Showing 36001 words to 39000 words out of 66129 words

Chapter 13 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf

15 Jul 2025

1184

sannan yajata kan kujera suka zauna yakalli pinky dake tsaye har a lokacin
yace zauna mana .
Zuly juyawa tayi takalle pinky danhar saida taji gabanta yafadi sabida ganin kyawun
pinky fuskanta a tsake tace sannu dazuwa murmushin karfin hali pinky tasaki sannan tace
yauwa mikewa zuly tayi tace baby muje kuyi break nasan dai bakuyi ba jan hannunshi
tayi sannan takalli pinky tace taso muje dakyar pinky ta iya tashi tabi bayansu har zuwa
dinning din zuly dinne tayi serving dinsu sannan takoma kusa da AJ tazauna suna ciyar da
juna abinci .

Abincin kadan pinky taci Tamike tsaye tabar wajen basu masan takoma parlour ba saida
suka gama suka ankara .
Komawa parlorn sukayi suka zauna sannan AJ ya gabatar mada zuly pinky a matsayin
wacce zatayi rainon cikin su murmushi tasaki sannan tace baby baka fada mun sunan taba
shafa kanshi yayi dan ya rasa sunan dazay fada mata dan baison tasan asalin pinky.
Pinky da taga haka cikin tsiririyar muryarta tace sunana farida murmushi zuly tasaki tace
amma mungode sosai AJ ne yakalli agogon hannunshi sannan yace wifey dauko gyalenki
kizo muje time yana wucewa mikewa tayi tawuce bedroom !
bata jimaba tafito tsanye da katon gyale mikewa tsaye sukayi AJ da zuly suna rike da
hannun juna har suka karasa wajen mota dakanshi yabude ma zuly wajen me Zaman
banza sannan yazagaya yabude mazaunin driver yashiga pinky ma tashiga sannan yatada
motan sukabar haraban cikin gidan! Tunda suka fara tafia suke hirar su dan har mancewa sukeyi akwai mutum abaya a haka
suka karasa reddington hospital yana parking pinky tayi saurin fita dan zuciyar ta sam babu
dadi!
suma fitowan sukayi sannan suka karasa ciki kai tsaye office din Dr Samuel suka nufa cikin
kankanin lokaci aka gama komai aka maida cikin jikin pinky !
Dr shawara sosai yabasu akan kula da pinky har zuwa ranan dazata haihu godia suka
ma Dr Samuel sannan sukabar asibitin suna barin asibitin gida suka wuce saida sukayi

sallan azhar sannan zuly da AJ suka shiga bedroom sukabar pinky azaune !
Bayan Sun shiga bedroom AJ yace yanzu zanje inkaita gidan da zata zauna sabida bana
son zama Dakowa zuly tace badamuwa hakan ma yayi amma dole saida me aiki AJ yace
nasani nariga nasa an Nemo mun wata dattijuwa !
Bayan sungama magana ne sukayi sallama da pinky sannan suka wuce wajen me zaman
banza pinky tashiga tazauna tuni zuly taji wani kishi balantana ma yanda taga sunyi kyau
dajuna dakyar ta iya daidaiita kanta tadaga musu hannu sukabar haraban cikin gidan!
📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕 PAGE
45
tunda suka fara tafia babu wanda yama wani magana har suka isa wani katafaran
Dan karamin gida horn yayi abakin gate din aka wangale musu suka shiga saida yayi
parking sannan yabude murfin motan yafita yazagaya yabude ma pinky kofan hade da
tsakar mata murmushi ita ma murmushin tasakar mai sannan tafito rike da handbag
dinta shikuma booth yabude yadauki akwatin kayanta sannan suka jera suka karasa
bakin kofan parlorn yasanya keys yabude sannan suka Shiga atare .
dakuna uku ne Kuma ko wanne akwai toilet aciki sannan sai dinning room dakuma
kitchen a gefen shi !
Har cikin bedroom yakai mata akwatin sannan yadawo parlour yasameta yace zaki
iya zama ke Kadai kuwa .
Hararar wasa ta watsa mai hade dacewa meka maidani AJ dake jingine ajikin bangon
parlorn yasanya hannayenshi acikin aljihun wandon shi yace matsoraciya mana .
turo baki tayi alamar shagwabea shikuma yasakar mata murmushi sannan yace duk
abunda kike bukata akwai idan ma kina bukatan wani abu ma saiki kirani sannan zuwa
gobe da yamma zaa kawo maki me tayaki hira .
OK tace sannan tashiga bedroom din da taga ya ajiye mata akwatin ta komi na dakin
fari ne hakan yasata tsakin murmushi hade da ajiye handbag dinta akan kujeran dake
gefen gadon .
Sannan tafito parlour inda tabarshi nan tasame shi wajen dinning tanufa hade dacewa
yamma yana kara yifa kada madam dinka ta tajiran ka murmushi AJ yasaki hade da
karasawa inda take yace yanzu dai ba wannan ba dame zakiyi dinner sai in miki take
away . Yamutse fuska pinky tayi tace ban fiye cin abincin waje ba yanzu ma kitchen zanshiga
In daura kaje kawai saida safe.
Tana gama fadan haka tawuce kitchen shima Bin bayanta yayi dasauri yace kinsan fa
baa son kina aiki sosai kifada mun abunda kike so in yaso sai in dafa maki dakaina
kinsan fa nidin gwani ne wajen iya girki juyowa tayi suka hada ido tayi murmushi tace
aa nagode bude fridge tayi tafito da nama leda daya sannan ta ajiye AJ harde
hannayen shi yayi yace kigaya mun abunda zan tayaki dashi pinky tace toh ka yanka mun
albasa .
store yashiga yadauko albasa sannan yafito yadauki wuka .
A ranan dai tare sukayi duk wani aiki hade dakai kayan dinning suka jera sannan
pinky takalleshi tace lokaci yanata tafia kada madam dinka fa tafara kiranka .
Kara gyara zama yayi hade dacewa zantafi amma sai naci abinci pls zo kiyi serving

dina .
serving dinshi tazo tayi sannan itama tazuba jalof din kuskus din Dan kadan tazauna
hira sukeyi kadan kadan har AJ yagama yamike yace nizan tafi dagowaa tayi takalle shi
hade dacewa mu kwana lafia.

murmushi yasaki hade dacewa babu ko yar rakiya kenan make kafada pinky tayi tace
uhm a gajiye nake fah saida safe kawai OK yace sannan yafice tabi bayanshi dakallo
tana ji yabar gidan !
Dogon ajiyar zuciya tasaki sannan tamike takwashe kayan takai kitchen sannan tawuce
daki miss calls tagani a wayanta leema tafara kira Sun dadai suna hira sannan daga
baya suka yi sallama!

ranan Kwanan kadaici pinky tayi dan dakyar bacci yadauketa a bangaren AJ kam
soyayyar su sukasha shida zuly!

Washe gari ruwan Tea kawai yasha zuly tarakashi har wajen mota hade da kissing
nashi sannan yabar gidan kai tsaye gidan da pinky take yawuce !
Horn yayi megadi yabude mai Gate din yashiga saida yayi parking sannan yafito
yakarasa cikin parlorn da sallama yashiga amma baiga kowa ba motsin da yajine a
kitchen yasashi karasawa tsaye yayi yana kallonta tana ta kiciniyar hada abun break
gyaran murya yayi dasauri tajuyo takalleshi tace zuwan sassafe haka daga mata gira
yayi sannan yace badole naba naringa zuwa duba ki kullin murmushi tasaki tace sabida
babyn ku dake cikina dai kazo .
Batare daya bata amsa ba yakarasa kitchen din yashiga tayata aiki atare suka gama
komai sannan sukayi breakfast suna gamawa yamike yana duba agogon hannunshi yace
idan nadawo office zanbiyo OK tace hade dacewa adawo lafia!
Cikin kwanakin nan gaba ki daya agidan pinky AJ yake wuni Kuma komi tare sukeyi
kaman mata da miji ga kuma wata muguwar shakuwa da suka karayi dan yanzu AJ hira
yake zama suyi sosai da pinky ita kanta tayi mamakin sauywan shi amma tasan duk akan
babyn su dake jikin tane !
yauma kamar kullin yana tashi a office kai tsaye gidan pinky yawuce da sallama
yashiga parlorn ita Kuma tana kwance akan kujera daga ita sai yar karamar blue gown
daya tsaya mata daidai gwuwa .
tana ganinshi tayi saurin tashi zaune tace sannu da zuwa murmushi kwance akan
fuskar shi yace yauwa hade da samun waje yazauna !
Cikin tsiririyar muryarta tace wallahi nidai nagaji da zaman gidan nan haka nan kullin ina
gida sai kace matar kulle AJ yace yaza kiyi tunda dai banga wajen daza kibi langwabe
kai tayi tace uhmm ko shopping ne mana muje Kuma mani shaawar amala nakeji Kuma
irin na Yoruba dinnan daria AJ yafashe dashi hade dacewa yanzu ina zan samo maki wani
amala koda asa iya ta tsiyo maki girgiza kai pinky tayi tace tare zamuje dakai dan me
zafi nakeso kuma miyan yaza mana akwai yaji sosai !
shafa kanshi yayi sannan yace toh tashi ki chanzo kaya saimu tafi tashi tayi dan har

tana hadawa dasauri tawuce daki shikuma yabi bayanta da kallo dan yaga takara wani
cikane gakuma cikinta yafara tasowa tunda yanzu cikin yana na cikin na wata hudune!
Bata jima ba tafito tsanye da doguwar riga har kasa sannan ta nada gyalen sai takalmin
data tsaka me shegen tsini dasauri AJ yatashi tsaye yace ina zakije da wannan takalmin
kallon rashin fahimta tamai sannan tace bangane ina zanje dashi ba alhalin kaganshi a
kafana ! AJ yace gaskiya baza kifita da takalmin nanba dan kawai ki mana asaran baby .
Hararar shi tayi tace toh ni wallahi dashi zanje komawa yayi yazauna akan kujera yace
indai dashi zaki fita babu inda zamuje turo baki tayi tace muguntar dai tana nan bazaka
chanza ba daman nasan Dan cikin dake jikina ne yasa baka mun muguntan daka saba
shikenan sai afasa fitan katafi gida kawai tana gama fadin haka takoma bedroom. Dafe kanshi yayi yace pinky rigima tashi yayi yabita dakin zaune ya tadda ita abakin
gado tana cika tana batsewa .
Gyaran murya yayi sannan yace tashi muje kisa kome kikeso juyar da kanta tayi tai
kaman bata ji shiba saida yakara magana sannan ta tashi tadauki handbag dinta suka fita
a waje suka tadda iya pinky tace iya saimun dawo
[10/13, 17:49] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 46

wajen me zaman banza tabude tashiga shikuma yashiga mazaunin driver yatada motar
suka bar Haraban cikin gidan kai tsaye the lagoon restaurant suka nufa yana parking suka
fito atare suka jera zuwa cikin restaurant din tunda suka fito idanun mutane akansu yake
har suka karasa ciki suka zauna sannan AJ yasa akawo ma pinky amala baa jima ba
aka kawo mata aka direshi agaban ta AJ yace gaki ga amala sai kibada himma murmushi
tasakar mai sannan tawanke hannunta tashiga cin amalan nan ba kakautawa tana cinyewa
tana kalli AJ daya zuba mata ido tace wallahi ban koshi ba Daria yayi sannan yace akaro
kenan daga mai kai tayi alamar eh .
girgiza Kai yayi sannan yasa aka kawo mata wani shima saida ta cinye shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login