Showing 21001 words to 24000 words out of 66129 words

Chapter 8 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf

15 Jul 2025

1187

tafi gida sannan yacika mata Jakarta da kudi.
ana kiran sallan azhar takarasa gida.
Zaune ta tadda leema aparlor tana kallo .
Kujera tasamu tazauna hade dacewa kai nagaji gaskiya leema tace uhmm sannu
Kallon rashin fahimta pinky tamata tace meye na uhmm leema murmushi tasaki tace
nidai fitan ki dazu yaja mun balai Dan kina fita captain yashugo gidan nan
Tsaki pinky tasaki tace sai akayi yaya leema tace ina cemai kinfita yahau balai ke
kamarfa yaduke ni Dan harsai dayasa nafada mai wajen Wanda kikaje.
Wani kallo pinky tawatsa ma leema sannan tace amma kinban kunya da girmanki
dakomai sojan ruwan kike tsoro .
Mikewa tsaye tayi hade da daukan handbag dinta tayi gaba tace nazauna anan sai
jinana yahau kuma wallahi zamu hadune Dan sai yabani wayata leema kam ido kawai
tazuba ma pinky Dan tasan duk zance takeyi itama tsoron AJ takeyi yanda baida
mutuncin nan! da dare kasa rintsawa yayi Dan tunanin pinky ne ya addabe zuciyarshi danko zuly
dasuka jima tare yake kuma sonta baya tunaninta haka a yan kwanakin nan to meke
shirin faruwa!

Washe gari karfe goma pinky ta tashi bayan tayi wanka tasanya three quarter ash
color sai riga Me hannun vest sannan tayi parking gashinta tafeshe jikinta da turare

sannan tasauko downstairs leema tasamu da mama magajia suna breakfast karasawa tayi
itama taja kujera tazauna hade dagaida mama magajia sannan takalli leema tace aro
mun wayarki.
Daukar wayar leema tayi Tamika mata
Pinky ta ansa tayi dialing din number dinta saiko taji yana ringing saida yayi ringing
harso biyu sannan aka dauka .
shima Dan yaga ansa leema ne shiyasa yayi picking.
Pinky a tsiwace tace da Allah malam ka kawo ma mutum wayarshi tunda bakai ka
tsiya munba .
Tsaki AJ yasaki dagacen sannan yace bazan kawo ba sai naji Shaka .
pinky tace dadin abundai kasan bana kashe mutane balantana na shakeka nidai kawai
ka kawo mun wayata ahe tana gama fadan haka ta tsinke wayar ta ajiye tanajan tsaki
leema da mama magajia kallonta kawai sukeyi.
AJ bin wayan yayi dakallo yasaki murmushi daman yau dason ganinta yatashi yarasa
dalili tashi yayi kawai yazira takalimin shi yadauki wayoyinshi hade da key car yafice ..
Yau wata babbar jeep yashiga Kai tsaye maitama yanufa
Mama magajia tace beauty kifa bi mutumin nan ahankali Dan naga alaman zay iya
aikata komai turo baki pinky tayi hade dacewa kar yakawo mun wayata yagani .
Bai jima ba yakaraso gidansu pinky abakin gate din yatsaya yayi horn megadi yabude
mai gate din yashiga.
leema tace inaga minister ne pinky tace m not in the mood ynxu kije kice mai bazan
samu fitowa ba.
Murmushi leema tasaki sannan ta tashi tafita mamaki ne yakamata da taga AJ ne acikin
motar fitowa yayi yace pinky fa leema dakyar ta iya bude bakinta tayi magana tace
tana ciki AJ yace zan iya shiga dasauri leema tace why not bismillahh gaba tayi yana
binta abaya Har suka karasa cikin parlorn cikin azababbiyar muryarshi yayi sallama dasauri pinky tajuyo
suka hada ido tawani saki tsaki hade da juya wa taci gaba dayin break dinta
Leema wajen zama ta nuna mai yamutse fuska yayi hade dazama kamar wanda aka
takura mawa
Karasawa dining leema tayi tace ke ga AJ fa pinky a hasale tace Aina ganshi kice mai
ya ajiye mun wayaata yatafi.
Mama magajia dasauri tace dakanki zakije ki amsa bata rai pinky tayi hade da turo
baki .
mama magajia ce takaraso parlorn AJ yana ganinta yayi saurin saukowa daga kujeran
yana gaida ita cikin tsakin fuska ta amsa Sannan tawuce dakinta
Leema ma upstairs tawuce yarage daga AJ sai pinky a parlorn dakyar ta tashi takarasa
parlorn tana wani hade rai
Wajen dayake takarasa ta tsaya hade da mika mai hannunta tace ina wayata take .
Dagowa yayi yakalletaa duk sai yaji haunshinta yakeji daya Tuna jia.
Mikewa yayi tsaye yakarasa inda take Dan har suna iya jiyo numfashin juna ..
A hankali yace jiya ina kikajee tsuki tayi tace babu ruwanka da inda naje nifa banson
sa ido kara matsawa yayi gabda ita itama tafara matsawa har saida sukaje karshen

bangon parlor yasanya hannayenshi yadafe bangon sannan yace tabbayenki nakeyi ina
kikaje jiya .
batare dawani tsoroba ko shakka tacee wajen saurayina naje ko akwai wani abune
Idon shine yayi wani ja sannan yace good kibada hamma yana gama fadan haka
yasaki bangon yakarasa yakwashe wayoyinshi yabar mata nata sannan yafice .
Tabe baki tayi tace matsalar kace tunda nidai ka kawo mun wayaata tanajin fitan
motanshi taja tsaki tace sojan banza kawai sai mugunta fal ciki !
[10/9, 20:22] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 35

Driving kawai yakeyi amma zuciyar shi zafi take mai da radadi kuma yarasa dalilin jin
hakan dogon tsaki yaja sannan yadau hanyan zuwa gida !
Daukar wayar tayi tafara duba miss calls tsaki tasaki Dan ganin yawan miss calls din
number din faiza ta danna bugu daya faiza tayi picking .
Pinky tace hello amaryar nasir dagacen faiza tace bawani amaryar nasir wayarki kullin
akashe tsaki pinky tasaki tace kema kinsan ba laifina bane abokin mijin ki dinnan baida
M.
Faiza dagacen tayi daria tace indai AJ ne yanzuma kuka fara Dan baida hakuri ko
kadan pinky tace ai daidai nake dashi Dan rainin hankalin !
Faiza tace yanzu dai yaushe zaki shugo Dan ko gidan baki saniba pinky tace nanda
kwana biyu zaki ganni kigaida munda ango OK faiza tace sannan sukayi sallama!

Koda yakoma gida part dinshi yawuce Dan yaga mami nada baki .
Yana shiga dakinshi yarage kayan dake jikinshi yashiga bathroom yana fitowa yagoge
jikinshi bayan yashafa mai da perfumes yasanya three quarter hade da singlet .
Sannan yakarasa dinning bude kulolin abincin yafara yi tuwon semovita ne da miyar
agusi saiko zuba kamshi takeyi dayar kulan kuma daya bude ferfesun kan sane yasha
kayan kamshi!
Sosai yazagey yaci tuwon Dan favourite food dinshi kenan !
Yana gamawa yawanke hannunshi sannan yadauki wayarshi yakoma parlour yazauna .
remote yadauka yachanza channel zuwa na Ball
Tunanin pinky yafado mai arai dasauri yadauki wayar shi yatura mata DM ta instagram
Kaman haka
hope dai baki fita ba Dan kika tsake kika fita saina dauka babban mataki akan danna
fahimci kanki narawa :
Tana kwance akan gado DM din yashugo hannunta takai tadauki wayan tabude tsaki
tasaki sannan tace akwai saidai kadau babban mataki akaina Dan yauma ba gida zan
kwana ba .
Kuma Dan Allah bana son sa ido dan na fahimta sojojin ruwan nan akwai shisshigi
hoton gwalo ta tura Mai
Yana karantawa yayi wurgi da wayar tafadi akasa tafashe .

Lokaci nata tafiay gashi yau saura two weeks bikin AJ da zuly kuma ayau ranan

Saturday zaa fara event har zuwa ranan daurin aure!
AJ wata hadaddiyar blue suit yasaka yayi matukar yin kyau Faisal ne yashugo dakin
yana murmushi yace ango angama shirya amarya fa tsaki AJ yasaki yace inbanda sherri
irin na zuly wai Dan hauka wani event ne fiye da guda goma sai kace hauka .
Faisal yace nidai muje dan kai take jira gaba AJ yayi Faisal yabi bayanshi.
Karasawa yayi inda amarya zuly take tare da wayayyun kawayenta yaran manya ita
kuma tsanye take da hadaddan Blue material sai kyallli yakeyi dayake da darene yana
yakarasawa yamika mata hannu ita kuma tasanya hannunta a nashi suka karasa wajen
motan da aka bude musu suka shiga sannan aka maida murfin kofan aka rufe a tsakiya
aka sasu kai tsaye Zeus paradise hotel suka nufa .
Gaskiya hall din ba karamin haduwa yayi ba dan fadan kyaun wajen bata bakine
Dan ankashe kudi wajen saruwan wajen abunku da bikin manya sosai event din yayi
kyau Dan duk wani meji dakanshi saida yaje event din.

Ranan Friday
aka daura auren captain alamin junaid da amaryarsa zulaiha fariz dabo!
anan Kano dinma saida akayi event wajen kala biyu sannan washe gari suka
dunguma zuwa Villa achen ma anyi shagalin biki sosai sannan zuwa dare kuma aka tafi
dinner a the glam hall ranan dai anyi barin daloli !
Pinky dakyar ta iya tashi daga kan kujeran zuciyarta ba dadi leema ce tadago takalle
ta tace amma gaskiya bikin yayi kyau ashe dai captain yana murmushin tsaki pinky
tasaki tace toh ina ruwana dashi tana gama fadan haka tawuce upstairs tashige Dakinta
tafada gado saidai Sam tunda aka nuna bikin AJ jikinta yawani chanza tsuki tasaki tace
uhm meye damuwana dan ya Aura wancen mummunan !

Bayan antashi daga dinner kai tsaye amarya gidanta aka wuce da ita dake efab
estate subhanallahi nikaina bazan iya fadan saruwan gidan ba Dan gari gudane kuma
irin ginin turawan nanne Tunda su suka kera abunsu.

Ana kaita kowa yawatse aka barta ita kadai Bayan tafiyansu bada jimawa ba AJ
yashiga dakin amaryar sa !

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login