Showing 45001 words to 47794 words out of 47794 words
Chapter 16 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt
ma kuwa?" Daddy ya kalleta a hankali, duk da cewa maganar Mommy ta taba ranshi amma bai nuna hakan ba, he was very calm. Yace "kema kin san ba abunda nake nufi ba kenan Habibty, naga shi auren nan nufin Allah ne. Duk iya kokarinmu da tursasawar mu a gare ta idan Allah bai nufa ba babu yadda zamu yi. Nima ina son in ga auren Uwata saboda nasan Martaba da Mutunci 'Ya Mace suna gidan auren ta ba gidan Iyayen ta ba sai dai kin san bana so in tursasawa Uwata ko kadan. Kema din you are just desperate ne, amma duka-duka nawa Nafeesahr take? She's just Twenty Two Habibty!!" Mommy ta dafe kanta, "Ya Allah meke damun ku ne Kun kasa gane abinda nake nufi?" Daddy ya dafa hannunta cikin sanyin murya yace "mun fahimta Habibty, sai dai muma ki fahimce mu mana. Na fada miki Auren nan...." tayi saurin cewa "naji, naji Habibty ba sai ka maimaita ba!" yayi murmushi, "ki dinga mata addu'ah kawai Habibty, amma tursasawar ki ba shine zai sa ko ya hana ba, only your prayers will" ta gyada kai gami da yin sighing cikin saddakarwa, "To Allah ya zaba mafi Alkhairi!" yace ameeen ko Ke fa Habibty? Na saki ajiyar zuciya a sace, muka ci gaba da cin abincin mu. Can kuma Mommy ta sake dagowa ta kalli sashin da nake, "amma meke tsakaninku ke da Harith ne?" na kalleta, "Mommy, sau dubu nawa kike so in gaya miki babu komi?" Mommy tace "to ku ne na rasa gane inda kuka sa gaba" ni dai na samu na lallaba na bar musu teburin kafin wata maganar ta sake bullowa. Wayata na cire a jikin Caji na shiga cikin whatsapp, dp din Abbu na daga, ya canza shi daga wani hoton shi daya dauka cikin suits bakake ya maida shi zuwa wanda suka dauka shi da 'ya'yan shi kamar a wani restaurant ne ma, na kura musu idanu ina kallo ina murmushi, precious memories dinmu dasu suka dabaibaye ni, take naji wasu irin kewar su ta cika min ciki, har na latso lambar shi zan buga sai kuma na fasa, na sake latsawa na fasa, a tunanina idan Abbu shi yana namiji ya iya kauda kanshi daga gareni why not ni mace? Tun ranar da muka yi waya dashi bamu sake wata wayar ba sai kimanin sati biyu da suka wuce, shima tambayana yayi wai ko ina da muradin zuwa BUK inyi D.E ni kuma nace mishi A'ah, daga ranar bamu sake waya ba sai dai muna exchanging din text messages dashi. A hankali nayi tsaki tare da ajiye wayar. Littafan makarantana na dauko na fara karatu ko na samu in daina tunanin Abbu. Gabadaya lamarin shi ya fara daure min rai, idan ya kira ni a waya ko ya min text, kulawar dake cikinsu sai su sa inyi zaton so ne yasa hakan, amma yanayin yadda mu'amalar mu take ko kadan bata yi mun kama da wani abu mai kama da so ba. Yatsun hannuna na nutsa a cikin gashina ina jan tsaki ganin har lokacin dai tunanin Abbu ne a cikin raina. Tashi nayi tsam na fara canza tsarin dakina gabadaya bayan na cika dakin da sautin music har sai da Mommy ta leko ta min magana sannan na rage.
Ranar Laraba a gajiye muka baro makaranta saboda Defense din IT da muka yi, da kyar na iya kai kaina bakin gate saboda gajiya inda nayi shatar tricycle zuwa gida, Harith baya Kaduna kwana biyu kenan, yaje New York wajen hado takardun shi saboda zai fara aiki. Na tura kofar gate din gidan na shiga, yamma tayi likis lokacin. Malam Idi maigadin gidanmu yana zaune a kan dan benci yana sauraron radio, na gaida shi ya amsa da fara'ar shi gami da min sannu da zuwa kafin na wuce falo. Ina shiga sallamar dana fara yi ta kakare a makogorona sakamakon Halittar da nayi ido hudu da ita..........
[truncated by WhatsApp]
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*30*
"Hafsy!!" na furta a hankali, surprisingly, shockingly. Yarinyar ta taso da gudunta ta nufo ni, da sauri na kai gwiwoyina kasa na tare ta muka rungume juna cikin farinciki muna dariya. Sai da muka nutsa na dago fuskarta daga jikina na kalleta da mamaki, "ya aka yi haka Hafsy? Waya kawo ki?" tace "Abbu ne!!" na zaro ido sosai, falon na karade da kallo babu kowa sai Mommy dake kallon TV abinta, a hankali kamar mai rada nace "Abbun yana ina?" tace "ya tafi wajen meeting, dama meeting zai zo anan shine nace sai ya kawo ni wajen ki" na gyada kai a hankali ina kokarin boye embarrassment din daya lullube ni, I am still a stupid again to think that musamman Abbu ya kawo Hafsy wajena ko shima yazo gani na ne, ko ni a su wa?? Na tashi na kama hannunta nace "taho muje dakina koh?" ta daga min Kai tana watso min jerarrun fararen hakoranta, na wa Mommy sannu da gida ta amsa tana jefo min wani kallo, ban kula da ita ba dai naja hannun Hafsy sai dakina. A can fa hirar yaushe gamo ta barke, naga ta kara girma Masha Allah kamar ba Ita ba.... Tace hutun makaranta suka samu jiya, su Qaseem suna gidan Anty Amernah ita kuma da Abbu yace zai zo Kaduna ta saka rigima sai daya taho da ita. Naja kumatun ta ina dariya nace Kin kyauta. Sai dana canza kayan jikina, muka fita muka ci abinci muka dawo daki na kunna mana cartoon muna kallo ni da ita, ga popcorn a gefenmu da lemu muna sha abinmu. Da yamma na dauke ta muka fita cikin gari, mun sha yawace yawacen mu har muka gaji, sai da aka kira sallar Magrib sannan muka dawo gida. Bayan mun gama dinner muka koma dakinmu, na bude jakar kayanta na fitar mata da kayan barci tasa muka kwanta.
Washegari har cikin makarantar mu na shiga da ita, bani da lectures kawai yawo muka shiga. Daga karshe dai muka dire a gidan Anty Uwani. Bayan La'asar muna zaune a falo ni da su AbdulMaleek, The Space Between Us muke kallo a tashar MBC, Sultan Babban dan Anty Uwani ya kalleni cikin tsokana, "wai don Allah meye matsalar ki da wannan film din? Last time da kika zo gidan nan ma fa sai da kika kalleshi" nace "kawai film din ya burge ni ne" ya tabe baki, "a haka kuma idan aka cewa mutum yana acting like a child sai yace ba haka ba, Kun zauna nasara suna raina muku hankali Kun hau kai Kun zauna" filon kujera na dauka na jefa mishi ya cafe yana dariya. Daidai lokacin wayata tayi ringing, da sauri na daga ganin sunan Mom, "Ke kiyi sauri ku dawo Baban Hafsat yazo daukar ta!" wani irin faduwar gaba ta ziyarce ni kafin inji wani irin sanyi ya dabaibaye min jiki, jikina har rawa yake yi lokacin dana tashi ina lalubar gyalena da jakata, duk suka bini da kallo mai dauke da alamun tambaya. Na cewa Hafsy ta tashi mu tafi Abbu ne yazo, yarinyar ta tashi tana gunaguni da turo baki, ban ko bi ta kanta ba. Abinda na damu dashi a lokacin kawai shine in ganni a gaban Abbu, in dora idanuna akan fuskar Abbu. Anty Uwani ta fito daga kitchen, cikin mamaki take kallonmu, "ku kuma sai ina haka? Ba dai tafiya ba koh?" nace "Mommy ce ta kira ni yanzu tace muje Abbun Hafsat yazo tafiya da ita" ta kuma kicin ta dawo dauke da Leda wadda aka saka plastic roba a ciki wadda nasan dambun nama ne a ciki sana'ar ta kenan, bakery gareta wanda ake sarrafa fulawa ta hanyoyi daban-daban, suna kuma yin dambun nama a can. Ta mikawa Hafsy ledar tace "ga wannan sai kici a hanya koh?" Hafsy ta amsa tare da mata godiya, su Sultan suka raka mu har waje. Mun bata mintuna goma kyawawa bamu samu abun hawa ba gashi an aiki direban gidansu, Sultan yace "Kema ku jira direba ya dawo mana, sai ya kaiku. Nasan ba zai jima ba yanzu zai dawo" na girgiza kaina, a yadda nake jina dinnan a kagare, gani nake idan da halin inyi fuffuke da wallahi sai nayi, jiran Direban nan daidai yake da buguwar zuciyata ta tsage, nasan tsakanin doki da kaguwa ma ba zasu bar ni. Naja hannun Hafsy muka fara tattaki, Allah ya taimake mu kafin muyi nisa muka samu mai Adaidaita Sahu muka shiga. Bamu muka isa gida ba kuwa sai karfe Shida saura, a farfajiyar gidan Motar Abbu ce a fake a cikin gareji inda ake ajiye Motocin gidanmu. Zuciyata ta fara wani irin tsallen murna, duk yadda naso in boye farin cikina abun yaci tura. Sai dai muna shiga falo murnata ta koma ciki ganin falon wayam babu kowa, na dan hade fuska. Kamshin abinci na jiyo yana tashi nasan Mommy ce take girki, na shiga kicin din na sameta tana zuba abinci a cikin kuloli tana gani na tace "yauwa, zo ki dauki wannan ki kai sitting room daddynki yana can shi da Baban Hafsat" ban san lokacin dana saki ajiyar zuciya ba a sace, ashe yana sitting room ni ai nayi zaton ya gaji da jiranmu ne ya tafi. Kafin in shiga kicin din babu irin tunanin da ban yi ba a raina, kila ya gaji ya tafi, kila ma bai zo ba gabadaya, kila motar shi ce ta lalace ya ajiye tashi a gidanmu ya dauki ta Daddy ya tafi, tunanika dai barkatai. Mommy ta kalleni ganin yadda nake grinning ear to ear, tace "lafiya?" da sauri na gyara fuskata nace "babu komi" ta min nuni da Tray din data shirya flasks da jugs na ruwa da lemu akai, na cicciba na fita. Sitting room din yana can a karshen falon, kofar shi ta waje ake shiga ta bayan gidan inda ake hango dan karamin garden din gidanmu, amma akwai karamar kofa a falon gidan wadda muke shiga ta ciki.
Na tsaya a kofar dakin ina kokarin daidaita nutsuwata, a lokacin babu abinda nake da burin yi irin in zubar da kayan hannuna in fada dakin ina tsalle da ihun murna in fada jikin Abbu, if that will not be possible kuma may be I should just shout? So that duniya da mutanen cikinta su san cewa ina cikin farinciki?? Ina jiyo sautin dariyar su dake tashi daga ciki, sautin dariyar shi kadai ma ta saka ni shivering ina ga kallon wadannan sparking brown oily eyes din nashi?? Na cije baki tare da yin knocking a bakin kofar, na tura na shiga a hankali kaina a kasa. Su biyun zaune suke a kan two seats wanda yake Fuskantar kofar shigowa, ina jin kaifafan idanun mutane biyu a kaina, hakan ya dan haddasa min hardewar kafafu. Na dora kayan akan table din dake tsakiyar dakin, na kuma zube anan kusa da teburin, "Abbu ina yini?" na furta a hankali kamar wadda take tsoron yin magana, cikin muryar nan tashi cike da ginshira ya amsa da "lafiya lau Nafeesah er Daddyn ta, kina lafiya?" Daddy ya mishi rada a kunne ban dai san me yace ba na dai ji sun kwashe da dariya a lokaci guda, na kara yin kasa da kaina ba tare dana amsa tambayar Abbun ba. Daddy yace "matso nan Uwata ki zuba mishi abincin, yanzu zai wuce" sai lokacin na dan daga kaina na kalleshi, ina dagowa muka hada ido dashi, nayi sauri na janye nawa idanun. Ban san ya aka yi ba kuma sai sake tsintar idanunshi a kaina nayi ina ga zuciyata taki aminta da hakan ne shi yasa na sake kallonshi ba tare dana shiryawa hakan ba, wannan kallon murmushi yake yi, yace ba tare daya dauke idanunshi daga kaina ba, "Ni fa ba yunwa nake ji ba, zan ci abinci idan muka isa gida" Daddy bai kula shi ba yace "zuba mishi abinci Uwata" na zaro plate na bude flask din na fara zuba Jollof din spaghetti sai da yawu na ya guda saboda yadda kamshinta yake tashi, na tsiyaya kunun aya mai sanyi a cikin cup na dora fork akan plate din na ja teburin zuwa gabanshi, kamshin turaren Hugo boss ya doki hancina lokacin dana matsa gab dashi, na dan lumshe idanu lokacin dana bude hanci na shaki kamshin ina jin wani irin shauki. Ina ajiyewa na kalli Daddy da niyar in tambaye shi ko in zuba mishi ne shima, yace "ni ba yanzu zan ci ba Uwata je ki kawai" na dan yi murmushi na mike na bar musu dakin. Hafsy na zaune akan kujera tana cin nata abincin Mommy kuma tana dakinta, na wuce dakina na shirya kayan Hafsy a cikin Jakarta. Na ciro wasu takalma dana siyo dama nace Hafsy zan ba shi, naje siyan takalmi ne irin shi ya burge ni kuma sosai sai dai babu size dina don haka na siya daidai size din Hafsy duk da ban san ranar da zan bata shi ba. Na kara duba wardrobe dina babu abinda na gani wanda zan bata sai kayan kwalliya kawai na kara mata, na dauki jakar na fita falo. Ina zama Daddy ya shigo falon yace Hafsy ta fita Abbu yana jiranta, tayi raurau da idanunta alamun bata so tafiya ba har ta bani dariya. Na kama hannunta na tasheta tsaye, Mommy ta fito daga dakinta hannunta dauke da leda ta mika mata, Daddy kuma ya ciro kudi daga aljihunshi ya bata. Na dauki jakar ta muka fita, Abbu har ya fiddo motar daga cikin gareji. Na budewa Hafsy passengers seat ta shiga ta zauna, na bude gidan baya na ajiye mata jakarta. Na kalli Abbu da shima yake kallona, cike da damuwa nace "Abbu ba zaku yi hakuri da tafiyar nan ba zuwa gobe kaga fa dare yayi" ya girgiza kai, "kar ki damu, ai In shaa Allah yanzu zamu isa, nan da Kano ai babu nisa" na rausayar da Kai gefe, "shi kenan since you insist, Allah ya kaiku lafiya" yace "Ameen" ya dauko wani kwali anyi wrapping dinshi da gift ribbon ya miko min, babu musu ko tambayar dalili nasa hannu na amsa, "nagode Allah ya saka da alkhairi" na furta a nutse, yayi murmushi "sai gani na biyu koh Nafee??" na kalleshi ina so in tambayeshi gani na biyu kuma as in how? Sai dai irin murmushin dake kan fuskarshi a lokacin ya daskarar dani na kasa daga bakina, ya tashi motar yana kara jifana da murmushi a hankali yaja suka fita, da kyar na samu kuzarin daga musu hannu ina waving dinsu har suka fita daga gate din gidanmu. Na juya a hankali na koma cikin gida, baby kowa a falon nasan suna daki zasu daura alwala saboda naji ana kiran sallar magrib. Nima na shiga dakina na ajiye abinda Ke hannuna akan gado naje na dauro alwala.
**********
Na kwanta rub da ciki akan gadona ina jujjuya wayata a hannu kamar ina jiran wani abu, koda yake jiran kira ko text din Abbu nake yi. Gabadaya raina ba a kwance yake ba da tafiyar nan ta dare da suka yi, gashi tun karfe shida da rabi har karfe tara babu alamun kiran shi bayan nasan duka-duka tafiyar bata fi ta awa biyu ba. Kamar yasan ina jiranshi, text din shi ya shigo wayata, "mun iso Kano lafiya lau, Pretty tana gaida ki" nayi saurin typing "Masha Allah! Sannunku da zuwa" na tura mishi. Sai a lokacin naji kuzari ya shige ni, na tashi zaune na bude kwarin daya bani. Tarkacen chocolates ne da cookies a ciki, daga kasan su na ciro wani frame, hannun mace da namiji ne sarke dana juna a jiki, anyi kananun rubutu da wani irin yare wanda ban fahimce shi ba, daga kasan hannun nasu dai anyi rubutu in bolds kuma in capital letter....... *"TOI ET MOI POUR TOUJOURS! (I Miss You in French)"* Na danyi tsaki kadan, ban san me yasa Abbu yake son rubuta min abu da wani yare na aljanu ba, saboda Allah how in hell would I be able to understand what is written there?? Na kara jan tsaki naje na rataye frame din a jikin bango.
*♡Jeedderh♡*