Showing 45001 words to 48000 words out of 66129 words

Chapter 16 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf

15 Jul 2025

1191

mugu baida kama
Allah dai yatoni asirin koma waye ya aikata hakan ameen suka amsa dashi .
Sannan ammi tamike tace sadiq kaje kataho dasu hajara tunda yanzu dai kahuta
murmushi yayi hade dacewa ammi tun dazu sukace zasu taho inaga ta Tsaya dauko
anwar ne a skull .
daidai lokacin me gadi yayi sallama yace alhaji anyi baki sadiq yace suwaye megadi
yace wata yar dattijuwa tare dawata yarinya dasauri abba yace kashugo dasu .
Koda ammi tashiga Dakinta harta tadda pinky ta tashi daga baccin murmushi tasakar
mata tace little tashi kiyi wanka ko zakiji dadin jikin ki pinky shagwabe fuska tayi tace ammi
kafana ciwo sukeyi dan dakyar ma nake iya dagasu da anbar Wankan nan zuwa anjima
murmushi ammi tayi hade da karasawa kan gadon tazauna tariko hannun pinky tana
hawaye tace da harmun cire rai da ganinki farida Allah ya isar mana dan duk wanda yake
da hannu awajen saceki Allah bazay barshi ba kuka pinky tafara yi hade da kwantawa ajikin
ammi tace yanzu babu wanda zay iya aurena a yanda nake ammi nidin fa ammi karuwa ce
duk da wacce ta rikeni bataso in taso a yanda nagan Taba gashi su abba suna neman
hada aurena da captain alhalin nasan cutar dashi akayi Dan nidin ammi saurin rufe mata
baki ammi tayi tana girgiza mata kai tace kada inkuma jin kin kira kanki da karuwa Dan duk
wanda yakalli faridana yasan macece Kamila kuka pinky tafashe dashi hade dakara
shigewa jikin ammi sadiq ne yashugo dakin da sallaman shi yace aa ammi da yar autar ta
badai ciki zaki komaba murmushi pinky tasaki ammi tace inta koma cikinma ba laifi bane
daria sadiq yayi yace marikiyan little ce tazo dasauri pinky ta daga kanta daga jikin ammi
tace Allah sarki mama .
Ammi kinsan mama tasoni fiye da kowa tasani a islamia da Boko tun ina karama saida
nagama ss3 ne naga hidima yana ma mama yawa shiyasa kawai nafada har ...
Dasauri sadiq yarufe mata baki hade dasanya hannunshi yana share mata hawayen dake
zubowa a idonta ammi tace nagaya maki kidaina kiran kanki da sunan da bai dace dakeba
maza tashi muje bathroom in wanke maki fuska daria pinky tayi tace Kai ammi sai kace
wata yarinya sadiq yace toke mecece inba yarinyan ba Daria tayi hade da tashi tawuce
bathroom ammi tabita dakallo duk sai taji tausayin yar tata yakamata sadiq shi kanshi
tausayin pinky saida yakama shi fita yayi daga dakin hade dacewa ammi ku ake jira!

Tana wanke fuskan ta tafito ammi takalleta tace kada inkuma ganin hawaye a idonki
Dan yanzu yin hawaye yakare murmushi pinky tayi a zuciyar tako godiya tama Allah daya

hadata da iyayenta masu sonta.
Rike mata hannu ammi tayi sannan suka wuce parlour leema tana ganin pinky tasakar
mata murmushi hade da tashi ta tarikota suka karasa suka zauna mama magajia pinky
tagaida hade dacewa mamana nayi kewar ki mama magajia murmushi kawai tasaki leema
kam da pinky suna manne dajuna . Mama magajia labarin yanda akayi ta tsinta pinky tabasu hade dacuro Dan karamin
diamond din Tamika ma ammi dake hawaye abba shi kanshi saida yayi hawaye.

wani Dan karamin yarone yashugo parlon dagudu yana daddy wajen sadiq yakarasa
yahaye jikinshi yana Daria yana nuna kofa ammi tace ina ka bar maman taka .
daidai lokacin hajara tashugo parlorn da sallama fuskanta dauke da murmushi gaida
kowa tayi hade dakallon ammi tace ammi ina little din take anan nuna mata pinky tayi
tashi hajara tayi takarasa ta rumgume pinky hade dakallon sadiq tace gadai little kinga
yayan nan naki kullin sai yayi maganarki murmushi pinky tasaki . [10/15, 12:11] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 52

sadiq yace she's my half dole kullin inyi maganar little daria pinky tayi tace kai yaya
daga mata kai sadiq yayi hade da kallon anwar yace anwar ga second mummy dinka
hannu pinky taware tace my boi dagudu yakarasa yafada jikinta ita kuma ta rumgume
shi tuni taji son yaron yashigeta . Ammi ce ta tashi tace little bari inkawo maki abinci kici sadiq yace kai ammi ansamu
little kuma Zaa manta dani abba yace kato dakai me kake so ammin naku tamaka pinky
tace ato abba gaya maidai hararar wasa sadiq yawatsa mata hade dacewa auren
captain dole sannan yamata gwalo hawaye tafara yi takalli abba tace abba kagan shiko ni
wallahi banson wannan AJ din leema dasauri tace aa pinky kidai fadi gaskiya duka pinky
takaima leema abba yace kunsan Allah idan Baku kyale mun auta ba ni dakune sannan
yakalli pinky yace rabu dasu babu wanda zay takura maki akan auren wanda baki so .
Daria akayi duka parlon ammi ce takaraso rike da katon trey tace hajara kuje dinning
akwai abinci kizuba masu Dan ni yau dakaina zan bawa little abinci mikewa sukayi hade
dayin daria yarage daga little sai ammi a parlorn ammi dakanta taringa bama pinky abinci
har takoshi sannan tamika mata ruwa tasha tace saiki huta kiyi wanka turo baki pinky
tayi tace wlhi ammi wankane ban iyawa yanzu da dai abari sai dare nayi sai inkwanta gaba
daya.



Abangaren AJ kam yana shiga dakinshi yazube akan kujera yana fitar da wani iska me
zafi zuly ce takaraso inda yake tasamu gu tazauna zata fara magana kenan yayi saurin
daga mata hannu hade dacewa ki koma bangaren Mami bana son surutu .
Girgiza mai kai tayi tace ka tsaya ka saurareni batare data bari yayi magana ba tace
hukuncin da abba ya yanke yayi daidai Allah yasa hakan shi yafi zama mafi alkhairi
yakuma baka ikon kyautata mana tuni AJ yaji jikinshi yayi sanyi tabbas yasan zuly macece

me hankali da hangen nesa baisan sanda yajawo ta jikin shiba yace Aameen wifey yhu r
too much Allah yabar mu tare murmushi tasakar mai hade dacewa Aameen.

Sannan tamike tace oya tashi muje muyi wanka sai muzo muci abinci hannunta Tamika
mai shikuma yasaka hannunshi anata yajanyota tafada jikinshi yashiga kissing dinta daga
nan kuma sai zance yachanza Dan AJ ba baya ba wajen bukata.

Ammi tace gidan da aka baki kyauta mamanki yakamata kibawa kyautar shi murmushi
pinky tasaki tace Ammi ai tuni nagama tsara hakan a raina saidai dole sai ansamu me aiki
.
Suna cikin magana leema tashugo parlon tace Ammi zamu tafi mama ta matsa Ammi
tace ahaba ai yau nan zaku kwana bari intashi inje in Sameta tashi ammi tayi Tabar parlon
leema kuma tazauna tana fuskantan pinky tace naji dadi sosai da Allah ya hadaki da
iyayenki bazance captain AJ bayyi kokari ba yayi kokari sosai tunda ta dalilinshi kika hadu
da iyayenki fatana kawai ki yarda da hukuncin da aka yanke akan hada aurenku da captain
.
Murmushi pinky tasaki hade dacewa hmm yayi kokari kam Saidai dole zan fuskanci
matsala sabida kinsan ko waye AJ leema tace zay Chanza idan har kinayin abunda yake
so tabe baki pinky tayi tace yanda yake son matar nan nashine zay wani kulani uhm .
Happy weekend
Goodnight fan's
[10/15, 20:09] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 53

Ammi dinning takarasa tace maman little aiko kwana zakuyi Dan little baza taji dadin
tafiyar kuba mama magajia tace toh shikenan Tunda kince haka .

da dare kunsan kwana su pinky sukayi suna hira .

washe gari kam tunda pinky tayi sallan asuba data koma bacci bata tashiba sai sha
daya nasafe dakyar ta iya saukowa daga kan gadon daidai lokacin ammi tashugo dakin
tace little harkin tashi .
Daga kai pinky tayi hade dacewa ammi na ina kwana lafia kalau ammi ta amsa dashi
hade dacewa bari in hada maki ruwan wanka sai kiyi breakfast.
Bathroom ammi tawuce tahada ma pinky ruwan wanka sannan tafito tace oya tashi kije
kiyi wankan ko kyaji dadin jikinki.
Shagwabe fuska pinky tayi tace wlhi ammi kafana ciwo take mun sosai .
Ammi tace inkin fito wankan na gasa maki kafan daman dole kiji haka.
tashi pinky tayi tawuce bathroom ta jima sosai tana gasa jikinta sannan tafito daure
da tawul tana turo cikin kan gado takarasa tazauna ammi tamata sannu hade dacewa
ga kaya idan kinshafa mai sai kisa bari inje wajen abbanki in bashi kayan break .

VILLA

Tunda sukayi sallan asuba sai goma suka tashi daga bacci AJ yadauki zuly yakaita
bathroom yace ke zaki mun wanka nikuma namiki daria zuly tayi hade da bubbuga
mashi kirji cire mata rigar baccin jikinta yashigayi ita kuma tacire matsa kayan jikinsa suka
fadan cikin jacuzzi saida suka sha soyayyan su tunkuna sukayi wanka suka fito kowa
shafa ma dan uwanshi mai yayi sannan suka shirya AJ cikin kananun kaya zuly kuma
riga da sket tasaka na atamfa suna gama shiryawa suka karasa dinning sukayi Breakfast
bayan sungama suka tashi suka wuce bangaren mami da sallama suka shiga parlourn
mami tana ganinsu tasaki murmushi zuly a kunyace tagaida mami hade dasamun waje
tazauna AJ kuma shafa kanshi yayi hade dacewa mami ina kwana antashi lafia Lafia
kalau ta amsa dashi sannan tace tun dazu abbanku ke jiran ka gashi harya fita .

cikin kwanakin da pinky tayi agidan su tasan cewa babu abunda yakai iyaye dadi
sabida duk abunda take bukata ana mata Dan kusan kullin sadiq da anwar da maman shi
suna gidan su ammi .

mama magajia da leema Kuma suna maitama gidan da minister yabama pinky duk da
itama leema kullin tana hanyar zuwa gidan su pinky.



Dayake yanzu ciikin pinky yashiga na wata tara ranan haihuwa kawai ake jira .


ammi dake gyasa ma pinky kafa da ruwan zafi tace ciki sai kace na yan biyu Daria
pinky tayi tace ammi me kika gani ammi tace naga yanda cikin yayi girmane sosai Allah
dai yasauke ki lafia kema kihuta Aameen pinky ta amsa dashi.


A bangaren su AJ kam sai shirye shiryen zuwan baby akeyi dan daki na musamman
suka ware ma babyn agidansu suka cika shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login