Showing 24001 words to 24397 words out of 24397 words

Chapter 9 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt

duhu,sai kuma wata murya da ta cika wurin baki ɗaya.


“Ke ce wacce aka zaɓa domin kammala mission mai muhimmanci. Dukkannin ƙarfin iko na power da suke ɓoye a jikinki su ne makulin da za ki ceto duniyarmu wacce aka rushe.Amma kafin nan dole ki zauna ki koyi yarenmu na ƙarnin baya,sannan ki san muhimmancin TUKUNYAR MAYU da kuma abin da take nufi” muryar na gama faɗar haka sai na ji ƙafata ta fito yayin da kuma wata ƴar mitsitsiyar tukunya kamar wacce Bugaje ke yin shayi ta bayyana a hannuna na haggu.

Daidai bakin tukunyar shayin wani hayaƙi ya soma fitowa mai yawa,ina taɓa shi wani irin shock ya damƙe ni kamar na lantarki dukkan idanuwana suka firfito yayin da kuma wani girgije ya bayyana a gare ni wanda ya hasko mini dukkan rayuwata ta baya da kuma ta wacce da zan yi a gaba.Lokacin da shock ɗin ya sake ni,sai na ji tamkar na ƙurmar ihu jin wai ba Mama ce mahaifiyata ba,sannan Mu'azzam yana ɗaya daga cikin ƙaddarar rayuwata wanda aka umarce ni da na kare daga sharrin abin harinsa.


Ido na lumshe tare da motsa laɓana,iska ne ya fige ni ya kawo ni can gidan Mu'azzam a kuma ɗakinmu.Zaune na yi dirshen a tsakiyar ɗaki ina kallon ƴar butar shayin wacce a zahiri ita ce TUKUNYAR MAYU da duk ƙasar Kamaru da kewayenta ke cece-kuce a kai.A zuci na ce ‘ kenan duk mutanen da ke ikirarin akwai tukunyar mayu a asibitocinsu ƙarya ne?’ wani ɓangare na zuciyata ne ya bani amsar ’eh duk ƙarya ce, wannan ta hannunki ita ce ta gaske kuma mallakinki ce,ke ce Goddess kuma ke kike da alhakin kula da ita’
Wani murmushi na yi na samun wata rayuwa a wata duniya ta daban kafin na yi wani furici kamar ƙyaftawar ido kuwa na tsinci kaina a cikin ƴar ƙaramar tukunyar,ta ƴar hudar nan na fito sai dai ba a siffar mutum a macijiya.Direct wajen taron ƴan diner na fantsama ina gudu haɗi da ziro harshe .

Daidai nan free page ya ida,duk mai son shiga paid group za ta biya 509 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822.Don Allah ga detail nan in kina so ki tura kai tsaye ki bani shaidar biya,wacce ta san kuma ba ta shirya ba ki yi wa girman Allah kar ki yi mini Magana

*NB:* yanzu nake typing 18.08.25 in kuma na kammala shi 1k ne kuɗinsa.

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login