Showing 18001 words to 21000 words out of 47794 words
Chapter 7 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt
A
Da gudu na karasa wajen shi na riko hannunshi dake rike da brief case, tambayoyi nake watsa mishi ba kakkautawa, "Abbu lafiya? Abbu mai ya samu kafar ka? Abbu accident kayi a kan hanya?!....." ya zauna akan kujera yana maida numfashi, "it's just a minor targade, an gyara min. Kar ki damu" jin hanyaniya su Hafsy duk suka fito daga dakunan su, ganin halin da yake ciki tuni Hafsy ta fara kuka, sai da Abbu ya jata jikinshi ya rarrashe ta sannan tayi shiru. Ya kallemu duk munyi carko-carko a gabanshi muna muzurai, bai san sanda ya saki dan murmushi ba. "nace muku lafiya ta lau guys, oya Nafeesah dauko min abinci anan zan ci" jiki ba kuzari na koma na zubo mishi iya wanda zai iya ci na dora akan karamin coffee table na kai mishi, na koma kicin na dauko ruwa shima na ajiye mishi. Mu kuma muka koma kan dinning table muna cin abincin amma fa hankulan mu suna kanshi, muna cikin ci Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, hankalina yana kanta har ta tsaya kusa da Abbu kamar suna yin magana ne, ta kalli kafar shi da yake nuna mata ta yi magana kafin ta nufo kan dinning din. Duk muka gaishe ta kafin muka koma wa cin abincin mu. Muna gamawa na tattara komi na kai kicin na wanke kayan tas na dawo falo, Abbu baya falon, na zauna ni dasu Abdullahi muka danyi kallo kafin na musu sallama na tafi dakina. Shirin kwanciya barci nayi na janyo wayana na shiga chats da friends dina ta whatsapp, dp din Muneer naga ya dora hoton wata kyakkyawar yarinya matashiya da alamun ta dan girme ni, naji wani abu ya soke ni a makogaro, kasa daurewa nayi na tura mishi tambayar "who is she?" mintuna biyu kyawawa kafin reply ya shigo, "a sister" nayi ajiyar numfashi lokacin dana ji wani sukuni yana ratsa ni, "Ohh! Ashe sistern ka ce.... Ya kake?" muka danyi chatting sama sama kafin ya min sai da safe wai barci yake ji, ni kuwa har da tura mishi hearts da clouds. Yana sauka nima na kashe wayana don dama saboda shi na tsaya.
Washegari ta kama daya ga watan mayu, public holiday ne don haka muna gida. Sai wajen karfe goma na fito daga dakina, nayi break fast na koma daki nayi wanka na sake fitowa falon. Su Qaseem suna zaune yanzu suna game, na zauna a tsakiyar su muka fara bugawa. Muna nan zaune muka ci karan intercom, Abdullahi yaje ya bude, sai gasu sun shigo shi da Aunty Ameenah. Da sauri na mike tsaye ina mata sannu da zuwa har ta zauna akan kujera, na shiga kicin na dauko mata lemu da ruwa na kawo mata, gaishe ta nayi ta amsa da fara'ar ta na koma gefe inan kallonta, wannan shine karo na farko da naga wani dan uwan Abbu a gidan tunda nazo. Qaseem ta tura yaje ya gayawa Abbu tazo, tare suke fito dashi, har yanzu yana dingisa kafar shi. Na bishi da kallo cike da tausayi har ya zauna, na gaida shi tare da mishi ya jiki ya amsa. Aunty Ameenah tace "tare muka zo da Abban Ikhlas, zai shigo ya duba maka kafar" na kai dubana ga kafar tashi, sai da cikina ya kada ganin yadda kafar ta kumbura suntum! Ya yamutsa fuska "kema na fada miki ba wani abu bane ba, targade ne an gyara min shi kuma, kumburin saboda targaden ya dade a jikina ne shi yasa" ta Harare shi, "ai ba cewa nayi kayi lecturing dina ba koh?" ta daga wayarta ta kira wata lamba, ba a jima ba wani kamilallen mutum da zai yi sa'an daddy na ya shigo falon, ya ba Abbu hannu suka gaisa. Kafar tashi ya kalla yana girgiza kai, "Anya haka zamu yi da kai kuwa Farfesa?" Abbu ya rausayar da kai kamar wani karamin yaro, "Abban Ikhlas kawai neman rigima ne irin na matar nan taka, sai dana fada mata targade ne amma taki yarda" ya kara kallon wajen, "anya targade anan wajen kuwa? Bari dai mu duba mu gani" ya fiddo kayan aiki, wata er karamar naura ya fiddo ya jona da wani abu, ya kara abun a kafar Abbu sai ga komi na kafar dake kasan fatar shi ya fito a jikin na'urar, amma babu abinda muka fahimta tunda ba profession dinmu bane, ya gama dube-dubenshi ya daga ido ya kalli matar shi, "tsagewar kashi ce!!" ta zaro idanu yayin dana dafe kirji, yace yanzu bari in kira mai gyara yazo tukun. Muna nan zaune jugum-jugum har mai gyaran yazo, har kuma zuwa lokacin bamu ga ko giccin Anty Mubeenah a cikin falon ba. Wani dan tsamurmurin farin dattijo ya shigo falon, maigadi wanda ya rako shi ya duba jikin uban gidan shi kafin ya juya ya fita. Mai gyaran ya fiddo kayan aiki ya fara, yana taba kafar Abbu na saki kara saidsai da duk suka juyo suka kalleni, jikina rawa yake, tsigar jikina tana tashi, Ji nake kamar nice naji ciwon. Abbu yace mu tashi mu koma daki amma fir naki, ganin mun ki tashi yasa ya kyale mu. Tunda aka fara gyaran kuka nake har da jan shessheka, ganin ina kuka sai Hafsy itama ta fara, nan da nan falon ya karade da kukan mu ni da ita, Anty Ameenah dariya ma ta hana ta lallashe mu. Mai gyaran ya gama gyaran da zai yi yawanci fara maida tarkacen kayan gyaran cikin jaka yana dan murmushi, "da alamun amaryar ce koh?" ya tambaya yana kallon Abbu, kusan a lokaci guda shi da Aunty Ameenah suka ce "ehhh?? Aah!!" ya bisu da kallon mamaki kafin ya murmusa yace to Allah ya kara sauki. Ya dauki jakarshi ya saba a kafada ya mike, mijin Anty Ameenah ta rufa mishi baya. Abbu ya kalleni a sanyaye, "bani ruwa Nafeesah!" da sauri na mike har ina hardewa, na dauko ruwan na kawo mishi na koma kusa da Hafsy na zauna.
[12/8, 7:35 PM] +234 813 546 1890: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*15*
*'In a nation where the Poor face hardships, suffering and fears, only the riches and the one's that has power lives in peace, thrives and prospers....... Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Ya Ibaadullaheessaaliheen!!!......'*
Sai gab da Magriba su Anty Ameenah suka mana sallama zasu tafi, na leka dakin Anty Mubeenah wadda tunda aka kira sallar la'asar ta tashi da niyar zuwa tayi sallah bata dawo ba, na gaya mata zasu tafi ta leko suka yi sallama ta koma dakinta. Ni dasu Hafsy har Abbu mai kafa sai da muka taka musu har gaban motar da Anty Rahina tazo da ita. Anty Ameenah ta kalleni na goya baby Jameel a bayana yana ta shakar barci abin shi, tayi murmushi cike da tsokana tace "to Hajiya Nafee a bamu baby din koh?" na fara kokarin sauke yaron daga bayana, "Allah Anty ji nake kamar ku bar min shi!" su duka suka kwashe da dariya, Anty Raliya tace "kina son yara ne har haka?" nayi dan murmushi, "sosai ma! Amma mommy taki ta haifo mana wasu" na karasa ina pouting kamar inyi kuka dana tuno diramar da muke sha da ita idan ina mata maganar me yasa bata kara haihuwa daga kaina ba? Sai tace ai Allah ne bai kawo ba, ranar nan ma dana takura mata da tambaya zagi ta dankara min tace in cewa daddy na ya karo aure mana sai a Haifa min yaran, na tuna lokacin kuka na fashe dashi saboda zagin data min, shi kuwa daddy dariya ya dinga mana. Daga ranar ban kara mata korafi ba, sai dai in yiwa daddy. Su Anty Ameenah kam dariya suke min, sun fahimci tsantsan yarinta da sokancin da aka san Yaya irinmu nayi a tare dani. Anty Ameenah tace "Kar ki damu, in shaa Allah kema zaki haifi naki, kinga kin huta kenan koh?" na gyada kaina ina murmushi, "daddy ma haka yace ranar nan!" suka kara sakin dariya kafin suka shiga motar, na mikawa Anty Ameenah babyn tare da maida murfin motar na rufe mata tare da daga musu hannu, suka ja motar suka tafi. Na dan saci kallon Abbu kallona yake sosai with astonishment in his eyes, murmushi yake yi kamar kunnen shi zai zage, na samu kaina da tambayar dalilin sudden change dinshi curiously. Na kama hannun Hafsy muka koma cikin gida ya biyomu a baya. Muna gama dinner na musu sai da safe na koma dakina, sosai nake jina a gajiye ga wani barci daya rufe min idanu.
Kwana uku muna jinyar Abbu ni da yaran shi, ba laifi ya warke duk da cewa bai fara fita ba, kuma har zuwa lokacin Tafiyar shi bata koma irin ta normal people ba. Cikin wannan lokacin mun ga jama'ah ba kadan ba, ko wace rana sai mun ga bakin fuska cikin masu zuwa duba shi gaskiya Abbu yana da jama'ah sosai. Saurayin Ni'ima zai kawo mata ziyara ranar alhamis, ranar a lab muka wuni tare dasu suna jira mu tashi su wuce gidan su dani, na gaya musu Abbu ya hana ni yawo amma ina! Suka ce they wouldn't take no for an answer, dole suka saka ni kiran shi. Na fita daga cikin lab din bayan na danna mishi kira, bugawa daya biyu ya dauka ana uku, a sanyaye na gaida shi tare da tambayar jikinshi ya amsa da lafiya, nayi shiru ina kamo bakin zaren daga inda zan mishi maganar har sai daya tambaye ni ya? Sannan na gaya mishi kamar wadda take tsoron tayi maganar, shiru ya biyo baya kafin ajiyar numfashi mai nauyi, "amma kada ki wuce karfe bakwai baki dawo ba" da sauri nace "in shaa Allahu Abbu" daga nan muka yi sallama. Ranar tun kafin lokacin tashin mu yayi muka tafi. Unguwar Galadanchi muka nufa, ashe mahaifin su shi yake rike da sarautar Galadanchi ta garin Kano, babban gida ne wanda ginin shi na asalin gidajen sarauta ne, sashen Hajiya Fati muka fara shiga ita ce mace ta biyu a gidan, mace mai karimci ta tarbe mu da faraarta, na kula su Ni'ima kamar babbar Yaya suka dauketa don a sashenta ma suka ce zasu saukar da Bashir din. Cike da girmamawa na gaidata ta amsa da fara'ar ta tare da sawa aka kawo mana ruwa, mun dan jima a sashen nata kafin muka mata sallama muka wuce sashen Hajiya Siyama mahaifiyar su Abbu. Sashen nata in ka shiga baka taba cewa dakin er dattijuwa ka shiga duk da cewa shima sashen Hajiya Fati babu laifi. Babban falo ne wanda yasha saitin royal kujeru ruwan zuma, muka zube a kan wani tattausan carpet muna gaishe ta tana zaune akan sallaya tana lazumi, kana ganin kamilalliyar fuskarta zaka san cewa ka kalli fuskar ma'abociyar addini, babu abinda Abbu ya baro nata sai dogon siririn hancinshi, ita nata yana da dan fadi, sai data gama lazuminta kafin ta amsa mana cike da kulawa. Daga nan su Ni'ima suka jani muka je dakin su muka yi sallah, kayan jikina na canza muka shiga kicin muka fara shirya kayan abinci kala kala. Na bata shawarar mu yi snacks wanda zamu basu a matsayin tsaraba idan zasu tafi gobe, don haka muka yi doughnuts wanda muka yi icing dinshi muka watsa shredded cheese da chocolate akai. Karfe biyar suka karaso shi da abokin shi, mun riga mun kai komi sashen Hajiya Fati, mun shirya koina sai kamshi kawai dake tashi a wajen. Ita uwar gida ta musu rakiya zuwa inda aka tanadar musu mu kuma muka tsaya karasa gyara kicin din, sai da muka gama gyaran jikinmu sannan muka je muka gaisa dasu. Bashir din nata kamar yanda take fada dan kyakkyawa dashi ga barkwanci, abokin nashi ne ma bai mun ba ko kadan, sai wani shisshige min yake yi yana jana da hira duk ya takura min don haka na mike nace musu zan wuce gida, duk suka kalleni da mamaki ni kuwa Na Kauda kaina gefe don ma kar suga fuskar hana ni tafiya. Sa'adiya ta taso ta kama hannuna muka fita, abokin Bashir da naji yana kira da Fahad ya taso ya biyo mu, ganin babu fuska yasa ya juya. Na saki tsaki kasa kasa, Sa'adiya tayi dariya tace da alamun gayen bai miki ba, kai kawai na girgiza mata muka wuce sashen Hajiya Siyama. Tana kan daya daga cikin kujerun falon tana kallon tashar Saudi, ta kalle mu cike da mamaki, "lafiya dai ko?" Sa'adiya tace "wai gida tace zata wuce!" tace Haba ai kin tsaya kici abinci koh?" nace "Hajiya Abbu...." tayi saurin katse ni, "kyale shi kawai, ba zaki tafi ba sai kinci abinci fa" bani da zabi dole na wuce dakin su Ni'ima don bazan iya komawa wajen su nataccen abokin Bashir ba kuma bazan iya zama kusa da Hajiyar ba.
Sai wajen karfe bakwai da rabi sannan muka fito ni da direban da xai maida ni gida, bayan naci tuwon tsakin masara da miyar kalkashi wadda taji yajin daddawa, tantakwashi da man shanu ga kunun aya mai sanyi da Gardi a gefe. Tare dasu Ni'ima muka ci abincin bayan Tafiyar su Bashir, ta bude tarkacen kayan tsarabar daya kawo mata ta ciro min kayan shafa, turare ne da kayan makulashe naki amsa, sai da suka yi kamar zasu yi fushi sannan na saka hannu na dauko turaren 'splendid' tsohon turarena ne tun a secondary school, daga baya ya bata na gaji da nema na komawa kamfanin lily cool, Sa'adiya ta kara min da tarkacen sweets muka fita falo. Kicin na shiga na dauko doughnuts din dana debar wa su Hafsy, Hajiya na falon a zaune na durkusa a kusa da ita na mata sallama, ta min godiya sosai har sai dana ji kamar in nutse a kasa. Ta mikawa Ni'ima wata karamar silver grey din jaka tace ta bani, na mata godiya sosai kafin muka tashi, sai da muka je ta sashen Hajiya Fati na mata sallama kafin muka fita waje inda direba yake jira na, na shiga motar muka kara yin sallama dasu kafin muka tafi. Nayi shiru a bayan mota ina tunanin abinda zan fadawa Abbu, a raina addua nake ina karawa akan kada Allah yasa yayi fushi dani, naki jinin fushin Abbu kamar yadda na tsani bacin ranshi. Har cikin gida direba ya shiga dani, na fito daga motar ina mishi godiya tare da sai da safe, iska ake yi sosai kamar ta dauki mutum tayi yawo dashi, idanuna a rufe saboda kasar da iskar guguwa ta watsa min na shiga falon bakina dauke da addu'ar da ake yi idan guguwa ta tashi, kamar hadin baki ina shiga aka dauke wuta. Na bude idanuna da kyar ina murza su, kafin inyi adjusting da dan guntun hasken falon wanda ya ratso ta cikin shara-sharan labulayen dakin daga farfajiyar gidan wanda lantarkin solar ta samo dashi, naji kafana tayi stepping akan wani abu mai tsananin sul6i, kafin in tantance meye naji ni na fara tafiya sululuuuu.....!! A tsakiyar dakin, na kwala ihu sosai ina salati tare da laluben abinda zan kama in rike tunanin farko daya fado min a cikin raina shine hango ni da nayi na kai da bakina, kyawawan kananun hakora na guda biyu na gaba malale a cikin jinin dake fita daga bakina....... Karo na kaiwa wasu hard muscled chest wadanda ko a cikin duniyar mafarkina ban taba hangoni a kansu ba, sai ga gangar jikina a jikinsu yau kamar a mafarki, dogayen tausasan hannuwa suka zagaye bayana, daya a kuguna daya a gadon bayana, jikina yake dauki rawa kamar wadda ta rungumi kankara cikin hunturun sanyi yayin da naji wasu dogayen zara-zaran yatsu suna suna tapping din gadon bayana a hankali., ban san lokacin dana saki ledojin hannuna, purse dina da wayata akan tiles din dake cikin falon ba.....!!.
*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:36 PM] +234 813 546 1890: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*16*
*-Search across the Oceans for who are been lost for two long......*
*'Searching for a secret in coming home we find we have what we need.....!'*
*-New Empire-* _Across the Ocean_
Hankalina gabadaya ya dauke daga jikina, babu abinda nake fahimta sai tattausan kamshin dake fita daga jikin Abbu, bugawar da zuciyar shi take yi da dan sauri-sauri, dumin dake fita daga jikinshi....... Ya dago fuskata daga jikinshi yana kallona kamar hadin baki, aka dawo da wuta lokacin. Na samu kaina starring at his brown oily eyes da suke wani irin sheki kamar zaiba, "Nafee, are you ok??" cikin daukewar tunani na daga baki nace "umh???" ba tare dana yi kokarin dauke idanuna daga kanshi ba, ya dan jijjiga kafadata, "hey!" kamar wadda aka daddaba daga barci, nayi firgigit ina kallon cikin falon, Ya Allahu! What the heck just happened?? Da sauri na durkusa na tattara kayana da suka zube nayi hanyar