Showing 1 words to 3000 words out of 24397 words

Chapter 1 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt

[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs ƙarshen ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________


01


Idona tab ƙwalla nake kallon Dr Bilal wanda ya kasance shugabanmu ,ina mai sake maimaita kalmar “Gidan gawa Dr ? Wai ni ce zan kwana da gawa?”

Ba tare da ya dube ni ba ya ce “nurse Fatee kin fi kowa sanin ba na magana biyu ki wuce kawai ki tafi, wannan gawar babban mutum ce ya zama dole a bata tsaro na musamman sannan ki tabbatar kin yi bincike a tsanake kin gano mene ne silar mutuwarsa”

Ji na yi tamkar ya kwaɗa mini guduma,haka na soma tafiya ina waiwayensa ko Allah yasa ya ji tausayina ya ce na dawo amma ina tuni ya shiga sabgar gabansa.Ina buɗe ƙofar ɗakin gidan gawar na yi tsaye ina kallon gadajen da ke ɗauke da gawarwaki kowanne kuwa da likafaninsa in aka cire gawar mutumin da na zo dominsa.
Jiki na ɗan kyarma na soma duduba gawar ina rubuta abubuwan da na samu matsayin result,ƙiiii! Na ji ƙofar da na bari a buɗe ta fitar da sautin.Da mugun sauri na juya sai na ga handle na motsi yayin da kuma ƙarar murza key ta ziyarci dodon kunnena.

Cike da firgici na motsa da niyyar guduwa sai dai tamkar da akwai wani abu mai mugun ƙarfi da ya riƙe ni na kasa motsi.

“A bani giya na sha na ɗan kurɓe” na ji wata murya ta faɗa amma babu alamun wanda yayi ta saboda ni ɗaya ce mai rai a ciki.Fiƙi-fiƙi haka nake baza na mujiyata waɗanda suke tsiyayar da ruwan hawaye kamar wacce aka zuba wa yaji,dukkan illahirin jikina kuwa rawa yake.
Takardar da ke hannuna ce na ji ta soma motsi,dubawar da zan yi sai na ga ta rikiɗa ta zama farin ƙyallen likafani daidai nan kuma na ga abin da ya girmi tunanina.Gawar mutumin ce ta tashi zaune raɗam kan gado,wani irin kallo ne yake jifa ta da shi da wasu IDON SHARRI(MRS SADAUKI) masu matuƙar firgici da kaɗa hantar mutum.Ban san inda ta haihu a ragaya ba sai tsintar kaina na yi kwance a gadon asibitinmu,gefena ƙawata ce Rahinatu ke zaune tana duba yadda ƙarin ruwan da ke maƙale a hannuna ke tafiya.

“Ƙawata kin tashi? ” ta furta tana mai tasowa tare da ɗora hannunta kan goshina da nake jin tamkar zai tsage.Ban kai ga bata amsa ba Dr Bilal ya shigo yana mai cewa “baƙonmu ya iso tun da ta tashi ku yi sauri ku fito kafin ya farga babu wani a cikin jerin sunan da za a basa”sai kuma ya fice.Rahinatu ta ja tsuki tana mai cewa“duk duniya na tsani tsatsauran mutum,sam bai da mutumci kawai don ya ga tauraronsa yana haskawa.Kin ga tashi mu tafi don yana iya sawa ma a kore mu” ta ida faɗar haka tana mai cire mini ƙarin ruwan,ina shirin saukowa kuma wata nurse ta sake leƙowa ta ce “Rahinatu Dr Bilal ya ce me kike jira alhalin ke ce za ki gabatar da kalaman farko na buɗe taro?” da wani irin mugun sauri Rahinatu ta fita tana yarfa hannu.Ni kuwa dakyar na iya ƙoƙartawa na tashi,duk jikina ciwo yake kamar wacce aka ɗirkawa na jaki.Baƙon da za a yi yau yana da matuƙar muhimmanci wannan ya aka shirya abubuwa da yawa,ciki kuwa har da jawabin da Rahinatu za ta yi sannan ni kaina an bani topic ɗin da zan gabatar amma tsabar yadda aka jijiga ruhina na manta shaf.



Ina fitowa direct ofis ɗin Dr Bilal na wuce so nake na yi ɗan watsa ruwa ko zan ji dama,ina buɗe toilet ɗin na yi tsaye ƙyam tamkar wacce aka shuka.Dukkan illahirin jikina kuma rawa yake,na fito da idona tulu-tulu ina kallonsa sam ban farga na yi suman tsaye ba sai da na ji muryar Dr Bilal yana kiran sunana firgigit na dawo hayyacina sai dai babu mutumen da na gani a yanzu yana fitsari.


“Me ki ke jira? Me yasa kike neman hanyoyi da za a kore ki Sweety?” Dr Bilal ya faɗa cikin taushin murya,na turo baki gaba kafin na shige banɗaki na share shi ba tare da na basa amsa ba.Wato Dr Bilal saurayina ne,amma in muna asibiti mancewa yake da wannan alaƙa yana yi mini tsawa kamar sauran da ke ƙarƙashinsa.Sai da na yi wanka na fito,na ɗauki farar rigar likitoci na ɗora daga sama sannan na nufi can saman bene inda ake gudanar da taron.

Ina shiga da fuskar mutumen nan na fara cin karo,fari ne dogo mai cikar ƙasumbar saje da kuma gemu.Sumar kansa doguwa ce sosai ba kamar ta sauran maza ba,don har sai da ya ɗan toje ta daidai tsakiya.Fuskarsa sam babu alamun wasa,kana ganinsa ka kai matsalalen nan masu baiwa ahalinsu da kuma na kewaye da su wahala.A takaice dai bayan miskilanci akwai izza,girman kai da ɗagawa a tattare da shi,da sauri na ɗauke idona a kansa ganin ya juyo facing inda nake,na nemi wuri na zauna ina mai sunne kai zuciyata na ɗan dokawa yayin da idona ke hasko mini irin yanayin da na same shi.


Zaune dai nake a cikin ɗakin taron amma sam hankalina bai wajensu,tunani ne barkatai ke kai komo a cikin laɓuɓuwar kwanyata da ba ta san komai ba sai soyayya.Ina cikin tunanin wasiƙar jaki na ji muryar Dr Rashid na cewa “Nurse Fateema ta zo kan dandamali domin gabatar mana da jawaben da ta samu dangane da binciken gawar da ta yi”

Wani irin rasss na ji,yayin da kuma na ɗago kaina da mugun sauri ina kallon mutanen da ke wurin waɗanda kusan duk kallonsu ya dawo kaina.Dr Bilal na kalla sai na ga yana yi mini wani kallo,sai kuma a yanzu na tuna cewa lokacin da ina toilet ya ce na ɗauki takarda na nan kan teburi.


Dakyar na iya miƙewa tsaye na nufi wurin,ƙafafuna na harɗewa cike da tsoro na ƙarasa Dr Rashid ya miƙo mini sifika.Shiru na yi kafin na ɗan lumshe idona nan take kuma na soma jin wasu jawabai na shigo mini kwanya waɗanda tabbas su ne suka faru da ni a lokacin da na shiga ɗakin gawa.


“Kamar yadda kuka sani ire-iren mutuwar nan ta zama ruwan dare game duniya,to yau ma irin ta ce ta faru ga yalaɓai Alhaji Lawan.A binciken da na yi na samu raunuka a wasu sassa na jikinsa waɗanda ido ba su iya ganinsu sai dai kyakkyawan ruhi.A takaice dai ƙafarsa ta hagu babu ita,sannan an cire sinadarin idonsa,hatta jinin jikinsa babu globules rouges/red blood cell hakan shi ya baiwa igiyar saita numfashinsa damar tsayawa cak,huhunsa kuma ya bushe ƙamas jijiyoyinsa kuma duk suka tsinke.Waɗannan hare-hare da ruhinsa ya samu su ne kuma suka bai wa shararrun likitocinmu damar saka masa oxygene sai dai abin da ba su sani ba shi wannan bututun iskan ba komai ba ne sai ...sai...sai...” yadda na ji an shaƙe mini wuya ya hana ni ƙarasa abin da nake so,a dole na buɗe idona sai dai babu kowa kusa da ni amma kuma tabbas ina jin hannu a maƙoshina.Cikin abin da bai fi minti biyu ba na fita hayyacina,na zube ƙasa da sauri aka soma bani taimako ina jin muryar baƙon namu yana cewa “ku ɗauke ta ku fitar da ita tana ɓata mana lokaci alhalin da sauran aiki gabanmu”

Nurse Rahinatu ce da wata nurse ɗin suka kama ni don fitar da ni,duk da ina cikin mugun hali bai hana ni zuba masa raunatatun idona ba ina kallonsa a matsayin mugu wanda bai da tausayi.


“Ku kai ta ofis ɗina ina zuwa” muka ji muryar Dr Bilal a bayanmu,hakan suka yi kuwa.Kan gadon da yake duba marar lafiya suka kwantar da ni,ita ɗayar ta yi tafiyarta yayin da Rahinatu ta zauna tana duba ni.

Murya can ƙasan maƙoshi na ce “miƙo mini takardar da ke kan teburi”
Zuwa ta yi ta ɗauko tare da miƙo mini,na karɓa na karanta jawaben ƙaryar da Dr Bilal ya rubuta waɗanda su ne yake so na gabatar.
Ina riƙe da takardar ya shigo,da sauri Rahinatu ta fita yayin da shi kuma ya matso cikin masifa yana cewa “me kika yi haka? Kin sha ƙwaya ne ko me? Wato ba don na dakatar da ke ba dukkan sirrin za ki sanar?”


“Me na yi? Wani sirri kuma kake faɗa Sweety?” na faɗa don ni sam ban ga aibun abin da na faɗa a ɗakin taron ba.

“Dalla yi mini shiru kin wani buɗe baki sai zuba kike yi kamar an kunna rediyo mtsww! Tashi ki fita” ya daka mini tsawar da na ji har ƙasan raina.

Idona tab da hawaye na ce “amma sweet...” cikin masifa ya katse ni “kin ga Fateema ki fita na ce,ki je gida zan neme ki daga baya”

A yadda nake ganin tsantsar ɓacin rai a idonsa yasa ban ƙara minti guda ba na fito ina kuka,idona sun rufe sam ban gani hakan yasa ban ga tawowarsa ba sai ji na yi na kai ma abu karo.Na yi baya zan faɗi ya taro ni,kafin kuma na ida tsayuwa kan ƙafafuna ya yaɓo mini wata baƙar magana cikin amon sautinsa mai matuƙar firgitarwa.

“Jarababbiya kawai!” sai ya yarɓa ni gefe,na yi tangal-tangal zan faɗi amma Allah ya tsare ban faɗin ba.Ta ƙasan gashin idona da ya jiƙe sharkaf da hawaye nake kallon lokacin da aka buɗe masa baƙar motarsa ya shiga.Sai da motar ta fita daga harabar asibitin kafin na ɗaga ƙafata na fito,taxi na samu ya kai ni gida sai bayan na sauka ma ne na tuna cewa na baro jakata can asibiti.Sai da na karɓo masa kuɗinsa wurin Mama wacce duk ta rikice na ganina da ta yi cikin halin baƙin ciki.

Ina shiga can uwar ɗaka na shige na rufe ƙofa,na ci gaba da rera kukana wiwi tsakanin kalaman Dr Bilal da kuma na baƙonmu sai na rasa na wanne suka fi yi mini ciwo.


“Anty Fatee don Allah ki fito ki sanar da mu abin da ke damunki,kin ga muna cikin murna amma kin zo kin ɓata mana tsari” ƙanwata Maryam ta faɗa daga can bakin ƙofa tana ɗan bubugawa.


Tashi na yi na buɗe,sai kuma na ƙanƙame Mama na fashe da sabon kuka tare da yi mata bayanin Dr Bilal ya yi fushi da ni.Sanin matsayinsa a zuciyata,yadda nake mugun ƙaunarsa da sonsa yasa Mama ta kira shi a waya don jin abin da ya haɗa mu amma sai da ta jera masa kira kusan biyar a ƙarshe ma sai ya dinga maido mata kiran kafin ya kashe wayarsa gaba ɗaya.

Duk ina zaune komai ya faru,abin da ya yi sai ya haifar mini da mugun zazzaɓi.Magani ma ƙin sha na yi,don na gwammaci na mutu kan na rasa Dr Bilal.Towel Mama ke jiƙawa da ruwan sanyi tana ɗora mini a goshi,yayin da kuma ƙanwata Maryam ke yi mini sannu.Ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba,ko da na farka jakata na gani ina shirin tambaya sai ga na tsinkayi Rahinatu kan sallaya.

Na ja ajiyar zuciya,ta juyo muna haɗa ido sai ta kawar da kai.Sai na ji jikina ya ƙara yin sanyi,miƙewa na yi ni ma don yin sallah sai dai ina shiga toilet na samu baƙon watana ya zo .Wanka kawai na yi na saka kaya maras nauyi na kimtsa sai na fito,kusa da Rahinatu na zauna ba tare da na ce komai ba.


“An bai wa Dr Bilal hutun wani lokaci,yana cikin fushi sosai duk ya farfasa abubuwa da dama.A shawarce ki ɗan basa lokaci har ya sauko” Rahinatu ta faɗa cike da rauni . Idona suka kawo ruwa na ce “ke ma laifina ki ke gani?”

Ta ce “eh to kusan haka ne,ke ma me yasa za ki faɗi abubuwan nan alhalin kin san faɗi tashin da ake yi na ƙaryata cewa akwai BAƘIN RUHI (MRS SADAUKI) a kaf asibitocin garin nan mai shayen jini?”

Murya a raunace na ce “amma ai abin da na gani ne na faɗa ”

“A'a ki ka dai ƙirƙiro,saboda a some aka kawo mana ke kowa ya san yadda kike da tsoron mutuwa da kuma gawa.Abin da ki ka faɗa kuma sam bai taɓa faruwa ba a cikin asibitinmu ba”


Na ɗaga kai na dube ta da kyau kafin na ce “ina so ki yarda da ni,wallahi duk abubuwan da na faɗa gaskiya ne”

“Kenan ke mayya cewa?”kamar subutar baki hakan Rahinatu ta faɗa ,sosai kuma kalmar mayya ta bugi zuciyata sai na ji kamar na shaƙe ta.Amma na yi shiru na ci gaba da juya na mujiyata ina kallonta da su,cikin tsarguwa da kallon da nake yi mata ta ci gaba da cewa “to in dai ba haka ba ta ya aka yi kika san da duk abubuwan nan da suka faru da Alhaji Lawan? Kuma in ba ki manta ba kwanan baya an yi mana darasin ceton kai inda aka faɗa mana siffofin Mayu da kuma yadda za mu gane mutum mugu ne,ke kuma ba ki da ko ɗaya ko kuwa kin taɓa jin sha'awar cin naman mutum?”

“Da a ce ni mayya ce da wallahi babu abin da zai hana na damƙe kurwar Dr Bilal ” na faɗa ina cije leɓe.Rahinatu ta yi murmushi ta ce “yanzu dai zan wuce gida sai mun yi waya”

Sai da na yi mata rakiya har bakin ƙofar gida inda motarta take sannan na dawo ciki.Jakata na buɗe na ciro wayata,nan na ci karo da saƙon Dr Bilal wai rabu da ni na je na nemi maye irina.


Saƙon na dinga maimataiwa ina karanta shi kamar mai lesson kafin na tambayi kaina “kenan yana nufin ni mayya ce?” sai kuma ga hawaye shaaaa.....
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________


02


“Wato Dr Bilal na nufin ni mayya ce? Ni mayya ce ahan ”

Ƙarar faɗuwar faranti yayi daidai da dire ayar tambayar da na yi kaina,Mama wacce ta saki farantin hannunta,idonta suka nuna tsananin firgici da tashin hankali ita na nufa ina mai tambayarta “Mama wai ni mayya ce?” ba ta bani amsa ba sai zaman ƴan bori da ta yi tana fitar da gumi,halin da na ganta a ciki sai ya mantar da ni nawa tashin hankalin.

“Mama? Mama?” haka na dinga kiran sunanta ina jijigata ganin ta ƙame ƙam kamar ɓeran da lantarki ya damƙe.

“Maryam? Maryam zo Mama babu lafiya” na faɗa cikin ɗaga murya,babu jimawa kuwa ta fito nan na ga ikon Allah Maryam na shafar fuskar Mama sai ta dawo normal tamkar ba ita ce shock ya damƙe ba.


Numfashi Mama ta ja haɗi da lumshe ido sai wasu guntayen hawaye suka sirnano mata,Maryam ta ja ajiyar zuciya tana mai dubana na wani ɗan lokaci kafin kuma ta ce “don Allah Mama kar ki ce komai ,in kika faɗa hankalin anty Fatee zai tashi sosai”

“Mene ne ba ki son a faɗa mini Maryam?” na tambaya.
“Ku tashi ku haɗa kayanku” Mama ta faɗa cikin bayar da umarni.Maryam ta soma miƙewa,a dole ni ma na take mata baya juyin duniya ta ƙi bani amsar tambayoyin da nake yi mata sai ma haɗa kayanmu take yi cikin manyan akwatuna.


A haka Mama ta shigo ta dube ni sai kuma ta kawar da kai,ta ce “ki ɗauki duk wani abu da kika san yana da muhimmanci ki bi bayan ƴar uwarki ku tafi”

“Ina za mu je? Wai Mama mene ne haka?” na tambaya tare da nufo ta.Ta ce “ban son yawan tambayoyi ki wuce ki bi bayanta ku tafi”

Idona na zubar da ruwan hawaye na ce “babu inda zan je har sai kin faɗa mini taƙamaimai abin da ke faruwa”


“Ba mu da wannan lokacin Fateema ki wuce kawai ku tafi kafin kowa ya san wace ce ke” Mama ta faɗa cikin ƙaraji.

Cikin sanyi na ce “wace ce ni kuma Mama? Meke faruwa haka?” ba ta kai ga bani amsa ba muka soma jin jifa ko ta ina haɗi da ashar.
Abin da na sani uwa tana bada amanar ƴaƴanta ne ga babba daga cikin yaranta,sai dai a yau karon farko na ga inda uwa ke damƙa amanar ƴarta babba ga ƙaramar ƴarta.

“Maryam ki kula da ita duk rintsi kar ki bar ƴar uwarki ta yi kuka,na baki amanarta ku je kawai sai in na same ku a can” Mama ke faɗar haka bayan ta damƙa hannuna cikin na ƙanwata Maryam wacce banda ɗaga kai babu abin da take yi.Ban taɓa sanin gidanmu nada wata ƙofa a baya ba sai yau da Mama ta buɗe mana ita,kaf kayanmu aka jera cikin wata tsohuwar mota ƙirar ta wani shuɗaɗen zamani.Dukkanmu a baya muka zauna,hannuna na dama na cikin na Maryam yayin da kuma na hagu na riƙe Mama gam ina hawaye sam bakina ya kasa furta komai.

Wata irin ƙara muka ji wacce ta fi kama da ta ɓalle ƙofa,sai a lokacin kuma Mama ta fizge hannunta da ƙarfi ta koma can ciki yayin da kuma motar wacce babu direba a ciki ta soma gudu da mu.

Faɗar tashin hankalin da nake ciki ɓarnar baki ne,kamar wata ƙaramar yarinya na ce “Maryam don Allah ki taimaka ki mayar da ni wurin Mama”

Ta ƙara jimƙe hannuna tana mai cewa “anty Fatee zamanki a Kibri ya ida na har abada,ki nutsu ki kwantar hankalinki za mu koma Duwala da zama can babban birni” ina shirin sake yin magana ta yi wata alama da tafin hannunta nan take kuma na ji wani abu ya rufe mini ido ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai da na ji Maryam na tashe ni tana cewa “anty Fatee ki tashi mun iso”


Dakyar na ware idona ina kallon yadda ruwan sama ke sauka ta tsohon gilashin motar.Maryam ce ta buɗe murfin muka fito,har zuwa yanzu kuma hannuna na cikin nata ta jimƙe shi.Sanyayyar iskan garin ce ta buge ni,yayin da kuma ta feso mini ruwan tsatsafin da ake a yi a fuska.Na ɗan lumshe ido kafin kuma na buɗe su ina kallon ƙatuwar Palace ɗin gabana wacce iya yadda aka tsara katangarta ma abin kallo ce ga shuke-shuke ko ta ina.


Muna ƙarasawa bakin ƙofar Mai gadi ya leƙo ta wata ƴar huda ya ce “su wane ne ku?”

Sai da Maryam ta dube ni kafin ta yi gyaran murya ta ce “ka ga motar da ta kawo mu can”
Mai gadin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login