Showing 42001 words to 45000 words out of 66129 words

Chapter 15 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf

15 Jul 2025

1182

cikinta sai kifara tunanin
abunda zaki mata .

Zuly tace kuma fah hakane Allah dai yasauketa lafia yanzu dai tashi muje inyi serving
dinka danyau zagewa nayi nama girki dakaina amma fa da taimakon kuku daria AJ yayi
yace Allah yasa dai yayi dadi turo baki tayi irin shagwaban nan tace koma bayyi dadiba
nadaiyi kokari tunda sabida kai nafara shiga kitchen Jan hannunta yayi yace ai koma
bayyi dadiba yayi dadi suna karasawa dinning yaja mata kujera tazauna sannan yace
dakaina zanyi serving namu sha zamanki kihuta murmushi tasaki harya zuba musu white
rice and stew hade da ferfesun kaji dansai Zuba kamshi sukeyi atare sukaci abincin har
suka gama AJ yace baga shiba yayi dadi haka nan zaki ringa dafa mun ina ci !

ranan dai in takaici maku zuly da AJ sunsha soyayya duk da daman mutanan kullin
cikin soyewa suke washe gari dawuri zuly ta tashi tashiga kitchen kuku yana nuna mata
harta gama hada abun break din sannan takaisu dinning tajera komai daidai lokacin AJ
yafito daga bedroom yana waya yana gamawa yakarasa dinning din yaja kujera yazauna
serving dinsu tayi soyayyen dankali ne da ferfesun kifi.
Suna gamawa tarakashi har bakin mota saida taga yatafi sannan takoma cikin gida !

kai tsaye office yawuce sai zuwa karfe biyu kiran sadiq ruma yashugo wayarshi
dasauri yadauka hade damai kwatancen gidan pinky suna gama waya yayi saurin hada
komi nashi yabar office din Kai tsaye gidan pinky yawuce Dan kusan atare suka isa
shida sadiq ruma AJ yana ganinshi yaga tsantsar kamannin da sukayi da pinky dasauri
yafito daga motar shima sadiq fitowa yayi suka gaisa cikin tsakin fuska sannan AJ yace
mukarasa daga ciki har cikin parlour Suka shiga Saidai basu tadda pinky ba har AJ
yatashi zay Kirata tafito daga daki tana tafia dakyar suna hada ido da sadiq ruma
gabanta yayi wani mummunan faduwa shima hakan ta kasance a gareshi karasawa tayi
tagaidashi sannan tasamu gu tazauna !
AJ kallonshi yayi yace meye tsakaninka da yarinyan da kaga gani a news dogon ajiyar
zuciya sadiq yasaki yace kanwa tace uwa daya uba daya Dan yanzu haka inada hoton
ta ranan da aka haifeta aka daukemu hoton mubiyu hannunshi yasaka cikin aljihun shi
yacuro hoton yamika ma AJ shikuma yamika ma pinky da tuni tafara hawaye tana ganin
hoton tafashe dakuka tace yaya shima tashi yayi dasauri yakarasa kusa da ita suka
fashe da kuka !
[10/14, 18:07] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 49
saida sukayi mai isar su sannan sukayi shuru dan kansu sadiq ruma kallon AJ yayi yace
badai kai bane mijinta kallon juna pinky da AJ suka yi irin na marasa gaskiyan nan sannan
daga baya AJ ya girgiza kai yace ba matata bace kallon rashin fahimta yama AJ yace
bangane ba matar ka bace gashi Kuma naganta harda ciki rasa bakin magana sukayi dan
basusan me zasu ceba .
saida yakara magana sannan AJ dakyar yace ba matata bace sadiq ruma yace toh ina
mijin nata hawaye sosai pinky takeyi AJ yace batada miji bude baki sadiq ruma yayi AJ

yace ina son kazauna ka fahimceni komawa sadiq yayi yazauna sannan yace ina jinka
labarin haduwar su da pinky yabashi har izuwa yanzu mikewa tsaye sadiq yayi yace
sam bazay Taba yuyuba haka kawai kabata ma kanwata rayuwa wato kai matarka tahuta
kanwa ta Kuma ta wahala dole ma su abba suji wannan maganar kuma yau zamu koma
Abuja tare da little a razane pinky da AJ suka kalli juna pinky zatayi magana kenan sadiq
yace little kada kice komai yau zaki bar garin nan Kuma dole adau babban mataki Dan
bazaka batawa kanwata rayuwa ba yana gama fadin haka yacema pinky ta tashi taje
tashirya tazo sutafi .
kuka tafashe dashi tace yaya wallahi kafana ko iya dagata banyi Dan Allah kayi hakuri har
in haifa abunda ke cikina sai intafi girgiza kai yace bazay yuyuba AJ yace Dan Allah
katsaya ka fahimce ni baana son kowa yasan wannan maganar murmushin takaici sadiq
yasaki yace bazay yuyuba koda nabar little anan dole fa sai magabata Sun sani dan haka
yau zankira su ammi da abba ingaya masu komai .

Shuru pinky tayi taci gaba dakuka AJ kam rasa abunda zayce yayi dakyar ya iya bude
bakinshi yace idan mr president yasani zay dauki fushi dani kallonshi sadiq yayi yace dole
kam yasani Dan yazama dole ka auri little mikewa tsaye AJ yayi pinky Kuma shi take
kallo yanda taga hankalinshi gabaki daya yatashi . Kafin sukuma magana har Yakira iyayensu yamusu bayanin komai hade dacewa Dan
gidan Mr president ne dagacen abba yace yanzu zankira shi inmai bayani kar kuma kama
ammin ku magana dan nafison sai zuwa gobe idan anhadu ayi maganar gaba daya kuma
ka tabbatar kataho da farida gida gobe suna gama wayan sadiq yace bazan bar little anan
ba har AJ zayyi magana wayarshi tayi ruri hannunshi yakai yadauka yaga abban shine
tuni hankalinshi yatashi saidai babu yanda zayyi haka nan yadauka .
Dagacen kuwa Mr president rufeshi da fada yayi hade dacewa ya tabbatar Sun taho abuja
gobe shida zuly baijira cewar shiba yakashe wayan.
hankalinshi atashe yayi saurin fita daga parlorn yawuce yashiga motarshi yabar gidan
[10/14, 19:08] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 50
yana barin gidan sadiq yace kidaina kuka komi yazo karshe daga mai kai tayi alama toh
sannan suka Fara hira duk da rabin hankalinta yana wajen tunanin AJ.

Dakarfi yake horn dagudu megadi yaje yabude mai gate din yana parkin zuly tafito zata
tareshi taga fuskanshi a daure gakuma alamar damuwa a tattare dashi haka nandai
takarasa tayi hugging dinshi tureta yayi ajikinshi yayi saurin shigewa parlour Bin bayanshi
tayi dasauri hankalinta tashe tace baby meke faruwa banza da ita yayi sannan yawuce
bedroom itama bedroom din tabishi tana kuma tabbayar shi abunda yafaru da yaga zata
matsa Maine yace zulaiha Dan Allah kyaleni kije dakinki gobe idan Allah yakaimu zakiji
komai jikinta duk yagama mutuwa tafice daga dakin.


Washe gari kamar yanda sadiq yace karfe sha daya yazo yadauki pinky hade da
kayanta tunda private jet zasu hau zuwa abuja karfe daya yamusu a Abuja suna sauka

driver yazo yadauke su a bangaren su AJ kuma sai sha biyu suka isa airport hankalinshi
gabaki daya baya tattare dashi Dan dakyar ma yake bama zuly amsa idan tamai magana.
Sadiq abba yakira yace su hadu a gidan Mr president shima AJ kai tsaye gida suka
wuce zuly kam hankalinta yafara tashi gashi babu daman ta tabbaye shi wani abu suna
shiga gidan ba da jimawa ba su AJ suma suka shugo.
dakyar pinky take tafia har suka karasa bangaren mami parlorn cike yake da mutane
saidai gabaki dayansu bakin fuskoki pinky tagani cikin dake gabanta kowa yabi dakallo
samun waje sukayi suka zauna dan pinky dakyar ma ta iya zama suma bayan
shugowan su zuly samun waje sukayi suka zauna.


Sannan aka gaigaisa Mr president ne yakai dubanshi gun AJ yace alamin yi bayani muna
sauraron ka AJ bayani yafara yi tunda ga haduwar su da pinky har izuwa yanzu sadiq
yana hawaye yace ammi abba ga little kuna kallo a gabanku ammi dasauri ta taso
tarumgume pinky tana kuka itama pinky kukan takeyi saida sukayi me isar su sannan Mr
president yayi gyaran murya yakalli AJ yace alamin dole Kayi hakuri ka auri yarinyan nan
wani zufa ne yaketo ma AJ saidai baida daman musa ma abban shi zuly kam hankalinta
In yayi dubu yatashi balantana da tagama jin labarin pinky .

Pinky ce ta dago da fuskanta tace Dan Allah kuyi hakuri kada ku hada auren nan Dan
bamu Taba son juna ba dakatar da ita sadiq yayi yace dole fa ya aureki Dan baza kiyi
wahala a banza ba ahe kuka tafashe dashi .
Abban tane yayi gyaran murya yace farida kiyi shuru yanzu sadiq kutashi mutafi gida
idan munje cen akira ita magajia muji ta bakinta mikewa sukayi hade dayin sallama dasu
mami Mr president kuma yakara basu hakuri sannan sukabar gidan a hanya sadiq yasa
pinky takira leema tabashi yabata address din gidansu. zone ii suka nufa wani katafaran gida suka dosa sukayi horn gate man yabude musu
gate din suka shiga cikin haraban gidan suna parkin ammi tafito dasauri takarasa
bangaren da pinky take tariketa sukayi cikin gida su abba kuma sukabi bayansu har zuwa
cikin katafaran parlorn . Daya daga cikin kujerun parlorn ammi takai pinky tazauna hade damata sannu abba
dasauri yakarasa kusa da ita shima yana mata sannu sadiq kuma fridge yanufa yadauko
mata ruwa yakawo mata shima yana binta dasannu tarairayanta kawai sukeyi sannan
daga bisani ammi dakanta ta taimaka ma pinky suka je bedroom din ammi din . Dan tasamu tadan huta !

suna fita Mr president yahau AJ dafada yace tayayaa zakuyi abu batare da kun nemi
shawaran muba hakuri AJ yafara bashi Mr president yace kuma auren ka da yar wajen
ruma babu fashi yana gama fadan haka yatashi yabar parlorn mami ma tashi tayi dan
bazata goyi bayan danta ba kuka zuly tafashe dashi wani mugun kallo AJ yawatsa mata
hade da tashi yabar parlon yawuce sashin shi itama tashi tayi tabi bayanshi !
[10/14, 19:56] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕

PAGE 51



pinky tana kwanciya bacci yayi awan gaba da ita Dan akwai gajia sosai a tattere da
ita tun kafin ta tashi ammi dakanta tashiga kitchen ta dafa mata abunda zataci .

Tana gamawa tasamu su abba a parlor suna tattaunawa saidai duk akan maganar
pinky ne waje itama tasamu tazauna abba yace nakira su yaya nasan zuwa anjima zasu
taho ammi tace uhm ni rayuwar nan tsoro yake bani tunani na har yakare amma har
yanzu banyi tunanin wanda yayi sanadin bacewar little ba abba yace ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login