Showing 21001 words to 24000 words out of 47794 words
Chapter 8 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt
dakina a sukwane, da sauri ya riko tsintsiyar hannuna, nayi cik ina sauraren abinda zai ce ba tare dana juya na kalleshi ba, "lafiyar ki kuwa Nafeesah?" da sauri na gyada kaina, "lafiya lau, kayi hakuri dan Allah" ina jin sautin murmushin daya saki, ya sakar min hannu dama abinda nake jira kenan don haka na bazama dakina a sukwane. Kofar dakin na maida na rufe tare da murza key, nayi wuri-wuri a tsakiyar dakin kamar wadda take neman wajen buya kafin na zube a kasan dakin akan gwiwa na, zuciyana wani irin gudu take yi, na rasa abinda yake min dadi a lokacin. Ban san iya lokacin dana dauka a wajen ina zaune ba, tare da taimakon Innalillahi.... Dana dinga ja na dan samu sukuni a cikin raina, tashi nayi na fara bandaki na watsa ruwa mai sanyi a jikina duk da sanyin da ake yi sakamakon iskan da aka gama yi. Na fito daure da tawul a jikina na tsaya a gaban mirror, lotion na shafa na saka rigar barci wadda ta tsaya min a gwiwa, duk abinnan da nake yi idanun Abbu suna cikin memory na, na rasa abinda zan yi da zai dauke min tunaninshi daga cikin raina, chatting! Zuciyata ta tuna min, da sauri na tafi inda nayi jifa da kayan hannuna tare da wayar na dauko ta, ina daga ta na dan saki kara ganin yadda screen dinta ya tsattsage, na ciza tattausan lebena na kasa ina ji kamar in dora hannu aka in saki ihu saboda yadda nake son wayata dinnan, bana so ko datti ya hau kanta. Ganin chatting din ma bai mun abinda nake so ba yasa na janyo system dina na kunna na fara kallon Baywatch, ajiyar zuciya na dan saki ganin hankalina ya dauke zuwa ga film din.
Sai Washegari na ba su Hafsy doughnut din dana kawo musu, tare dasu ma muka cinye shi a cikin mota. Yau Daddy da kanshi yazo daukata, yazo duba jikin Abbu ne. Sai da aka yi sallar la'asar muka wuce Kaduna, bakin daddy bai yi shiru ba a hanya yana ta bani labarin kirki da mutunci irin na Abbu, bai san cewa yanzu bana cikin mood din sauraren labarin Abbu bane, ko sunan Abbu aka ambata sai naji faduwar gaba, shi yasa yau nayi duk kokarin da zanyi wajen ganin na kaucewa haduwa dashi, nayi, sai dai dole sai da na ganshi lokacin da muke mishi sallama ni da daddy. Kaina na jinginar da jikin seats din da nake kai na lumshe idanuna kamar mai barci, hakan yasa daddy ya kama bakinshi ya bame har muka isa Kaduna.
Da dare Ni'ima ta kira ni, bayan mun gaisa take fada min wai Fahad dinnan ne abokin Bashir ya dame ta akan ta bashi number na, na tabe baki nace "kada kiyi kuskure bashi Ni'ima" tace me yasa? Nace ban gane ba? Waye a cikin ku bai san cewa Akwai wanda nake dating ba? Taja tsaki, dallah dating ko crushing?? Waye bai san cewa crushing din Muneer kike yi shi baya son ki ba?? Na dan dakata kadan kafin inyi magana, "Ramlah mai bakin Aku!! Ita ta fada muku koh?" daga can tace that doesn't matter ko kadan ai, ni ai zan bashi number! Nace cikin gatse, "ki bashi din toh, zaki gani ne" na katse wayar tare da jifa da ita akan gado. Muneer!! Na maimaita sunan, it's kinda strange. Rana bata taba fita ta koma ga ubangijinta ba ba tare dana tunana bawan Allahn nan a cikin raina ba, amma har ga Allah yau dai, yau gabadaya na manta da existing dinshi a duniya, Anya lafiya ta lau kuwa??! Tashi nayi na koma falo wajen su daddy muka sha hirar mu, sai dana fara hamma sannan na musu sallama na wuce dakina.
Da safe na ba daddy waya na nace a canza min screen din, Koda ya tambaye ni dalilin tsagewar ta cewa nayi faduwa tayi, to me zan ce mishi? Kafin azuhur sai gashi da sabuwar Samsung edge plus, nayi tsalle, nayi ihu na rungume shi, wayar da nake masifar so kenan sai dai bana so in takurawa iyayena da zancen wayar da nasan kudin abincin wani na shekara daya ne, shi yasa nayi shiru, sai gashi yau Allah ya bani ba tare dana roka ba. Daddy kam yasha addu'a ranar kamar bakina zai tsinke, haka nake ni kam, idan aka min kyauta sai in wuni ina wa mutum godiya. Mommy na cewa ta bada ayi fura don na kula Abbu yana so sosai, duk ranar dana kai fura ranar ita ce abincin shi har ta kare. Washegari na doshi hanyar Kano cike da tsaraba don sai da muka shiga shago na saiwa Hafsy dasu Qaseem sannan muka wuce, cike kuma da wani longing, longing to see someone wanda na ma rasa a wane matsayi zan ajiye shi cikin raina., abokin Babana ko kuwa Abokin Rayuwata??!
Aunty Mubeenah da wata kanwarta Shakirah kadai na taras a gidan, ina ga Abbu ya fita zagaya unguwa kamar yadda yake yi lokaci zuwa lokaci da er sandar taimaka tafiya, na durkusa na gaida su, Anty Shakirah ta mun sannu da zuwa har tana tsokanata da ina tsarabar ta tunda Allah yasa tana nan nazo. Matar tana da kirki, duk tafi sauran en uwan Anty Mubeenah da suke zuwa gidan, wasu idan suka zo ko kallon mutane basa yi balle su amsa gaisuwar su, wasu kuwa kallon mutane suke yi kamar kiyashi shi yasa nima bana kula da kurar data debe su. Dariya na dinga yi tana tsokanata, na ciro chocolate din kit-kat babba na bata nace ta kaiwa yara, na ciro wani hadadden turaren wuta na asalin en maiduguri na ba Anty Mubeenah inji Mommy na, ta amsa babu yabo babu fallasa, babu godiya ba komi kamar wadda ta bani ajiya, naji haushin abun ba kadan ba, na mike daga zaunen da nake na dauki jakar hannuna na wuce dakina. Kayayyakina na ciro na shirya komi a inda ya dace, na ciro fura da nonon da aka wa Abbu na Kai fridge na ajiye, daga kicin ina jiyo hirar dasu Anty Shakirah suke yi saboda a falo na biyu suke wanda yafi kusa da kicin din, Anty Shakirah ce take tambayar Anty Mubeenah mai yasa bata son turaren? Tace to mai zanyi dashi? Idan baki so ki bani ai ban rasa wanda zan ba bane, da sauri naji tace ina so wallahi, turaren ne yana da tsada naga gashi yana da wahalar samu shi yasa! Nayi kwafa ina girgiza kaina, wato kyauta ma tayi da turaren wutar da babu yadda ban yi da mommy akan ta bani in kaiwa Anty Haleemah ba mommyn taki ita ala dole sai ita, to ga abinda ya faru nan ai!. Dakina na koma cike da takaici ban jima da shiga ba naji hayaniyar su Hafsy a falo, da sauri na fita. Suna gani na suka kwashi ihun murna duk suka rugo, kowannen su so yake ya rungume ni, ni kam dariya kawai nake ina ihun su sake ni daga cakumar da suka kin kar su kayar dani amma ina! Sai da suka gaji dan kansu sannan suka sake ni, Abbu yana bayansu ya jingina bayan shi da kujera yana kallonmu cikin murmushi, da sauri na zube a kasa ina gaida shi, can kasan zuciya ta wani irin farin ciki yake mintsini na. Yaran naja muka tafi dakina tun kafin inyi abinda zan zo ina dana sani don wani sashen na zuciyata wai rada min inje in rungume shi yake yi. A daki na baza musu tsarabar dana kai musu, nan muka baje muka ci wasu a gun wasu kuma suka diba suka tafi daki lokacin da aka kira Magriba, ni da Hafsy kuma muka yi tamu a daki.
Muna gama dinner na mike da niyar inje in kwanta, Abbu ya kalleni yace "Nafeesah Akwai fura ne?" na gyada kaina a hankali, wata irin kasala ta rufar min saboda yadda ya kira sunana, yace dama min pls. Na wuce kicin na dama mishi furar, nasa ayaba lokacin da nake damawa dana gama kuma na watsa kankara a ciki na dauki bowl din dana juye furar a cikin na koma falo, yana sec parlour a kishingide akan kujera da alamu waya yake amsawa, cikin harshen turanci yake wayar. Na ajiye a gabanshi na fara kokarin zubawa a cikin cup ina satar kallonshi, wayar yake amsawa cike da wata irin yanga yana yi yana wani lumshe ido, accent din turancin shi ko kadan bai yi kama dana bahaushe ba, idan kana ji sai kayi zaton ko rainon kasar Ingila ne, to waya sani? Naji ance a LA ya kammala digiri dinshi na farko. Na danyi murmushi ina girgiza kai, sau tari ina mamakin yadda Abbu yake da yanga kamar wata mace, zaka iya mistaking kace yanga ce kam idan baka zauna dashi ba don a zahirin gaskiya haka yake naturally. Ya ajiye wayar hannunshi akan kujerar yana zama sosai, "what's funny?" da sauri na girgiza kaina "ba komi?" na mika mishi cup din, ya kura min idanu kamar yana so ya karanci abinda ya saka ni murmushin da kanshi, nayi kasa da kaina, ina jin sighing din daya saki kafin ya amshi cup din, da sauri nayi niyar tashi ya tsayar dani ta hanyar tambayana ya Daddy na? Nan fa na zauna na fara zuba mishi labari har na wayar da daddy na ya canza min, ya daga girarshi yana dan murmushi, "inye! Her daddy's girl!!" na sadda kaina kasa ina murmushi in ma zan iya cewa kila har da blushing, ya jefo min tambayar data kada min ciki, "garin yaya har screen din wayarki ya fashe?" na yi wuki-wuki da idanu kamar wadda aka kama tayi karya, ya sake tambayana, kafin in lalubo abinda zan ce wayar shi tayi kara, yana dauka na lallaba na mike da sauri sai dakina. Ina shiga na ajiye numfashi da karfi, Allah ya cece ni yau. Kayan barci na saka, na dauko log book dina na bude na dan dudduba kafin na janyo system dina na cigaba da kallon Pinocchio dana fara yi. Wajen karfe tara da rabi naji wayana tayi kara, na daga ganin bakuwar number yasa na daga da sallamata, daga can wata familiar murya ta amsa sallamar tare da karawa da "gorgeous!" cike da mamaki nace "waye?" sai dana kusa dakin zagi lokacin da naji yace "Fahad ne, abokin Bashir Saurayin Ni'ima" na hade fuska kamar yana gani na, jin nayi shiru yasa yace "gorgeous, baki gane ni bane?" a raina nayi exclamin kalmar 'wai gorgeous!' cike da jin haushi nace na gane ka mana, and please suna na Nafeesah ne ba wani abu wai gorgeous ba ka gane!" ya saki wata dariya data kara kular dani, "Haba gorgeous! To me kin cancanci abinda yafi wannan sunan ma. Kawai ki bani dama in nuna miki how precious you are to me, wallahi tun ranar dana saka ki a idanuna naji cewa na samu macen dana dade ina nema a rayuwata, tun daga ranar na baki wani matsayi mai girma a cikin raina, Gorgeous, wallahi u've become a very special part of my being, you are my happiness, you've got everything I need from my wife you are classy, beautiful, hafiza.....!!" blah-blah-blah ya shiga jero labarai har na gaji da saurare, ganin yaki dasa aya yasa na tsaida shi, "please Malam! Ita wadda ta baka number dina bata yi maka bayanin ina da Mijin aure bane?" ya kara sakin dariya, "ta dai fada min cewa kina da wanda kike so and unfortunately though to my relief baya sonki in return, baby just leave him, bai san ciwonki ba. I promise you zan so ki fiye da yadda yake sonki, na miki alkawarin mantar dake cewa kin so gayen can baby, just give me a chance kinji?" ni kam ina baki? Zuciyata cike da takaicin tonon sililin da Ni'ima ta min. Da kyar na saisaita kaina daga ihun da nake ji a cikin kaina na son in sossoka mishi zagi na dai yi kokari nayi calming din kaina, after all ai ba laifin shi bane, zamu gauraya da mai laifin. Duk da haka ban iya tsaida tsakin daya fito min ba, nace "Malam I don't need your love or whatever trash you are talking about ka gane? Don Allah Kar ka sake kira na!" na kashe wayar da sauri. Ni'ima na kira, cikin sa'a ta dauka a ringing din farko, ko sallama ban bari tayi ba na fara zazzaga mata ruwan masifa, daga farko hakuri ta fara bani, daga kuma sai ta fara tsokanata wai akan ta ma taimake ni? Nace taimakon ki din banza? Nace miki ina so ne? Tace baki fada ba, zuciyar ki ta fada min. Ganin ta maida abun wasa na kashe wayar ina kara maimaita mata ta kira Fahad ne koma uban waye sunan shi ta gaya mishi kada ya sake kiran wayata don duk ranar daya kuma sai naci Mutuncin shi, ita kuma ta jirayi haduwar mu gobe!! Tace "Allah ya kaimu" cike da izgilanci, na kashe wayar ina kwafa. Ajiyar zuciya nake saukewa cike da takaici kamar zan hadiyi zuciyata in mutu. Karan wayata naji, da sauri na wawuri wayar ina tunanin kalar zagin da zan narka, ganin sunan Mommy ne yasa na dan saki fuskata kafin na dauka, gaisawa muka yi ta tambaye ni na sauka lafiya? Na amsa mata da lafiya lau. Mun danyi hira da ita kafin muka yi sallama, na dora wayar akan bedside drawer ni kuma na kwanta bayan nayi dimming din wutar dakin.
*♡Jeedderh♡*
[12/8, 12:46 PM] +234 810 910 7052: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*17*
*HADITH*
Abdullah bin `Amr bin Al-`as (May Allah be pleased with them) reported: A man asked the Messenger of Allah (PBUH): "Which act in Islam is the best?'' He (PBUH) replied, "To give food, and to greet everyone, whether you know or you do not.''
[Al-Bukhari and Muslim].
Washegari kam su Ramlah sun ga tsiya a lab, Tunda muka zo na samu gefe daya na zauna fuskana a cune, ban mata magana ba balle sauran en lab din, su Ni'ima ma Suka zo naki kallon inda suke, ina ji suna tambayar Ramlah meke damuna ne tace itama tunda taxo a haka ta same ni. Har muka tashi a ranar ban kalli inda suke ba, sunyi maganar sunyi tsokanar duk a banza. Muna fita na fara kokarin wuce su, Ramlah tayi saurin tare ni tana harara ta, "wai ke dallah malama meye kike wani yazga mutane tun dazu?" nima na harareta, nace "ban sani ba dallah bani hanya!" Ni'ima ta matso tace "in dai akan zancen Fahad ne don Allah kiyi hakuri, wallahi dana san Abun zai bata miki rai da ban bashi number din ba, kiyi hakuri sis kinji?" na ajiye numfashi tare da kallonta, "ni fa ba bashi number din da kika yi bane ya bani haushi sai zuwa da kika yi kina yada sirrina a wajen stranger. Saboda Allah meye na zuwa kina gaya mishi wai ina crushing din wani?" tayi fuskar tausayi "Nima nasan ban kyauta ba, da gaske ban san lokacin dana gaya mishi ba wallahi, hira ce tayi hira ni kuma na saki baki ina bashi labari, amma don Allah kiyi hakuri" nace shikenan ya wuce, ta rungume ni tana er dariya, thanks sissy. Na harari Ramlah nace "ke kuma ba zaki bani hakurin bane?" ta zaro ido waje, "ni kuma me nayi?" nace waye ya gayawa su Ni'ima cewa ina crushing Muneer idan ba ke ba?" ta ta6e baki, "dadin ta ma ba karya nayi ba" nayi murmushin yake, zan ga ranar da Ramlah zata yi abu like a good girl in dai akan zancen Muneer ne, she's always playing bad, making it obvious that bata son gayen ko kadan, to amma ya zan yi? A gani na Allah ne ya dora min son Muneer bani na dorawa kaina ba. Da haka dai muka shirya muka hau hira har Malam Bala yaxo muka tafi har su Ni'ima din zasu je su ga jikin Abbu. A can muka Tarar dasu Anty Rahina suma sun zo, nan muka wuni dasu muna ta hira har Yamma tayi kafin Suka tafi. Tun daga ranar kuwa ban sake ganin kiran wayar Fahad a waya na ba.
Satin Abbu uku yana jinyar kafar shi kafin ya warke ya fara fita harkokin shi. Naje gida weekend muka je Malumfashi, Malam Inuwa kanin baban su Daddy ya rasu, kakanni na na ainihi sun jima da rasuwa ban yi wayo na ganni dasu ba, shi yasa su Hafsy suke burge ni ba kadan ba, suna da kakanni ta kowanne fanni abin su. Wato naji dadin zuwa Malumfashi wannan karon ba kadan ba, cousins dina duk sun dawo daga makaranta wasu hutu suka zo wasu kuwa sun zo wajen gaisuwa ne, nan muka hadu muka yi ta yawace-yawace da ziyara har ban so lahadi tayi ba, haka dai muka yi sallama da dangina muka wuce gida. Muna isowa na wuce Kano Saboda yamma tayi don haka a gajiye likis na isa gida, babu abinda na iya tsinanawa, ina gama sallah na bi lafiyar gado sai da gari ya waye.
Mun je lab Ramlah take bani labarin wata er ajinmu a Kasu zata yi aure wannan week din, er Kano