Showing 42001 words to 45000 words out of 47794 words
Chapter 15 - Ni Da Abokin Baba Na Book Complete JeedderhLawals.txt
muka yi na 1-4, ni da Ramlah muke tafe a hankali a cewarta sai ta raka ni bakin gate, muna gab da fita daga parking lot kawai muka ga tsayuwar mutum a gabanmu kamar daga sama., Muneer ne! Na daga idanu na kalleshi a hankali, tunda abun nan ya faru ban kara waya dashi ba haka tunda muka dawo school bamu taba haduwa dashi ba. He was still the same Muneer kamar yadda na san shi, dogo, wankan tarwada....., Ramlah ta jefa mishi wata irin harara, "Malam Lafiya zaka tare mutane a hanya kamar wani tsoron thug?" bai kula da Ita ba idanuwanshi na kaina, ya kira sunana cikin sanyayyar muryar shi wadda ada nake jinta tamkar busar sarewa amma a yanzu, jinta nayi kamar kukan jaki. Yace "Nafeesah! Dan Allah zaki iya bani minti biyar muyi magana?" Ramlah ta yunkuro zata yi magana nayi saurin dakatar da ita, "it's okay Ramlah I've got this. I'll talk to him" ta kalleni sosai kafin ta dan matsa gaba ta bamu waje, na kalleshi a tsaitsaye, "so me kake son fada Ango-Muneer??" na fada sarcastically. Yace "Nafeesah I am really sorry akan abinda ya faru that night, sai daga baya na fahimci I acted rudely towards you, am sorry. Ba niyya na kenan ba na in tozarta ki, ban...." nayi saurin katse shi, "kaga Muneer! Idan akan wannan maganar ne kada ka damu, I've move on already, ni kaina sai daga baya na fahimci kuskuren da nayi na makalewa wanda baya sona. Kai ni sai daga baya ne ma na fahimci ashe ba sonka ne nake yi ba, burge ni kawai kake yi ni kuma da yake I was stupid then I thought it was love ashe it wasn't...." fuskar shi dauke take da wani irin expression wanda ya kusa saka ni dariya a take, daga ganin yadda yayi bai ji dadin maganar da nayi ba. Ko yana tunanin dana ganshi zan zube a gabanshi ina rokon ya aure ni ne? Ya kalleni da fuskarshi cike da damuwa, "Nafeesah......! Would you please give me a second chance? I promise to be what you want me to be, wallahi sai daga baya na fahimci cewa ina son ki, plss ki bani wata dama" ga mamakina maimakon farin ciki sai naji zuciyata tayi wani irin baki, lallai ma Muneer ni zai rainawa wayau? Fuska na hade nace "Muneer ka riga kayi wasa da damar ka in which I am very grateful for that don haka tun wuri kaje ka rungumi amaryar ka kafin kwado ya maka kafa itama ka rasa ta. All the best!" na zagaya ta gefen shi na wuce, da sauri ya tari gabana, "plsssss Nafeesah! Just a second chance! I know u love me, and I know that u didn't get over ur feelings for me!!" cike da wani irin jin haushin shi da kuma kaina ma gabadaya nace "feelings my a**!! Yaudarar kan ka kake so kayi Muneer, I don't Love you any more!!" na fada cikin daga murya, "now if u can please fuck the hell out of my sight plsssss, you are disgusting!!" amma da alamun ko kadan maganganuna basu shiga kunnen shi ba, kokarin matsowa gare ni ya fara yi da sauri naja da baya, just when he was about to take another step closer na jiyo muryar Harith daga bayan mu, "Nafeesah my Love!!"
~So What did you think about today's Chapter?
~What did you think about Harith sudden appearance in the story?
~Don't forget, recommendation door is open to me, so feel free to recommend and correct me anytime you spot a mistake in my writings
~Follow me on Wattpad @Jeeedorhh
~♥~Much love Ni Da Abokin Baba Na Fan's.....~♥~
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*28*
A hankali na juya na kalleshi, ya sake wanka yasa wani wandon jeans din Vogo da rigar CK mai V-neck, ya matso kusa dani ya tsaya gab dani yana kallon Muneer fuskar shi a cunkushe, sun dauki lokaci suna kallon-kallo shi da Muneer babu wanda yayi magana a cikin su, sai da naga shirun yayi yawa sannan na daga kafa na fara tafiya, na kalleshi nace "muje koh?" babu musu ya biyo bayana muka jera muka tafi, muna fara tafiyar ya tsaya cak tare da juyawa ya kalli Muneer da shima ya juyo yana kallonmu, yatsa ya nuna mishi cikin kashedi yace "and dude, stay out of my Fiancé side, if not....." ya juya ya cigaba da tafiya cikin takama har yana hadawa da wani bouncing, na bi bayan shi ina dan murmushin jin dadin shocked and horror expression din dana gani akan fuskar Muneer. Ramlah dake tsaye a gefe tana kallon dramar da muke bugawa ta kamo hannuna taja gefe tana tambayana wai da gaske na daina son Muneer? In ka kalli fuskarta a lokacin sai ta baka dariya, grinning take ear to ear kamar yaron da aka ba kyauta alewar bounty. Na sabule hannunta daga nawa nace mata "kinga jirana ake yi, anjima zamu yi magana" muka yi sallama na wuce na shiga motar Harith har ya tashe ta don haka ja kawai yayi muka wuce. Harara na jefa mishi, ya juyo ya kalleni "what??" nace "what was that for? That fiancé thing??" yayi rolling idanunshi, "baki gane bane? I was just trying to save you from him so that next time ba zai kara damun ki ba koda bana nan, by the way waye shi?" na danyi sighing softly kafin na kalleshi fuskana a dan hade don ya dauki maganar da zan mishi seriously nace "sanin waye Muneer ko rashin sa babu abinda zai tsinana maka don haka stay out of it, maganar fiancé kuma kada ka kara koda cikin wasa ne kuwa ko trying to help kamar yadda kace" ya kalleni yana murmushi cikin tsokana, "ko dai baki son inji cewa crush dinki ne yayi dumping dinki kuma ya dawo yace yana son ki?" kaina na kawar gefe naki kallonshi, naki jinin a tuna min da tarin yarinta da rashin hankalin da nayi akan Muneer. Amma Harith bai kyaleni ba cewa ya sake yi "tunda baya sonki me zai hana ki zo mu sasanta dake?" a fusace na kalleshi "stop messing with me fa Harith!!" ya tabe baki, "well, m not ai dama" nace "to ni nan da kake gani na I am taken ka gane?" ya juyo ya kura min ido na dan lokaci kafin ya maida hankalin shi ga tukin da yake yi yana chuckling, ban kula shi ba na janyo wayata ina latse-latse har muka isa gida. Yau ko godiya bai samu albarkacin jin ta ba, na fita daga motar har ina banging nayi cikin gida. Kai tsaye dakina na shige, nayi jifa da jakata akan gado kafin nabi bayanta nima na kwanta a rigingine ina tariyo abinda ya faru a makaranta ranar.
Vibrating din da wayata ya dauka daga cikin jakata ne ya dawo dani cikin hankalina, na danyi tsaki lokacin da nake laluben wayar, da kyar na iya bude idanuna da suka fara min nauyi saboda gajiya da barci na dora su akan fuskar wayar, sunan dana gani yana bouncing a jikin screen din wayar ne yasa naji zuciyata ta fara daka tsalle cikin wani irin farin ciki. Ya Allah! Yaushe rabona da inji muryar Abbu a rayuwa har na manta, Kun ganni nan kullum ina cikin page dinshi a facebook ina bibiyar rayuwar shi amma na kasa samun kwarin gwiwar kiran shi duk da cewa nayi kewar shi kuwa fiye da tsammanin mai karatu. Ganin kiran yana shirin katsewa yasa nayi saurin dagawa, sallama na mishi a nutse kuma cikin Karya murya, ya amsa cikin wannan muryar tashi cike da kasaita da wani irin huskiness daya kusa saka ni narkewa akan katifata saboda yadda naji wani electricity yana yawo a magudanar jini na. Daga can naji yana magana wadda tayi sanadiyar dawo dani duniyar Earth daga tafiyar da nayi zuwa Mars, cewa yayi "wato Nafeesah idan shekara zamu dauka ba tare da mun gaisa ba hakan bai dame ki ba koh? Ba kya neman mutane idan ba neman ki aka yi ba koh?" da sauri nace "Abbu ba haka bane ba fa!" yayi wata irin sassanyar dariya, "to ya ne Nafeesah?" na dan sosa wuyana tare da dan gyara muryata ina kokarin boye yadda dariyar Abbu ta kassara min gabbai, nace "Abbu muna karatu ne kuma dai bana so in kira ka ko kana aiki ko wani abu in takura ka" 'ina tsoron ka gaji dani, ina tsoron yin sabo da abinda zai zo yayi hurting dina daga baya" yace "that's not an excuse Nafeesah, when you feel like calling me just don't hesitate and call, zan amsa a duk inda nake no matter what m doing" na gyada kai kamar yana ganina nace "toh Abbu" ya sauya akalar hirar zuwa ta harkar karatuna, mun dauki lokaci muna hira kafin yace "Jiya muka dawo daga Beijing, nayo miki lodin tsarabar favorites chocolate crunch dinki, gabadaya na manta baki gidan ashe" nayi shiru kamar ba zanyi magana ba, wani irin dunkulallen abu ne naji ya makale min a kirji da kyar na iya danne shi na bude baki nace "Eyyah!! How I wish ina nan" yace "that's what m saying" nace "a ba Hafsy shi kawai, Allah ya nufa ba rabo na bane shi yasa" yace "um-uhm, abinda yake naki ne dole ki zaki ci shi Nafeesah. Pretty da kowa yaci nashi don haka kema dole naki zaki ce" na saki murmushi cikin jin dadin maganar shi, a hankali kuma cike da wani irin expectation nace "to ya za ayi yanzu?" shima yayi kasa da muryar shi har tafi tawa yin low, "ya za ayi? M thinking of coming to give it to you, Personally!" na karkada kunnena kamar ban ji sosai ba, sai dana dan yi hesitating kafin a hankali na maimaita "you?? Personally???!" sai dai can kasar zuciyata tsoro ne ya cikata, ina tsoron yace ba haka yace ba kila yace ba haka yake nufi ba.... Ya wanke min zargina ta hanyar cewa "yes, I'll come to you in baki tsarabar ki Nafeesah!!". Murnar dana ji ta cika min ciki ta ware a take lokacin da confusion ya dabaibaye ni, nace "amma why would you??" yace "because.... Because...... I.......!!" numfashi na ya dauke yayi sama yaki dawowa, na tabbata zuciyata ta buga sau dari cikin sakwannin da basu fi goma ba ina jiran inji karshen maganar shi, "..... Because I Can Of course Nafeesah!!" sai a lokacin numfashi na ya dawo kasa daga sama din da yayi, na fara yaki da zuciyata wajen ganin gudun da take yi marar adadi da numfashina da yake daidaituwa sun daidaita, a gefe guda wani irin disappointment ne ya lullube min zuciya. I'm such an idiot to think that Abbu zai fada min kalaman so! Yakamata in dawo daga duniyar Fantasy da Tunanin cewa wai Abbu zai so ni, Abbu yana da matar shi har da 'ya'ya abinsu and duk da cewa maimakon Happily, they are peacefully living together rather. Yace "besides Tu Me Manques!!" na dan yamutsa fuska, "Too mey Manqwe? Me kenan??" yayi er dariya, "just..... Sai anjima dai kawai. And please kiyi Kokari ki dinga kira na fa!" daga haka ya kashe wayar ya barni jiki a sanyaye kuma a sankame.
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*29*
Aunty Shafa tana ta shirye-shiryen komawa nan da kwana biyu don haka bata zama a gida, tana ta faman ziyarce-xiyarce da sallama gidan en uwa da abokan arziki. Ranar juma'ah karfe sha biyu muka gama lectures, muna fitowa ni da Ramlah daga lecture hall din na hango Harith jingine da motar shi hannunshi rike da lemun team yana sha, yana ganin fitowar mu ya dago mana hannu. Ramlah ta kalleshi ta kalleni tace "wai meke tsakanin ki da Harith ne?" na girgiza kai, "to wa ya sani Ramlah? Nima kin ganni nan ban sani ba wlh" ta tabe baki, "to Allah ya kyauta!" nace "ameeeeen". Daga nan muka yi sallama. Tun kafin in karasa ya bude min kofar motar, na shiga na zauna ya maida ya rufe. Yana shiga motar na fara jefa mishi korafi ko bari ya tashi motar ban yi ba, "Wai Harith ba nace na yafe zuwa dauka na da kake yi ba?" sai daya tashi motar muka fara tafiya kafin yace "I was just in the neighborhood ne, nayi dropping Sister gidan Amarya Murja ne, shine nace bari in biyo in dauke ki tunda nasan kin gama lectures dinki" nace "ni ban ga kana shirin komawa ba" ya juyo ya kalleni yana murmushi, "why?? Saboda kin gaji da ganina? To babu inda zan koma, na gama karatuna ai" na juya na kalleshi sosai, "woah! Da gaske?" yayi murmushi more like a grinning, "nayi kankanta koh?" kaina na gyada mishi ina kara kare mishi kallo, dariya ya saka har yana dukan sitiyari. Yayi parking a kofar gidanmu, na dauki handbag dina na rataya a kafada nace thanks fa! Ya gyada kai, "Anytime!". Kallona ya tsaya yana yi, har na saka kafa ta daya waje na juyo ina kallonshi, "meye kake kallona?" murmushi yayi ya kalleni fuskarshi na nuna yana shirin yin serious magana ne, yace "Nafeesah! How about We come together with a plan and help ourselves??" na kalleshi cike da mamaki, "mu taimaki juna? Me kake nufi??" ya daga kafada kamar maganar da zai yi ba mai amfani bace, "you see, there's this girl that I like....." yayi shiru yana kallona, ban ji mamaki ba haka babu shock din da naji saboda maganar shi, to ma akan me zan ji mamaki? Hankalina na mayar kan shi gabadaya ina sauraron shi, ya cigaba "she likes me too, sai dai bata son muyi aure nan kusa. Tana karatu a Turkish ne a Abuja and sai nan da shekara biyu zata gama, ni kuma na kosa... U know....!!" ya daga min gira ni kuma na Harare shi, ya kauda kai. Gyaran murya nayi a hankali bayan na gama digesting maganganun shi, nace "to daka gaya min mai kake tunanin zan yi ne??" ya juyo yana fuskanta ta sosai, "I want us to just play a game ta yadda zamu samu wadanda muke so Cikin sauki." nima na kara gyara zamana, "so??" yace "we will pretend to be lovers infront of them, I mean idan muka yi haka kishin mu zai sa su dawo kan hanya daga kaucewar da suka yi, zamu fara da Muneer ne ko menene? Tunda Ikhram 'Cara Mia' sai nan da two months zata zo gida" na hade fuska sosai, take naji raina ya wani baci, a xafafe na harare shi nace "idan har saboda Muneer kake zaton I'll be your partner in this game then you are wrong Harith, Muneer has become 'a past' ya daina existing a duniyata!" ya sadda kanshi kasa embarrassingly, nace "But we can play it with someone, not Muneer dai" ya dago yana kallona fuskarshi dauke da murmushi, "Really Nafeesah? Oh you're really going to save my life, thank you! But waye wanda zamu bugawa wasan?" nayi rolling idanuna, "just..... By the way meye ma'anar Cara Mia din da kace?" yayi murmushi sosai, "it means My Darling in Russia" na tabe baki nace "wani fi'ili!! Ni kam bari in shiga gida toh!" muka bude motar a tare muka fita yana cewa bari ya shiga ya gaida Mommy.
A hankali rayuwa tana tafiya tana juyawa, cikin Ikon Allah minti yake shudewa ya zama awowi, awowi su koma raneku, raneku su koma satika kamar yanda satika suke juyewa su koma Watanni. Kimanin watanni biyu suka zo suka shude, ni da Harith mun yi developing wani irin shakuwa a tsakaninmu, da yawan mutane suna cewa soyayya ce a tsakaninmu ciki har da su Mommy da Ramlah, mu kadai dai muka san menene Ainihin Akalar mu da juna.
A matukar gajiye muka shiga gidan ni da Daddy a safiyar ranar Sunday kenan muna ajiye numfashi daya bayan daya, Gym muka je wanda yake a cikin unguwar mu kamar yadda muke yi a cikin weekends. Muna shiga falon kicin na wuce na dauko mana ruwa mara sanyi na mikawa Daddy daya, nima na fara shan dayan. Sai da muka dan huta kafin muka wuce dakinmu, ruwa na watsa a jikina na saka kaya kawai na fita falo. Su Mommy har sun fara breakfast don haka nayi joining dinsu, a nutse muke cin abincin, ina jin Mommy tana gayawa Daddy bikin diyar wata Kawarta da za a fara cikin satin, tunda suka fara maganar na sha jinin jikina, a gaggauce na fara tura abincin ina so in tashi in bar musu wajen. Kamar daga sama naji Mommy ta jefo min tambayar da nake gudun tayi, "Ummiey Ke kam yaushe zaki gabatar da naki Mijin ne?" sau biyu kenan tana min maganar turo da wanda muke soyayya wanda nasan Harith take nufi, na turo baki tare da kara cusa fried plantain a cikin bakina, Mommy ta kalli Daddy tace "Habibty kana jin mu fa!" Daddy yayi dariya yace "ina jin ku, kina bukatar bakina ne?" Mommy cike da jin haushi tace "Allah Habibty hakan bai dace ba fa! Yarinya kamar Nafeesah saboda Allah ace har yanzu tana gabanmu babu zancen aure, ina mata zancen ta fitar da miji kuma wai ka wani dinga wani tambaya na ko bakin ka nake bukatar ji?? Anya Habibty kana ma so Nafeesah tayi aure