Showing 6001 words to 9000 words out of 47794 words
Chapter 3 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt
isha'i sai ki dawo mu yi" da murnarta ta tashi ta tafi, har ta kai bakin kofa ta dawo da gudu ta rungume ni, "Aunty thank u" dariya nayi na bita da kallo har ta bar dakin, kai na girgiza na tashi na fada bandaki.
Bayan sallar isha'i ina kan sallaya a zaune Qaseem yayi sallama ya shigo dakin, yace Aunty Nafeesah wae Mami tace kizo mu ci abinci, ba musu na tashi nabi bayanshi don dama yunwa nake ji. A kan dinning na samesu su duka suna cin abinci, gefen Hafsat naja kujera na zauna. Ganin kowa serving din kanshi yake yi yasa na dauki plate na bude flask din abincin, tuwo ne kaman na semovita miyar danyen kubewa, tunda naga miyar tsululu kamar ba danyen kubewa ba nasan cewa tuwon sai a hankali, Illa kuwa ina kai loma daya bakina da kyar na hadiye, tuwon gashi nan latab kamar danyen gari alamun bai gama dahuwa ba, miyar sai dan banzan yaji kamar da taruhu kadai aka yi ta, babu taste ko na anini sai shegen karnin kifi. Da kyar na iya hadiye lomar farko, ban yi kuskuren kai wata bakina ba don na tabbata idan na kuskure ta sake shiga bakina sai na amayar da dan guntun abincin daya rage a cikina. Su kansu na ga tsakura kawai suke yi, kallonsu kawai nake yi cike da mamaki. Ta ya za ayi mutane su rayu da irin wannan abincin a duniya? Koda yake yau ne karo na farko dana ci abincin gidan, ban sani ba kila rana ce ta bacewa mai girkin kawai, da wannan tunanin na gyada kaina na tashi daga kan table din bayan na wa Anty Mubeenah sai da safe. Dakina na koma naje nayi brush na wanke bakin da mouth wash, cikina wani irin hautsinawa yake yi saboda yunwa, jikar dana fita da ita dazu na bude, wata irin ajiyar zuciya na sake ganin Pack din cookies din New Yorkers, na manta dashi ma ni shaf dazu muka saye shi a cikin makaranta. Zama nayi akan gado na bude shi na fara ci, wayata na hannuna ina chatting, Hafsat ta shigo dakin. Tare da ita muka cinye cookies din, daga nan na koya mata aikin da aka basu, kallon film dina da nake kallo muka ci gaba dayi sai wajen karfe goma da rabi ta min sai da safe, na shafa kanta nace ki tashi lafiya pretty., kar ki manta pa kiyi addu'ar kwanciya barci kinji? Ta gyada kai, "thank u Aunty, sai da safe" na dan hade fuskata, "ohh pretty, sau nawa zan gaya miki bana son Aunty dinnan? Call me Yaya Nafee, bai fi dadi ba?" ta girgiza kai cikin tsokana, "babu dadi gaskiya" kofar dakin na nuna mata "oya, bi can sai da safe" ba musu ta tashi ta fita tana er dariya kasa-kasa. Tana fita na janyo wayata ina kallon screen din, a cikin messages nake ina shawara da zuciya ta akan abinda nake shirin aikatawa, daga karshe dai nayi typing, *"you sleep?"* na turawa Muneer, tsawon mintuna sha biyar babu amsa, na sake tura *"seems like you are, good night!"* na kashe wayar na dorata akan bedside table na kashe wuta tare da yin addu'ar kwanciya barci na kwanta.
*♡Jeedderh♡*
[12/9, 8:40 PM] +234 816 965 3238: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*
©JeedderhLawalS
*06*
Nayi tunanin idan na tashi zan ga reply daga Muneer ko kuma missed call dinshi, sai dai har na gama shirina tsab babu shi babu alamun shi. Sai zuwa lokacin ne na fahimci imma dai yana sane yaki min reply jiya ko kuma yayi barci wulakanci ne ya hana ya biyo sahuna da safe, kwafa nayi ina jijjiga kai.
Ranar ma dai abincin safen sai godiyar Allah, plaintain ne aka soya da shayi da soyayyen kwai, tsakani na da Allah nasan ba zan iya cin abincin nan ba, haka nan dai na dan tsakura har zuwa lokacin da Bala yazo muka dunguma gaba daya har su Hafsat muka fita. A mota daya muka tafi dasu, sai da muka biya ta makarantar su muka ajiye su sannan muka wuce. Da rana koda muka dawo bamu samu Anti Mubeenah a gidan ba, har dare bata dawo ba sai bayan isha'i likis sannan. A zaman sati dayan da nayi a gidan zan iya cewa zama ne na takura, if not for Hafsat dasu Abdul I didn't think I would've survived. ita dai matar gidan yadda na kula da ita, bata cika jan mutane a jikinta ba, ni dai tunda nazo gidan ban ga bare ya leko ba, makota ne, abokai ko dangi. Tsakanina da ita gaisawa ne kawai, idan mun hadu a dinning mu danyi hira sama-sama, ga yawo, idan ta saka Kafa ta fita daga gidan tun safe sai dare take dawowa duk da Hindatu mai aikinsu naji tace tana da saloon da take kula dashi. GA er aikinsu kuwa ban ma san me zan ce ba, ni ban ga dalilin da zai sa in dauko er aiki ba kuma ba zata min gamsasshen aiki ba in kyaleta duk da cewa ni har ga Allah I dont have any plan na daukar er aiki Ina nayi aure, ga Hindatu dai kam abin babu bayani, ita ba ga girki ba, ita ba ga gyare-gyare ba. Aikin data iya daya; ta sha kona sanwa idan ta dora ta fara kallo.
A takaice dai kafin zagayowar ranar juma'a sai da naji Kano ta fita daga raina, ni ban saba irin rayuwar kadaici dinnan ba. Ranar juma'ar kuwa Ina dawowa daga wajen IT dama dan karamin kit dina a Shirye yake tsab, Anty ta fita yawon data saba sai sako na bari a wajen Hindatu nace tace mata na tafi weekend gida, dama Daddy ya turo wanda zai dauke ni, a farfajiyar gidan ma na dawo na tarar dashi yana jirana don haka babu bata lokaci muka wuce Kaduna. Sai wajen karfe biyar da rabi muka isa gida saboda yanayin go slow da muka samu a hanya kafin mu fita daga cikin Kano, da ihu na da komi na shiga gidan, kit dinma sai driver ne ya shigo min dashi. Mommy tana kicin tana girki ita kadai, na rungumota ta baya ina tsallen murna, juyowa tayi tana kallona cikin murmushi, "oh ni wannan yarinya tawa ban san yaushe zata girma ba" na buga kafa cike da shagwaba nace "mommy!!" dariya tayi ta rungumo ni jikinta cikin nuna kewa. Dakina na shiga an share min shi tass sai tashin kamshi yake yi, na cire kayan jikina na fita zuwa kicin na kamawa Mommy girkin, muna yi muna hira, yawancinta tambaya ce akan wajen da nake zaune, babu matsala dai ko? Kina cin abinci? Tambayoyi dai iri-iri. Muna nan Daddy ya dawo, har cikin kicin din ya shigo ya daga ni sama Cak yana juyi dani, dariya na saki na rirrike shi har ya dire ni kasa. Sannu da zuwa na mishi ya amsa yana shafa kaina, na amsa brief case din hannunshi na raka shi har dakin shi kafin na fito na barshi ya shirya.
Bayan isha'i muna falo zaune akan babbar tabarmar cin abinci, hira nake musu, duk abinda nake yi a Kano babu wanda ban tsallake ba, su kuma suna sauraro cikin nuna rashin gajiyawa na dariya su yi, na mamaki kuma su jinjina kai. Ranar kam sai wajen karfe sha daya muka yi barci muna ta hirar yaushe gamo. Kwana na biyu a gida na koma Kano cike da kewar iyayena, ji nake kamar inyi zama na acan.
Hindatu kadai na samu a gidan, tace yaran dama a gidan kakannin su suke yin weekend, ita kuma Anty Mubeenah tace wajen bikin kanwarta mawuyaci ne ma idan ba kwana zata yi a can ba, na jinjina kai tare da kwaso tsarabar fruits dana musu a hanya na shirya su a cikin fridge. Wajen karfe takwas na dare ina zaune gidan shiru babu motsin kowa, nasan da su Hafsat suna nan da yanzu suna dakin ko dai muna hira ko kallo ko kuma ina koya musu assignment. Horn din mota naji a bakin gate kafin naji karar bude gate, a raina nace Anty Mubeenah ta dawo kenan. Hasken motar ya ratso ta cikin windown dakina zuwa cikin labulaye na da yake window din dakin a kusa da garejin gidan take. Minti kamar biyar na bata na tashi na fita da niyar inje in mata sannu da zuwa. Tsaye a jikin fridge hannunshi dauke da gorar ruwan Sanah yana sha directly daga cikin gorar, hannunshi daya rataye da suit dinshi yana kuma rike da brief case. Dogo ne ba can ba, idan da ba don na sanshi a hoto ba to da zan iya rantsewa da Allah ince bashi bane, saboda ko a cikin hoton ban hangi yarintar dana gani a tattare dashi ba a lokacin, da nace yarinta ba wai ina nufin yaro bane, aah Ina nufin wanda bai kai girman daddy na ba; Abban su Hafsat ne. Wata irin gigicewa naji nayi, haka kawai naji kafafuna sun yi wani irin sanyi wanda ban iya daurewa ba sai dana dangana gwiwoyina da marble din dake malale a tsakiyar falon, ban sani ba tsabar kwarjinin da yayi min ne yasa gabana ya tsananta faduwa ko kuwa wani abu daban?? Cikin rawar murya nace "sannnnnu da..... Zuwa...... Abbbbuh!!".........
*♡Jeedderh♡*
[12/9, 8:45 PM] +234 816 965 3238: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*07*
_*"There are no rules when it comes to love. I just let love surprise me because you never know who you're going to fall in love with. You never know who's going to come into your life.....*_ ___Taylor Swift.
Wasu kyawawan idanu farare tas suka dago suka kalleni, ban sani ba ko tsananin hasken da falon yayi ne ta dalilin hasken chandeliers din falon ko kuwa idanunshi ne a haka? Brown eyelids suna ta wani sparkling da sheki, haka kawai na tsinci kaina da faduwar gaba. Ya sauke robar ruwan daga bakinshi ya jefa ta cikin waste bin tare da cewa, "lafiya qalau Nafeesah! Kin zo bana gari koh? Hope komi lafiya?" na gyada kaina da kyar, wani irin nauyin mutumin naji ya dabaibaye ni. Ya gyada kai, "OK!" ya wuce dakin Anty Mubeenah abin shi. Kafa na na masifar rawa na tashi na fada daki, hannuna dafe da kirjina kamar wadda take kokarin tsayar da racing din da zuciya na take yi wanda ya wuce misali. Idanu na zare sosai ina kallon reflection dina a jikin mirror, I couldn't believe wai a haka na fita gaban Abbu. Kafar wando na daya a gwiwa, gashin kaina wani yayi baya, wani ya zubo a kafaduna, wani kuma ya tattare a gaban goshina saboda hular dana saka., idan ka ganni dai a lokacin babu bata lokaci zaka danganta ni da psychiatric patient dinnan irin stage one ma, kunya ta rufe ni sosai kamar in nutse a kasa haka naji. Tsalle nayi na dira akan gado na fara birgima, sai da nayi kaca-kaca da gadon sannan na saurara ina maida numfashi...
Karfe bakwai da mintuna biyar na safe na fito daga dakina a shirye na tsab, babu kowa a cikin falon. Kan dinning an shirya kuloli manya masu kyau, kila saboda dawowar maigidan ne aka fiddo sabbin kuloli don ban taba ganin irin su a gidan ba. Na bude kulolin, farfesun kan sa ne sai kamshin er daddawa da tafarnuwa yake yi, sai masa fara tas itama tana ta tururi a cikin wata kula, kunun gyada har da kosai. Kujera naja na zauna na zuba farfesun na fara ci kunnena har motsi yake yi, duk yadda aka yi abincin ba daga cikin gidan yake ba, idan ma daga gidan yake to ba Harira er aikin su bace ta dafa. A raina nace kila Anty Mubeenah ce ta dafa, Amma koda wasa ban ji kamshi yana tashi ba jiya ai. Na dai ture tunanin komi na ci gaba da dura abinci abu na, ina nan zaune na kusa gamawa Anti Mubeenah ta fito daga dakinta sanye da wando da riga na barci, ni kaina ina mace sai da shigar ta bani haushi. Gabadaya kirar ta marar fasali ta fita, tumbinta da zai sa kayi tunanin cikin en biyu ne ya fito yayi nashe-nashe a gaban ta, gashin kanta yayi buzu-buzu dan ma wai tana da yalwar gashi babu laifi, fuskarta sai naso take yi bana tunanin tunda ta tashi da safe ta wanke ta. Nayi kokarin kauda takaicin ta daya taso min na gaishe ta, ta amsa a kaikaice tana wani basarwa irin yadda take amsa min ta bude kofar dake fuskantar dakinta ta shiga, ina tunanin nan ne dakin maigidan don ban taba ganin ta shiga ciki ba tunda nazo gidan. Ni dai na gama cin abinci na na wuce abina. A farfajiyar gidan Malam Bala yana jira na, cike da girmamawa na gaida shi na bude bayan motar da kaina na shiga saboda na hana shi ya dinga bude min. Y'all ja motar muka tafi har cikin makaranta, ranar an kai wasu sabbin en IT lab din daga Leather Research Zaria don haka bamu samu cunkushewar ayyuka ba. Cikin dan lokaci muka saba dasu. Ranar tun karfe daya da rabi muka tashi, bayan mun fito daga lab din Zainab da Ikram suka mana sallama suka wuce gida, ni da Ramlah muka zauna a dan karamin garden din da muke zama muna tattaunawa akan saurayinta da yake so ya tura gidansu ita kuma tana ki wai bata so tayi aure yanzu ni kuma ina nuna mata rashin dacewar hakan, muna nan na hangi motar gida tana tunkaro mu duk da ba wadda aka saba kawo ni bace amma nasan duk motocin dake gidan, wannan shine karo na farko ma da aka zo daukar mu da motar, Anty Mubeenah naga tana jan motar. Na tashi muka yi sallama da Ramlah na tunkari motar, sai da nace tazo mu sauke ta tunda gidan su a hanyar mu yake amma tace zata jira Anti Haleemah don haka na kyaleta. Tun daga nesa Hafsatu ta fito daga cikin mota a guje tana min oyoyo, na tare ta da dan guduna muka fara juyi a wajen kamar wata yarinya, sai da muka gaji sannan na ja hannunta muka tunkari motar. Sai dana jira ta shiga sannan nima na shiga, na daga baki da niyar gaida Malam Bala kamar yadda na saba, "Malam Bala barka da war hak.....!" naji maganar ta kakare min sakamakon wanda na gani a gaban motar yana kokarin tada ta, da saurin na sadda kaina kasa tare da cewa "Abbu ina yini?" ya amsa idanunshi na kan titi. Ji nayi kamar wadda aka jefa ni cikin kankara, na kasa maida hirar dasu Qaseem suke min kamar yadda muka saba idan muka taho sai dai in gyada kai ko in bisu da uhm da ehh har muka isa gida. Cikin sauri na bude murfin motar na fita har ina hadawa da tuntube, ban tsaya a ko ina ba sai cikin dakina. Na zauna a gefen gado ina ajiye numfashi da kyar da kyar, ni kam me ke damuna ne haka? Ni dai nasan bani da wahalar sabo da mutane, amma me yasa a gaban mutumin nan nake ji na kamar wata haliita daban? Me yasa na kasa sakewa dashi? Me yasa nake jin kwarjinin mutumin har cikin tsakiyar kaina? Wata zuciyar tace min saboda ban jima da sanin shi bane, after all babban mutum ne kuma idan zan iya tunawa tun daga kan abokan daddy na har zuwa en uwanshi ni dai bude ido nayi na gansu tare, wannan kuwa daga sama kawai na san dashi, hakan da nake ji rashin sanayya ne kawai, idan na saba dashi komi zai daidaita. Da wannan tunanin naji na samu hope, na maida bayana na kwantar akan gadon tare da lumshe idanuna, a hankali barci ya sure ni, nasan biyan bashi ne tunda jiya ban samu nayi barcin kirki ba.
*♡Jeedderh♡*
[12/9, 8:46 PM] +234 816 965 3238: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*08*
*...Then I cross a bridge for over million reasons to hold on.., hide away with me, walk away with me......*
*.....Then I cross a bridge for over million troubles to meet....., nothing is easy, nothing is easy......!* -Savina Drones_Glass Bridge.
Sai wajen karfe biyar da rabi na yamma na tashi daga barcin, toilet na shiga nayi wanka na fito na kimtsa jikina cikin wasu simple Pakistan