Showing 24001 words to 27000 words out of 29422 words

Chapter 9 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf


Dabira tayi murmushi tace, "ka gafarceni yakai abbana hakika na wuce gona da iri".
Shima sarki Raihan sai yayi murmushi sannan ya dubi yazila yace, "yake 'yar uwar Dabira kiyi
sani cewa a halin yanzu a ko yaushe abokan gaba zasu iya baiyana a kofar birninmu kuma
labari ya riskemu cewa sun zo da mayaka masu tsananin yawa da ya wuce misali domin har
gudummawar mayaka suka samu daga sauran kasashen makwabtaka.

Tabbas yanzu bamu da wani zabi wanda yafi mufita mutari abokan gabar nan tun gabannin su
iso".
Koda sarki raihan yazo nan azancensa sai yazila ta dubi Dabira tace, "yake 'yar uwata kisani
cewa nice sarkin yakin birninmu kamar yadda kike sarkin yakin nan birnin, saboda haka nasan
dukkan sirrin mayakanmu da irin yanayin yakinsa, lallai zan bayar da gagarumar gudummawa a
wannan yaki daza ayi kuma na tabbatar da cewa ba karamar barna zan yiwa su sarki Daksur
ba.
Babban burina shine, na kashe sarkin yaki da sarki Daksur da hannuna".
Koda jin haka sai Dabira tayi murmushi tace, "ni kaina burina kenan domin dole ne mu dauki
fansa akansu bisa bakin cikin da suka jefa mahaifiyarmu a ciki.
Ya ke 'yar uwata tunda dai yanzu allah yasa kin karbi addinin musulunci na san cewa zuciyarki
zata sake kekashewa ga barin tsoro kuma zaki sami kwarin gwuiwa fiye da da can, saboda
haka ina ganin idan muka hada karfi da karfe ni dake a wannan yaki zamu iya samun nasara
akan abokan gaba ". Kafin yazila ta budi baki tace wani abu sai sarki Raihan ya tari numfashin Dabira yace, "ba haka
bane yake 'yata,ke dai kawai munemi taimakon allah, amma ai karfinmu ko dabarar mu baza su
sa musami nasara ba akan makiya ba domin na tabbatar da cewa suma baza su fito ba kai
tsaye sai da kyakykyawan shiri irin wanda basu taba yin kamar saba. Yanzu abin da nake so dake yake Dabira ki tafi tare da 'yan uwarki yazila ki tara dukkan
mayakan kasar nan ku fara shirye shiryen dabaru na yaki wanda yakamata kuyi, nima yanzu
zan je na tara dukkan 'yan majalisata domin mutattauna akan wannan yaki, amma dai kusani
nine wanda zan jagoranci wannan yaki inyaso kubiyu kurufa min baya idan allah yasa narayu
abayan wannan yaki ™Nasiru Muhammad™ kuma nasami nasara za a daura aurena da
mahaifiyarku domin mun daidaita junanmu".
Sa'adda sarki raihan yazo nan a jawabinsa sai yazila da dabira suka kamu da tsananin farin ciki
basu san sa'adda suka rungume sarki ba a tare lokaci guda suka sumbaci goshinsa.
Batare da bata lokaci ba Yazila da Dabira suka fice daga cikin dakin da sauri suka nufi wani
bangare daban na gidan sarauta inda suka iske wani barde a tsaye cikin shigar yaki.
Dabira ta dubi Barden tace, "ma za ka busa kahon tara mayaka domin yanzu nake son mu
shirya yadda zamu bullowa wannan yaki". Koda jin haka sai barden yacika Umarni.
Ai kuwa nan take dakaru suka dinga tuttudowa daga wajen gidan sarauta suna rugawa izuwa
filin fada suna taruwa da jeruwa a sahu-sahu.
Wannan shine abin yafaru abirnin misra bayan jaruma yazila taga mahaifiyarta da 'yar uwarta
Dabira kuma ta karbi addinin musulunci.
*** ***
A can birnin kisra, bayan sarkin yaki da sarki Daksur sun yi bincike a cikin halwar tsafi sun ga
duk abinda ya faru ga jaruma yazila wadda ta bijire musu kuma tazama babbar abokiyar
gabarsu sai hankalinsu ya duguntsuma ainun domin sun tabbatar da cewa aikin dake gabansu
ba kadan bane. Bisa wannan dalili ne sarki daksur yasa aka shiga sauran kasashen kafirai dake makwabtaka
don neman gudummawar Dakarun yaki. Duk sarkin da wasikar ta iskeshi sai yaba da hadin kai
ya aiko da dakarun masu yawa da makamai da kuma isasshen guzuri.
A yamma da birnin kisra akwai wata babbar kasa mai suna tashwar.

Birnin tashwar na karkashin mulkin wani sadaukin saurayi ne, kyakykyawan gaske mai tarin
arziki da karfin mulki.
Wani iko na allah shi dai wannan sarki baya tsafi kuma ™Nasiru Muhammad™tsafi baya tasiri
akansa. Bisa wannan daliline gaba dayan sarakunan dake mulki a nahiyar suke shakkarsa
domin ba a taba kai masa hari ba ko wargi.
Shi dai wannan sarki ana kiransa da suna Uhaisu bn kairuf. Sarki uhaisu yana da matukar karfin
damtse na allah ya isa, domin komai girman giwa idan yayi mata naushi daya sai ta fadi kasa
idan zai jarraba karfinsa ya kansa karti dari su rufar masa shi kadai, sai dai kaga ya bazarda su
gaba dayansu sun baje a kasa suna yoyon jini a hanci da baki. Idan kuwa ya naushi mutun iya
karfinsa tofa ko kashin karfe gareshi sai ya karye.
Sarki uhaisu bashi da wani addini don haka bai matsawa kowa ba a kasarsa duk addinin da
mutun yaga dama yana da ikon yinsa. Wannan ya samo asali ne tun daga iyayensa da
kakanninsa, haka ya taso ya samesu, basa addini kuma basa hanawa ayi.
Akwai wata rana sa'adda mahaifin sarki uhaisu ke kan gangarar mutuwa wato yana kwance
acikin jinyar cutar ajali awannan yammaci da suka ka daita su biyu kacal a cikin turakar sarki sai
uhaisu ya dubi sarki yayin da hawaye ya zubo masa yace, "ya kai abbana ina son nayi maka
wadansu tambayoyi guda biyu wadanda suka dade suna yawo acikin zuciyata" Koda jin wannan batu sai mahaifin nasa ya kamo hannunsa ya dorasu akan kirjinsa kuma ya
kura masa idanu alokacin da shima idanunsa suka ciko da kwalla sannan ya budi baki da kyar
yace, "ya kai dana na san tambayoyinka dake ranka kuma na dade ina jiran ranar dazaka
gabatar dasu agareni. Tabbas yanzu ne lokacin daya dace kayi mini wadannan tambayoyi domin tun kana karami na
boye amsarsu, kuma gashi harka girma kakai munzalin dazaka gajeni amma baka san amsar
tambayoyin ba wadannan suke faman damunka acikin zuciya.
TAMBAYARKA TA FARKO AKAN ADDINI CE. Kana so kasan dalilin dayasa bamu da addini?
Tambayarka ta biyu kuwa itace kana so ka san dalilin da yasa naki yin aure, kuma kaima ban
taba nuna maka ina da ra'ayin kayi aure ba? Kasaurara da kyau kaji amsar wadannan
tambayoyi naka kuma kayi amfani da basirarka wajen amfani dasu domin idan baka nutsuba
har abada bazaka sami daraja da daukaka ba irin wadanda na samu a rayuwata.
Dalilin dayasa bamu da addini shine, mahaifina kafin yarasu nayi masa irin wannan tambaya,
domin yadda ka taso babu addini. Kuma babu aure haka nataso amsar da yabani itace.
"Ya kai dana kayi tunani yanzu addinai sun yi yawa a cikin wannan duniya, akwai masu bautar
rana, wata, ruwa, wuta, gumaka, dabbobi da sauransu. Kai wasu ma aljanu suke bautawa.
Mahaifina yaga yamin cewa addini guda daya ne, kuma ubangiji daya ne wanda shine na
gaskiya mai ikon komai da kowa. A wannan zamani babu wannan addini kuma kaima zaka riski wannan addininne a karshen
rayuwarka, abu ne mawuyaci kasan wannan addini amma wata kila in ka sami haihuwa danka
yasan wannan addini.
To ka gaya masa cewa duk ranar da wani gagarumin yaki ya taso ya halarceshi domin a
wannan tafarki ne zai san wannan addini na gaskiya har ya fahimceshi kuma ya aminta da shi "
Sa'adda mahaifina yazo nan azancensa sai na cika da mamaki na dubeshi nace, "ya kai
abbana ashe baka gaya min cewa yaki ba zai taba zuwa birnin tashwar ba? Ya kuma yanzu
kake mini batun yaki ?"™Nasiru Muhammad™

Koda jin haka sai mahaifina yaja numfashi tamkar ransa zai fita, a sannan yace, "bana nufin
yaki zai zo har nan ya riskeka, ina nufin za'a aikomaka da sakon gayyata. Lallai ka amsa
gayyatar, amma kafita yakin kai kadai, kada ka kuskura ta tafi da kowa idan har kana son kasan
addinin gaskiya. Dangane da tambaya ta biyu dake ranka kuwa ba wani abubane face batun aure. Tun da
mahaifiyarka ta rasu ban sake yunkurin aureba.
Haka mahaifina ya kasance, shima mahaifina haka rayuwarrsa ta wanzu har izuwa kan
kakanmu na arba'in da daya.
Abinda nake nufi anan shine duk wanda yai aure acikinmu haihuwa daya yake samu kuma sai
matarsa ta mutu, shima sai yamutu yabar abinda ya haifa.
Lokacinda aka haifeka sai naji babu abinda nake so a duniya sama da kai, kuma naji ina son
kayi nisan kwana a duniya.
A cikin gidan sarautar nan akwai wani daki guda daya wanda ba'a shigarshi kuma kai ma baka
taba ganin an shigeshi ba, haka ne?"
Kodajin wannan tambaya sai na jinjina kaina nace, tabbas na san da wannan daki kuma na
dade ina mamaki da tunani akansa."
Mahaifina ya sake ajiyar zuciya yace, "Akwai wani aljani bawanmu a cikin wannan daki wanda
bama bauta masa shima kuma baya bauta mana, amma zaman amana ne da kauna tsakanin
zuri'armu da tasa. Duk abinda zai samemu a rayuwa shi wannan aljani ne ke sanar damu.
===========================================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

***★BAKIN ARTABU**cigaban**JARUMA*YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE B
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
===========================================================
A iya tsawon rayuwata ta duniya sau daya na taba. Ganawa da wannan aljani kuma shine ya
gaya mini cewa kada na kuskura na kara yin aure a rayuwata. Idan kuwa nayi sai an kawo harin
yaki izuwa kasata an kawar dani. Yakai dana kaima kayi amfani da wannan nasiha wacce
wannan aljani yayi mini kuma kada ka kuskura ka shiga dakin da wannan aljani yake domin ku
gana sai ranar daza ka fita wannan gagarumin yaki da aka gaiyaceka. "
Har kullum sarki Uhaisu baya mancewa da wannan jawabi na mahaifinsa don haka sai ya
hakura da batun aure gaba daya a rayuwarsa saboda yana son yayi nisan kwana a cikin daular
mulki daya tsinci kansa a ciki.
A ranar da wasikar gaiyata izuwa yaki ta riski sarki Uhaisu daga birnin kisra sai yacika da
tsananin farin ciki domin yasan cewa lokacine yazo da zai cika babban burinsa na duniya domin
yasan mahaifinsa ya gaya masa cewa bayan anyi wannan gagarumin yakinne zai iyayin aure
har ya sami magaji kuma lallai zai yi tsawon rai a duniya. Lokacin da maga-takarda ya gama karanta wasikar gayyata a fadar sarki Uhaisu fadawansa
suka ga ya cika da farin ciki sai mamaki ya kamasu domin su a saninsu babu sarki ya tsana

sama da yaki kuma babu abinda yafi so sama da zaman lafiya. ™Nasiru Muhammad™
Sarki Uhaisu ya kasance mutum mai adalci, tausayi da jin kai, gashi da karrama mutane, wato
bai iya wulakanci ba bashi da izza da jin kai irin na sarakai, duk da cewa allah ya bashi karfi,
kyawu da dukiya mai yawan gaske.
Bisa wannan baiwa da allah ya baiwa sarki Uhaisune ya zama cewa 'yan mata, 'ya'yan sarakai,
attajirai da manyann matsafa suka kamu da tsananin kaunarsa, wasu da yawansu a dalilin
kamuwa da sonsa ne ma suka kamu da cututtuka saboda rashin samun kaunarsa. Wasu ma
sanadin ajalinsu kenan. A duk sa'adda sarki uhaisu ya ci ado kuma yayi hawa ya fito daga cikin gidansa sai dai kaga
mata suna fitowa da gudu domin kawai su ganshi. Idan dakaru suna hanasu zuwa kusa dashi
sai kaga suna kuka kamar wadanda akayiwa mutuwa.
Duk wacce ta sami nasarar koda taba dikin sa ma kuwa sai kaga sauran mata na rungumeta
don su sami albarkaci. Idan kuwa maca tasami nasarar koda taba hannun sarki Uhaisu ne sai
dai kaga ta yanke jiki ta fadi sumammiya saboda tsananin farin ciki.
Daga wannan rana kuwa mata sun dinga kai mata ziyara kenan suna bata kyaututtuka ba
adadi.
Hakika a tarihin nashiyar kasar tashawar ba a taba samun saurayi mai farin jini ba a wajen mata
kamar sarki Uhaisu, kuma labarinsa ya bazu ko ina, har zuwa ake yi daga kasashe
daban-daban domin kawai aganshi.
Tabbas duk mutumin da yake shakka akansa da zarar yazo ya ganshi dole yake gasgatawa.
Komai hassadar mutun da kushensa idan yayi arba da sarki Uhaisu take yake sallamawa.
Sukansu maroka idan sarki Uhaisu ya fito suka fara yi masa kirari sai masu rasa irin kalmomin
dazasu rinka fada wadanda suka dace da shi akwai wani maroki wanda yafi kowa iya kodashi,
shine ya kance dashi:
Kaico! Ina gwanin wani ganawa? Ga saurayi uban samari tauraron kyawawa mai magance
yunwa da kishirwar yan mata. ™Nasiru Muhammad™
Gaka jarumi. Sarki sadauki mai ragargazar maza yau fa ga mai tekun zinare mai shanye
kogunan attajirai. Ga ruwan sanyi mai sanyaya zuciya talakawa kufara nan ga bargon kankara
mai kashe gobara daga kogi. Marhaban da babbar gona nomanta sai shekara dubu ! Aduk sa
adda marokin ya haukace ya kama sambatu saboda sai da dinare ya rufeshi ruf tamkar an
nutsar da shi a cikin yashi tun yana kirari. Ya koma yin waka sannan ya fashe da kuka ya dinga
mari da cizon kansa har sai da aka tattarashi shi da dukiyar daya samu aka kaisu gidansa
lokacin da sarki uhaisu yaga fadawansa sun cikada mamaki bisa ganin yadda ya kamu da farin
ciki don jin sakon gaiyata izuwa yaki. Kuma ya fahim cewa hankalinsu ya dugunzuma ainun sai
ya dubesu yayi murmushi sannan yace. ” Yaku yan majalista ku kwantar da hankalinku. Ku sani
cewa wannan yaki bai shafi kowa ba awannan kasa tawa face nikadai. Don haka nikadai zan
shirya na tafi wannan yaki. ”
Koda jin wannan batu sai mamaki da fargaba suka dada kama yan majalistar wazirin sarki
uhaisu wanda ake mazwan ya dubishi cikin tsananin damuwa yace. ” Haba ya shugaban kasani
cewa mu da sauran talakawanka muna. Matukar kaunarka kuma tunda ka hau kan karagar
mulki bamu taba rabuwa da kaiba dai-dai da rana daya. Mun tabbatar da cewa idan babu kai babu wanda zai iya yi mana mulki acikin adalci irin naka.
Tayaya kake tsammanin zamu iya barinka ka tafi yaki kai kadai ? Katuna fa cewa baka da mai

gadonka bare idan muka rasaka musami halifanka?"
Lokacin da waziri yazo nan a jawabinsa sai sarki Uhaisu ya mike daga kan karagarsa yayi tafiya
izuwa tsakiyar fadar sannan ya tsaya ya dubi jama'a gabas da yamma, kudu da arewa, kawai
sai hawaye ya zubomasa ya ce, "ya ku jama'ar birnin tashwar kuyi sani cewa a iya rayuwata ta
duniya babu abinda nake kishinsa kuma ™Nasiru Muhammad™ nake matukar kaunarsa sama
da birnina da jama'ata.
Yau shekara a shirin da takwas a duniya amma ban taba zuwa yakiba.
Duk wannan daukaka da ni'ima wacce nake da ita a duniya bata gani ba sai jitake yi kawai.
Yau gashi dama tazo wacce za a sanni. Bugu da kari. Ina mai sanar daku cewa wannan yaki da
zan fita ne zan cika babban burina na duniya harna sami damar aure na sami wanda zai gajeni
yaci gaba da yi muku irin mulkin da nake muku bayan babuni. "
Koda sarki UHAISU yazo nan a zancensa sai fadar gaba daya ta rude da shewa, mutane suka
cika da farin ciki asannanne sarki Uhaisu ya sallami kowa fadar ta watse nan labari ya bazu ko
ina a kasar cewa gobe sarki Uhaisu zai fita yaki shi kadai kuma ga sakamakon da zai biyo baya
idan ya fita yakin. Nan fa jama'a suka yi farin ciki da bakin ciki ba face rabuwar daza a yi da sarki izuwa tsawon
kwanaki ko watanni ba a san ranar da wowarsa ba. Haka kuma ba a san irin hadarin da sarki
zai gamu da shiba akan hanyarsa, babu tabbacin zai iya tsira da rayuwar sa duk da an san irin
gagarumar jarumtakarsa amma kuma ai ba a taba ganin kwazonsaba a filin yaki ba. Dayawa daga cikin jama'ar gari kuwa basu yi bacciba a wannan dare, musamman mata. Duk
gidan da kaje sai kaga ana koke-koke tamkar mutuwa akayi.
Yayin da dare ya raba sai sarki Uhaisu ya shiga cikin wannan daki na musamman wanda tunda
aka haifeshi bai taba shiga ba.
Kofar dakin a lullube take da yana gaba dayanta alamar cewa an dade ba'a shigaba tsawon
shekara da shekaru.
Batare da fargabar komai ba sarki Uhaisu yasa kwagirin sarauta ya share wannan yana sannan
yasa daya hannun nasa ya murza marikin kofar dakin nan take kofar ta bude ya kunna kai
ciki.™Nasiru Muhammad™
Da shigarsa sai ya ga dakin faba daya a haskake yake da wani irin haske na musamman
wanda bai taba ganin irin saba kuma yarasa daga ina hasken yafito. Babu komai acikin dakin
face wata farar kujerar karfe guda daya jal a ajiye agefe daya. Sai sarki uhairu ya dubi gabas da
yamma. Kudu da arewa na dakin. Amma bai gawata halita nai rai acikiba. Kawai saiya ya juya
da baya domin ya fiche daga cikin dakin. Har ya iso bakin kofa yasa kafarsa guda a waje sai
yaji an kira sunansa da wata murya wacce tabbas ya taba jin muryar amma sai yakasa tuno mai
muryar cikin hanzari da mamaki uhairu ya waigo. Kawai sai yayi arba da wani tsohon aljani.
Siriri mai dogon fuska gashin kansa da gemunsa fari ne fat kai da gani kasan cewa yadade
aduniya. Aljanin na zaune akan wannan farar kujera fuskarsa cike da annuri. Kallo daya mutun
zai yiwa aljanin ya tabbata da cewa yana cikin koshin lafiya domin akwai alamun kuzari a tare
da shi babu wata nakasa mai nuna alamu tawaya ko gazawa bisa dalilin tsufa. Aljanin ya sake
kiran sunansarki uhaisu akaro na biyu yace. ” Haba dan uwana ya zaka juya ka fito ko gaisawa
bamu yiba alhalin yau ne ranar farko da zamu fara ganawa ”. Koda jin haka sai sarki uhaisu ya
mai dawa aljanin martanin murmushi yataho gareshi cikin sanyin jiki. Da isowar uhaisu daf da
aljanin sai ya mike tsaye cikin girmamawa yayi masa nuni da kujerar da yake zaune akai yace

dashi ya zauna. Uhaisu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login