuwansu ko fitarsu,tubda ba sashe na bane saidai idan
wata matsala da buqatar zuwa wajena ya zama dole"
"Ina kishinki shahida" cak ta tsaya tana kallonsa,kalamansu sunyi shigen kama dana juna,ya
tuna mata dashi dole saboda yanayin yadda yayi furucin,hakan ya sanya ta miqe kawai ba tare
data samu abun fada ba
"Kinsan sonki yake?" Ya jefa mata tambayar sanda take bakin dan qaramin fridge dinta tana
ciro masa ruwa da lemo,saita waiwayo tana dubanshi,murmushi ya qwace mata
"Wani abu makamancin haka bai taba shiga tsakanina dashi ba,kar ka saka komai a ranka,kai
kanka shaida ne na wace shahida,abu mai sauqi ne samun hanya zuwa zuciyata kai tsaye har
haka?" Maganar tata ta bashi qwarin gwiwa,sai yayi shuru yana nazarinta,harta dawo ta aje
masa lemon da ruwan a gabanshi,yayin dashi kuma ya dire mata ledar daya shigo da ita "Ga abinci nan,inajin kamar kina da buqatarsa shi yasa dana tsaya naci nayo miki naki takeway
din,don nasan ko xuwa nayi nace kizo muje muci taren ba zuwa zaki ba" ya fada cikin jefanta da
magana,tasan yana jin haushin hakan,ita kuma ra'ayine sam bata dashi,sabida haka tayi
murmushi kawai,ko yanzun ma ba zata iya cin abinci yana kallonta ba shina ya sani,amma duk
da haka saiya soma bude mata ledar yana cewa
"Kiyi haquri yau dai daya kici a gabana,saimu tattauna abinda ya kawonin,kada lokacin break
dinki ya qare na shiga haqqin company",bai gama budewa aka sake bude qofar aka
shigo,dukansu suka maida hankali ga qofar,saddam ne hannunshi dauke da ledar gidan abincin
dake daura dasu,wanda shahida tafi order abinci acan,fuskarsa cike da murmushi ya nufosu kai
tsaye ba tare daya dubi nuradden ba ya iso gabanta,dora abincin yayi saman na nuradden daya
bude mata yace
"ga favourite dinki nan", wani abu ne ya takorewa nuradden wuya,ya daga kai ya kalli saddam
cikin fushi
"Wanne irin rashin hankaline malam?" Dubansa saddam yayi
"Da akayi me?"
"Ta yaya zaka shigo kai tsaye ba tare daka nemi izni ba,sannan ka samemu zaune zata ci
abinci ka dora wata ledar a sama?" A dage saddam yace
"Matarka ce?"
"Koba matata bace ina zaton tare ka ganmu" cikin halin ko in kula yace
"Auto da sauqi abun,kaga kenan allurar cikin ruwa ce,mai rabo ka dauka" ran nuradden saiya
kai qololuwar baci,hakan ya sanya shahida ta dubi saddam
"Banason tashin hankali saddam,meye haka?" Baison nuradden ya gane cewa bai taba furta
mata kalmar soba bare ya sake samun qwarin gwiwa,hakan ya sanya ya dubeta
"Ba manufata na bata miki rai ba,sai anjima" ya juya ya fice.
Sosai yake jin babu dadi cikin ranshi,saiya dubi shahidan
"Shahida...tsorona da fargabata ta sake daduwa,inajin har cikin raina bani da tabbas idan har
baki amsa min cewa ni kikeso ba kuma ni xaki aura ba" gaba daya sai lissafinta ya nemi
dagulewa,batason ta dauki alqawarin da zai zame mata ciwo ko nauyin da wuya ta zaiyi wahala
ya iya dauka,saboda haka cikin sanyin murya da kwantar dakai tace "Tsoron meye haka nuradden,ka kwantar da hankalinka don Allah".
Duban nafisan yayi fuskarshi a hade" me kikayi haka kenan?,me yasa tun farko baki duba
lafiyar atm din naki ba saida kika gama siyayyar?,bayan kinsan accnt din aya samu matsala sai
xuwa gobe zai soma aiki?"langabe mishi kai tayi
"Please anwar...don Allah kayi magana da mai kamfanin gaba daya,na tabbatar ka sanshi tunda
naji kace bakason yasan ka shigo kamfanin,tunda ka bada rabin kudin yanzu zai amince ka aiko
da saura idan ka koma office,Allah wannan sarqar nasha wahala na dade ina nemanta,kuma
kanaji suma sukace dsign dinta kadai yayi saura,ba lallai idan na ajeta naje na dawo na
sameta" idanunsa ya lumshe kaman bazaice komai ba,haka kawai yakejin kasala tunda ya tashi
yau,hakanan zuciyarsa da jikinsa sam babu dadi,baice komai din ba ya fita daga wajen da
kanshi ya taka zuwa sashen biyan kudi,suka tarbeshi don tunda ya shigo kamfanin suka gane
waye,hakan ya sanya suketa nan nan dashi,daya daga cikin ma'iakatan ya yiwa magana yana
son ganin rayyan
"Ranka ya dade,oga bai shigo ba,amma babu damuwa zaka iya ganin rahama" dan shuru ya
sake yana fidda wayarsa daga aljihunsa ya duba lokaci,sannan ya lalubo wata number ya
kira,bata shiga ba,duka lambobin rayyan din basa tafiya,saiya sake kiran wata number din,ba
jimawa aka daga,ya ambaci adadin kudin da yake buqata ya gaya masa inda zai kawo masa "In sha Allah yallabai ina hanya" daga haka ya maida wayar aljihunsa
"Ai...ranka ya dade basai ka zauna jira ba,rahaman kawai zaka yiwa bayani shikenan zata
shigar ne cikin kundin bayanan shiga da fitar kudi na kamfanin" lokaci ya kuma dubawa,shi
kansa baison zaman,saboda jiransa da ake,banda ya riga da yayiwa nafisan alqawari kuma
baison rashin cika alqawari da baiga abinda zai zaunar dashi har haka ba "Ba damuwa,bani number din office din"
"To ranka ya dade" ya fada yana gaya mishi cikin sauri kai tsaye ba tare da an sanar da mai
office din ba saboda sanin wayeshi baida buqatar sai sun hadashi da mai masa iso,a nutse ya
juya ya soma takawa
"Ina zaka?" Nafisa dake addu'ar Allah yasa su gama lafiya su fita lpy karya hutsance mata ta
tambaya
"Ki jirani" kawai ya fada yanayin gaba.
Kallon number office din yayi sosai sannan yaja da baya ya kalli qofar,ya dora hannunshi
saman handle din ya tura a hankali wanda hakan ya sanya basuji alamun bude qofar ba.*zafafa
biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqatar siya zaki
tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
2️⃣5️⃣
Tafiyar awa biyu cif ta shigar dashi garin katsina,tuqi yayi lafiyayye cike da nutsuwa da kuma
tunani kala kala,kai tsaye unguwar kakanninsa ya nufa.
Yana qoqarin parking motarsa kawunshi modu ya fito da alama masallaci zashi saboda
yadda yake dan hanzari,bai ganshi ba hakan ya sanya anwar kirayenshi,saiya waiwayo yana
dubanshi cikin murmushi
"Ikon Allah,yau kaine a garin da kanka?" Yana murmushi gami da kashe motar yace
"Wallahi kawu,mun sameku lafiya?"
"Lafiya qalau...mu shiga daga ciki"
"A'ah kawu,gwara na soma yin alwalar tukunna"
"To...to,shiga daga mana saika daura"
"Ah ah kawi,kar naje su tsaidani mu rasa jam'i,idan mun idar ma shuga tare" daya daga cikin
yaran da sukazo wucewa kawu modu ya qwalawa kira ya sashi ya shuga ciki ya debo musu
ruwa a buta
"Dan kuwa yau inna ta samu nayi,kazo yau zuwan ba zata sanda ba'a tsammaci ganinka ba"
murmushu anwar yayi
"Wallahi kawu,Allah ne ya kawo tafiyar haka"mintuna kadan yaron yafito dauke da 'yar
matsakaiciyar buta,anwar ya karba suna dan taba hira da kawu madun harya gama alwalar
suka rankaya zuwa masallacin.
"kaine yau kuma?" Inna ta fada sanda yake qoqarin zama kan daya daga cikin kujerun
dake falon,murmushi ya saki yana dubanta,sun riga da sun camfashi baisan dalili ba
"Nine inna,kaman wanda bai zuwa?,kodai rikicin tsufa ya soma samunki ne kike zaton na jima
sosai banzo ba?" Baki ta tabe tana rufe kwanon shan data gama shan ruwa a ciki
"Idan ina rikicin tsufa na kasa lissafi ai kawunka ahmadu baiyi tsufan da zai kasa lissafi ba ko?"
Dariya ta bashi sosai har sai daya danyi sannan yace
"To shikenan yanzu Allah ya shiryeni,saime kuma?" Harararshi ta danyi
"Allah yasa"
"Amin inna" gaisheta yayi cikin mutuntawa ta amsa tana tambayarshi su anty usaina
"Lafiya lau take,tana gaisheku dakyau"
"Muna amsawa" daidai lokacin rashida 'yar kawu ahmadu ta shigo da kwanon abinci guda
biyu,cikin girmamawa ta isa gaban anwar ta aje tana gaidashi
"Duba cikin dakina ki dauko kwanon sha ki debo masa ruwan a randa idan zai iya sha" dariya ta
sake bashi,ya fuskanci rikici yau take ji da gaske,saboda wancan zuwan da yayi tace ya zabi
daya cikin yammatan 'yan uwa dake katsina ya hada da wdda zai aura a kano duka ya
aura,yasan yau zai kashe bakin tsanya ne gaba daya shi yasa bai tada maganar ba ya barta
take rikicinta
"Sha kuwa harda shaye shaye...amma ba yanzu zanci abincin bane,zanje wata unguwa ne na
dawo,saqonku na tsaya saukewa don na ragewa motar nauyi" duban rashida yayi dake zaune
gefe tana kallonshi,ji take daman a gidansu yake
"Inasu abdurrashid?"
"Suna qofar gidan malam"
"Maza jeki kiraminsu" da hanzari ta miqe ta fice kawu ahmadu ya sako kai hannunsa dauke da
ruwan roba da lemon roba ya aje gaban anwar yana cewa
"Garin yau ana zuga rana da zafi,ko rashin saukar ruwan sama ne kwana biyu ya saka haka
oho?"
"Ba mamaki kawu,kasan ko yaya hadari ua hadu ba ruwa sai gari ya bada zafi" daga haka
kawun ya samu waje ya zauna suka shiga taba hira kan harkar noma da abinda ya shafi
damina har yaran suka shigo.
Cikin girmamawa suka gaidashi kowa na murnar ganinsa,ya amsa musu cikin kulawa ya
dubi kawu da inna
"Kawu xanje wata unguwa na dawo,Allah yasa zan sameka idan na dawo din,akwai maganar
da nakeso mu tattauna"
"Eh nima inason dan fita in duba shago na yau aike akemin,dalilin ma daya sanya ka ganni gida
ban fita kasuwa ba kenan,amma ba jimawa zanyi ba,zan sallami yaranne na dawo"
"To ma sha Allah,kafin sannan na dawo,inna zanje na dawo"
"Allah ya tsare hanya" ta fada tana aje carbin hannunta sannan suka fita da yaran ya bude
motarsa ya fito da duka kayan da yake nasu ne,yace sukai cikin gidan,sai daya tabbatar sun
shige sannan ya tada motar ya fice daga layin.
Sassanyar ajiyad zuciya ya fitar sanda yake gab da isa unguwar,qwaqwalwarsa na masa
bitar abinda xaije ya aiwatar din,jiki da zuciyarsa tana gaya masa abinda zaiyi din shine dai
dai,a nutse ya kutsa motar cikin layin,bai tsaya ba sai daya rage daura gida daya ya isa qofar
gidan sannan ya kashe motar,zamansa yayi ciki yana tunanin ta yadda zai soma shiga
gidan,daada zata ganeshi kuwa?,zata karbi zancansa?,zata yarda da qudurinsa?.
Idonsa ya bude sosai sanda yaga saurayin daya saba aike zuwa gidan lokaci xuwa lokaci ya
leqo ya koma da sauru,addu'a yake Allah yasa ya sake fitowa.
Da hanzari sulaiman ya koma zuwa cikin gida da sauri yana kiran
"Daada,daada" dattijuwar da ake kira da daadan wadda ke zaune cikin rumfarta tana daura
busashshiyar kubewa ta daga kai kawai tana kallonshi har ya iso rumfar tata
"Haba sule,wannan wacce iriyar dabi'ar banza ce haka?"
"Daada wallahi saurayin nan da yake bani saqo lokaci lokaci nake kawo miki wanda kikace
bakisan waye ba kema shi na gani a tsaye a qofar gida,kince duk randa ya sake zuwa na
tsaidamiki shi shi yasa nake sauri na gaya miki kar yana bada saqon ya tafi"
"Miqo min mayafina....duk abinda ya baka kada ka amsa kace masa lallai lallai ya shigo inason
ganinsa"
"To" sulaiman ya fada yana bata mayafin sannan ya sake fitowa da hanzari.
A nutse yake nufo motar anwar,wanda shima ganinsa yasanshi sauke glass dinsa har sanda
sulaiman din ya qaraso bakin window bakinsa a washe,anwar ya miqa masa hannu kaman
yadda suka saba,yana Murmushi sulaiman ya miqa masa hannu sukayi musabaha,yana bala'in
son musabaha da anwar din,koba komai zai gogi qamshinsa dake burgeshi yaji laushin fata
sannan kuma hannunsa ya shaqi sanyin acn dake cikin motar kamar yadda sulaiman din ke
cewa
"Kwana biyu yallabai?" Sulaiman ya fada yana sosa kai,murmushi anwar din yayi sannan yace
"Ko zaka yimin iso gurin mutanen gidan?"
"Me zai hana?,dama daadan nason ganinka,ta roqeni ma kan don girman Allah yaudai ka shigo
taga me mata aiken nan" murmushi ya kuma saki yana cire belt din jikinsa sannan ya maida
glass din motar sama ya bude murfin ya fito,sai daya rufe motar sosai sannan sulaiman yayi
gaba anwar din na biye dashi a baya.
A bakin qofar gidan anwar ya coge yana duban soron gidan yana tuna wani abu daya taba
faruwa a wajen shekaru shida baya,a shekarun baya da suka wuce idan aka ce masa zai sake
taka soron saiya qaryata,amma dattako mutunci da qaunar da dattijuwar ta nuna masa a baya
ya dawo dashi yaci gaba da nuna mata nashi karamcin,sulaiman ya dubeshi "Ka shigo mana,bismillah" kai ya kada
"Shiga tukunna ka gaya mata zan shigo" anwar din ya masa kwarjini da yawa don haka ya kasa
musa masa,ya saka kai zuwa cikin gidan karo na biyu.
"Tace ayi maka iso" sulaiman din ya fada yana duban anwar,a nutse ya sanya qafafunsa
soron yaci gaba da takawa bisa jagorancin sulaiman.
Qarqashin bishiyar dake gefe daya na tsakar gidan tabarma ke shimfide,nan sulaiman ya
nuna ma anwar,ya sabule saucikin dake qafarsa ya ajesu sannan ya isa saman tabarmar ya
zauna,dai dai lokacin da daada ke fitowa daga rumfarta hannunta dauke da kwanon sha wanda
ke cike da ruwan randarta mai sanyi,idanunta akan anwar din harta qaraso,duk da ganinta
dashi sau biyu ne tak a rayuwa,a lokacin da yafi haka qarancin shekaru da rashin cikar xati da
kamala.
Hannu yasa ya amshi kwanon sanda take shirin xama ya ajeshi gabanta,saida ta zauna
sosai sannan ya soma gaidata
"Mun sameku lafiya?"
"Lafiya qalau alhmdlh....yaro kaike hidima damu haka tsahon shekaru uku amma baka taba
tsayawa na ganka ba ko wani cikin 'ya'yana ya ganka ba bare yayi maka godiya" murmushi yayi
har fararen haqoransa suka bayyana idanunsa a qasa,sai taga ya sake koma mata anwar din
sak,anwar din da har kwanan gobe takeson tasan ina yake?,meya rabashi da jikartata,amma
har yau idan zata tambayi shahidan sau dari bazata tada kai ta bata amsa ba,harsai ta gaji tayi
shuru
"Amma saurayi....sai naga kamar anwaru ko?,anwarun shahida" daga kai yayi yana duban
dadan tare da jinjina ma qoqarinta data iya ganeshi
"Shine daada" gaba daya fuskarta ta washe da fara'a sosai,wani irin farinciki ya
mamayeta,tunda taga anwar din a wancan shekarun Allah yasa mata qaunarsa,ya shiga ranta
sosai,dai daikun ranaku ne da zasu zo su shude bata tuna dashi ba
"Ma sha Allah,Allah abin godiya,kana nan dama anwaru?,har kana iya zuwa guna ka aikomin
da saqo amma ka kasa shigowa na ganka mu gaisa ko sau daya ne?,haba anwar,me muka yi
maka haka?" Murmushin dai ya sakeyi
"Kawai haka Allah ya tsara mana daada,shi ya raba ganawarmu sai yanzu daya qaddara
haduwar tamu"
"Wannan haka yake" ta fada tana jinjina kai cike da gamsuwa,har yanzu bakinta ya kasa rufuwa
"Ashe daada baki manta dani ba?" Baki ta kama tana cewa
"Ta yaya zan manta dakai anwar,bani bama hatta da qannen mahaifin shahida sun kasa
mantawa dakai,kaiba irin mutumin da za'a manta dashi bane anwaru,gashi shekara kusan uku
kanamin alkhairi ba tare daka bari nasan cewa kai bane....kai sule,zo nan zoka amsowa anwaru
damammiyar fura da nono" tafada tana qoqarin kunce daurin habar zaninta dake daure da
kudi,da sauri anwar ya dakatar da ita
"A'ah daada,don Allah karki wahalar da kanki" dakatawa tayi da abinda take
"Karka tsaidani anwaru,nasan yana daya daga cikin abinda kafison sha rahama ta gayamin tun
lokacin ban manta ba,wannan shine kadai abinda nakejin zan iya maka" saiya qyaleta ta kunce
kudin ta baiwa sulaiman ya amsa ya fice.
"Wanne laifi muka yi maka haka anwaru daka gujemu haka?,ka bace mana bat,ina tsaka da
murnar jikata ta samu nagartaccen miji,tunda har naji isma'ila Allah ya jiqan rai na yawaita
maganarka na tabbatar da nagartarka,dana ganka kuma saina sake tabbatarwa lallai
nagartaccen ne kai,ita kuma waccar almurar koxan kwana kwana tambayarta ba zata cemin
kanzil ba" gyara zamanshi yayi sannan a nutse yace
"Dukkan abinda ya faru a rayuwar bayi ba shakka muqaddari ne daga Allah,kisa a ranki
hukuncin ubangiji ne bacewata daga rayuwarku..."
"Gaskiya ne" ta amsashi tana gyada kai,sadda kanshi qasa yayi sosai
"Zuwa nayi ki bani aurenta daada" kyakkyawan murmushi ya subuce kan fuskar dattijuwar,cikin
ranta tana godewa Allah tare da hamdala,tayi tsammanin shahidanta ta rasa nagartaccen
anwar din nan,sai gashi ya dawo a sanda basu zata ba
"Wannan ai tsohon zance ne anwar,shahida ai taka ce" wani abu ya tsaya masa a wuya,zayafi
kowa farincikin jin hakan da ace a baya ne sanda shahidan take shahidan anwar ba yanzu data
zama ta kowa ba
"Na sani daada,amma wannan karon nazo ne a bani auren shahida da gaske ba kamar a bayan
ba"
"Indai wannan kake da buqata kana iya komawa da aurenta,bamu da haufi kanka anwaru,koda
mahaifin shahida na raye nasan haka zai fadi" hakanan yaji wani sasauci a ranshi da
zuciyarsa,wanda ya danganta hakan da nasarar da zai samu ce ta nunawa shahida da
saurayinta cewa shiba sa'ansu bane takowanne fanni
"Amma duk da haka,ka jira zuwa gobe zan kira kawunnanta na tabbatar musu da aurenka da
shahida"
"Na gode qwarai