Showing 3001 words to 6000 words out of 29422 words
Chapter 2 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf
daukeki domin ya
dauki fansar yar uwarsa da na kashe amma bai sami nasara ba lallai yazama wajibi naje na
sanar wa sarki daksur wannan al'amarin domin mu dauki matakin gaggawa saboda nayi
mamakin yadda abokin gabarmu ya shigo har cikin kasarmu ya sace min mata batare da
munsaniba yake matata ki sani yau shekara goma dayin auranmu amma bamu taba samun
haihuwaba sai yanzu lallai acikin farin ciki nake mara misal tuwa dan haka yanzu da ganan
birnin kisra zamu wuce nanunawa sarki wannan kyakykyawar 'ya" dakika haifa mini kuma na
gaya masa maganar makiyammu Sarki raihan koda gama fadin haka sai barzuk ya shiga cikin
keken dokin ya zauna kusa da nuzaira sannan daya daga cikin yaransa ya hau gaban keken
dokin ya fara sarrafa dawakan aka cigaba da tafiya aka nufi hanyar da ta nufi birnin sin.
Tunda aka fara wannan tafiya zuciyar nuzaira ta fara bugawa da karfi domin ta tabbatar da
cewa da zarar sun isa gaban sarki Daksar asirinta ya tonu bisa karyar data shirgawa mijinta
cewa yaran sarki raihanne suka saceta domin shi sarki Daksur ka sur gumin ma tsafine wanda
ka iya ganin duk abinda yafaru tun gabannin su isa fadar tasa har aka iso cikin kisra hankalin
Nuzaira atashe yake bata da sukuni al'amarin dayasa barzuk ya dubeta kenan yace yake
matata lafiya naga kamar kina cikin damuwa? Tunda muka fara wannan tafiya bakice uffanba
kuma babu walwala da annu shuwa afuskarki koda jin haka sai nuzaira tayi murmushi tace
yakai mijina kasani cewa ban taba shiga fadar sarki Daksur ba da girmanaba saboda tun ina
yarinya wata rana sa'adda mahaifina ya je dani naga an sare kan wani mutun a gabana saina
firgita ainun na tsandara ihu tun daga wannan rana kullun sai nayi mafarkin wannan abu ina
firgita acikin barcina saida ma haifina yanaimi taimako awajen bokansa sannan na daina
wannan mugun mafarki yanzu dakace zamu fadar sarki daksur sai mafarkin ya fadomin arai
saboda haka nidai bana son shiga fadar sarki Daksur ka samomin masauki agari kafin mu isa
fadar. Sa'adda Nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk ya bushe dadariya yace kadaki damu
yake matata lallai bazanje fadar sarki batare dake.
Kamar yadda barzuk yayi alkawari haka abin ya kasance wato da shigarsu birnin kisra sai ya
kai nuzaira cikin wani kasaitaccen gida irin na sarakai wanda ke dauke da komai na jin dadin
duniya harda barori da kuyangu masu hidima. Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan
domin bata ga lokacin da aka biya kudin hayar gidan ba kuma da zuwansu kofar gidan ta ga
masu gadin gidan sun tsube kasa sun kwashi gaisuwa har nuzaira ta bude baki zata tambaye
shi batun wannan gida sai yace saboda me zakiyi mamakin mallakar wannan gida agareni ?
Shin kin manta ina daya daga cikin makusan tan sarki? Nuzaira tayi murmushi ta ce bana
mamakin mallakar wannan gida agareka amma ina mamakin dalilin da ya hana ka sanar dani
labarinsa Barzuk yayi murmushi yace so nake na shammace kine nabaki mamaki kinga kenan
zamu tare a sabon gida nuzaira tace yanzu idan katare anan birnin ya zakayi da wakilcin sarki a
kauyen Himsarul Aswad? Barzuk yayi dariya yace aiba tarewa zanyi ananba kece dai zaki tare
a cikin birnin nan domin na fison 'yarmu tataso da wayewa ta zama cikakkiyar 'yar birni mai
wayewar kai in yaso duk karshen mako nazo nata fi daku tare ku biyun.
Bayan barzuk ya nunawa Nuzaira bangarenta a cikin wannan gida harta shiga ciki ta kwanta
tana hutawa kuyangi suka fara mata shidima sai barzuk yayi shiri ya tafi izuwa fadar sarki
daksur.
Fadace kasaitacciya wadda aka kawatata da kayan alatu iri iri tamkar aljannar duniya sarki
daksur na zaune bisa wata kerarriyar kara gar mulki ta ka saita fadawa sun kewaye shi a
tsakiyar fadar ga wasu tsala tsalan 'yammata sai tikar rawa suke cikin mummunar shiga mai
baiyana tsaraicinsu.
A kaida duk sa'adda sarki ke kallon wadannan 'yammata yayin da suke tikar rawa yana dariya
da murmushi amma a yau sai sarki ya turbune fuska babu annuri atare da shi ko kadan kuma
tun da ya fito fadar haka ya ka sance cikin rahin walwala da sukuni kallo daya mutum zai masa
yasan yana cikin tsananin bacin rai. Al amarin daya matukar dugun zuma hankalin fadawa kenan domin sun sancewa fushin sarki
ba karamin tashin hankali bane agaresu gaba daya. Ana cikin wannan haline akaga hakimi
barzuk ya shigo fadar cikin farinciki kamar wanda aka yiwa albishir din mulkin duniya cikin sauri
har da hardewa barzuk ya isa gaban sarki Daksur ya zube kasa ya kwashi gaisuwa ya dago kai
domin yayiwa sarki bayanin abin farin cikin da ya sameshi sai sarki yayi farat ya tashi tsaye
kawai sai ya dubi barzuk yace kabiyoni izuwa cikin dakin gani ina son magana dakai a sirrance.
Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yanu fi dakin gani nanfa Barzuk ya bishi da sauri aka
bar fadawa da jama'ar gari a zazzaune sun yi tsurutsuru da idanuwansu suna mamakin abin da
ke faruwa. Yayin da sarki Daksur da Barzuk suka shiga dakin gani sai sarki ya tsaya a tsaye
maimakon ya zauna ya juyo suka fuskanci juna shida Barzuk yace kazone kayi mini aibishir
bisa cewa matarka ta haifi "ya" mace koba hakaba? Cikin muryar rawar murya burzak yace
hakane ya shugabana Daksur yace tokasani kasani wannan "ya" data haifa ba "yar ka bace
"yar" dan uwanka ce Hukairu amma ita matarka "da" na miji ta haifa kuma a mace yazo duniya
hakika matarka ta yaudareka kuma karya ta shiryama domin ka jaddada magana ta yanzu zan
nuna maka duk abubuwan da suka faru azahiri. Kagani da idanuwanka. Gama fadin hakan ke
da wuya sai sarki yayi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bango take hoton al'amarin suka rinka
gudana tun lokacin da Nuzaira tayiwa 'yar uwarta Humaira alkawarin cewa lallai awajenta zata
haihu har lokacin da aka bata jariri yarnan koda ganin wannan al'amari sai barzuk ya kwarara
uban ihu cikin tsananin bakin ciki jikinsa gaba daya ya kama tsuma ka wai sai ya zare ta kofi ya
juya da nufin yaje ya sare kan Nuzaira amma sai sarki daksur ya daka masa tsawa ya tsaya cak
ya juya ya durkusa bisa guiwowinsa a gaban sarki daksur ya mayar ka takofinsa bisa kubenta
ya sunkuyar da kansa kasa alokacin da hawayen takaici yake zubo masa yace ya shugabana
yanzu me ya kamata nayi? Sarki daksur yayi ajiyar numfashi sannan yace ya kai Barzuk kayi
sani bisa bin ciken da nayi idan muka ka bar matarka da wannan "ya da aka bata wannan fari
da annoba da muke fama dasu a gari zasu kare nan da sati biyu kacal gari zaiyi lafiya amma
inda masifar take shine wannan jaririyar da matarka ta zo da ita idan har ta girma zama
gawurtacciyar jaruma kuma mayakiya fiye da sarkin yakinmu sadauki Hauzar bin Mausus duk
yakin da muka taro sai ta sami nasara amma fa duk sanda ta san sirrin tsafina mun banu mun
lalace sai mulkimmu ya rushe. Kuma sai talakawanmu sun zama shugabanninmu sun dauki
fansar zaluncin da muka dade muna yi musu tsawan shekara da shekaru ta han ya daya ce ka
dai zamubi kada azo da ita fadata kada abari tayi arba da fuskata kuma kada ka nunawa
matarka bacin ranka koka gaya mata abin da muka tattauna anan yanzu.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani
***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE D
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
A can daji kuwa inda manomi hukairu yayi gidansa sun wayi garine a cikin farin ciki da bakin ciki
dalili farincinsu shine na haihuwa da humaira tayi nayaya tagwaye mata duk da cewa tayi
kyautar bayar guda ga 'yar uwarta nuzaira shi kuwa mummuna mafarkin wanda himaira tayi a
jiya da daddare da safe sa adda humaira ta farka daga bacci ta fara bawa mijinta hukairu
labarin mafarkinda tayi a jiya al amari daya matukar dugunzuma humaira duk hankalinsa kenan
dalili kuwa shine a iya saninsa da matarsa humaira duk abin datayi mafarkinsa saiya tabbata a
gaske. Bawani abu humaira ta ganiba acikin mafarki ba face saukar wadansu dakaru kamar
daga sama wadanda suka bukawa gidan wuta ya kone kurmus babu abin da ya tsira. Lokacin
da hukairu yaji labarin mafarkin da humaira tayi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun rasa abin
dake masa dadiya shiga tunani mai zurfi daga can saiya dubi ita humaira yace yake matata
kinsani cewa wajibine a garemu muyi hijra mubar gabadaya yankin wannan kasa tamu idan har
muna son mu da abin damuka haifa mutsirada rayuwarmu naji ajikina cewa sarki daksar
kasurgumin matsafine don haka na tabbatar da cewa abinda ya faru tsaka nimmu da 'yar uwarki
nuzaira ya gani kuma ya nunawa barzuk bisa wannan da lilinne za su turo a hallakamu lokaci
yayi da zan gaya miki wani sirri wanda bantaba gaya mikiba. Tun muna yara nida dan uwana
barzuk bokan ma haifina wanda muka sami sirrikan tsafi a wajensa yace mana cewa agaba
daya kasar nan babu wani mahaluki mai karfin sihirinmu face sarki daksar amma duk 'yar da
muka haifa idan tayi arba da idan sarki daksar to zata samu duk irin sihirin da sarki daksar yake
da shi a cikin kwana uku harta samu nasarar Hallaka shi ta hau kan karagarsa face ya kasheta
kafin cikar kwana uku shi kansa sarki daksar ya san da wannan sirri don haka bazai taba barin
abun da muka haifa arayeba dun haka ba zai barmuba yazama wajibi muyi shirin gaggawa
yanzu muyi hijira mukara gaba. Sa adda hukairu yazo nan azancensa sai humaira ta ce yanzu
ina kake tsammanin zamu shiga mu buya ba tare da sarki daksar yaturo an kashemuba Hukairu
yace waje daya ne zamu iya zuwa muyi rayu wa acan kuma mu tsira daga sharrin sarki daksar
da dan uwana Barzuk. Bawani waje bane face birnin misra inda sarki Raiyan ke mulki. " Koda
jin haka sai idanun Humaira suka zazzaro tace "ya ya za ayi muje birnin misra kuma muyi
rayuwa alhalin mutanen can sun kasance musulmai mukuma ma abota tsafine da gunki?
Humaira tace "shin ka manta ne sarki daksur bashi da wani makiyi wan da yafi sarki Raiyan na
birnin misra? Ai idan sarki raiyan ya fashinci cewa mu mutanen birnin kisra ne sai yasa anyi
mana kisan gilla domin ya dauki fansar ran 'yar uwarsa gimbiya Numaira wacce sarki daksur ya
ka she yayin da aka fafata kazamin yaki da su a shekaru uku baya. " Hukairu yayi ajiyar numfashi sannan yace "duk nasan da wannan al'amari amma abinda nake
so ki fahimta shi ne abinda ya koro bera yafada cikin wuta ya fi wutar zafi. " Koda gama fadin
haka sai hukairu ya mike tsaye yakama hada kayyayyakinsu domin suyi hijira. Bayan ya gama
hada hada komai a waje guda ya dora a kan rakumansa wasu kuma akan shanunsa sai yaje
tsakiyar filin gidan ya haka rami sai ga shi ya tuno wata laya. Nan take ya rataya layar a
wuyansa, sannan yakira Humaira ta fito da ga cikin daki goye da jaririyarta. Ba tare da bata
lokaciba suka hau kan rakumansu biyu sukayi gaba suna janye dabbobinsu. Koda hukairu ya
juya ya dubi gonarsa da wannan gida nasa sai idanunsa suka cikoda kwalla saboda takaicin ya
tafiya bar kasa mai albarkar noma wadda abu ne mawuyaci ya sake samun irinta.
Bayan kamar sa a hudu da tafiyar hukairu da matarsa humaira sai ga sarkin yaki haizar bin
mausus bisa doki tare da dakaru dari biyar suna take masa baya dukkaninsa dauke da muggan
makaman yaki tun daga nesa haizar ya dauko wani gilashi na sihiri wanda sarki daksur ya bashi
ya ce da shi da wannan gilashi ne kadai zai iya hango gidan hukairu. Haizur yasa gilashin a kan
idanunsa amma bai hango komaiba dan haka sai suka kara kaimin gudu bisa da wakansu. Jim
kadan da faruwar haka sai suka hango gidan daga can nesa. Daya daga cikin daka runnasane
ma ya fara hangowa ya nuna masa al'amarin daya matukar ba shi.mamaki kuma yaba shi tsoro
ya fara tunanin duk yadda a kayi su Hukairu basa gidan kuma lallai ya tone wannan laya wacce
sarki daksur ya bashi labarin cewa hukairu ya binneta a tsakiyar gidansa. Tun da ga inda suka
hango gidan Haizar yabada umarnin a fara harba kibiyar wuta izuwa gidan. Ai kuwa cikin kan
kanin lokaci gidan gaba daya ya kama ya kama da wuta yana ci balbal. Su sarkin yaki haizar
suka karqso gaban gidan aguje bisa dawakansu suka yiwa gidan kawanya kuma suka dana
kwari bisa baka suna jira suga wani abu mairai yayi fitar burgu don ceton ransa su harbeshi
amma hargidan yagama konewa kurmus yazama toka ko kyanwa basu ganiba. A sannanne
sarkin yaki haizar ya sakko daga dokinsa ya duba tsakiyar gidan nan take kuwa yayi arba da
wannan rami wanda hukairu tone ya cire layarsa ta sihiri. Cikin tsananin ta kaici da fushi haizar
ya kwarara ihu sannan ya dakko mudubin tsafinsa ya shafeshi sau uku yana mai karanta
wadansu dalasiman tsafi guda uku. Faruwar hakan keda wuya sai ga fuskar sarki daksur ta
bayyana akan madubin suka dubi juna. Kafin haizar ya budi baki yace wani abu sai sarki daksur
ya tari numfashinsa yace "maza ku ruga gaba domin tuni Hukairu da matarsa sunyi nisa, taza
rarku da su ta kai nisan sa'a hudu. Idan kuka yi sakaci suka shiga yankin kasar misra shi ke nan
baza ku taba riskar suba. Tun da hukairu na tare da wannan laya baza ku taba ganin koda
sawunsuba amma i dan kayi amfani da wannan gilashin sihiri da na baka zaka i yaganin
sawayensu. Idan har kana son kariskesu sai kunyi ta fiyar kwana uku bayada zango babu barci.
Idan har kasami nasarar cika wannan aiki kana dawo wa birnin kisra zanbaka wazircina kuma
zanbaka dukiya ninkin goman abin da ka mallaka a yanzu. Koda gama wannan jawabi sai
fuskar sarki daksur ta bace bat, daga cikin madubin sarkin yaki haizar nan take yaji farin ciki ya
lullubeshi dan haka sai yaruga kan dokinsa yayi tsalle ya haye kan dokin ya zabure shi cikin
matsanancin gudu koda ganin haka sai suma ragowar dakarun suka sakarwa dawakansu
linzami suka rufa masa baya.
Tun dasu sarkin yaki haizar suka cigaba da wannan tafiya basu tsaya ba har rana ta fadi, gari
yasoma duhu. A wannan lokacinne yunwa da kishirwa ta suka fara addabarsu. Sai da ta kai
suna ta fiya da wakansu suna sassarfa domin suma sun gaji dokin haizar ne ka wai bai gaji ba
saboda shi ba doki bane na gaskiya, dokine na sihiri. A duk sa'adda daya daga cikin dakarun
yayi yun kurin tsaya wa don ya huta kodan ya nemi ruwan sha sai haizar ya da ka masa tsawa
ya shiga taitayinsa, idan kwa yaki bin umarni nan take haizar zai zare takobi yasare kansa nan
take bisa dole suka hakura suka hakura suka ci gaba da tafiyar a hankan bayan kwana daya ne
dakarun suka rinka yanke jiki suna fadowa daga kan dawakansu matattu saboda tsananin
yunwa da kishirwa sakamakon basu taho da isasshen gazuri ba masu tsananin juriya da taurinri
ai ne suka kai kwana na uku amma suma alfijir na ketowa suka fadi kasa matattu ya rage saura
sarki haizar shi kadai bisa dokinsa shi kansa in badon yana tsafiba ya sami ruwansha da tuni ya
mutu saboda azababben zafi ranar da ake yi ga shi dazuzzukan da suke ratsawa gabadayan su
saharane ko bishiya daya mutum ba zai gani ba. Lokacin da rana ta take ne haizar hango su
hukairu a can gabansa tazarar da bata wuce taku dari biyar ba tsakaninsu sun doshi kofar
birnins misra koda ganin haka sai haizar ya zare takofinsa yasa karwa dokin sihirinsa linzami ya
zabureshi cikin masifaffen gudu. Su hukairu na cikin tafiya sai suka jiyo sukukuwar doki a
bayansu. A firgice suka juyo hango wanda ke kokarin kawo musu hari cikin hanza hukairu
yazare takobinsa ya tsaida rakuminsa sannan ya dubi humaira ya ce maza ki ruga bakin kofar
binin misra ni kuwa zantsaya na tari wannan mahayi da ya durfafomu. Ba wanibane.face sarkin
yaki haizar lallai sarki daksur ne yaturoshi ya hallakani. Koda jin wannan batu sai humai tafa
she da kuka ta ce ni kam bazan tafiba na barka sai dai mutafi tare. Cikin tsananin fushi hukairu
ya dakawa ya dakawa humaira tsawa ya ce idan ban tsaya ba na tareshi zai cimmanane ya
hallakamu gaba daya har jaririyar dake goye a bayanki. Fatana shine ke da jaririya kutsira da
rayuwarku ai ni nagama cika burina kunda har na kawo kunan bakin birninmu da na misra. "
Koda jin wannan batu sai humaira ta zaburi rakuminta da gudu tanufi bakin kofar birnin misra, a
wannan lokacin baifi taku arba'in ba haizar ya iso gaban hukairu Hukairu ya juya yayiwa
Humaira kallon kar she cikin guntun murmushi, a lokacin da kalla ta cika idanunsa. Wai gawar
da zaiyi haka sai yaga sarkin yaki haizar dab da shi har ya kawo masa wawan sara da nufin ya
sare masa kai. Cikin zafin nama hukairu ya sunkuya ta kobin haizar ta sari iska shima ya zare
takobinsa suka fara a zababben yaki. Nanfa suka fara kai wa juna sara da suka cikin tsananin
zafinnama, juriya da bajimta ya zamana cewa dayansu ya kasa cutar da dayan al'amarin da ya
matukar baiwa sarkin yaki zaihar mamaki kenan domin bai taba sanin cewa HUkairu jarumine
haka ba.
Lokacin da ake wannan mugun artabu
tsakanin Hukairu da Zaihar tuni humaira
ta isa bakin kofar birnin misra amma sai
ta ja linzamin rakumin ta ta tsaya cak ta
kasa shiga birnin ta juyo cikin tashin hankali tana kallon gumurzun da akeyi
tsakanin mijinta da sadauki zaihar.
Lokacin da sadauki zaihar yaga wankin
hula zai kai shi dare sai ya fusata ya fara
amfani da