Showing 18001 words to 21000 words out of 29422 words

Chapter 7 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

isha'i sai Humaira ta caba ado sannan ta shirya kasaitaccen abinci akan
teburin dake falonta wanda aka yi shi da farfesun irin wannan tsuntsayen da su dabira suka
farauto a daji.
Lokacin da Humaira ta gama wannan kintsi sai ta sallami dukkan kuyanginta suka fice daga
cikin turakarta gaba daya sannan ta zauna tasa wannan abinci agabanta tana kallonsa kawai a

lokacin da jikinta ya kama tsuma saboda mamaki da fargabar zuwan sarki Raihan. Nassey dey
talk
Tana cikin wannan hali ne taji anyi mata sallama. A razane ta amsa sallamar ta dago kai tayi
arba da sarki Raihan a tsaye shima ya caba ado na kure a daka fuskarsa Cike da annuri. Nan
take kamshin turaren jikinsa ya cika falon gaba daya.
Koda ganin sarki Raihan sai Humaira ta mike tsaye zumbur a lokacin da jikinta yaci gaba
tsuma, yayinda ™Nasiru Muhammad™sarki raihan yaga Humaira a cikin wannan hali sai shima
ya kasa bude baki yace wani abu har ya zo kusa da ita ya tsaya.
Tsawon 'yan dakiku suna tsayen dayansu baice uffan ba kuma kowannensu kansa na sunkuye
suna kallon kas, sai sarki Raihan yayi gyaran murya sannan yace, "ya ke ummul Dabira shin na
iya zama akan wannan kujera?".
Koda jin wannan tambaya sai Humaira ta dago kai ta dube shi cikin mamaki gami da murmushi
tace, "ya shugabana ai da wannan kujera da kuma wannan dakin duk a karkashin ikonka suke.
"
Koda jin haka sai sarki raihan yayi 'yar karamar dariya sannan yace, "A'a ina shakka. Na yarda
cewa da wannan kujera da wannan daki a karkashin ikona suke amma banda mai dakin. Ya ke
Humaira ki tuna cewa tun da kika zo garinnan tsawon shekaru goma sha takwas ban taba
umartarki da wani abuba sai yau, kuma yau ne karo na biyu da muka taba kebewa tare. Kin ga
kuwa ashe ke ba a karkashina ikona kike ba, kina dai karkashin alfarmata. Na san zaki yi
matukar mamaki bisa ganina ayau na kawo miki ziyara har cikin turakarki, kuma bama keba
hatta gaba dayan hadiman gidannan suna mamaki don gudun zargin wani abu shi yasa ban
rufe kofar wannan daki ba leka bayanki ki gani".
Cikin sauri humaira taleka bayan sarki sai ta hango wadansu dakarunsa mutun biyu a tsaye
suna hangen duk abin dake faruwa tsakaninta da sarki amma kuma basa iya jiyo abin da suke
tattaunawa koda ganin haka sai humaira tayi murmushi sannan tace. ” Haba ya shugaba ai shi
kansa shaidan ba a ko ina yake samun nasara ba na yarda da imaninka da tsoron Allah ka don
haka ina da yakinin cewa babu wani mugun abu da zai shiga tsakaninmu face alkhairi yanzu sai
ka zauna kaci wannan abinci wanda ka umarceni da na dafama maka ”. Koda jin haka sai sarki
raihan yayi murmushi yace. ” Na yarda zan zauna naci abinci amma bisa sharadin cewa zaki
cire™Nasiru Muhammad™ dukkan tsoron dake ranki ki daina tsuma haka”.
Da jin haka sai humaira tayi yar karamar dariya tace. ” Na amince amma ai bai kamata kaga
laifina ba domin kwarjininka ne da mamakin wannan ziyara taka ta bazata su suka janyo mini
lokaci guda duk su biyun suka yi dariya sannan suka zauna a tare zamansu ke da wuya sai
sarki ya bude kwanukan abincin dake gabansa kamshi ya doki hancinsa ya shaki kamshi cikin
farin ciki koda ya wanke hannunsa acikin bakinsa ya yanko loma guda ta abinci ya sa acikin
bakinsa ya tauna ya tsaya cak ga barin cin abinci ya kurawa kwanon abinci idanu kawai al
amarin da ya dugunzuma hankalin humaira ke nan tayi zaton ko abincin ne bai yi dadi ba.
Dag cai saita ga hawaye ya zubowa sarki raihan cikin kaduwa humaira ta dubi sarki kuma ta
dubi baki da kyar tace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskuren komai ba a cikin
wannan girki ?” Koda jin haka sai sarki raihan ya gyada kai sannan yasa daya hannun nasa ya
share hawayensa ya dubi humaira yace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskure
komai ba acikin wannan girki kuma tsananin dadin girkin ne yasa na tuno da matata marigyiya
da kuma yar uwarta ina so ki sani cewa rabona da cin abinci mai dadi irin wannan tun daga

ranar dana rasa wadannan masoya nawa saboda bakin ciki rabuwa dasu. Ina so ki sani cewa
idan har ban zo bana baiyana miki wata muhimmiyar magana dake raina tsawon shekaru a yau
bato har abada ba zan sami damar hakanba.
Yake ummul dabira kiyi sani cewa tundaga ranar da Nassey dey talk mutane suka zo dake tare
da jaririyarki dabira naji ina matukar kaunarki a zuciyata, amma sai naji bazan iya furta miki ba
saboda tausayinki bisa ganin halin da kike ciki na bakin ciki rashin mijinki wanda aka kashehi a
gabanki dakuma yadda kika bani labarinki naji cewar kin rabu da daya 'yar taki wato usainar
Dabira wacce kika bayar da ita ga 'yar uwarki Nuzaira. Tun™Nasiru Muhammad™ daga sannan
na ji na kamu da tsananin tausayinki da kuma kaunar dabira, shiyasa na rokeki akan cewa
komai dadewa kada kisanar da dabira cewa bani ne na haifeta ba har sai bayan shekara ashirin
alokacin da zatayi aure murabu da ita an nuna mini a mafarki cewa a gobe-gobennen allah zai
kawo wani sadaukin jarumin musulmi daga can nashiya daban wanda yafi Dabira jarumtaka
kuma suna haduwa zasu kamu da son junansu akan wannan daliline na yi kundun bala na
shirya wannan haduwa tamu domin na bayyana miki sirrin zuciyata. Idan harkin amince da
tayina ina son a daura aurena da ke gobe".
Koda jin wannan batu sai humaira ta fashe da kukan farin ciki taji kamar ta rungume sarki
raihan humaira ta budi baki domin tace wani abu sai kawai suka ga dabira ta fito daga cikin
turakar humaira idanunta sun yi sharkaf da hawaye. Cikin firgici da matukar mamaki sarki raihan
da humaira suka mike tsaye suka kura mata idanu. Dabira tasa hannu ta share hawayen ta
sannan ta dubesu daya bayan daya tace, "me yasa kuka buye mini wannan sirri tsawon
shekara da shekaru ? Na rantse da girman allah duk inda 'yar uwata take sai na tafi nemanta!
Waye ya kashemini mahaifina? Kuma ko waye ya kashe mahaifina sai na bincikoshi duk inda
yake na hallakashi! Ina tabbatar muku da cewa bazan taba yarda nayi aure ba face na cika
wadannan burika ".
Koda gama fadin haka sai taji ta tsani birnin kisra da duk mutanen cikinsa saboda jin cewa
asalin mahaifiyarta humaira daga can take. Nassey dey talk
Koda sarki raihan da humaira suka ga dabira ta fashe da kuka sai han kalinsu ya dugunzuma
suka yunkura zasu je gareta domin su rarrasheta amma saita ruga waje da gudu ta nufi
turakarta. Da zuwa sai ta shiga can cikin dakinta mai kofa ta rufe ta sake fashewa da sabon
kuka. Cikin sauri humaira da sarki raihan suka karaso kofar dakin dabira suka yi ta rokonta akan ta
bude kofar amma taki, duk suka hakura suka koma turakar Humaira™Nasiru Muhammad™
suka zauna.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {3}
TYPE C
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================

Tsawon lokaci duk su biyun sukayi tagumi basu ce komai ba. Daga can sai sarki ya mike tsaye
ya dubi Humaira yace, "yanzu muna cikin tashin hankali da damuwa saboda haka sai gobe naji
amsar tayin dana yi miki "
Koda gama fadin hakan sai sarki yajuya ya fice daga cikin falon gaba daya. I ta kuwa Humaira
ta bishi da kallo kawai cikin damuwa da tunani.
Har dare ya raba sosai Humaira bata rintsaba saboda fargaba da tunani bisa jin abinda Dabira
tafada cewar duk inda 'yar uwarta take saita tafi nemanta kuma sai ta nemi wanda ya kashe
mahaifinta. Shima shi.
Abinda ya tayar wa da humaira hankali shine, tasan irin bala'in sarki Daksur da sadauki Zaihar
da irin sadaukantakar da karfin tsafinsu,don haka yana tsoron karonta da su don tana ganin
cewa zasu iya hallaka farat daya muddin ta kai kanta inda suke.
Haka dai humaira ta kasance acikin tsananin tashin hankali ta kasa zaune ko tsaye ta dinga kai
komo acikin turakarta. Tana cikin wannanhali ne ta tuno da batun tsoho kasim nan take ta
aiyana zuwa dakin tsoho kasim ta tasheshi koda kuwa barci yake yi. Batare da bata lokaciba
humaira tafito daga cikin turakarta acikin dare da durfafi bangaren da dakin tsoho kasim yake
duk inda ta ratsa sai taga dakaru a tsaitsaye suna kan aikinsu na gadi kuma gaba dayan gidan
sarautar a haskake yake da fitilu gwanin ban sha awa duk inda tazo giftawa sai dakaru su ratse
su bata hanya babu inda aka dakatar da ita har ta iso kofar dakin tsoho kasim.
Da zuwanta sai ta iske kofar dakin a kulle take ruf. Haka ma gaba dayan tagogin dakin. Koda
ganin haka sai jikin humaira yayi sanyi ta tuna cewa yau fa tsoho kasim acikin matukar gajiya
yake sakamakon artabun da yayi™Nasiru Muhammad™ da kurayen nan har maya sami
raunika saboda haka bai kamata ta tasheshi daga barci ba nan take humaira ta juya da baya da
nufin ta koma turakarta. Amma sai ta jiyo sautin kuka acikin dakin tsoho kasim kuma sautin na
muryar mace ne. Al amarin daya matukar bata mamaki ke nan domin ita a saninta ai tsoho
kasim ne aciki wannan daki to mene neya shigar da mace cikin dakinsa ? Cikin fargaba da
sanda ta Nassey dey talk koma izuwa kofar dakinta leka ta cikin kafar kubar ai kuwa tana
lekawa ta hango zabgegiyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance zaune akan kujera tana
faman sharba kuka a gefe daya daya ga wadannan tufafi na tsoho kasim ajiye a gefe daya
wadannda akansu an dora layu da guraye na tsafi humaira ta kurawa fuskar budurwa idanu
kawai sai ta lura da idanunta taga iri daya ne sak! Dana dabira. Koda ganin wannan al amari sai
zuciyar humaira ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayenta biyu ta juya baya cikin ajiyar
numfashi tace a ranta. ” Duk yadda aka yi wannan yata ce ussainar dabira tazo mana a cikin
kamannin tsoho kasim mene ya kawota garin nan ? Shin tazo neta cutardamu ko kuwa ta gano
cewa mu jininta ne ta zo domin mu sadu ? ”
Nan fa humaira ta kasa baiwa kanta amsar wadannan tambayoyi cikin tsananin fargaba da
tashin hankali humaira ta koma dabaya don ta koma turakarta. Lokacin da ya rage saaura kiris !
Ta iske kofar turakarta sai kawai taga dabira tsulum ! A gabanta kamar daga sama ake jefota
kafin humaira ta budi baki tace wani abu sai dabira ta dubeta tace. Yake ummata menene ya
kaiki dakin bakonmu tsoho kasim ? Ki sani cewa nida sarki duk bamu yarda da tsoho kasim Ba
kuma na fuskanci cewar akwai wata alaka tsakaninki da shi. Da shi saboda haka gobe kafin na
bar garin nan zaki yi mini cikekken bayani akan rayuwarki kafin ki baro birnin kisra ki da dawo
nan misra da wannan kalami nake miki sallama allah ya tashe mu lafiya ” koda gama fadin
™Nasiru Muhammad™hakan sai dabira tajuya ta koma izuwa cikin dakinta tamai da kofa ta

rufe nan fa humaira ta sake rudewa ta kidime ta rasa abin da ke mata dadi a duniya domin bata
san bayanin daya kamata ta yiwa dabira da sarki ba a goben. Da kyar humaira ta koma cikin
dakinta ta kwanta taci gaba da tunani da zullumi. Har aka yi assalatu bata sami damar yin
barciba. Kamar yadda humaira ta kasa barci hak shima sarki raihan ya kasa barci saboda
tsananin damuwa har yaje masallaci da asuba. Ya dawo turakarsa bai rintsaba. Itama dabira
bata rintsa ba wato dai duk su ukun basu yi barciba amma wani ikon allah ita jaruma yazila
batasan saadda barci yasace taba daf da lokacin daza ayi sallar asuba. Lokacin da aka idar da
sallah a masallaci sarki ya waiga ko ina bai ga tsoho kasim ba sai jikinsa ya sake bashi lallai
akwai wani boyayyen al amari a kansa don haka sarki na baro masallaci sai ya tura aka kirawo
dabira yace da ita ta tafi izuwa dakin bako tsoho kasim ta fada dakin cikin shammace taga a
halin da yake ciki domin baizo masallaci sallar asubaba lallai akwai wani abu na shin gaskiya a
tare da shi. Domin tun da ya garin babu wanda ya ga yayi sallah koda jin wannan batu sai
dabira tatafi izuwa dakin tsoho kasim a fusace wadansu dakarunta guda biyu na biye da ita.
Tana sanye da hularta ta karfe.
Da zuwan kofar dakin tsoho kasim sai tasa kafarta guda ta daki kofar. Take kofar ta burma ciki
ta fadi kasa. Karar dukan kofar na yasa yazila ta farka firgigit! Kafin tayi wani yunkuri sai kawai
taga jaruma dabira tare da dakartunta biyu tsaye akanta rike da makamai koda su dabira sukayi
arba da yazila sai suka cika da tsananin mamaki. Gashi dai agefe daya kuma suka ga wannan
tsufaffun kayan tsoho kasim ga layu da gurayen tsafi akansu sai al'amarin ya daure musu kai.
Nan fa Dabira ta kurawa yazila ido tana tunani a zuciyarta. Abinda ya fadomata a rai shine,
tasan fuskar yazila tun da sun gwabza yaki ba sau dayaba, amma ™Nasiru Muhammad™bata
taba yimata kallon kurilla ba sai yau. Tabbas dai yanzu ta gane cewa abokiyar gabarta ce tayi
bad-da-kama ta shigo birninsu domin ta cutar dasu. Amma kuma me yasa a bokiyar gabar tata
take kama da ita? Anya kuwa yazila ba ita ce 'yar uwarta ba? Ai waka abakin mai ita tafi
dadi,bari naji daga bakinta.
Nan take dabira ta dubi yazila tace, "wace ce ke, kuma meyasa kika batar da kamanninki kika
shigo birninmu?".
Koda jin wannan tambaya sai yazila ta bushe da dariya tace, "Nice jaruma Yazila babbar
abokiyar gabarki! Kuma na shigo wannan birnin naku ne domin kawai nayi yakin karshe dake
mu bambance tsakanin aya da tsakuwa!!!".
Da jinhaka sai itama Dabira ta bushe da dariya sannan ta hade rai tace, "ke tsohuwar abokiyar
gaba kiyi sani sani cewa kinka wo kanki GIDAN MUTUWA! Lallai bazamu kashekiba da azaba
ko taron dangi ba, lallai nida ke zamu raba raini a yau dinnan. A matsayin ki na mai laifi, dole ne
yanzu nasa a kamaki akaiki kurkuku a tsare ki inyaso yau da farkon yamma yammaci afito dake
izuwa filin fada inda zamu fafata yakin karshe ni dake inda za arufe mu a cikin keji har sai
dayanmu ya wanda duk ya rayu sai ya bude kejin ya fito. " Nassey dey talk
Koda gama fadin hakan sai dabira ta dubi dakarunta dake tare da ita tace dasu su sawa Yazila
ankwa sannan su tafi da ita kurkuku,
Bisa mamaki sai dabira taga yazila ta tsaya kyam! Ansa mata ankwa a hannayenta da kafafunta
batare da tayi wani yunkuriba sai murmushi kawai take har aka tusa keyarta a gaba aka tafi da
ita. Al'amarin daya matukar jefata cikin tsananin mamaki kenan da wasi-wasi domin a sanin
dabira yazila jarumace ta gaske ko ita kanta ™Nasiru Muhammad™ bata isa tasa mata ankwa
ba cikin sauki, amma sai gashi dakarunta sunsa mata ankwar sun tafi da ita.

Abin dabata saniba shine yazila tana sane ta saki jiki aka kamata saboda dalili uku. Dalili na
farko shine tana son su fafata yaki domin dabira ta cire mata wannan laya dake wuyanta dalili
na biyu shine tanason takai dabira kas har ta cire wannan hular karfe ta kanta domin taga
kamanninta dalili na uku shine bata son dabira tace zata bita sutafi izuwa birnin kisra don
daukar fansa akan sarki daksur shiyasa taki gayamata cewa ita yar uwartace ta jini
Bayan an tafi da yazila izuwa kurkuku sai dabira ta tattara wadansu layu da guru na tsafi ta
kunna musu wuta nan take suka kune kurmus ! Suka zama toka. Har tajuya zata fita daga cikin
dakin sai taga jakar guzurin yazila a rataye ajikin bango kai tsaye ta nufi inda jakar take zata
dauko ta duba abin dake ciki sai kawai taji an kira sunanta. Tana waigowa sai taga ashe sarki
raihan ne a tsaye da kansa. Sarki raihan ya dubeta fuskarsa babu walwala yace " yanzu kin
daina fushi damu zaki iya sauraron bayanin dazan yimiki ?” Koda jin haka sai idanun dabira
suka ciko da kwalla. Tace. ” Ka gafarceni yakai abbana. Kayi sani cewa nima nayi nadamar
nuna muku fishina. Ina fatan zaku gafarceni ? ” Koda jin wannan batu sai sarki raihan yayi
murmushi yace. ” Babu komai yake. Yata yanzu dai kizo muje fada akwai wani gagarumin abu
daya taso wanda zamu zauna mu tattauna tare da sauran yan majalista hukuncin da kika yanke
yanzu akan wannan abokiyar gaba tamu dataso ta yaudaremu yayi kyau ”.
Koda jin haka sai dabira ta taho wajen sarki raihan ta ruke hannunsa suka jera suka fice daga
cikin dakin ya zamana cewa gaba daya ta manta da batun wannan jaka ta yazila. ™Nasiru
Muhammad™
Ita dai wannan jaka babu komai a cikinta face wadansu kayayyakin tarihi wadanda da zarar
humaira tayi arba zata shaidasu. Domin kaya nena yar uwarta nuzaira wanda ayanzu haka tana
da irinsu aajiye kuma kullum sai ta kallesu don tunowa da yar uwarta ta. Banda wadanda kayan
tarihi kuma. Akwai rigarda aka sawa yazila aranda aka haifeta kuma dabira ma tana da irin rigar
wacce har yanzu humaira nanan da ita aajiye don tarihi. Dabira ta sha ganin humaira tana
dauko rigar tana kallenta kawai har tana kwallah amma duk saadda ta tambayeta dalili sai tace
da ita kawai ta tuno wahalar data sha ne a lokacin data sami cikinta saadda ta haifeta. Lokacin
da sarki raihan da jaruma dabira suka iso fada sai suka iske gaba dayan yan majalistar a
zaune. Suna jiran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login