Showing 21001 words to 24000 words out of 29422 words

Chapter 8 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

karasowarsu al amarin daya razana dabira kenan domin ta san cewa duk
saadda taga yan majilista sunyi irin wannan taro ya zamana cewa kowa ya zo to lallai akwai
wani abu gagarumi al amari daya taso. Ko dai annoba ta barko. Ko kuma yaki zaayi.
Da shigowar dabira da sarki cikin fadar sai suka je suka zauna inda suka saba zama. Zaman su
keda wuya sai wazirin sarki Raihan yayi kyaran murya sannan yace, "yaku 'yan majalissar
wannan birni namu mai albarka, da yawa daga cikinku sun san dalilin taruwarmu anan. Ga
wadanda basu saniba, yanzu sai su sani. Wannan al'amari ba komai bane face a yau dinnan kimanin sa'a daya data shude mun sami
rahoton cewar abokan gabarmu mutanen birnin kisra sun taho da zugasama da dakaru miliyan
dari hudu da hamsin domin su yakemu.
Wannan zuga ta hada da dakarun gudummawa daga sauran kasashen kafirai na wannan
nashiya, kuma sun taho da alwashin cewa wannan karo adan za a shekara ana wannan yaki
bazasu janyeba har sai sun tabbatar da cewa sun baje birnin mu sun kashe mazajenmu sun
kama matayenmu da yaranmu a matsayin bayi sun kwashe dukkan dukiyoyinmu. ™Nasiru
Muhammad™
Ku sani cewa adadin wadannan dakarun abokan gaba ya ninka namu sau goma, wato gaba

dayanmu bamu wuce kaso daya ba a cikin kaso gomansu ba. Yanzu menene abinyi? Tabbas
idan muka ce zamu fita mu tari waddannan abokan gaba za su iya murkushemu a cikin dakika
kadan. "
Sa'adda waziri yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Dabira ta mike tsaye zumbur! A fusace, kuma
ta zare takobinta a lokacin da jikinta ya kama tsuma. Cikin fushi ta dubi waziri tace, "yakai waziri
kayi sani cewa bamu da wani karfi wanda yawuce karfin allah katuna cewa bayau ne karo na
farko da muke fita yaki da abokan gaba da kuma ya zamana sun fimu yawa, amma sai kaga
mun yi RAGAS dasu kokuma musami nasara akansu. Duk bawan da yayarda da allah kuma ya
sallama al'amuransa a gareshi tabbas allah zai iya masa abinda ya gagareshi. Ina tabbatar
muku da cewa koda abokan gaba yawansu ya kai cikin duniyar nan gaba daya idan ni kadai ce
na rage musulma a wannan birni na rantse da girman Allah sai na fita na yakesu dan kare
martabar addinin allah koda kuwa zasuyi gutsin-gutsin da sassan jikina. Na sani nan dagobe
wadannan abokan gaba zasu iso kofar birninmu don haka zan jagoranci dakarunmu mufita mu
yakesu wanda duk yake ganin zai bi bayana yabi, wanda ba zai bi ba yayi zamansa!".
Koda dabira tazonan azancenta sai sarki Raihan ya zare takobinsa yace, "Ina bayanki ya ke
'yata, lallai dani za ayi wannan yaki gobe!".Nassey dey talk
Koda ganin haka sai fiye da rabin 'yan majalissar ma suka yi abinda sarki raihan yayi. Kalilanne
daga cikinsu basu yi hakan ba, domin sun gama tsorata da wannan yaki daza ayi, kuma
imaninsu ya raunata.
Wannan shine a binda ya faru a fadar sarki raihan bayan 'yan majalisar kasar sun yi taro na
musamman.
Al'amarin yazila kuwa, lokacin da aka kaita kurkuku aka kulleta sai taji ko kadan bata damu ba
face kawai tana zumudin yamma tayi a fito da ita a kaita filin fada inda zasu yi yakin keji ita da
jaruma Dabira.
Har rana ta take Yazila ta kasa tsaye ta kasa zaune a cikin kurkukun. A lokacin ne aka kawo ma
ta abincin rana. Ko kallon abincin batayi ba bare ma taci.
Ai kuwa bayan an idar da sallar la'asar da kimanin rabin sa'a sai aka bude kofar kurkukun aka
tasa keyar yazila izuwa fada. Tana tafe tana jan sarkar da aka daure kafafunta da hannayenta,
dakaru na biye da ita.
Lokacin da aka iso filin fadar da jaruma YAZILA sai taga filin fadar ta cika makil da jama'a fiye
da kullum, harma mutane sun rasa inda zasu tsaitsaya sai akan katangau.
A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wannan katon kejin karfe mai tsawo da fadi wanda aka yi masa
'yar karamar kofa ta shiga. ™Nasiru Muhammad™
A can gefe daya kuwa, sarki RAIHAN ne da 'yan majalisarsa a zaume kuma daf da shi
JARUMA DABIRA ce a tsaye cikin gagarumar shigar yaki fuskarta a rufe cikin hular karfe kamar
kullum.
Koda aka ga anzo da YAZILA sai aka yi sauri aka bude kofar wannan keji. Cikin hanzari aka
kwancewa yazila sarkokin dake hannayenta da kafafunta aka bata takobi sannan aka ingizata
izuwa cikin kejin. Nan take Jaruma Dabira ma ta baro inda su sarki suke ta nufi inda kejin yake.
Koda ganin haka sai fadar ta rude da kabbara aka rinka yiwa Dabira Jinjina har ta shiga cikin
kejin aka rufe kofar kejin.
A sannan ne aka yi tsit! A fadar gaba daya tamkar mutuwa ta gifta. Nan fa aka fara kallon-kallo
tsakanin jaruma Dabira da Jaruma YAZILA.

Jaruma Dabira ta dubi yazila cikin murmushi tace, "yau mun hadu a inda babu damar gudu,
kuma babu yankewar yaki face dayanmu ya sami nasara akan daya.
Ina so ki sani cewa tuni na kona gaba dayan layoyinki da gurayenki na tsafi yanzu dame kuma
za kiyi dogaro?".
Koda jin wannan tambaya sai Yazila ta bushe da dariya tace, "ke yarinya, aikin kashe micijine
baki sare kansa ba. Kin ga wannan laya dake wuyana wani malami ma'abocin addininku ne ya
bani ita bayan an bashi dukiya mai tsananin yawa. Kuma ya tabbatar mini da cewa in dai ina
tare da ita babu wani mahaluki daya isa ya sami nasara akaina ".Nassey dey talk Koda jin haka sai Dabira ta fusata ta zare takobinta ta afkawa yazila suka ruguntsume da
azababben BAKIN ARTABU wanda ya dugunzuma hankalin kowa a wajen, domin su biyun
babu wanda ke da alamun samun nasara akan abokin gwaminsa.
~WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GAGARUMAR HADUWA DA AKAI ?
~SHIN DABIRA ZATA CIRE LAYAR WUYAN YAZILA ITAKUMA TA CIRE HULAR KANTA? IDAN
SUN SAMI NA SARAR HAKAN ME ZAI FARU ?
~YAUSHE ZA A KWABSA YAKI TSAKANIN RUNDUNAR BIRNIN KISRA DA RUNDUNAR
BIRNIN MISRA?
~A WANNE HALI HUMAIRA MAHAIFIYAR DABIRA TAKE CIKI?
~SHIN DABIRA DA YAZILA SUNA GANO CEWA SU 'YAN UWAN JUNANE ? IDAN SUN
GANO ZASU JE DAUKAR FANSA ABIRNIN KISRA AKAN SARKI DAKSUR? Muhadu a littafi
mai suna BAKIN ARTABU cigaban JARUMA YAZILA don jin cigaban wannan kasaitaccen
labari. Alhamdulillah a yau mun kawo karshen littafin JARUMA YAZILA 1-2-3 Sai mu hadu a
cigabansa
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★BAKIN ARTABU**cigaban**JARUMA*YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE A
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya fara da cewa:
====================================
Lokacin da aka kacame da azabebban yaki tsakanin jaruma dabira da jaruma yazila acikin
keji sai suka wanzu suna masu kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama. Juriya da
jarumtaka tamkar jikinsu bana jini da tsokabane. Sai da suka shafe sa a uku cur suna wannan
gumurzu amma dayansu bai sami nasarar koda lakuyar jikin abokin gwaminsa ba. ' Yan kallo
kuwa da sarki raihan hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin yadda ako yaushe yakin nasu
dabira kekara tsamari. Tashin hankalinsu sarki raihan shi ne. Idan jaruma yazila ta sami nasarar
hallaka dabira sunyi asarar sarkin yakinsu wacce babu kamarta aduk fadin mayakan birnin.
Lokacin da sa a uku ta cika sai dabira da yazila suka tsaya da yakin suka jada baya suka yi
cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru saboda gajiya.
A sannan ne dabira ta fara tunanin hanyar dazatabi ta sami nasarar akan yazila amma kuma

bisa mamaki sai taji zuciyarta na bugawa da karfi a duk sa adda ta kalli fuskar yazila.
Abu na biyu daya fado mata arai shi ne batun wannan laya dake wuyan yazila anya kuwa
wannan laya dake wuyan yazila ba ita ce tasa nakasa samun nasara akantaba ? Yazama wajibi
agareni na cire wannan laya daga wuyan yazila tunda dai tace daga hannun musulmi take.
Koda gama aiyana haka acikin zuciyarta sai tayi jifa da takobinta gefe daya ta dubi yazila tace ,
” tunda dai munkasa yiwa junanmu illa da makami saimu gwada yar kashi domin mu kawo
karshen wannan gabatamu ”.
Koda jin haka sai jaruma yazila ta bushe da dariyar mugunta irinta ma abota shirka sannan ta
murkushe fuska kuma itama tayi wurgi da takobin tace. ” Ai dama haka nakeso. Domin ta haka
ne kadai zamu iya bambancewa tsakanin aya da tsakuwa ” ™Nasiru Muhammad™
Nan take duk su biyun suka dunkule hannayensu suka gyara tsayawa sannan suka fara zagaya
juna. Kwatsam ! Sai suka kacame da azababban fada suka rinka kaiwa juna naushi da bugu.
Hannu da kafa.
Babu abinda zai baiwa mutane mamaki face yadda suke bugun jikinsu tamkar suna bugun
buhun hatsi. Ma ana ko gezau basayi. Sai dai kaga sun shanye dukan sun maida martani.
Aikuwa kafin an juma sun hadawa junansu jini da majina. Ana cikin haka ne suka jada baya
alokacin guda suka bayar da tazarar taku shida shida sannan suka rugo da gudu kowacce ta
daka tsalle sama. Suna haduwa sai kowacce ta gabzawa yar uwar mummunan naushi a
kumatu tun a saman feshin jini yai fitsar burgu daga cikin yanayi mai kama da suma Suma.
Al amarin daya sa gaba dayan mutanen dake fadar suka mike tsaye zumbur cikin firgici domin a
zatonsu jaruman biyu sunyi ragas babu wanda hankalinsa yatafi na kowa dugunzuma face sarki
raihan domin yana mikewa tsaye a dimauce bai san sa adda maya ruga da gudu izuwa bakin
kejin dasu jaruma dabira keciba. Al amarin humaira kuwa dama bata fito ba zata iya kallon
wannan gumurzu da za ayi ba tsakanin yazila da dabira.
Lokacin da gari ya waye taji gaba dayan gidan sarautar tayi tsit tamkar babu mai rai acikinsa sai
ta gane cewa lallai kowa na can fada ana kallon wannan fada daza ayi. Dama tun a daren jiya
tsakanin yarta dabira da tsohuwar abokiyar gabarta tazila wanda tazo musu a siffar tsoho
kasim. Bayan humaira ta gama dan kintse kintsenta saita mike tsam ta fito daga cikin turakarta
ta kamaa tafiya acikin harabar gidan sarauta inda ta rinka arba da dai daikun dakaru masu tsaro
da bayi masu kai kawokai tsaye humaira tawuce izuwa dakin da aka sayki bako ™Nasiru
Muhammad™kasim duk inda ta wuce sai aka ga dakaru da bayi suna rissinawa suna gaisheta
har ta isa kofar dakin da zuwa ta iske kofar dakin a bude batayi mamaki ganin hakan ba saboda
dama tasan yanzu ankama yazila an tafi da ita.
Duk da cewa humaira taga fuskar jaruma yazila ajiya da daddare amma har ayanzu zuciyarta
na wasi wasi akan anya kuwa yazila yarta ce?
Zuciyar humaira na bugawa da karfi ta kunna kai izuwa cikin dakin ai kuwa tana shiga tayi arba
da jakar guzurin yazila wacce ke rataye ajikin bango. Kawai sai ta dauko jakar ta sauketa akas
ta bude.
Nan take idanunta suka yi arba da wadansu surutu wadanda dabira tanada irin su sak. Sannan
kuma taga rigar da aka sawa yazila a ranar da aka haifeta wacce dabira ma tanada irinta.
Koda ganin wadnnan tufafi sai humaira ta dubesu ta rungumeshi a kirjinta sannan ta fashe da
matsanancin kuka domin a yanzu ta tabbata da cewa lallai yazila yarta ce kuma yar uwar

dabira. Tana cikin wani hali ne ta tuno da cewa yanzu haka fa yazila da dabira na can fada suna
yaki kuma za su iya kashe junansu.
A firgice humaira ta mike tsaye ta juya da baya a guje ta rungume da wannan tufafi ta nufi filin
fada. * * *
Lokacin da yazila da dabira suka baje akas cikin mawuyacin hali. Sarki raihan ya rugo da gudu
izuwa bakin kejin yana isowa sai yai turjiya bisa ganin abin daya faru.
Bawani abu bane yafaru ba face tashin yazila da dabira atare lokaci guda kamar wadanda suka
farfado daga dogon suma.
A tare yazila da dabira suka mike tsaye. Kowacce ta sake dunkule hannayenta kuma suka goge
jinin dake yoyo abakinsu. Kawai sai yazila ta kurawa hular karfen dake kan dabira idanu.
Itakuma ta kurawa layar wuyanta ido take suka sake rugowa da gudu batare da sunyi ™Nasiru
Muhammad™ yunkuri daka tsalle samaba. Cikin bakin zafin nama dabira ta kaiwa layar yazila cafka tayi saar damketa kuwa itama yazila
saitayi sa'ar damkar hular karfen dabira
. Alokaci guda kowacce ta cire abinda ta damka. Wato yazila tasami nasarar cire hular karfen
dake kan dabira. Sai ga kyakkyawar fuskarta ta baiyana a fili dogon gashin kanta mai haske da
kyalkyali ya zuba har kasan kwankwasonta.
Dabira kuwa sai tasami nasarar cire layar dake wuyan yazila tayi wurgi da ita. Atare duk su
biyun suka naushi juna da kafa a kirji kowacce tayi baya taga taga kamar zasu fadi kasa. Amma
sai suka cije.
Adai dai wannan lokaci ne sarki raihan da sauran gaba dayan jama'ar dake fadar suka kame
kamar gumaka saboda tsananin mamaki bisa ganin yadda kamannin yazila da dabira suka zo iri
daya sak tamkar an tsaga kara yazila da dabira suka kurawa juna idanu kowacce jikinta na
tsuma cikin mamaki. Bisa mamaki kuma sai kowacce ta sunkuya ta dauki takobi suka ruga ga juna suna ihu irin na
manyan sadaukai domin su sake kaurewa da sabon yaki. Lokaci guda suka sake tsayawa suka
waigo baya sakamakon jiyo muryar humaira wacce ta taho da gudu tana daka musu tsawa bisa
umarnin su dakata da wannan yaki. Ai kuwa sai suka kame suka kura mata ido. Da isowar
humaira sai tayi sauri ta bude kofar kejin dasu yazila ke ciki ta kamo yazila da dabira ta
rungumesu atare ta fashe da matsanancin kuka
Gaba dayan jama ar dake wajen sai suka rude da kabbara ™Nasiru Muhammad™
Cikin yanayin rashin fahinta dabira ta janye jikinta daga cikin na humaira ta dubeta tace. ” Yake
ummina yanzu kina nufin kice yazila ce yar uwatace da nadade ina son na gani ? ” Humaira ta
gyada kai tace. ” Kwarai kuma ga cikkakkiyar shaida ”. Nan take humaira ta tunawa dabira
wannan riga ta tarihi tace, "kin shaida wannan riga kuwa ? Irin taki ce da kike ta ajiyarta. Ki gafarceni yake 'yata hakiki na boye miki wani babban sirri na dangane da asalinki da kuma
tarihin tawa rayuwar. "
Koda humaira ta zo nan azancenta sai hawaye ya zubowa dabira ta dubi yazila tace, "ke kuwa
me yasa kika boye kamanninki agareni ? Yanzu ashe ke jini nace amma ban saniba, yanzu inda
da tsautsayi da shikenan sai dayammu ya kashe daya".
Yayinda yazila taji wannan batu sai itama zuciyarta ta karaya, hawaye ya zubo mata. Kawai sai
ta bude hannayenta biyu tana mai fuskantar Dabira.
Nan take Dabira ta fada kan kirjinta suka rungume juna kuma suka fashe da kuka a lokaci guda

suna dada kankame junansu.
A wannan lokaci gaba dayan jama'ar dake fadar suka cika da tsananin mamaki bisa ganin
yadda Jaruma Dabira ta rungume babbar abokiyar gabarta.
Bayan dabira da yazila sun dan jima a rungume da juna kuma fadar tayi tsit kamar babu mai rai
acikinta, sai yazila ta janye jikinta daga jikin Dabira ta dubeta cikin murmushi tace, "yake 'yar
uwata kiyi sani cewa tun daga ranar da nazo garin nan naku naga irin yanayin rayuwarku naga
ya banbanta da irin tamu ainun akan adalci,karamci da zaman lafiya, sai naji nakamu da
sha'awar wannan addini naku Ina son yanzu take ki shigar dani wannan addininaku. Ina son
yanzu take kishigar dani cikin addinin".
Koda jin haka sai Dabira ta cika da tsananin farin ciki batare da bata lokaci ba Dabira ta biyawa
yazila kalmar shahada ta maimaita.
Koda sauran jama'a suka ji YaZILA tayi kalmar SHAHADA, sai suka rude da kabbara. Shi kansa
sarki Raihan bai san sa'adda yakama murmushi ba saboda farin ciki.
Nan take sarki RAIHAN maya shiga cikin kejin ya kamo hannun DABIRA da YAZILA yajasu
suka tafi izuwa cikin gidan sarauta, HUMAIRA nabiye dasu.
A sannanne fadar ta watse kowa ya kama gabansa kai tsaye sarki raihan, humaira, yazila da
dabira suka wuce har izuwa turakar sarki raihan suka zauna.
Zamansu keda wuya sai wadansu likitoci mata guda biyu suka hau duba Yazila da Dabira suka
samusu magani a fuskokinsu inda jini yafito. ™Nasiru Muhammad™
Bayan sun kammala aikinsu na likitoci sun fita sai Sarki Raihan ya dubi Yazila da Dabira cikin
murmushi yace, "ya ku wadannan zaratan jarumai kusani yau ni da mahaifiyarku muna cikin
matukar farin ciki bisa ganin yadda allah ya hadaku har kuka gane juna.
Tabbas shigowar yazila izuwa cikin addinin allah cigaba ne babba a garemu. Yanzu dai kafin na
yiwa yazila bayanin halin da muke ciki ke humaira sai ki basu tarihin rayuwarki da yadda yazila
da Dabira suka rabu tun suna jarirai, har izuwa lokacin da kika gudo izuwa nan kofar birninmu
tare da mijinki aka kashe shi a gaban idanunki". Batare da bata lokaciba Humaira ta kwashe dukkan labarinta ta zaiyane wasu yazila.
Ai kuwa tana gama bayar da labarin, Yazila da Dabira suka fashe da matsanaicin kuka saboda
bakin ciki kuma suka harzuka ainun.
Cikin tsananin fusata Yazila ta mike tsaye ta dubi Dabira tace , "yake 'yar uwata kizo mu tafi
izuwa birnin kisra yanzu domin mu dauki fansa akan sarkin kisra da sarkin yakinsa. "
Koda jin wannan batu sai dabira ta kama kafadun yazila tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa
zuwa da shiri yafi zuwa da wuri.
Ina tabbatar miki da cewa ahalin yanzu wadannan abokan gabar tamu ba a zaune suke ba,
harma sunyi gagarumin shirin yaki sun taho nan garin domin su baje wannan birnin namu.
Labari ya riskemu....."
Kafin dabira ta gama fadin abinda ke bakinta sai sarki Raihan ya tari numfashinta yace, "yake
Dabira ai wannan jawabi bana bane, nawane".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login