Showing 27001 words to 29422 words out of 29422 words

Chapter 10 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

dubi aljanin cikin mamki yace. ” Saboda meza kace na zauna akan
kujerarka wacce kasaba zama a kanta tun kafin a haifi kakan kakana ? ”. Da jin wannan batu
sai kwallah ta ciko a idanun aljanin sannan yace. ” Yakai uhaisu ka sani cewa kaine sarki na
arba in da biyar daga cikin sarakan da suka yi sarauta a gidannan kuma kowanne sarki yayi
zamaninsa tare dani. Amma gaba ™Nasiru Muhammad™dayansu babu wanda ya shigo cikin
dakin nan ya mai da mini da martanin murmushi sai kai kadai.
Kai ne kadai sarkin daya shi shigo wajena cikin kwanciyar hankali da saukin kai bada jin tsoro
ko izza ba. Turbude fuska kamar wanda aka aikawa da sakon mutuwa yace. ” Bani ne zan
sanar da kai wanna addini ba kai da kanka zaka ganeshi zuciyarsaka ta gamsu da shi “. Koda
gama fadin haka sai aljani aznaihul markas ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a cikin
dakin muryarsa na cewa sai mun sake saduwa idan har ka dawo gida a raye cikin nasara. ”Nan
take sarki uhaisu ya fice daga cikin dakin ya janyo kofar ya rufeta. Aikuwa yana rufe kofar sai
yaga yana ta sake lullubeta tamkar ba a taba bude kofar ba. Nan dai sarki uhaisu ya tafi izuwa
turakarsa zuciyasra cike da sake sake da zullumi abinda ya fara yawo a ransa shine. Bayanin
karshe da aljani aznaihul markas yayi masa cewa sai sun sake saduwa idan ya dawo a raye
kuma cikin nasara. "
Shin wannan batu yana nufin kenan babu tabbacin zai tsira da rayuwarsa ? Kuma babu
tabbacin zai sami nasara acikin burinsa na duniya?"
Nan take hankalin Uhaisu ya dugunzuma. Ya rasa abin da ke masa dadi aduniya, amma da
yatuna matsoraci bashi zama gwani, kuma ya tuna shima jarumine sadauki mai tarwatsa maza,
sai yaji dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa.
Haka dai sarki uhaisu ya isa cikin turakartsa ya kwanta. Kwanciyarsa keda wuya sai barci ya
saceshi domin shidai a rayuwarsa bakin ko kishiyarsa, tunani ko ™Nasiru Muhammad™fargaba
basu taba hanashi yin barciba domin ya kasance mutum wanda bai taba sa wani abu a ransa
ya dame shiba. Kashegari kuwa tun da dukudukun safiya sarki Uhaisu ya tashi ya kintsa aka kawo masa wani
farin ingarman doki gami da isasshen guzuri. A wannan lokaci sarki uhaisu yayi gagarumar
shigar yaki, kuma yasa hular karfe wacce ta rufe fuskarsa idanunsa kadai ake ake gani.
A lokacin ne gaba dayan fadawansa da jama'ar gari suka taru a fadar don yin bankwana da shi.
Fadar tacika ta batse babu masakar tsinke duk inda mutun ya duba fuskarsa maza da mata
daga masu kwalla sai masu zubar da hawaye saboda alhinin rabuwa da sarkinsu uhaisu.
Yayinda sarki uhaisu yaga jama'arsa acikin wannan hali sai ya kamu da tsananin tausayinsu yaji
kamar ya fasa yin wannan tafiya amma daya tuna cewa wannan tafiya itace fa cikar burinsa na
duniya sai yaji bazai iya fasa taba.
Nan take sarki uhaisu ya cire hular karfen kansa sannan ya hau kan mumbari dake tsakiyar
fadar ya fuskanci jama-arsa ya shiga jawabi na rarrashi gami da ban baki, kuma yanuna musu
mushimmancin wannan tafiya da zai yi cewar a dalilinta ne zai samu tsawon rai kuma birninsa
zai samu daukaka irin wacce bai taba samuba. Duk da jin wannan bushara sai jama'a suka ji sudai basa son su rabu da sarki Uhaisu domin ji
suke kamar zasu rabu da hanyar kirjinsu.
Lokacin da sarki Uhaisu ya gama jawabinsa ya sauko daga kan mumbari ya hau kan dokinsa ya
sanya wannan hular karfe. Koda ya kada linzamin dokinsa ya nufi kofar fita daga fadar sai
jama'a suka rude da ihu, kuka da dimauta mata kuwa da yawansu yanke jiki suka rinka yi suna

faduwa kasa sumammu saboda bakin cikin rabuwa da masoyinsu wanda suka dade suna
begensa a cikin zuciyarsu.
Hakika sarki uhaisu ya cika tauraron samari, maganin ™Nasiru Muhammad™ yunwa da
kishirruwar 'yam mata, domin babu wata 'ya mace a cikin birninsa wadda bata kamu da
sonsaba face matan aure da tsofaffi. Kai wadansu matan auren ma idan sarki Uhaisu zai auresu
zasu iya kashe aurensu haka dai sarki Uhaisu yacigaba da tafiya babu waiwaye, kuma babu
sassauci har ya fice gaba daya daga cikin birninsa. Sai da ya kwana ashirin ba daya yana keta
dazuzzuka da birane sannan ya isa birnin kisra.
Kafin ya iso birnin kisra yayi arangama da 'yan fashi iri-iri da kuma muggan dabbobin daji
amma komai yawansu da karfinsu sai ya ga ya tarwatsasu ya kashe na kashewa, masu nisan
kwana kuwa saidai su gudu.
Shikansa sarki Uhaisu yayi matukar mamaki bisa ganin irin jarumtakarsa domin bai taba tsintar
kansa a cikin irin wannan haliba na yaki a daji da mutane da yawa ko dabbobi.
Lokacin da sarki uhaisu ya iso fadar sarki Daksur sai ya iske fadar a cike makil da manyan baki
da sarakai wadanda ke zaune a can saman fadar kusa da karagar sarki Daksur. A kasa kuwa,
sauran dakarun yakine masu yawan gaske wadanda suka rako sarakuna don zuwa wannan
gagarumin yaki wanda za a yi abirnin Misra. A wannan lokaci fadar tsit, sarki daksur ne kadai yake bayani ana sauraron muryarsa, kwazam!
Sai akaga mutun yashigo fadar bisa kan doki sanye da kayan yaki ya rufe fuskarsa da hular
karfe.
Karar kofatun dokin nasa ne tasa sarki Daksur yayi shiru kuma kowa yajuyo yana kallonsa.
Mahayin yaci gaba da tafiya kai tsaye ya durfafi inda karagar sarki take batare daya tsaya ya
gabatar da kansa ba.
Koda ganin haka sai dakaru sama da dubu suka yunkura zasu afka masa.
Cikin hanzari sarki Daksur ya daka musu tsawa suka tsaya cak! Shima mahayin dokin sai yaja
linzamin dokin nasa ya tsaya a waje guda.
Sarki daksur ya mike tsaye ya tako da kafarsa, yazo har gaban mahayin sannan ya risina a
gareshi yace, "lale marhaban da sadaukin sadaukai, kuma sarkin sarakuna na wannan nashiya
tamu, mai birnin tashwar wato sarki Uhaisu bin kairuf".
Koda akaji sarki Daksur ya ambaci wannan suna sai idanun kowa ya zazzaro aka cika da
tsananin mamaki bisa ganin yadda sarki Uhaisu ya iso fadar shi kadai batare da dakarunsa sun
rako shiba, sannan kuma sai kowa ya zuba ido domin yaga fuskarsa domin da yawan jama'a
basu taba ganinsaba labarinsa kawai suke ji. Abinda yakara baiwa mutane mamaki shine, yaya aka yi sarki daksur ya gane cewa sarki
uhaisune wannan har ya taso ya taryeshi alhalin ba a gabatar da zuwansaba.
Abinda suika manta shine, sarki daksur babban ™Nasiru Muhammad™matsafine.
Nan take sarki uhaisu ya sauko daga kan dokinsa sai sarki daksur ya rungumeshi cikin tsananin
farinciki tamkar wanda yaga dan uwansa na jini.
Batare da sarki Uhaisu ya cire hular karfen dake kansa ba sai sarki daksur ya jashi suka tafi
izuwa har can inda karagarsa ta mulki take take suka zauna akan karagar mulkin su biyu.
Abinda ya daurewa kowa kai kenan, domin babu wani mahaluki wanda sarki Daksur ya taba
girmamawa haka ya darajashi sai sarki UHAISU. Nan take aka kawowa sarki uhaisu abinci da abin sha iri-iri mai daraja irin na sarakai na alfarma

wanda babu kamarsa a wajen sarki uhaisu ya saki jikinsa yaci abinci sosai har sai da yaji ya
koshi sannan ya dubi sarki Daksur yace, "a kaini masaukina ina da bukatar na kwanta na huta
domin na huce gajiyar tafiyar da na sha ".
Batarte da gardamar komai ba kuwa sarki daksur ya kira wani Hadimi yace da shi ya kai sarki
uhaisu izuwa masaukinsa, wani wuri wanda shine mafi kyau da tsaruwa a gaba daya gidan
sarautar. Nan take kuwa aka tafi da sarki Uhaisu,
A she gaba dayan sarakan dake zaune a cikin fadar ransu ya baci bisa ganin yadda sarki
daksur ya tarbi sarki Uhaisu cikin karramawa da girmamawa fiye da yadda aka tarbi
kowannesu.
Bayan bacewar sarki uhaisu da hadimin da ya tafi kaishi masaukinsa sai wani sarki mai ji da
kansa wanda ya kasance babban abokin sarki daksur wanda ake kira ma aruf bn saurud ya
dubi sarki daksur yace "haba abokina ka tuna fa cewa yau kwanamu arba'in anan muna taruwa
kullum muna tattaunawa da shiryawa akan yadda zamu bullowa wannan yaki. Yanzu ne muka
yanke shawarar mu tafi izuwa yakin amma sai gashi mutum daya yazo ya tsaida komai. Yanzu
shikenan sai dai mujira har sai sa'adda yayi barci ya tashi sannan zamu tafi?"
Lokacin da sauran sarakai suka ji wannan batu sai duk ™Nasiru Muhammad™ suka goyi bayan
sarki ma'aruf, fadar ta rude da hayaniya.
Shi kuwa sarki Daksur sai ya kama murmushi. Daga can sai ya daga hannu sama akayi tsit
sannan yai kyaran murya yace, 'yan uwana ina so ku sani cewa sarki Uhaisu ne zai jagoranci
wannan yaki da zamu je kuma dukkan nasararmu na tare da shi, idan muka kuskura muka tafi
yakin babu shi tabbas baza sami nasaraba ". Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke gaba dayan jama'ar dake cikin fadar sarkin yaki ya
dubi satki daksur cikin biyayya yace, "haba ya shugabana, yanzu duk yawannan namu amma
ka ce ba zamu sami nasara ba face Uhaisu ya jagorancemu? Kai da bakinka kace damu
yawanmu ya ninka na abokan gaba sau dari ba. Ai kuwa ina ganin cewa koda Uhaisu ko babu
shi dole ne mu sami nasara a wannan yaki. "
Sa'adda sarki daksur yaji wannan batu sai ya mike tsaye ya dubi kowa dake cikin fadar, sannan
yayi ajiyar zuciya yace, "yaku 'yan uwa ina so kusani cewa ni nasan abinda babu wanda ya
sanshi a cikinku nan gaba daya A halin yanzu sarkin yakimmu ta da, wato JARUMA YAZILA
tana can birnin misra kuma ta karbi addininsu, don haka ita da 'yar uwarta JARUMA DABIRA
zasu hada KARFI DA KARFE su yakemu.
Tabbbas su biyu kacal sun isa su iya yi mana mummunat barna a wannan yakin, domin a duk
fadin wannan nashiya babu wani sadauki ko mayaki wanda wanda ya isa ya taresu face sarki
Uhaisu. Ina tabbatar muku da cewa ahalin yanzu babu wani sadauki mai karfin damtse irin na
Uhaisu a duk fadin duniyarnan kuma shine mutumin da baya tsafi, kuma tsafi baya tasiri a
kansa domin ku gasgata zancena yanzun nan zan nuna muku ku gani da idanunku ".
Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yayi nuni da hannunsa izuwa ga saman bangon fadar
saiga hoton irin gwagwarmayar da sarki Uhaisu yayi da 'yan fashi da masu yawan gaske
wadanda adadinsu ya kai dubu ™Nasiru Muhammad™ ashirin da doriya sun yiwa sarki uhaisu
kawanya 'yan fashin sun kasance gabza-gabza masu kirar mutanen farko kuma kowannensu na
dauke da muggan makamia lokaci guda suka yiwa sarki uhaisu rubdugu shi kuwa sai ya wanzu
yana mai gididdigasu cikin tsananin zafin nama irin wanda ido bai taba ganiba.
Cikin sa'a daya jal ya ragargazasu duka dayansu bai tsira da rayuwarsa ba, sai gashi filin dajin

gaba daya ya cika da gawarwakin 'yan fashin, duk inda mutum ya duba sai dai yaga jini na
malala da kwaranya tamkar ruwan sama akeyi.
Babban abinda ya baiwa kowa mamaki shine ganin sarki uhaisu a tsaye bisa dokinsa cikin
koshin lafiya babu inda jikinsa ya sami rauni koda kwarzanewa kuwa, kai ba ma shiba, hatta
dokinsa ma babu abinda ya taba lafiyarsa.
Bayan wannan gwagwarmaya sai kuma aka ga wani azababben yaki da sarki uhaisu yayi da
wadansu dodanni wadanda yawansu ya wuce misali domin ninka na wadannan 'yan fashi sau
biyar. Sai da sarki Uhaisu ya shafe kwana guda da yini daya yana yaki da dodannin bai gajiba
kuma bai guduba sai ragargazarsu kawai yake yi, suna zubewa kasa matattu. Yawan dodannin
sai ya zama na banza ya yin da bala'I yakai bala'I da kansu suka rinka guduwa suna neman
maboya.
Nan take sarki daksur ya sake nuni da hannunsa izuwa ga bangon fadar hoton komai ya bace.
A sannan ne gaba dayan jama'ar dake fadar suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda saboda
tsananin mamakin ganin irin wannan a zababbiyar jarumtaka ta sarki Uhaisu wacce ko a tarihi
basu taba jin taba kuma gashi jarumtaka ce ta zahiri wacce babu sihiri ko tsafi acikinta. Nan take kowa ya sallama ya gamsu cewa lallai sarki uhaisu nezai jagoranci wannan
gagarumin yaki da za a tafi izuwa birnin misra.
Sai da rana ta fadi sannan sarki uhaisu ya farka daga barci domin huce gajiyar shi. A sannan ne
kuyangi suka ™Nasiru Muhammad™ kai shi kewaye suka yi masa wanka a cikin bahon zinare
mai cike da ruwan kamshi na turaren miski da furanni iri-iri.
Bayan angama yimasa wanka an shafeshi da mai sai aka kawo masa kayan yakinsa ya sake
sanya su ya mayar da hular karfensa yasa a kansa sannan ya taho fada yana zuwa cikin fada
sai kowa ya mike tsaye don girmamawa, hatta sarki daksur kuwa. Maimakon sarki uhaisu yaje
ya zauna sai dubi sarki Daksur yace, "a kawo mini dokina yanzu zamu kama hanya mu durfafi
Birnin MISRA.
Batare da gardamar komai ba kuwa sarki Daksur yasa aka kawowa sarki Uhaisu dokinsa ya
hau kawai sai ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya fice daga cikin fadar.
Cikin hanzari sarki Daksur ya bayar da umarni ga dukkan sauran mayaka da a fita ayi hawa abi
bayan sarki Uhaisu. Nan da nan kuwa aka bi wannan umarni.
Kaico! Tashin han kali ba a samasa rana.
Inda ace mutun yana wannan wuri idan yaga irin tsananin yawan wadannan mayaka da kuma
irin maggan makaman da suka debo dole ne ya firgita domin gani zaiyi kamar zasu iya tashin
duniya gaba dayanta a cikin rabin sa'a.
Gaba dayan mayakan da suka fito wannan yakin babu abinda suke son gani face fuskar sarki
Uhaisu da kuma irin kirar jikinsa amma sai gashi har yanzu bai cire hular karfen dake kansaba
kuma bai kwabe kayan yakin da suka rufe jikinsa ba su kansu kuyangin nan da suka yi masa
wanka dukkansu dimaucewa sukai suka fita haiyacinsu saboda ganin irin tsananin kyawun
surar da allah ya baiwa sarki Uhaisu.
MENENE ZAI FARU A WANNAN GAGARUMiN YAKI DA ZA A YI A BIRNI MISRA?
WACE CE MATAR DA SARKI UHAISU ZAI AURA? Mu hadu a BAKIN ARTABU na biyu domin
jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
====================================
Anan zamu dakata

Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login