Showing 30001 words to 33000 words out of 47794 words
Chapter 11 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt
koma gaban su Daddy na, ina so inyi nisa da Abbu da gaggawa, he has started putting some effects on me wanda duk iya kokarina nason ganin na hana su affecting dina abun ya ci tura, shi yasa nake so in bar gidan as soon as possible kafin abubuwan su fi karfina. Hira na fara jan ta dashi ina tsokanar ta, nan da nan ta ware ta fara dariya, tare da ita muka cigaba da shirye shirye, na fidda kaya masu dama da wasu daga cikin kayan kwalliyata na ba Harira tayi ta godiya kuwa. Ana kiran magriba muka bar shirin muka yi sallah, Hafsy ta dauko littafan ta na taya ta muka yi bitar karatu har aka kira Ishai'i muka yi, muka fita wajen cin abinci. Muna gamawa muka koma kan kujeru muna kallo, duk da kallon daga ni sai Hafsy ne su Abdullahi wasan su suke yi abin su. Abbu da Anty Mubeenah suka yi sallama suka shigo falon, muka musu sannu da zuwa duk suka wuce dakinsu da alamun kayan jikinsu zasu canza. Anty ce ta fara fitowa, kamar yadda nayi zato ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga, Kai tsaye kan dinning ta wuce ta zauna. Ba a jima ba Abbu yayi joining dinta shima ya canza kaya zuwa na barci, riga da wando na M$S, muka cigaba da kallonmu har suka gama cin abincin suka dawo inda muke suka zauna. Hirar su suka fara yi su da 'ya'yansu, Anty tace "Nafeesah gobe sai tafiya gida ko?" nayi murmushi tare da gyada kai, tace "eyyah! Zamu yi kewar ki ko don dadadan girke-girken ki" Abbu ya jefa mata wani irin kallo, Qaseem yace "Yaya Nafee amma zaki dinga kawo mana ziyara koh?" nace sosai ma. Hafsy tayi caraf tace "anan ma zata dinga mana weekend koh?" na kalli su Abdullahi da suke kallona cikin zakuwa da son jin amsa ta, murmushi nayi nace "ehh" a hankali. Suka dauki shewa suna ihun murna, kallon su kawai nayi ina murmushi. Karfe goma tana yi na tashi na musu sai da safe, Hafsy ta mike da sauri ta biyo bayana, ina ji Abbu ya tambayeta, "pretty ina zuwa?" ta juya tace "ni dai a wajen Yaya Nafee zan kwana yau" yace "a'ah zo ki wuce dakin ki, zaki takura mata" aikuwa ta bare baki zata fara kuka, nayi saurin janyota jikina, "babu komi Abbu, taho muje kinji?" ta ware hakora tana dariya, naja hannunta muka shiga daki. Brush muka yi muka fito, nace ta zauna bari inje in dauko mata kayan barci, na fita. Falon babu kowa duk sun tafi dakinsu, naje na dauko mata kayan. Na fito kenan daidai Abbu yana fitowa daga dakinshi, ya kalleni, da sauri na sadda kaina kasa nayi niyar wuce shi da sauri, cikin wata irin murya da ban taba jin ta a gun Abbu ba naji yace "Nafeesah!" na tsaya cak duk da ba haka naso in yi ba, so nayi in yi kamar ban ji ya kira ni ba in shige dakina wanda bai fi taku takwas daga inda nake tsaye ba, but damn me and my legs. Ya tako a hankali har inda nake tsaye, zuciyata bugawa take yi da sauri har naji tsoron kar ya jiyo sautin, shiru ya biyo baya na fiye da minti biyu, jikina ya bani cewa kallona yake yi don haka naki daga fuskata balle in kalle shi. Yayi ajiyar numfashi a hankali, yace muryar shi kasa-kasa, "are you sure Pretty ba zata takura miki ba?" na tabbata ko nayi magana ma da kyar muryata ta fita don haka na gyada mishi kai kawai. Yace "umh.... Da gaske zaki dinga zuwar mana weekend?" nan ma kaina kawai na iya gyadawa. Yace "good! I'm happy to hear that. Je ki kwanta sai da safe" da sauri na wuce har kafafuna suna hardewa na fada dakin kamar wadda aka jefa, Hafsy ta daga kai ta kalleni da sauri, murmushi na sakar mata na mika mata kayan barcin ta saka nima na sa nawa, wando ne iya gwiwa don nasan ba fita zan sake yi ba da rigar vest mai budadden gaba zan iya cewa Rabin kirjina a waje yake. Na mana addu'ar kwanciya barci ni da Hafsy muka shafa, na janyo bargo na rufe mu tare da kashe mana wuta. Ban sani ba tsautsayi ne ko kuwa Kaddara ya saka ni janyo wayata na shiga social media?? Well, that's the worst moment I've regretted the most in my life!!!.
*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:29 AM] +234 816 390 1222: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*21*
Ban san lokacin dana saki wayar hannuna akan carpet din dakin ba, na jingina bayana da allon gado ina kallon wayar kamar wadda aka turo mata da ranar mutuwar ta, hoton Muneer ne shi da wata tsaleliyar yarinya ya dora a shafin shi na instagram, a kasan hoton naga yasa *Finally Engaged Alhamdulillah..., getting married in the next 6 months!*. Ban taba sanin cewa numfashin mutum ya kan dauke, zuciyar mutum ta daina bugawa ba alhalin mutum na raye sai a lokacin, lokacin da nayi kokarin warto numfashi na sai gani a tsakiyar carpet din dakin dafe da kirjina, Zufa ta shiga keto min ta ko'ina, jikina rawa yake yi kamar mazari. Allah kadai Yasan iya adadin lokutan dana kwashe cikin wannan hali. Kamar wadda aka zungura nayi zumbur na tashi tare da daukar wayata, ban damu da cewa lokacin karfe sha daya da rabi bane, abinda na sani kawai shine ina so inji daga bakin Muneer, cewa da gaske aure zai yi, wata zai aura ba ni ba. Na kalli Hafsy da take barcinta cikin natsuwa bana so in katse mata barcinta saboda nasan a yadda nake ji na ba zan taba yin kasa da muryata ba, ji nake kamar in bude baki inyi ta kwarara ihu har sai mutanen Duniya sun ji halin da nake ciki. Falo na fita, wutar falon a kashe take duk da haka akwai haske wanda kwayayen waje suka samar. Number Muneer na danna, take ta shiga ta fara kara. Kai kawo nake a tsakiyar falon na kasa zaune na kasa tsaye har tayi karan ta gama bai dauka ba, na sake danna mishi wani kiran, sai dana jera mishi missed calls takwas ina kirgawa ban kuma yi niyar dainawa ba, nayi imani a lokacin idan zai kwana bai daga kiran ba nima haka zan kwana ina kiran shi ba tare da gajiyawa ba. Ana tara ne ya daga cikin muryar barci, "hello Nafeesah lafiya??" sai na ma rasa abinda zan ce mishi, wani irin kuka yake shirin kufce min na datse hakorana ina maida shi ta karfi, Muneer bai kai wannan matsayin ba kuma, kuka akan namiji? Har abada! Ya sake cewa "Nafeesah, are you ok??" cikin gritted teeth nace "Muneer, you evil bastard!!" shiru ya biyo baya da alamun he was in shock, I couldn't suppressed my anger shi yasa, "what?! Excuse me??!" ya fada shockingly, cikin rawar murya mai cike da bacin rai nace "You betrayed me Muneer!! Kayi wasa da zuciyata ka maida ni sakara, abinda ka mun ka kyauta kenan? Kana ganin hakan dacewa ne?" yace "me kike fada ne haka Nafeesah? Me na miki? Ta yaya na yaudare ki??" cikin karaji nace "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what? Aure?? Baka yi tunanin halin da zan shiga ba?" yace "I never Loved you Nafeesah!! Saboda kawai kina so na sai kiyi tunanin zan tauye kaina da rayuwata saboda ke? Why would I?? I mean ban taba cewa ina sonki ba, in fact, ban taba nuna signs na so a gare ki ba ko na taba?" kai na nake girgizawa cikin tsananin bacin rai da bakin ciki, ni Namiji yake gayawa baya so na da Babbar murya!! Muryata ta fara rawa, nace "ka cuce ni Muneer! Kaki ka so ni ka hana ni inso wadanda ke so na, you are one big devilish bastard on earth!" yace "enough Nafeesah! I've heard enough please, bani nace ki so ni ba, ban taba rokon ki akan ki so ni ba don haka you have no right da zaki saka ni a gaba cikin daren nan kina zagina da tuhumata akan laifin da ban sani ba kin gane?" na gyada kaina a hankali kamar wadda take gaban shi, nace "you are right Muneer!! You are right!! Laifina ne, ni naki yarda inji maganar mutane da kashedin da suke min, duk a tunanina kana so na ashe yaudarar kaina kawai nake yi..... Sai da safe kawai, sai dai I'm not sorry about waking u up, ina maka fatan uncomfortable sleep through out the night!!" na kashe wayata gaba daya. Zubewa nayi a kasan falon saboda yadda kafafuna suka yi sanyi, zuciyana kuna take yi kamar wadda ake soyawa. Duk yadda naso akan in daure kukan da yake tuko ni kasawa nayi, gani nayi idan ban yi kukan ba zuciyata zata iya fasa kirjina ta fito. Kuka na fashe dashi sosai kuma da karfi, a wannan lokacin ban damu ba wai Don mutane sun san cewa ina kuka saboda Namiji yayi dumping dina. Sai da nayi kuka na mai isa ta sannan na tashi ina hardewa da layi na shiga dakina, a dakin ma wani sabon kukan na dasa. Bakin cikin dake raina was incomparable da ko wani irin halin bakin ciki dana taba shiga a rayuwata, wallahi ko a cikin mafarki ban taba zaton cewa ni Nafeesah za a samu wani namiji a duniyar nan da zai daga baki yace baya so na ba sai gashi wanda na kwashe shekara curr cikin son shi da mafarkin kasancewar shi uban yaya a gare ni ya daga baki ya fadi kalma mafi munin saurare a gare ni, Lallai Duniya mai cike da abubuwan mamaki. Sai gabannin Asubahi barci ya suraro ya sace ni ina xaune a kasa na jingina kaina da jikina da gado.
*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:27 AM] +234 816 390 1222: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*22*
_'Some nights I can hear you., Screaming on the phone over something that he did....., And I wonder what can I do to make you throw him out so you can let me in.....!'_
A song by *Shayne Ward* Titled *'Melt the Snow'*. I hope you will enjoy listening to it.
Juyi yake yi akan gado, barci yake ji sosai amma ko kadan barcin yaki zuwa. Gadon da yake Kai ya mishi fadi, gado ne wanda a kalla zai iya kwashe mutane biyar ba tare da wani ya takura wani ba amma kullum ta Allah shi kadai yake murzar shi, yana Juyi a kanshi, yana jin shi kamar wani mara galihu. Disappointedly ya sauka daga kan gadon, kan sofa yaje ya kwanta, yafi jin dadin kwanciya anan duk da cewa kafafun shi suna kan hannun kujerar ne saboda tsawon shi. Wani modem daya shigo dashi ya tuna ya baro shi a parlour, wasu muhimman bayanai ne a ciki ba shiri ya tashi ya fita, babu kowa a Cikin falon, wutar falon ya kashe yayi amfani da wayar hannunshi ya dauko Modem din. Kan three seats ya koma ya kwanta a parlour na daya, Family picture dinsu ya kurawa ido yana kallo. Ya gaji haka nan, Ya gaji da jiran canzawar halin Mubeenah, Ya gaji da kasancewa kamar wani marar aure alhalin yana da mata kuma yana da right din karo guda uku kwarara, yana bukatar rayuwar aure irin ta kowane normal mutane, rayuwa mai cike da soyayya da girmamawa ba irin rayuwar auren gidanshi ba, rayuwar auren da ba zaka taba ganin murmushi ko kafar matar auren ka a dakin ka ba sai idan tana bukatar either kudi ko bukatar namiji ta motsa mata, kai kuma naka bukatun ko oho! Yana ganin lokaci yayi da zai maida komi inda yake, maganar gaskiya yana bukatar mace ya kuma gaji da bin kan Mubeenah tana yankwana shi kamar wani mara galihu, Allah ya gani yayi iyaka Kokari da hakurin da zai yi. Yana nan kwance Cikin zazzafan tunani zai iya cewa ma barci ya dauke shi yaji karan bude kofar daki, a hankali ya bude idanunshi yaga Nafeesah ta fito daga dakinta, da mamaki ya bita da kallo a cikin ranshi yana tambayar ko lafiya? Yanayin tsayuwar da tayi tana tapping kafafunta a kasa nervously ga waya a kunnenta ya sashi cikin tunani me ke damun Nafeesah ne haka? A hankali idanunshi suka fara yawo a jikinta, duk da babu wadataccen haske a falon amma hakan bai hana shi hango surar jikinta cikin gajeren wando da vest din data saka, wani irin tension yaji yana building a cikin jikinshi babu shiri ya rufe idanunshi da karfi yana hadiyar yawu yana gayawa kanshi it's not right! A hankali ya sake bude idanun yana kara kare mata kallo yadda jikinta yake swaying halittun jikinta suna motsi suna kara tada mishi hankali, yana so yayi motsi yadda zata san da wanxuwar shi a cikin falon, but hell! He couldn't. God Forgive him but he's enjoying seeing her in that attire, making him go mad, making him want to just drag her and kiss her senseless may be yayi wani abun worst than kiss.....! Maganar da tayi cikin fushi da daga murya ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi, "Muneer you evil bastard!" yaji duniya ta tsaya mishi cak kamar an tsaida kowane wucewar minti da dakika, may be he was mistaken, ba Muneer tace ba, kila ba sunan Namiji ta kira ba, kila Muneerah tace kunnenshi yake gaya mishi Muneer. Ya sake lafewa akan kujerar da yake yana kara kasa kunne, "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what?! Aure??!...." da sauri ya saka hannu ya danne kofofin kunnenshi yana girgiza kai, no! No way!! Karya ne!!! Kwatakwata ya manta a ina yake balle yace ga abinda yake yi, wani irin rugugi yake ji yana mishi ihu a cikin kunnenshi, maganganu mafi muni da daci daya taba ji an furta a gare shi, maganganun da suka girgiza shi suka yi turning rayuwar shi up-side-down, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un ya dinga nanatawa har yaji nutsuwa ta saukar mishi, maganganun Nafeesah sun matukar girgiza shi, the fact that tana son wata halitta, halittar ma jinsin Namiji, abu ne da bai taba zato ba, bai taba zaton cewa tana da wanda take so ba, bai kuma taba zaton cewa abun zai yi affecting dinsa sosai kamar yadda yayi yanzu ba. Yana jin lokacin data tsuguna tana kuka sosai a tsakiyar falon, he wanted to man up yaje ya rarrasheta sai dai a halin da ake ciki shima rarrashin yake bukata, yana ji kamar shima ya fashe da kukan ko ya samu yaji sauki daga azabar zafin da zuciyar shi ta dauka, har ta gama kukan ta tashi ta koma dakinta bai iya tabuka komi ba sai bin ta da kallo helplessly. Lokaci mai tsawo yana cikin wannan hali kafin yayi karfin hali ya tashi zuwa dakinshi, alwala ya dauro ya kalli Al-Qibla ya fara jera nafilah yana mai rokon Allah akan ya mallaka masa Abinda ya jima yana kwatanta nashi ne.....!.
☆☆☆☆☆☆☆☆
A hankali na bude idanuna da nake ji sun min wani irin nauyi marar misali, na kai hannu na dafe kaina da naji yana sarawa kadan wuyana ya rike shima na kai hannu ina dan taba shi, idanuna suka sauka akan agogo, karfe shida ta wuce, da sauri na tashi tare da daddabar Hafsy ta tashi, muka shiga bandaki muka yi alwala muka fito muka yi sallah, dakinta nace taje tayi wanka ta shirya nima na shiga na watsa ruwa, nayi iyaka Kokari na wajen mantawa da abinda ya faru Jiya da dare, bana son tunawa ko kadan. Na fito daga toilet din daure da tawul a kirjina, na tsaya a gaban mirror ina tsane lemar jikina, idanuna sun tasa sosai sunyi luhu-luhu, ni dama nasan za a rina irin kukan dana sha jiya, kayan kwalliyata na janyo na shiga shafe-shafen abubuwa amma duk kokarin da nayi idanuna basu da alamun dawowa normal dama-dama ma fuskata swollen din da tayi ya rage sosai, tsaki naja na janyo wet tissue na goge kwalliyar da nayi, nayi simple one ko janbaki ban sa ba, riga da zani na saka nayi simple daurin dankwali, na dauki jakata na jefa wayata a ciki ba tare dana damu akan in kunna ta ba. Shades na saka a fuskata wanda ya rufe idanuna da yawancim fuskata, na zura takalmi flat na fita. Yaran ne kadai a falon suna kari iyayen basa nan, naja kujera na zauna a gefen Hafsy yayin da duk suka bini da kallo, dan murmushi nayi kawai, suka gaida ni na amsa Hafsy ta jefe ni da tambayar "Yaya Nafee me ya samu fuskar ki kika sa glass?" sai da nayi gyaran murya saboda dusashewar da tayi kafin nace mata "idanuna suke ciwo, bana so in goga muku ciwon ido ne" ta gyada kai tace Allah ya sauwake Yaya Nafee, Kai kawai na