Showing 9001 words to 12000 words out of 29422 words

Chapter 4 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

sa adda na
rabu da su a can gidansu daji amma na taba ji a bakin sarkin yakin garin nada wato sadauki
zaihar cewa hukairu da humaira tare da yarsu sun gudu izuwa birnin misra amma ya bisu har ya
riskesu kafin su shiga birnin har ya fafata yaki da mahaifin naki hukairu ya sami nasarar
kasheshi amma bai sami damar kashe humaira da yar uwarki ba domin dakarun birnin misra ne
suka yiyo kansa ya gudu ya yin da yazila taji haka sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar za ta
kone tace yanzu sarkin yaki zaihar ne ya kashe mahaifina ?“.
Nuzaira tace tabbas haka ne babu shakka “ yazila kuwa indai mahaifiyata da yar uwata suna
raye tabbas suna cikin birnin misra ni kuwa ta kowanne hali sai na shiga birnin misra na sadu
da su dama ina da burin naje na sadudA jaruma dabira domin ta cire mini wannan laya dag
wuyana kuma ina son muyi yakin karshe da ita domin nasami damar kaita kas har na cire hular
karfen da take sawa a kanta domin naga fuskarta kin ga kenan ina da manyan bukatu har guda
uku acikin birnin misra don haka zama bai kamani ba dole ne nayi shiri na tafi birnin misra".
Koda jin wannan batu sai hankalin Nuzaira ya dugun zuma ta dubi yazila cikin firgici tace, "yake
'yata kin sani cewa mutanen birnin misra sun kasance ma'abota addinin muslunci saboda haka
zuwanki birninsu abu ne mai hadarin gaske da zarar sun ganki zasu hallakaki tun da kin
kasance tsohuwar abokiyar gabarsu. Ki tuna cewa kin kashe musu jama'a ba adadi. A bu na
biyu koda 'yar uwarki da mahaifiyarki suna nan araye yanzu kodai suna kurkuku kokumaa suma
sun zama musulmai don haka baza suyi mar haban da keba tun da kun banbanta addini da
yanayin rayuwa. Ke koma dai babu banbancin komai ai baza sutaba shaidakiba tun da basu
sankiba kema baki sansuba. Shekara goma sha takwas ai ba kwana goma sha takwasbane. Na
tabbata yanzu 'yar uwata Humaira ta tsufa, kamar yadda nima na tsufa, ta yaya zata shaidaki
alhalin rabonta da ke tun kina jaririya?".
Lokacin da nuzaira ta zo nan a zancenta sai yazila ta mike tsaye ta kama kai kawo sannan ta
tsaya cak ! Ta dubi nuzaira tace, "yake ummina ki sani cewa dan uwa-dan uwane, har abada
idan ka hada jini da mutum sai kaga wani abu ya zamo iri daya da nasa bare kuma ni da 'yar
uwata mun kasance tagwaye ai dole ne asami kama ni da ita kamar yadda kika bani labari
cewa tamkar an tsaga kara muke. "
Nuzaira tayi ajiyar zuciya sannan tace, "nidai na umarceki da kada ki kuskura kice zaki ce zakiyi
wannan ta fiya izuwa birnin misra kuma ina mai gargadinki da kada ki kuskura kice zaki je
kiyiwa sarkin yaki zaihar wani abu, domin kina tabashi mijina da sarki daksur zasu gane cewa
na sanar dake sirrin rayuwarki don haka komai zai iyafaruwa a gareni. Yake yazila ki tuna cewa
nice na shayar dake harkika girma kika zama mutum, ki tuna nice naci kashinki, na sha
fitsarinki, kuma nice na sha wahalar renunki idan kika bari su sarki daksur suka cutar dani lallai
kinci amanata kuma kinci amanar zumuncin dake tsakanina da mahaifiyarki."
Koda gama wannan jawabi sai nuzaira tayi shiru bata kara cewa komai ba , sannan ta mike
tsaye ta fice daga cikin dakin ta bar jaruma yazila a zaune cikin tsananin damuwa, gami da
tunani mai zurfi.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {2}
TYPE B
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
Haka dai yazila taci gaba da sake-sake acikin zuciyarta ta kulla wancan ta kwance wancen har
dare yaraba ya zamana taka sayin barci sai kai kawo kawai takeyi acikin dakin nata tana zarya.
Bayan tayi dogon nazari da tunani akan abinda zai fishsheta sai taje ta dakko takadda da
alkalami ta rubuta wata wasika ta ajiye a karkashin matashin kanta sannan ta cire kayan jikinta
ta sanya wadansu bakaken sulke na yaki ta dauki makamanta na yaki ta soke a jikinta nan take
tayi girgiza bace bata bayyana ako ina ba sai a kofar gidan sarkin yaki zaihar da baiyanarta sai
taga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikinsu kai tsaye jaruma yazila ta durfafosu koda masu
gadin suka hangota sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganinta a cikin wannan lokaci na
tsawon dare cikin ladabi da biyayya masu gadin suka risina suka gaisheta yazila ta dubeshi a
fusace tace kubude mini kofa da salama na shiga domin naga mai gidanku idan kuma kuka yi
gardama yanzun nan takobina zata sha jininku !“.
Koda jin wannan batu sai jikin masu gadin ya kama karkarwa cikin firgita sukayi sauri suka bude
mata kofar ta kunna kai ciki da shigar yazila cikin gidan sai tazare takobinta taci gaba da kutsa
kai tana leka cikin dakunan gidan domin taga inda sarkin yaki zaihar yake. Karar zare takobin
yazila daga cikin kubbenta ne yasa sadauki zaihar ya bude idanunsa alokacin da yake kwance
tare da matarsa acikin turakarsa dama bai dade da kwanciya ba bisa bata lokaci da yayi wajen
bincike a hallarar tsafinsa. A cikin binciken da yayi ya ga wata gagarumar masifa dake shirin
afko masa amma sai ya kasa gane irin masifar da kuma lokacin dazata zo masa abin da ya
saya kasa barci ke nan ya kwanta kawai yana tunani cikin fargaba. Koda zaihar yaji karar zare
wannan takobi sai yayi wuf ya mike daga kan gadonsa yayi sauri yasanya kayan yakinsa
sannan ya zare tasa takobin ya fita waje yana neman wanda ya shigo masa gida cikin wannan
tsohon dare. Nassey dey Talk
Lokacin da jaruma yazila ta shigo cikin wani katon falo na gidan wanda babu komai acikinsa
face shimfidar jan kilishi mai taushi da kujeru na alfarma sai tayi kicibus ! Da sarki yaki zaihar
tsaye ruke da takobi a wannan lokaci falon a haskake yake dahasken fitilu tazarar dake
tsakanin zaihar da yazila bata wuce taku asirin ba. Koda zaihar ya ga ashe yazila ce ta shigo masa gida acikin wannan dare sai ya cika da
tsananin mamaki kuma yaji ajikinsa cewa lallai ba lafiya ba akwai wani abin daya faru da dai dai
ba saboda haka saiya tsaya a inda yake ya dubeta yace yake halifata mene ne ya kawoki
gidana a wannan dare?“ Yazila ta dubi zaihar a fusace tace ,“ nazo na dauki fansar mahaifina
dakakashe ne ya kai babban azzalumi !“
Cikin matukar mamaki zaihar ya dakawa yazila tsawa yace ,” wannan kuma wacce irin maganar
banza kikeyi ? Shin ke ba yar mai girma barzuk bace ? Yaza ayi kice na kashe mahaifinki
alhalin barzuk na nan araye ?”.
Dajin haka sai hawaye ya zubowa yazila tace ”
Kayi tunani izuwa shekaru goma sha takwas baya lokacin da kabi bayan hukairu dan uwan

barzuk sa adda ya gudu tare da iyalinsa izuwa birnin misra daf da kofar birnin misra kuka fafata
yaki kai da matarsa humaira tan goye da jaririyarta to ka sani cewa wannan jaririr yar uwata ce
mun kasance tagwaye nida ita kuma hukairu ne ya haifemu ita kuwa nuzaira abin data haifa
mutuwa yayi sai humaira taba ta daya daga cikin tagyayen data haifa kuma ni ce jaririyar da aka
bata kagake nan hukairu shine mahaifina ba barzuk ? Lallai mahaifina ka kashe , babu makawa
sai na dauki fansa a kanka kuma a yanzu ”. Nassey dey talk
Sa adda yazila tazo nan a zancenta sai sarkin yaki zaihar ya bushe da mahaukaciyar dariya. Ya
ce ” yake yarinya karyarki tasha karya. Ba a zama wane a banza. Kafin na sami wannan
matsayi na sarkin yakin birnin kisra sai dana taka mukamai masu daraja da yawa kuma sai
dana sha bakar wahala. Duk abin da kike takama da shi a yanzu na mallakeshi tun kafin kizo
duniya saboda haka yanzu ga fili ga mai doki idan kina ganin zaki iya daukar fansar mahaifinki
ki jarraba ki gani ina tabbatar miki da cewa kamar yadda na kashe mahaifinki haka kema zanka
sheki !”.
Kafin zaihar ya gama wannan jawabi tuni zuciyar yazila ta fara tafarfasa kawai sai ta daga
takobinta sama ta ruga gareshi shima sai ya daga tasa sama ya rugo gareta suna haduwa
kowanne su ya kaiwa dan uwansa mugun sara kowannensu ya kare saran da takobinsa da
takobinsa tara tsatsin wuta ya fantsama izuwa kas. Nan fa suka rugunzume da azababben yaki
ya zamana cewa suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta.
Wohoho ! Idan sabon hannu da tsohon hannu akahadu a gumurzu dolene aga tsagwaran
jarumta t ban al'ajabi. Ita yazila tana ta kama da kuruciya gami da sadaukan taka ta zamani
shikuwa zaihar yana ta kama da kwarewa da sanin makama ne. Da dabarun yaki irin na
tsofaffin sadaukai inda aka sami babban bambanci shine, ita yazila tafi zaihar juriya da dadewa
ana gumurzu, shi kuma yafi ta zafin nama.
Sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan gumurzu dayansu bai sami na sarar komai ba, ya
zamana cewa dauki ba dadin da sukeyi yasa gaba daya hadiman gidan sun rugo izuwa falon da
suke fafatawa a dimauce. Itama matar zaihar saita farka daga bacci a firgice ta ruga izuwa
dakin da danta ke barci, wani karamin yaro dan shekara hudu kawai, saita sungumi yaron a
kirjinta taruga izuwa falon da ake gumurzu tsakanin yazila da zaihar.
Dazuwa sai ta iskesu cikin masifaffen artabu. Gaba daya hadiman gidan sun ra kabe a tsorace
suna kallon abin dake faruwa. Nan fa itama matar zaihar ta kasa yin komai saita tsaya ka wai
tana kallon fafatawar cikin tsananin tsoro da fargaba da mamaki bisa ganin wacce ke gumurzu
da mijinta. Nassey dey talk Saboda zafin naman zaihar sai ya shammaci yazila ya yanketa acinya. Kafin tayi wani yunkuri
ya sake yankarta a damtsen hannunta na hagu. Bisa dole yazila tayi alkafira da baya ta koma
nesa kadan da shi ta durkushe kasa bisa guiwowinta a lokacin da ta dafe raunikan jikinta biyu
cikin jin zugi da radadi. Koda taga jini na zuba saita fusata ainun kuma tayi sauri. Ta daure raunikan da wani tsumma
dake daure a kugunta. Ka wai sai ta mike tsaye ta sake zare wata takobin a kuibin cinyarta ta
hagu ya zamana cewa ta hada takubba biyu ahannunta.
Koda ganin haka sai shima zaihar yaciro wani gatari dake rataye a bayansa ya hada da takobin
hannunsa ya fuskanceta. Kawai sai yazila ta rugo gareshi suka sake kacamewa da sabon
azababben yaki amma awannan karon sai yazila ta sauya salon fadan ya zamana cewa tana
tsalle tana alkafira a kasa da sama. Nan da nan kuwa ta ruda zaihar, bai ankara ba sai yaji ta

dankara masa sara acinyarsa. Take wajen ya dare jini yayi tsartuwa. Zaihar ya rankwala uban
ihu yatafi da baya taga-taga ya fadi
Koda matar zaihar taga abinnda aka yiwa mijinta zaihar sai itama tarusa ihu ta fashe da kuka.
Yazila ta kara rugowa da gudu izuwa kan zaihar ta ci gaba da kaimai sara da suka cikin iya zafin
namanta bata yarda ta bashi damar da zai daure raunin nasaba. Nan fa jini ya cigaba da zuba
daga cinyar zaihar har jiri yafara dibarsa amma saboda naci da juriya irinta 'YAN MAZAN JIYA
sai yaci gaba da yakin a haka. Ya yin da zai har ya fuskanci cewa idan akaci gaba da wannan
gumurzun a haka har izuwa wani lokaci mai tsawo zai iya gala baita yafadi saka makon jinin
dake zuba a kafarsa sabo da haka sai ya fara amfani da karfin sihirinsa yana watsawa yazila
mugayen abubuwa kamar; masu, wuta, kibiyoyi da sauransu. Bisa mamaki sai Nassey dey talk
yaga tsafin baya tasiri ajikinta, domin karfin sihirin nasu yazo daya duk abin da ya watsa mata
sai itama ta watso masa irinsu sulalata juna. Al'amarin daya dugunzuma hankalin zaihar kenan
ya tabbatar da cewa bashi da wata mafita face yayi amfani da iyakar karfin dmtsensa da
kwarewarsa ta yaki. Bisa dole yakara ZAGE DAMTSE suka cigaba da bakin gumurzun,
yazamana cewa sun tashi hankalin komai da kowa dake cikin falon.(Ni ma dakyar na rakabe a
ani lungu) Sai da suka shafe sa'a biyu suna wannan gumurzu ya zamana cewa kowannensu
yasake samun nasarar yiwa abokin gwaminsa rauni. Zaihar ya sami nasarar saranta a kirji, ita
kuma ta sami nasarar sokarsa agefen kirjinsa na dama alokaci guda duk subiyun suka kwala
ihu suka ja da baya taga taga kamar zasu fadi amma sai suka sake rugowa suka kacame da a
zababben yaki.
Hakika idan mutun ya ga irin wannan juriya, naci da jarumta irin ta zaihar da yazila dolene ya
jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika zaratan sadauki ababan misali. Bayan sun dada
kwarmazuwa bisa hadawa da naushi da bugun juna sai suka jigata ainun ya zamana cewa da
kyarma suke kaiwa juna hari. Duk wannan abu dake faruwa matar zaihar na rakabe a gefe daya rungume da danta ta na
kallongumurzu cikin tashin hankali kuma tana kuka.
A na cikin wannan fafatawar ne duk su biyun sukA yiwa juna wani irin mugun naushi a
fuskokinsu har jini yai tsartuwa bakunansu suka zube kasa kafin yazila tamike tsaye sai zaihar
yayi sauri ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da atsini ya wurgawa yazila wukar ta tafi tsananin
gudu zata cake ta cafi wukar ta maida ita inda aka jehota nan take tsinin wukar ya lume acikin
goshin zaihar nan take zaihar ya sulale kasa matacce koda ganin abin daya faru sai matar
zaihar ta kwala ihu ta rugo kan gawar mijinta ta ajiye danta a gefe daya ta rungume gawar tana
kuka sauran hadiman gidan kuwa sai suka firgice suka kama guje guje suna ficewa daga cikin
gidan gaba daya jaruma yazila ta taka kafafunta da kyar ta nufi inda matar zaihar take koda
ganin haka sai matar zaihar ta dago kai ta dubeta ba tare da tsoron komai ba tace.” Yake dirkar
birnin kisra ma zaki kasaro ki kasheni ni da dana domin na huta da wannan abin takaicin da
kika bar mini ban ga amfanin rayuwarmu a duniya tun da kin yanke mana farin cikin rabamuda
masoyinmu. ”.
Yazila tayi shiru bata ce komai ba har ta iso kan gawar zaihar kawai saitasa hannunta ta zare
wannan wukar wacce ta lumamai acikin goshin zaihar sannan ta dubi matarsa a lokacin da
hawaye ya zubo mata. Tace ina bukatar alokacin wannan wuka domin da sonki san cewa bazan
kashe kiba kuma bazawara kamar yadda uwata humaira ta zama bazawara kuma inason
wannan da naki ya zama maraya kamar yadda ni da yar uwata muka zama marayu ina son ki

isar da sakona ga sarki daksur cewa ni “jaruma yazila ” na kashe sarkin yaki zaihar bisa sanin
cewa shi ne ya kashe mahaifina na gaskiya bisa umarninsa don haka ya saurari ranar Nassey
dey talk da zanzo daukar fansa a kansa ki sanar dashi cewa na san sirrin layar da suka rataya
mini a wuya tun ina jaririya kuma na tafi inda za ayi cire mini layar koda gama wannan furuci sai
jaruma yazila ya goge jinin dake jikin wannan wukar daga jikinsa ta daura a kugunta kawai sai
ta juya ta fite daga cikin gidana tana tafe tana tangadi ita kuwa matar zaihar sai ta bita da kallo
kawai cikin tsananin mamaki bisa jin abubuwa data zaiyano mata a matsayin sako sarki daksur.
* * *
Al'amarin hadiman gidan zaihar kuwa, dasu da masu gadin gidan Bayan yazila ta sami nasarar
kashe maigidansu Sai suka ruga da gudu izuwa gidan sarki daksur suka isar da labarin abinda
ya faru ga man yan hadiman gidan. Ai kuwa acikin wannan dare labari ya riski sarki Daksur.
Cikin tsananin firgici da dimauta sarki daksur yamike zumbur yayi shigar yaki ya jagoranci
dakaru dubu a shirin da kansa acikin dare suka bazama neman jaruma yazila acikin birnin kisra
amma sai da suka duba ko ina basu gantaba.
Shikuwa hakimi barzuk yajin labarin abin da yafaru sai ya ruga izuwa dakin yazila a fusace rike
da takobi. Da shigarsa cikin dakin sai ya iske matarsa nuzaira atsaye rike da wasika tana
karantawa tana zubar da hawaye cikin fushi barzuk ya fisge takardar ya karanta jawabin dake
cikinta kamar haka. YAke ummata ki gafarceni bisa abinda zan aikata. Kiyi sani cewa bani da wani zabi face na
aikata hakan kuma ki gayawa mijinki da sarki daksur abinda ya faru da sarkin yaki zaihar suma
yananan tafe garesu nan da wani lokaci a ko yaushe kuma ina gargadinsu akan idan suka taba
lafiyarki nima saina taba lafiyar dukkanin danginsu, sai na tabbatar da cewa na share dukkanin
zuri'arsu daga doron kasa. Idan har sun matsu. Da son ganina su nemeni acan birnin
misra..........."
Koda barzuk yazo nan akara tun Nassey dey talk wasikar sai zuciyarsa ta kama ta farfasa
kamar zata kone. Saboda tsananin fushi da bakin ciki ka wai sai yasa hannu ya fyade nuzaira ta
fadi kasa sumammiya. Nan take ya kwalawa wasu hadi mansa kira yace su dauki nuzaira su
kaita can babban kurkuku na kasar suce asamata sarka atsareta har sai ranar daya nemeta.
Nan take kuwa wadannan hadiman suka cika wannan umarni. Bayan hadiman sun tafi da
nuzaira sai yafita da sauri ya hau dokinsa yatafi gidan sarki da zuwansa kuwa ya iske sarki
daksur ya dawo daga neman gimbiya yazila bai gantaba. Yana zaune a fada shi kadai cikin
tsananin fushi tamkar zai kona gidan sarauta gaba daya barzuk ya zube kasa gaban sarki
daksur ya sunkui da kansa kas cikin tsananin ladabi alokacin da gaba daya jikinsa ke karkarwa
don tsoro kada fushin sarki ya kare a kansa
Bazato ba tsammani sai barzuk ya bushe da ma haukaci yar dariya. Al'amarin daya matukar
bashi mamaki ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login