Showing 12001 words to 15000 words out of 29422 words
Chapter 5 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf
nan ya dago kai a tsorace yana kallonsa.
Sarki daksur ya turbune fuska sannan yace , "hakika matarka taso ta watsa mana dukkan
shirimmu ta tona mana asiri bisa sakacinka na kula da sa ido akanta. Hakika in ba don kayi
mata hukunci ba da kanka kasa ankaita kurkuku da tuni kai da ita duk nayi muku hukuncin kisa.
Bisa bincike da nayi a halin yanzu na gano cewa tuni jaruma yazila tayi nisa da barin wannan
birnin wannan kasa tamu saura tafiyar kwana daya da yini daya jal ! Ta isa kofar birnin misra.
Jaruma yazila tana da matukar karfin sihirin tsafi don haka bani da wa dansu hadiman aljanu da
zan turasu su hallakata kafin ta isa cikin birnin misra. A cikin binciken da na yi na gano cewa
idan ta shiga cikin birnin misra bazata sami nasarar samun abinda taje nemaba. Kuma zata sha
tsananin wahala wacce zata iya zama sanadin ajalinta. A kwai wani lokaci da zaizo muyi yakin
karshe da sarki raihan na birnin misra a wannan yaki ne zamu sami nasara akansa mukama
birnin nasa gaba daya a sannanne zamu shiga har cikin birnin mukama yazila da mahaifiyarta
humaira sannan mu binciko duk inda 'yar uwarta take dabira itama mu hallakata. "
Sa'adda sarki daksur yazo nan azancenta sai farin ciki ya lullube barzuk bai san sa'adda ya
bushe da dariyar murnaba. Nan fa duk su biyun suka ci gaba da kyakyata dariyar kamar bazasu
dainaba.
A dai-dai lokacinne matar zaihar ta shigo cikin fadar ita kadai rungume da danta tana zubar da
hawaye. Batare da fargabar komaiba ta iso har gaban sarki Daksur ta risina ta kwashi gaisuwa
sannan ta zaiyana musu sakon da jaruma yazila tabata.
Koda matar zaihar ta gama jawabi sai jikin sarki daksur ya kama tsuma. Nan da nan zufa ta
karyo masa. Zuciyarsa ta kama bugawa da karfi kamar zata fado kasa cikin tsananin zafin
nama ya zare ta kobinsa ya fille kan matar zaihar ta saki dan dake Nassey dey talk hannunta ya
cafeshi da hannu daya. Gangar. Jikin matar zaihar ya sulale kasa alokacin da dan nata ya fashe
da kuka. Sarki daksur ya yunkura zai sare kan dan sai barzuk yace, "kayi masa rai ya
shugabana ai kankanin yarone"
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani
***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {2}
TYPE C
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
Sarki daksur ya sauke takobinsa kasa sannan ya bushe da dariyar mugunta ya killawa barzuk
wannan yaro ya cafe yace dashi katafida shi izuwa gidanka ka raineshi ya taso a cikin bayinka
masu yi maka hidima hakika mahaifiyarsa ta cuceshi data sayi ajlinta a lokacin da yafi bukatarta
a rayuwa tayi kuskure babba da tazo gabanmu da mugun lafazi domin itace mace ta farko
datata ba zuwa gabana ta fadi mugun sako. “ Koda gama wannan ne abin daya faru sarki
barzuk ya nufi hanyar fita daga fadar rike da wannan yaro yana ta tsala kuka bai fasaba. “
Wannan shi ne abin daya faru a birnin kisra tsakanin jaruma yazila dasu sarki daksur bayan ta
sami labarin asalinta. Acan birnin misra kuwa tun kimanin shekaru sha takwas da suka gabata
wato a lokacin da sarkin yaki zaihar ya kashe hukairu a gaban matarsa humaira saita ruga da
gudu izuwa kan gawar mijinta a lokacin da masu gadin kofar birnin suka rugo izuwa wajen suka.
Kewayeta suna kallonta kawai cikin alamun tausayawa domin sun fahimchi cewa mijinta aka
kashe. Kuma ga jaririya a goye a bayanta. Bayan humaira ta dade tana kuka har ta gaji sai
wadannan dakaru suka haka kabari suka binne gawar hukairu a gabanta sannan suka shigar da
ita mata jagora har izuwa cikin birnin misra daya daga cikin yayi masa bayanin duk abin daya
faru ga humaira a gaban idanunsa bayan Nassey dey talk wannan badakare ya gama jawabi
sai sarki raihan ya dubi humaira cikin alamun tausayawa yace wannan bakuwa ina mai yi miki
marhaba izuwa wannan birnin. Namu mai albarka wato birnin misra kiyi sani ma abota addinin
musulunci ne kuma bisa tafarkin addininmu bamu yarda da zalunci ba saboda haka muna son
kibamu labarinki iyakar gaskiya bisa abin dake tsakanin da wancan mutumin wanda ya biyoku
har izuwa kofar wannan birnin namu ya kashe mijinki kuma igudu idan har kina da gaskiya
akansa da iznin ubangiji duak inda ya gudu zamu tura a kamoshi domin ayi masa hukunci dai
dai da laifin da ya aikata kafin sannan muna son muji sunanki da kuma sunan garin da kika fito.
“
Lokacin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai humaira ta sunkai da kanta kas kamar
bazatace komai ba kuma taji tsoro ya shigeta bisa sanin irin tsananin gabar dake tsakanin birnin
kisra da birnin misra amma data tuna cewa sarki raihan yace shi mai adalci ne sai taji dukkanin
tsoro ya kau daga zuciyarta nan take ta baiyana masa sunanta da kuma kasardata fito. Koda jin
haka sai gaba dayan jikin sarki Raihan yakama tsuma, idanuwansa suka kada, zuciyar sa
takama tafarfasa kamar zata kone bisa jin sunan kasar mutanen dasuka zamo sana diyar
mutuwar 'yar uwarsa guda daya jal a duniya wadda yake matukar kauna fiye da komai a
rayuwarsa.
Cikin tsananin fushi sarki raihan ya kai hannunsa izuwa kan kuben takobinsa da nufin ya zare
takobin ya sare kan humaira amma sai ya kasa kawai sai hawaye ya zubo masa ya kasa yin
komai ya kura mata ido kawai. Daga can sai yayi ajiyar numfashi sannan yace, "yake Humaira
hakika kinci albarkacin adalci irin na ma'abota addinin musulunci amma da Nassey dey talk tuni
yanzu nasare kanki da takobina. Kiyi sani cewa na tsani kasarku, na tsani mutanen kasar ku
domin sarkin kasar ku ne ya kashe min 'yar uwata wadda na fiso fiye da komai aduniya a ranar
da mukafara yaki. Haka kuma sarkinku ya tsani mutanena ya tsani addininmu. A duk sa'adda
wani daga cikin jama'armu yaje kasar ku koda da zummar fatauci ne sai yasa a kamashi ayi
masa Kisan gilla. Ki sani cewa mu bazamu kashekiba bisa tarbiyyar addininmu, amma akwai
sharadi mai girma a tsakaninmu daku. Ba zamu yarda kuzauna a kasarmuba face kun karbi
addininmu idan kina ganin bazaki iya karbar addininmu to kijuya ki tafi izuwa wata kasar daban
inda zasu iya karbarki".
Ya yin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai Humaira ta fa she da kuka sannan tace, "ya kai
wannan sarki mai adalci, kayi sani cewa babu wata kasa dazan iya zuwa na tsira daga sharrin
sarkinmu da mijin "yar uwata face wannan kasa taka. A iya abin da na fahimta yanzu a zuwana
kasarka nagane cewa wannan addinin naku addinine na adalci gami da tausayi da jin kai,
domin da farko dakarun da suke gadin kofar birnin sun kamani da karfin tsiya zasu kawoni
gabanka amma dasu fahimci halin dana ke ciki suka an kashe min mijina kuma suka ganni da
goyon Jaririyata sai suka tausaya min suka tsaya suka binne gawar mijina sannan suka taho
dani izuwa nan fadar ka cikin salama ba tare da cin zarafinaba ko su taba lafiyata ba. Kaima da
aka kawoka gabana da kaji cewar na fito ne daga birnin kisra sai zuciyarka tayi baki ka harzuka
kamar zaka ka sheni amma saboda tausayi da adalci irin naka sai kakasa kasheni. Tabbas iya
wannan karamci dana gani daga gareku ya isa na gamsu cewa wannan addinin naku shi ne
addinin da yafi cancanta ga bil'adama a doron kasa. Saboda haka ni yanzu a shirye nake dana
karbi wannan addini naku mai daraja. "
Koda Humaira tazo nan azancenta sai taji gaba daya jama'ar fadar sun rude da Nassey dey talk
kabbara kuma kowa ya kamu da tsananin farin ciki.
Shikuwa sarki rai han baisan sa'adda fuskarsa ta fadada da murmushi ba. Nan take sarki raihan
ya biyawa humaira kalmar shahada ta maimaita sannan ya umarci wani hadimi nasa yace da
shi a kai Humaira cikin gidansa na sarauta abude mata dakin matarsa marigayiya kuma a bata
sutura da duk abinda take bukata. Nan take kuwa wannan hadimin ya tafi da Humaira izuwa
cikin gidan sarki ya cika wannan umarni. Daga wannan rana Humaira ta tsinci kanta a cikin
sabuwar rayuwa mai cike da dumbin farinciki da kwanciyar hankali, domin babu abinda tanema
tarasa. Haka kuma sarki yasa wata baiwa masanar addinin musulunci ta dinga koya mata
yadda ake ibada kuma ta dinga karan tar da ita addinin musulunci.
Humaira taci gaba da renun jaririya dabira tataso a cikin son addini kawaici, fasa ha da jarumta.
Tsananin kyawun dabira ya dimauta gaba dayan mutanen birnin misra, don haka tun tana da
shekara bakwai 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai suka rinka zuwa wajen sarki raihan kamun
kafa. Shikuwa sai Nassey dey talk yarika gaya musu dabira 'yace ta amana awurinsa don haka
ba shi da ikon bayar da ita face ta girma ta zabawa kanta miji.
Lokacin da sarki raihan yaga dabira ta taso da.matukar basirar daukan karatu da kuma
jarumtaka taban al'ajabi sai ya ji ya kaunaceta ainun tamkar hi ya haifeta. Bisa wannan daliline
yasa yazamana cewa kullum sai ya tura a daukota ta yini a wajensa yana koya mata karatu da
kansa kuma yana koyamata yaki. Hakane yasa dabira ta shaku ainun da sarki sarki raihan ta
dauka azuciyarta cewa shine mahaifinta, don haka tana kiran sane da "abbanta". Ita kanta
Humaira bata gayawa dabira gaskiyar al'amari ba domin kada hankalin dabiran ya dugunzuma
ta shiga wani hali. Kai a birnin ma gaba daya in banda wadanda suka san taihi zuwan Humaira
garin da yawan matasa sun dauka cewa dabira yar sarki raihan ce ta Cikinsa.
Wani abin mamaki shine, a tsawon wadanan shekaru har dabira ta cika shekara goma sha
takwas sarki raihan da Humaira basu taba zama tare ba tsawon dakika dari da sittin. A koda
yaushe duk su biyun suna gudun faruwar hakan domin gudun kada soyayya ta shiga
tsakaninsu. A binda basu saniba shine sun makara, domin tun a ranar da sarki raihan ya
musuluntadda ita duk su biyun suka ji suna kaunar juna.
Shidai sarki raihan tun da matarsa ta mutu a lokacin da tazo haihuwa ya zamana cewa dan
cikin nata ma yarasu sai yaji gaba daya baya sha awar yin aure a rayuwarsa domin a ganinsa
ba zai taba samun wacce zata maye gurbinta ba. Tun a sannan ne yayi al'kawari a zuciyarsa
cewa bazai sake soyayya ba. Ita kuwa humaira a duk sa'adda ta tuno da tsohon mijinta Hukairu sai taga kamar butulci za tayi
idan ta sake yin wani auran. Abu na biyu idan ta tuno cewa itafa ba jinin sarauta bace sai taga
babu yadda za ayima sarki raihan ya sota har ya aureta. Bisa wannan daliline ta dunga
baya-baya da shi ta na tsoron duk wani abu da zai jawo wata hulda a tsakaninsu duk da cewa
sautari ta kanji begensa yana darsuwa azuciyarta domin gaba dayan halayensa suna burgeta.
Nassey dey talk
Al'amarin gimbiya dabira kuwa lokacin da ta shekara goma sha takwas, kyawunta ya kara
bayyana karara a fili fiye da ko yaushe kuma ta zama gawur tacciyar mayakiya kuma jaruma
wacce babu kamarta akasar gaba daya. Sai sarki yasa aka bata sarautar sarkin yaki. Tun daga
wannan rana ne dabira ta samu damar rufe fuskarta da hular karfe, bata cire wannan hula face
tana cikin turakarta amma ko acikin gidan sarauta idan zata je wajen mahaifiyarta ko wajen
sarki sai tasa hular sai ta shiga wajen nasu sannan take cire hular saboda yawan kallon da
mutane suka yi mata yayi yawa bama maza ba, hatta 'yan uwanta mata da zarar sun ganta sai
kaga sun kura mata idanu baza su daina kallonta ba face ta kule.
Allah yayi dabira da tsananin kyawu na dirin jiki,sannan gashin kanta baki ne sidik ga kyalli da
sheki tamkar madubi ya zubo har kasan kwankwasonta. Saboda tsananin kyallin ga shin idan
mutum ya tsaya a bayanta sai ya dinga ganin fuskarsa a cikin gashin.
Dabira nada dara-daran idanu farare soll masu dauke da digon baki tamkar yankan wuka. Tana
da dogon wuya tamkar na barewa. Kalar fatar jikinta kuwa bata kasance fara ba ko ja ba, wani
irin launine na musamman wanda ido bazai iya tantance waba saboda tsananin kyau. Kai a ta
kaice dai babu wani da namiji da zaiyi arba da jaruma dabira ba tare da ya kamu da tsananin
sonta da begen taba.
Lokacin da samari masu isa suka yi caa ! A kan neman auren gimbiya Dabira sai ta taka musu
birki tace baza tayi aureba har sai ta sami na sarar yaki a kan mutanen birnin kisra, kuma duk
saurayin daza ta aura sai ta tabbatar da cewa yafita ilimin addinin muslunci.
Al'amarin daya matukar firgita samarin kenan guiwowinsu sukayi sanyi domin sun san cewa
Dabira tasa sharadin abin da ba zai taba yiyuwa ba domin a kasar gaba daya ana ganin cewa
babu mai irin iliminta. Hatta manyan malaman kasar ma shakkar ta suke domin tun sa'adda
tana yarinya 'yar karama ta rinka kure su yayin da a ke musabaka ta karatun Al'qur'ani da
fassararsa.Nassey dey talk
A bangaren ilimin tauhidi da fighu kuwa' dabira ta na zarcie littattafai da dama. Wasu ma jama'a
da yawa basu taba nazarin suba saboda tsananin yawon neman iliminta da bincikenta da kuma
baiwarta ta saurin daukar karatu. Duk abin da aka biyawa dabira ko aka gaya mata ta haddace
shi kenan har abada tamkar a littafi aka rubuta shi, komai tsaurin karatu da yawansa kuwa. Kai
da yawan mutanen kasar misra sun daina kiran ta da dabira sai dai suce da ita "YAR BAIWA"
saboda al'amarinta ya wuce yadda kowa ke tsammani.Lokacin da jaruma yazila ta hango kofar
birnin kisra daga can nesa, dabara ta fadomata na yadda zata shiga cikin birnin bisa batar da
kamanninta koda wannan dabara tazo mata sai ta tsayar da dokinta ta sauka, sannan ta daure
dokin agindin wata bishiya. Dama awannan lokaci rana ta kwalle gashi ta gaji ainun kuma
guzirinta ya kare har ta fara jin yunwa da kishirwa. Ka wai sai yazila ta shimfida darduma a
karkashin wannan bishiya ta kishingida akai tana tunanin yadda zata shiga cikin birnin misra.
Tana cikin wannan hali ne kawai sai ta hango an bude kofar birnin, sai ga tawagar wadansu
dakaru kimanin su arba'in sun fito bisa dawakai a cikin shigar yaki kuma sun durfafo inda take
zaune.
Cikin hanzari jaruma yazila Nassey dey talk tayi girgiza, nan take ta rikide ta zama tsohon
mafarauci sanye da walki da rigar fata, kuma. A rataye da kwari da baka. A kafarsa yana sanye
da ta kalmin fata. A kan dokinsa kuwa tsuntsayene kala-kala kimanin guda bakwai duk matattu
alamar cewa harbosu yayi. Nan take dardumar dake shimfide a kasa itama ta rikide ta zama buzu. tsohon yana ki shingida
akan buzun yana hutawa
A dai-dai wannan lokaci ne wannan lokaci ne wannan tawaga tazo za ta gifta ta gaban
mafarauci. Koda ganin wannan mafarauci sai shugaban tawagar yaja linzamin dokinsa ya tsaya
a gabansa. Bawani bane shugaban tawagar face jaruma dabira. Tana sanye da kayan yaki,
kuma tarufe fuskarta da hular karfe, kofofin idanunta da hancinta da bakinta kadai ake gani. Jaruma dabirA ta dubi wannan tsohon mafarauci sama da kasa tare da karemasa kallo cikin
nutsuwa sannan ta daka masa tsawa tace, "yakai wannan tsohon mafarauci wanene kai, kuma
daga ina ka fito sannan menene ya kawoka nan kusa da kofar birninmu?".Nassey dey talk
Da jin wannan tambaya sai tsoho yakama makyarkyata cikin alamun tsoro yace, 'ki gafarceni
yake shugabata sunana kasim kuma ni bakon mafaraucine na fitone daga kasar rum. Na shigo
cikin dazuzzukan dake kusa da iyakar kasarku ne da tamu ina farauta sai guzurina da ruwan
shana suka kare shina na zonan na zauna ina hutawa idan rana tayi sanyi na shiga kasarku na
sayar da 'yan tsuntsayen dana harbo na sami abin da zan sake yin guzurin na koma kasata". Koda jin wannan batu sai jaruma dabira tayi murmushi saboda jin cewa tsohon daga kasar rum
yake domin birnin rum ma'abota addinin musuluncine a wannan lokaci, kuma akwai alaka
tsakanin mutanen birnin Rum da mutanen birnin Misra.
Dabira ta dubi tsuntsayen da tsohon ya harbo wadanda ke kan dokinsa taji sha'awarsu domin
babu irinsu a cikin yankin dazuzzukan kasar misra don haka sai ta dubi tsohon ta ce "yakai
kasim nayi sha'awar wadannan tsuntsaye naka saboda haka ni zan siyesu nawa ne? Kuma
inaso ka raka mu izuwa dajin daka harbo irin wadannan tsuntsaye domin nima na farauto irinsu
domin a halin yanzu farautar muka fito. Zan biyaka da lada na musamman idan kayi mana
wannan rakiya "
Koda jin haka sai farin ciki ya Nassey dey talk lullube tsoho kasim yayi godiya. Nan take jaruma
Dabira tasa aka bawa tsoho kasim abinci da ruwa sha ya cika cikinsa ya koshi, sannan ya hau
dokinsa ya wuce gaba yayi musu jagora izuwa cikin daji.
A wannan lokaci zuciyar tsoho kasim daka take kamar zata tsaga kirjinsa ta fado kasa domin
bai san dajin da zai kai su dabira ba su sami irin wadannan tsuntsaye na sihiri da ya samar
dasu.
~MEZAI FARU TSAKANIN YAZILA DA DABIRA A CIKIN WANNAN TAFIYA TA SHIGA DAJI
DOMIN FARAUTA?
~SHIN JARUMA YAZILA ZATA CIKA BURINTA BISA ABIN DA YA KAWOTA BIRNIN MISRA?
~YAUSHENE DABIRA ZATA GANE CEWA YAZILA 'YAR UWARTACE TA JINI, KUMA IDAN TA
GANE HAKAN MAIZAI FARU ?
~SHIN IDAN HUMAIRA TA HADU DA YAZILA ZATA SHAIDATA A MATSAYIN 'YAR CIKINTA
KUWA ?
~YAUSHENE ZATA KOMA BIRNIN KISRA KUMA IDAN TA KOMA MAI ZAI FARU?
Muhadu a JARUMA YAZILA littafi na uku don jin cigaban wannan kayataccen labari.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani
***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {3}
TYPE A
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***