Showing 3001 words to 6000 words out of 47794 words
Chapter 2 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt
dubu biyar na fita da sauri ina dariya, kallo kawai ta bini dashi. A Unguwar Rimi suke zaune, sai dana tsaya na sai dangin fruits a bakin hanya sannan na karasa gidan. A can na wuni sur, sai gab da magrib sannan ta sa direba da danta na biyu AbdulJalal wanda yake kusan sa'ana ne suka rako ni gida. Daddy har ya dawo, Allah ya taimake ni ban sha fada ba saboda Daddy baya son yawo ko kadan. Bayan sallar isha'i ina zaune ina kallon film din Kaabil daga cikin laptop dina Ramla ta kira ni, murmushi nayi da naga sunanta a jikin wayata, wato har ta gama fushin kenan?? Da er dariya ta na daga kiran, "Lauratu ya ne?" haka nake kiranta idan naso tsokana. Ina jin dan siririn tsakin data saki, "ke pa u r a prof a ruining mood din mutum wallahi, meye wani Laure kamar wata Goggo a kauyen kayau?" dariya na sheke da ita cikin tura haushi, hakan ya kara tunzura ta kuwa. Sai da na gama tsokanarta sannan na tsaya ina sauraronta, hakuri ta bani game da abinda ya faru ranar, nima hakurin na bata tunda dukanmu we are at fault. Daga nan hira muka hau yi da ita, mun share fiye da awa daya muna hira har sai dana gaji don ni dama can ba gwanar hira bace musamman ma hirar waya, sallama muka yi kowa ya ajiye wayarsa.
Da dare muna falon daddy mu duka muna en hirarraki, aka kira daddy a waya. En maganganu suka yi kafin ya ajiye wayar yana kallona, "Uwata kinji an karbi letter dinki pa!" ban san dalili ba, gabana ya fadi ras! Rasa abin cewa nayi kawai na tsaya ina kallonshi, yaci gaba, "ranar Sunday zaki tafi mun gama magana da Ibrahim din. Sai ki fara shiri koh?" jikina naji yayi sanyi sosai, kafin kace me! Hawaye sun fara min yawo a kumatuna, cike da damuwa daddy yake kallona, "Uwata lafiya?" kai na gyada mishi a hankali, "I just started missing u ne daddy!" Dariya ya saki yayin da mommy tayi murmushi, hannu na ya rike a tausashe, "ohh my loving princess.... We gonna miss u!" group hug muka hada kamar zamu yi kuka.
Shirye-shiryen zuwa Kano na fara yi, hada tarkace, sallama da dangi da en abubuwa. Komi cikin sanyin jiki nake yin sa, wannan shine karo na farko da zanyi tafiya ta fiye da watanni uku. Daddy dinmu dan asalin garin Malumfashi ne ta Katsina, danginshi duk a Katsina suke zaune don haka mu kan je can idan mun samu hutu in musu kwanaki zuwa sati. Amma Ina jin wannan tafiyar ta banbanta, zuwa zanyi fa in zauna da mutanen da ban sani ba na tsayin watanni hudu zuwa biyar, a garin da ban sani ba duk da cewa mun yi zaman Kano na shekaru biyu, amma that was then, I think tun ina primary 5 ne??? Haka dai naci gaba da Shirye-shiryena har zuwa ranar Sunday. Sai wajen karfe biyar na yamma muka bar Kaduna, daddy ne ke jan motar, mommy na gefen shi ni kuma ina gidan baya. Tafiyar tayi min wani irin sauri, sai naga kamar muna tafiya ne akan iska ba kan kwalta ba. Cikin dan lokaci kankani mun isa Kano, unguwar Tal'udu muka wuce tunda anan gidan yake. Naji daddy yana ba Mommy labari game da abokin nashi, yace lecturing yake yi amma ba a staff quarters yake zaune ba, yace dan asalin garin Kano ne kuma yanzu haka yana neman kujerar dan Majalisa ne. Yaran shi uku da matar shi daya..., ni dai tunda naji yace yana harkokin siyasa na maida hankalina kan wayata, dan siyasa? Allah ya gani basu cika burge ni ba, ban son siyasa.
Kugi na karshe da motar tayi a cikin garejin gidan ne, tun daga cikin mota nake karewa gidan kallo. Ba wai yanke hukunci kai tsaye ba, yanayin gidan tafiy kafin ace mallakin just a lecturer (sorry lecturers, m not underestimating ur payment or something). Gida ne hawa daya, parking lots din gidan cike yake da manyan motoci ba na wasa ba, ga bikes da kekuna ina ji na yaran shine. Daga nan kana iya hango wani dan karamin garden a can gefen gidan, har wani dan karamin wajen wasanni na gani.
A hankali muka fito daga cikin motar, already wani da nafi kyautata zaton mai gadi ne ya fara kwasar kayana yana shiga cikin gidan dasu. Shi yayi mana jagora zuwa wani babban falo daya min kama da fadar uwargidan sarkin Kano, ya sha jere na wasu narka narkan leather seats kala biyu, farare da browns, ko wane jeren kaya yana da nashi dinning table, Plasma TV wadda zaka yi zaton zata cinye bangon falon saboda girmanta. Kafafunmu suka nutse cikin wani tattausan rug carpet kamar auduga, nayi iya bakin kokari na wajen ganin cewa ban hangame baki nayi kauyanci ba, maganar gaskiya ban taba shiga tsarraren falo irin wannan ba duk da cewa ba laifi nayi shige-shige a parlours da gidaje na manyan mutane, wannan kam looks extraordinary sosai. Kujera muka samu muka zaun 3 seats, ina tsakiyar su daddy, er aikin gidan ta fito daga kitchen ta gaida su daddy kafin ta shige wata kofa a cewarta zata kira madam. Ina jin lokacin da daddy yake gayawa Mommy ai Ibrahim din baya nan, yaje wani seminar. Ni dai ba baki, I was very nervous a lokacin. Mintuna kamar goma sai gata ta fito, Ya Allahu!! Meye wannan a gabana? Naji zuciyata tana tambaya lokacin da nayi tozali da matar. Don fari fa Akwai fari kamar Baturiya, kyawu ma Akwai shi Masha Allah, wata irin kiba marar fasali ne da ita. Lokacin data zauna akan kujera suna gaisawa dasu daddy sai naga ta shirge a waje guda kamar kayan wanki. Da kyar na iya saisaita kaina na dan zame daga kan kujerar na gaisheta, da er fara'ar ta ta amsa har da ambatar sunana, "Safeenah ko?" na gyada mata kai a hankali. Ta maida kanta gasu daddy suna er hira, idanuna suka ci gaba da wandering a cikin falon bana ma jin me suke fada. Aka kira magrib daddy ya fita sallah, ni da Mommy kuma muka yi a cikin falo don bamu samu albarkacin samun gayyata zuwa dakin matar gidan ba, kuma ba a nuna min inda zan zauna ba, karewa kayana ma suna nan baje a tsakiyar falon. 'yar aikin gidan muka tambaya ta nuna mana bayi dake nan cikin falon muka shiga muka dauro alwala, motar daddy naje na dauko prayer mat muka shimfida anan muka yi sallah abinmu.
Daddy yana dawowa daga sallah yace mommy ta tashi su tafi, nan fa idanuna ya raina fata da naga Mommy ta yiwa er aikin gidan magana akan taje ta gayawa matar gidan zasu tafi, idanuna suka yi raurau kafin kace me na fara hawaye shabe-shabe. Ba a dauki mintuna biyar ba sai gata ta fito tana taku da kyar, ban sani ba na takama ne ko kuwa dalilin kibar ta ne? Sallama suka yi dasu ta koma daki abunta. Hannuna mommy ta kama na musu rakiya har bakin motar su, zuwa lokacin kam kuka nake har da shessheka, suka saka ni a tsakiya suna lallashina har na samu kukan ya lafa. Ina nan tsaye suka shige mota suka ja suka tafi bayan na sha nasihohi daga gare su. Na bi bayan motar nasu da kallo har suka bar gidan aka maida gate aka rufe, na maida kallona ga dankareren gidan da zan rayu a ciki zuciyata cike da tarin damuwa iri-iri, daga can kasan zuciyata ina jin wata irin nadama na dabaibaye ni, Me ya kaini???? A hankali wasu siraran hawaye suka biyo kan Kumatu na.....!
Just want to say thank u for those following me, commenting and voting on this story. Please keep it up, keep voting, comment, and share it with your friends......
T
[12/9, 8:32 PM] +234 816 965 3238: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*
©JeedderhLawalS
*04*
Sai dana kwashe lokaci mai tsawo a cikin farfajiyar gidan a tsaye kafin na samu kwarin gwiwar jan kafafuna da kyar na koma falon. Ina shiga na ci karo da er aikin gidan wadda saboda tsabar wata irin shiga mara fasali da tayi yasa na kasa gane ko wace irin yare ce, cewa tayi in zo muje ta nuna min dakin da zan kwanta inji madam dinta, babu musu na dauki jakar hannuna na janyo daya daga cikin jakunkunan dana taho dasu nabi bayanta bayan itama ta dauko wasu. Abinda na kula duka dakunan gidan a falon kasa suke, ni tunda nazo ban ga kowa ya hau saman ba. Wani dan madaidaicin daki cikin jerin dakunan dake cikin falon ta bude muka shiga ciki. Dakin yana da fadi ba laifi, Akwai toilet a ciki ga wani medium size gado ruwan golden, mirror da closet sai er karamar sofa da study table. A tsakiyar dakin an malala wani tattausan circle carpet baki, sauran dakin kuwa malale yake da wasu en ubansun marbles fari da gold, well, ba laifi ya burge ni sai dai yadda aka tsara dakin ne sam bai min ba. A raina nace sai na canza shi. Ina ta karewa dakin kallo har ta gama shigo min da kaya na duka, ta tambayeni idan Akwai abinda nake bukata? Kai kawai na girgiza mata tare da mata godiya, ta min sai da safe ta wuce abinta. Jakar hannuna na jefa akan gado na samu gefen gadon na zauna Ina kara karewa dakin kallo, tashi nayi na leka toilet, Shima babu laifi ya hadu, na dawo na bude closet din babu komi a ciki sai er guntuwar kura data yi, tsumma na lalubo na goge ta tas na lalubo turaren kaya a cikin kayana na watsa a gefen closet din kafin na fara shirya kayana a ciki, sai dana cika ta tsil da kaya wasu ma da kyar suka shiga, na makare kan mirror na da tarkacen kayan shafa dana kwalliya da nau'in perfumes kamar a wani dan karamin super store. Sallar isha'i nayi na hada da shafa'i da wutiri, ina gamawa naji wayana tana kara, ringing din dana sakawa daddy ne. Da sauri na tashi na daga kiran, gaisawa muka yi ya fada mun sun isa gida lafiya, mun danyi hira kadan yaba mommy wayar itama muka dan yi hira, sai data kara min da en nasihu akan wadanda ta min sannan muka yi sallama na ajiye wayar. Ruwa na watsa a jikina na nemi kayan barci marasa nauyi na saka na kwanta, amma kwata-kwata barci yace bai san idanuna ba, tunanika iri-iri suka dinga min yawo a kwakwalwa, daga karshe waya ta na dauko na fada duniyar gizo.
Washegari kamar yadda na saba da asubahi na tashi nayi sallah, shiru Ina kan abin sallah a zaune ina debating akan in fita in taya matar gidan aiki ko kuwa in zauna a daki? Daga karshe dai kawai na tashi na fada wanka, usual ways din harkokin rayuwata na bi, kwalliya data kwashe ni kyawawan mintuna talatin, minti ashirin na fiddo kayan sawa da shiryawa, zuwa lokacin dana tsaya a gaban dogon yaro ina sake duba kaina, karfe bakwai da mintuna ashirin. Cike da tunanin yadda zan karasa cikin makarantar BUK na fito falo, babu kowa a cikin falon amma na jiyo motsi a can wata kofa dake gefen dakin matar gidan. A hankali na karasa tare da lekawa, hangame baki nayi kamar zai rabe biyu. Wani dankareren kicin dana gani wanda zan iya cewa ya lunka dakina sau biyu, kayan electronics na kicin babu kalan wanda babu. A gaban gas cooker na hangi er aikin gidan tana soya plaintain, karasawa wajenta nayi muka gaisa cikin girmamawa, na tambayeta matar gidan tace min wai bata tashi daga barci ba, Kai na gyada cike da mamaki. Wace matar aure ce ke kai karfe takwas na safe saura tana barci?? Tambayarta nayi yadda zan isa wajen IT dina, tace ai Direban da zai kaini yana waje yana jirana, tun dazu yayi magana. Juyawa nayi na fita, daga kicin din tace min breakfast fa? Nace mata zanyi acan. A farfajiyar gidan na hangi direban, a mutunce na gaida shi ya bude min gidan baya na shiga yaja motar muka wuce. Mintuna talatin mun shiga cikin BUK, har gaban microbiology lab muka je yayi parking, tare dashi muka shiga lab din ya samu lab attendants suka yi maganganun da zasu yi, ya tafi ya barni bayan ya fada mun lokacin da zai dawo ya dauke ni. Ina zama sai ga Ramla sun shigo ita da Antin ta, nan muka rungume juna cike da murna, itama Anty Halima tafiya tayi ta barmu anan. Da yake ranar farkonmu ce a wurin babu wasu ayyuka da muka yi, wajen karfe goma sha daya muka fito ni da ita zuwa Cafeteria din dake cikin department din. Tafiya muke yi a hankali, tsarin makarantar ya burgeni kwarai, er hira muke yi da ita game da wajen har muka shiga cikin cafeteria din, babu students sosai zama kawai muka yi muka yi order din abinda zamu ci.
Muna gama cin abincin lab muka koma, lab attendants din were very friendly don haka cikin dan kankanin lokaci muka saba dasu. Wadanda suke yin aikin project dinsu sun kawo ayyuka, nan ne fa muka tashi muka fara aiki. Sai wajen karfe biyu muka tashi, wani dan karamin garden muka zauna muna ta hirarmu ni da ita ina jiran Direba yazo tunda ita sai ta jira Anti Halima ta gama ayyukanta, sai wajen karfe biyu da rabi sannan Bala Direba ya iso. Ina hango motar na gane ta saboda a cikinta muka zo. Da sauri nawa Ramla sallama na tashi nayi wajen da yayi parking, a mutunce na gaida shi na bude bayan motar na shiga.
*♡Jeedderh♡*
[12/9, 8:35 PM] +234 816 965 3238: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*
©JeedderhLawalS
*05*
Wata kyakkyawar yarinya cikin kayan makaranta dogon wando navy blue da shirt fara ta dago kyawawan idanunta tana kallona, ban san lokacin dana sakar mata murmushi ba saboda tsananin burge ni din da tayi, a gaban motar kuma maza biyu ne suma cikin shigar kayan makaranta irin na yarinyar, duk suka juyo suna kallona. Zama nayi sosai a gefenta ina ta watsa musu Murmushi yayin da direba yaja motar, yarinyar da nake tunanin shekarunta zasu kai bakwai zuwa takwas tace min ke ce bakuwar da daddy yace zata zo mana gida? Na gyada kai ina kallonta, nice beauty, ya sunanki? Murmushi tayi, sunana Hafsah amma daddy yana ce min pretty Hafsey, su yaya Abdallah kuma suna ce min Hafsatu... Ta karasa tana pouting cike da shagwaba. Er dariya nayi tare da jan kumatunta, "kai amma Yaya Abdallah bai kyauta ba! Hafsatu ai sunan tsofi ne" ta gyada kai tana turo baki tare da kallon wanda yake kama da shine babban yayansu, "ai kullum sai na gaya mishi amma sai yace wae ai nima tsohuwar ce" na kalli yaron Ina Murmushi, "Yaya Abdallah baka kyauta ba gaskiya, tana yarinyarta ka dinga ce mata tsohuwa?" yaron yayi dariya, "sunan maman Daddy gareta pa, don Allah ba tsohuwar kenan ba?" daya yaron na gefenta ya kwashe da dariya, "tsohuwa ce mana, baka ga har ta fara furfura Akanta ba?" Hafsat ta kai mishi duka a kafadar shi, ya kauce yana mata dariya. Tsokanarta suka ci gaba dayi suna dariya har sai data fara kwalla sannan na tsaida su, "here, enough with the teasing, a kyale pretty haka nan ko?" ta gyada kai tana min murmushi, kanta na shafa ina jinta har cikin raina. Yarinyar tana da wani irin kyau duk da suma sauran yaran suna dashi amma ai kun san kyan mace ya banbanta dana namiji, ina mamakin inda ta gado shi a raina nace kila sai dai wajen mahaifinsu don babu mai kama da mahaifiyar su, dama dama dai Qaseem mai bin Abdallah, naga suna dan yanayi da Anti Mubeenah. Kafin kace me mun saba da yaran, dama ni bani da wahalan sabo suma naga hakan a tattare dasu. Muna isowa gida na dauki school bag din Hafsat ita kuma ta rike lunch box dinta, hannunta cikin nawa muka shiga falo ina taya ta miming din wakar twinkle little star. A daya daga cikin kujerun falon, Anti Mubeenah ce zaune ya harde tana duba jarida, yaran suka zube a gabanta suna bata labarin makaranta, sai dana bari suka gama hayaniyar su sannan na duka na gaida ta. Fuskarta dauke da dan murmushi ta amsa tare da ce min Akwai abinci a kicin, godiya na mata tare da cewa sai nayi sallah, dakina na wuce nayi sallah, na janyo wayata na kira mom don nasan daddy yana office ni kuma ban cika son kiranshi a wajen aiki ba, mun jima muna hira da ita kafin muka yi sallama, ana kiran sallar asr nayi na janyo system dina na kunna kallo tunda babu abinda zanyi, da a gida ne kila na shiga kicin ina taya mommy na girkin dare.
Ina zaune anan ina kallo Hafsat ta shigo cikin kayan makarantar islamiya, na daga Kaina na kalleta ina dan murmushi, "pretty Hafsat an dawo ne?" ta zauna a gefena tana turo baki, "malam ya bamu aiki a makaranta kuma ban iya ba, gashi Abbu da yake koya min karatun baya nan" zama nayi sosai akan gadona nace bani littafin in gani, ta bude jakar ta ta miko min na duba, Tawheed ne, tambayoyi akan imani. Murmushi nayi na kalleta nace "yanzu dai je ki kiyi sallahr magriba tunda an kira, bayan