Showing 33001 words to 36000 words out of 47794 words

Chapter 12 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt

gyada mata. Muka fara cin abincin a nutse, ni kam caccakar abincin kawai nake yi duk yadda naso da inci abincin abun ya gagara, xuciyata a cunkushe take sosai, takaici da bakin ciki ya cika min ciki har babu wajen da abinci zai shiga. Suna gamawa muka fita, hango bakar Matrix da nayi nasan cewa yau Abbu ne zai kaimu kenan, mamaki ya kamani ko me ya hana shi yin break ne?? Muka shiga cikin motar, as usual a baya na zauna. Muka gaida shi ya amsa cikin wata hargitsattsiyar murya wadda tasa na kalli fuskar shi sosai kamar wadda take so ta gaskata Abbu ne ko ba shi bane? Ban taba jin muryar Abbu a hargitse haka ba, wani hargitsattsen kallo daya watso min wanda ya kada min yayan hanji babu shiri na sadda kaina kasa, ina jin Hafsy fadi ba a tambaye ki ba tana gayawa Abbu wai ciwon ido nake yi ina tsoron kar in goga musu shi yasa nasa glass, harara nake jefa mata a kaikaice sai dai wannan shine ainihin abinda bahaushe ya kira da 'harara a duhu' saboda ba gani na take yi ba. Har muka ajiye su a school dinsu ban dago kaina daga sadda shi din da nayi ba, suna fita na tashi na koma gaba kamar yadda muke yi, Abbu ya tashi motar muka wuce su Hafsy suna dago mana hannu. A hankali yake jan motar kamar ba tafiya muke yi ba, ya juyo ya kalle ni a karo na barkatai tunda muka fara tafiyar, gudun da zuciyata yake yi ya cigaba da karuwa a duk wucewar dakika. Kamar daga sama naji ya jefo min tambayar da nake tsoron ya jefo min, "Are you ok Nafeesah???!"





*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:30 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*23*


Kalmar 'Are You Ok' kalma ce da nake matukar tsoro idan ina cikin halin damuwa. I am a very emotional person, shi yasa idan ina cikin halin damuwa bana son mutane a kusa dani saboda gudun su tambaye ni lafiya? Don zan iya fashewa da kuka, ni a gare ni tambayar are you ok kamar fama min gyambo ne. Yanzu ma sai da nayi iyaka kokarin da zanyi na danne kukan da yake kokarin barke min nace "m fine Abbu, kawai bana jin dadin jikina ne" ya kalleni kawai nasan bai yarda da abinda nace ba, ban ga laifin shi ba don yadda nake a hargitsen nan babu wanda zai yarda wai gajiya ce ta maida ni haka. Ya kalleni sosai kamar wanda yake so yayi magana sai kuma kawai ya maida kallonshi ga titi, a raina naji dadin hakan nasan tambaya daya zai kara jefo min zan fashe da kuka, kuka kuma ba abinda nayi niyar in ci gaba dayi bane saboda Muneer. Har yayi parking a parking lot din dept din Microbiology, na yunkura zan bude motar ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana, na Juya a hankali na kalleshi. Idanuwan shi fes a kaina suke, naji wani slight rawar jiki kafin in sadda kaina kasa, muryar shi a sanyaye yace "akwai abinda yake damunki Nafeesah wanda kika ki gaya min and I wouldn't force you to tell me, kawai ina so in gaya miki cewa komi na rayuwa sai da hakuri, koma menene yake damun ki kiyi hakuri ki dauke shi a ba komi. Idan ma wani abu ne kika rasa kike ganin kamar ba zaki iya hakuri da rashin ba kada ki manta Allah yana tare da Ke. Shi ya mana alkawarin canza mana abinda yake sharri ne a gare mu zuwa ga mafi alkhairin shi don haka ki roke shi game da abinda yafi alkhairi a gare ki ba kiyi holding into something wanda yake ba alkhairin ki bane kin gane?" na gyada kaina a hankali maganganun shi sun shige ni. Abinda ya kamata in tuna kenan a lokacin da naga hoton Muneer da amaryar shi jiya, abinda ya kamata inyi kenan ba wai in kira shi ba ina kara fallasa kaina da disappointing kaina, sai yanzu naga cewar hakika abinda nayi jiya ban kyauta ba, naji kunyar kaina ta kama ni har ma data Muneer din, ko da wane ido zan sake kallonshi kuma yanzu??. Nace "na gane Abbu nagode sosai, In shaa Allahu zan yi amfani da shawarar ka" yace "good" shiru ya biyo baya a cikin motar, can naji ya sake magana cikin whisper, kamar kuma wanda yake tsoron yin maganar, "anjima kuma sai gida koh?" na gyada kaina a sanyaye, barin rayuwar Abbu da iyalan shi!! Tunani ne mara dadi dake fadar min da gaba a duk lokacin da ya fado min a cikin raina don haka nake iyaka kokarina wajen ganin na kauda tunanin daga cikin raina. Na sake tsintar muryar shi yana tambayana, "da gaske zaki dinga zuwa kina mana weekend?" nace ehh, a cikin raina nasan fada kawai nake yi ba don zan dinga zuwa ba sai don kawai kada su dameni da tambaya. Kamar yasan abinda nake tunani, yace "da gaske kike ko kuma kina fada ne kawai?" shiru nayi wannan karon, yayi murmushi tare da kallona kawai yace na gane. Dash board ya bude ya ciro wata karamar jaka fara mai hannu ya miko min, na amsa fuskana dauke da alamun tambaya, yace "it's a small thank u gift, thank u for staying with us Nafeesah, we enjoyed having u in our life and we wish you will come back to us forever!" na dan rausayar da kaina cikin alamun rashin gane inda maganar tashi ta saka gaba, me yake nufi ne? Murmushi yayi ganin ya saka kwalwa na cikin rudani. Yayi murmushi yace "oya! Up you go! Naga abokan ki suna jiran ki tun dazu" sai lokacin idanuna suka koma ga inda muke zaune, su Ni'ima na hango tsaye a kofar shiga lab dinmu suna hirarsu da Ramlah, cikin sauri na jefa jakar daya bani cikin handbag dita na mishi godiya tare da bude murfin motar na fita. Gabadaya kallo suke bina dashi cike da alamun tambaya nasan bai wuce na mamakin abinda muka tsaya hirantawa da Abbu bane tun dazu, naja fuska tare da kara gyara zaman gilashi na a fuskana. Tun kafin in karasa wajen su suka iso gare ni, Saadiya da Ni'ima suka kamo hannuna Ramlah kuma ta dafa kafadata, cike da damuwa suke tambayana, "Nafeesah are you ok?" ni duk sai naji sun ma bani haushi, na cire gilashin idona ina kallonsu cike da takaici, "why?? Saboda crush dina zai yi aure sai kuke zaton karewar rayuwata ne yazo ko me?" gabadayan su were relieved da yadda suka ga nayi, Ramlah tace "yeah! I thought about more than that ma, nayi zaton zan ganki kamar sabuwar kamu ne wallahi sai kuma na ganki da hankalinki dai, but are you really ok?" na gyada kaina "yeah, I am Ramlah but that doesn't mean ban ji haushin abinda Muneer ya min ba" Ramlah ta rungume ni da sauri tana tapping bayana, "ohh my poor friend, Am really sorry. Don Allah kiyi hakuri, nasan in shaa Allah wanda yafi Muneer alkhairi a gare ki yana nan zuwa" na danyi murmushi, kwatankwacin abinda Abbu ya gama fada min. Na janye daga jikinta ina kallon su Ni'ima dake tsaye suna kallonmu nace "ba kuna da lectures ba wai me kuke yi anan?" Sa'adiya tace "wallahi Ramlah ce ta kira mu wai muzo mu tayata baki hakuri don tasan yau a hargitse zaki xo sai kuma muka ga akasin haka" ajiyar zuciya nayi nace "na hargitse kam Sady but Alhamdullillah na dawo cikin hayyaci na kuje kawai" suka mana sallama suka tafi mu kuma muka shiga lab. Ranar babu aikin da muka yi, sallama muka yi da staff da lab attendants na dept din don haka wajen karfe sha daya muka bar lab din cike da kewar mutanen da muka zauna dasu. Wajen su Ni'ima muka je na kara musu sallama, daga nan na wuce gida. Ita Ramlah tana Kano tukun.

Ina zuwa gida na kara hada kan kayana na zauna zaman jiran Daddy don yace shi zai zo ya dauke ni. Bayan an fito daga masallaci sai gashi har da Mommy, sai da muka yi Sallar La'asar sannan muka yi sallama da iyalan Ibrahim Galadanchi cike da kewa, kauna da zullumi. Zullumin ko zan sake ganin su a rayuwata ko kuwa? Zullumin ko zan iya da korar wadannan kananun feelings da nake ji game da Abbu? Zullumin ko zan iya yin normal rayuwa kamar da wadda nake yi a gaban Iyaye na? Magana ta gaskiya watanni shida da nayi tare da Iyalan Ibrahim Galadanchi watanni ne masu muhimmanci da tarihi a gare ni, sun koya min abubuwa da dama a rayuwata, sun kuma gaya min ainihin abinda ni, Zuciya, da gangar jikina suke so da Muradi.

Na daga idanu a hankali na kalli Hafsy dake hannun Babanta tana rusa kuka da iyakar karfinta tana ihun Ita sai ta bini, na kalli su Qaseem suma duk fuskokinsu cike suke da jimami har da kwalla a cikin idanunsu, hakika bahaushe yayi gaskiya da yace 'Sabo turken Wawa' dana kalli fuskar Abbu kuwa sai da naji kamar in balle murfin motar in fito ince na fasa komawa gidan. Damuwar dake fuskar shi was obvious, na karance ta kuru-kuru cikin idanunshi, kallona yake yi da dukka idanunshi, yanayin shi ya min kama da wani wanda yake tsoron rasa wani abu mai matukar muhimmanci a gare shi. Daddy ya bude murfin motar ya shigo ya mata key, Abbu da iyalan shi suka daga mana hannu bakinsu dauke da addu'ar Allah ya kiyaye hanyar yayin da naji kwalla ta cika min idanu, Daddy ya ja motar muka tafi. Nabi gidan da kallo idanuna cike da kwallah, Allah kenan! Kamar a ranar ne nazo gidan, na tuna sanda su Daddy zasu tafi kukan rabuwa dasu nayi, gashi yau kuma ina kukan rabuwa da iyalan Abbu. Tafi tafiya na fara bajewa daga kukan dana fara, su Daddy hirarsu suke tayi game da karamcin iyalan Abbu, ni kam kallon gefen hanya nake yi kawai. Barci ya dauke ni bani na tashi ba sai da muka isa gidanmu shima Mommy ce ta tashe ni, na fito daga motar fuskana a washe ina kallon gidanmu, Finally dai! I am back!. Muka dauki wasu kayan muka shiga dasu yayin da Maigadi ya shigo da sauran, Dakina a shirye na tarar dashi kamar ina gidan don haka ina shiga na ajiye jakar hannuna akan kujera daya dake dakin na zube akan gado ina ajiyar numfashi.





*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:31 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*24*


_Follow me on wattpad *@Jeeedorhh*_


Ana kiran sallah Mommy ta leko dakina tace in fito Daddy zai ja mu sallah, sai lokacin na tashi daga kwanciyar da nayi na shiga bayi na dauro alwala na fito, dogon hijabi na dauka na tafi dakin Daddy. Wani dan karamin dakine a cikin dakin shi wanda yake aiwatar da ibadojin shi a ciki, dakin lullube yake da darduma sai tashin kamshi yake yi, shelves shelves na littafan addini a gefe a shirye gwanin ban sha'awa. Daddy ya ja mu sallah, muna gamawa ni da Mommy muka dauko littafin Arrijalu Wan-nisa'u fil Jannah Daddy ya ja mana karatu har aka kira sallar Ishai muka yi. Muka fita zamu yi dinner amma abinci fa yace sam bai ga wajen zama a cikina ba, Mommy ta kalli yadda nake ta juya cokali a cikin Irish Supper data mana wanda yana daya daga cikin favorites dina, na tabbata saboda ni tayi shi amma na kasa ci, tace "Baby lafiyan ki lau kuwa kin kasa cin abinci?" Daddy ya dago yana kallona, cikin sauri na girgiza kai nace "m fine Mom, cikina ne a cike kawai" Daddy ya tsiyayo Pineapple and coconut juice da Mommyn ta hada ya miko min, na amsa tare da kaiwa bakina na kur6a, aikuwa har da lumshe idanuna saboda gardi da sanyin daya ratsa ni, da taimakon lemun na dan samu na kara tura abincin haka nan kafin na musu sai da safe na tafi dakina. Ina shiga na fara kokarin kimtsa kayana cikin wardrobe duk a kokarina na kauda tunanikan dake dankare a cikin raina. Na janyo handbag dita ina kokarin rataye ta a bags rack naji nauyi a ciki, cike da mamaki na zura hannuna ciki na fito da karamar jakar da Abbu ya bani da safe, a hankali na zauna a gefen gado tare da janyo dan karamin purple akwatin dake ciki, cike da mamaki na fiddo shi ina jujjuya shi a hannuna. Ina budewa na zaro idanu sakamakon wata siririyar sarka dana gani a ciki da dankunnenta har da zobe, sarka doesn't look that out of ordinary but daga ganinta kasan ba karamar sarka bace. Hannuna rawa ya shiga yi na rasa abinda zanyi, tashi nayi da dan akwatin a hannuna na fita falo, su Daddy suna zaune suna kallo duk suka bini da kallo, na zauna a gefen Daddy tare da mika mishi akwatin nace Abbu ne ya bani dazu, da mamaki Daddy ya karbi akwatin yana jijjiga shi a hannunshi yace "Shi Ibrahim din ne ya baki wannan sarkar?" na gyada kai a hankali, ni kaina na kasa yarda da hakan gani nake kamar a mafarki, Daddy yace "amma me yasa?" na jijjiga kai "nima ban Sani ba Dad kawai bani yayi" Mommy ta karbi sarkar itama ta dudduba, ta kalli Daddy tace "da alamun sarkar Babba ce fa Habibiy, Anya zamu karba kuwa?" Daddy yace "abinda nake tunani kenan exactly..." yace min "ki je daki ki kwanta, da safe zan tuntube Ibrahim din inji" nace "toh" na musu sai da safe na wuce dakina. Ina kwanciya barci ya kwashe ni, after all it has been one exhausting and stressful day.
Washegari Daddy ya dawo min da sarkar da Abbu ya bani, ban tambayi abinda ya cewa Abbu ba ni dai yana bani na bude na zura zoben a cikin yatsa na. A ranar sai ga Anty Ameenah ta kira ni, korafi ta min akan na tafi ba tare dana musu sallama ba, hakuri nayi ta bata akan cewa Lokaci ne ban samu ba, bata hakura ba sai dana dauki alkawarin cewa zan je gidanta musamman sannan. Bayan mun gama wayar shiru nayi ina kallon wayar a raina ina tuhumar kaina akan ba mutane false hope na ganina da ziyartar su bayan nasan cewa ba haka bane a cikin raina.

Nayi shiru akan gado duk kadaici ya ishe ni, a raina na raya da ace a gidan Abbu nake da war haka ko dai muna hira dasu Hafsy, ina kicin ina girki ko kuma muna wasa a gym kamar yadda muka saba kwanan nan idan bama aikin komi. Wayata na janyo na latso lambar Abbu, sai kuma na kasa danna mishi kiran, a raina ina mamakin kaina me zan ce mishi ne idan ya dauka? Me zan ce mishi ne dalilin da yasa na kira shi?? Kawai sai na maida akalar wayar zuwa ga Anty Mubeenah, ta shiga tayi ta ringing amma ba a dauka ba, shiru na bata mintuna biyar ko zata kira amma bata kira ba sai na kira wayar Abdullahi, cikin ikon Allah ya dauka, cike da doki muka gaida dashi. Nace ya bani Hafsy mu gaisa yace ai tana gida yau bata je makaranta ba, nace me yasa? Yace ai Tun jiya take kukan Ita lallai sai an kawo ta wajena shine yau ta tashi da zazzabi, a raina naji ba dadi don haka nace idan sun koma gida ya kira ni yace toh. Yana kashe wayar na kira Ni'ima, muna gama gaisawa tace "yanzu kuwa Babban Yaya ya bar nan" nayi jim ina kokarin yin maraba da sunan shi da naji ta ambata, haka kawai naji zuciyata ta dauki bugu da karfi, "umh ya su Mama?" nayi Kokari na kauda hirar Abbu da take kokarin sakowa amma duk da haka ban tsira ba, "next week ne bikin bude kamfanin shi a Beijing, how I wish zan samu zuwa" na hangame baki cikin mamaki nace "Da gaske?" tace wallahi kuwa. Nace "Masha Allah! Lallai zan kira shi in taya shi murna, na dade da jin labarin bude kamfanin wajen Bala Malam, ni nayi zaton ma an jima da budewa ashe har yanzu?" tace "kin san dama bude kamfani a kasar waje is not something easy musamman ga wanda yake ba dan kasar ba, don ma abokin aikin nashi haifaffen Beijing din ne shi yasa" na gyada kai. Tace "Hajiyar mu tayi mamakin tafiyar ki fa dazu da Babban Yaya yana gaya mata, tayi ta korafin baki masu bankwana ba" a raina naji babu dadi, sai lokacin naji ban kyauta ba, haka na baro Kano bayan Iyalan Abbu da Anty Haleemah babu wanda na wa sallama, nace "in shaa Allah duk ranar dana kara shigowa Kano zan zo in gaishe ta" tace better! Muka dan kara hira kafin muka yi sallama. Later in the evening Daddy ya dauke mu muka fita yawon gari, shiga nan fita nan har gidan Anty Uwani muka je acan ma muka yi sallar Magriba kafin muka juyo gida.

Sai dana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login