Showing 12001 words to 15000 words out of 24397 words
Chapter 5 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt
ban son ji,ban son kuma mutane masu sonsa”
Dr Mu'azzam ya ƙara tawo kusa da ni idonsa na wani irin hasken imani,ya ce “tun da har ba ki son haka to ki fita ki koma duniyarku,ki bar gangar jikin nan ta zauna lafiya”
Murya a shaƙe ruhin da ke cikin jikina ya ce “gangar jikina ce,saboda ita ɗin tawa ce kuma babu wanda ya isa ya mallake ta in ba ni ba ”
Mu'azzam na jin haka ya soma yin wasu addu'o'in masu mugun ƙarfi wanda hakan ya saka ruhin jikina don dole ya koma ya lafa sai tunanina ya dawo.Wata irin gajiya ce na ji a jikina wacce ban san dalili ba,don duk abin da ya faru da ni na manta ban riƙe komai ba.
Shi ne ya zo ya miƙar da ni tsaye, toilet ya kai ni bayan ya yi addu'ar shiga.Fuskata ya wanke mini da bakina da kuma hannu da ƙafa,ya motsa baki dakyar ya ce “ki ida wanke sauran jikinki sai ki saka wannan ” sai miƙo mini irin rigar wankan nan da ake sakawa kafin ya fice.
Hijabina da rigata da suka ɓace da jini na cire da kuma sauran suturar da ta rage,na jawo pampon na ida watsa ruwa ga dukkan jikina bayan na gama na saka rigar kamar yadda ya ce sai dai fa ba zan iya fita da ita ba saboda ba ta saka ƙasa ba.
“In kin gama wankan ki buɗe ƙofa ki karɓi wannan ” na ji muryarsa daga bakin ƙofa,sai na je na ɗan buɗe tare da miƙa masa hannu sai ya miƙo mini leda na karɓa na maida ƙofar.Da na duba sai na ga iya auduga ce babu pant ga kuma wanda nake da duk ya jiƙe,dole tasa na yi dabara na saka ta haka nan sai kuma na ƙara zuwa bakin ƙofa na yi tsaye.
“Ki fito” ya faɗa a dake,cikin rawar jiki na fita ina ƙanƙame jikina.Ya ja wani dogon tsuki kafin ya kamo hannuna,ganin zai fita da ni murya na ɗan rawa na ce “na baro pant ɗina a toilet,kuma...kuma haka zan fita?”
“Kin ga malama ki yi mini shiru da bakinki,shi pant ɗin a tare aka haife ku? ” ya faɗa yana hararena,idona suka kawo ruwa na ce “rigar ba ta sauka ƙasa ba ƙafafuwana a fili”
Cak ya tsaya ya soma yi mini masifa “to me za a kalla a jikinki? Wa ki ga yana da lokacin kallonki a kaf asibitin nan? Ko ba ki ga duk mahaukata ne ba su sun san wani abu kallon jiki?”
“Kenan kai ma mahaukaci ne?” na samu bakina da furtawa.Wata irin damƙa ya yi wa hannuna har sai da na saki ƴar ƙara kafin ya soma jana ƙiiiiii har muka fito harabar asibitin,cikin sauri na ce “ka tsaya ƙunzuguna ya faɗi!” tamkar zai shaƙe ni haka ya tsaya yana kallona daidai nan kuma wasu likitocin maza suka nufo mu.Da mugun sauri ya buɗe mota ya tura ni ciki,ya duƙa ya ɗauki audugar da na yi amfani da ita ya cillo min abata.
Daga inda nake zaune na ga suna magana da likitocin amma ban ji abin da suka ce ba,can kuma ya buɗa mota ya shigo tare da yi mata key muka bar asibitin.
Yana tsaka da tuƙi ya soma jan tsuki wanda ban san dalili ba,da na ga ya mayar da tsukin kamar mai jan casbi na ce “ya dai meke faruwa?”
A zafafe ya ce “ina ruwanki da ni ? Ki iya da taki matsalar ki bar mini tawa ”
Cikin sanyi na ce “ka yi haƙuri na yi tunanin ko zan iya taimakonka ne” bai ce mini ufan ba har ya zo wajen irin toilet ɗin nan na kan hanya ya tsaya,sai da ya da ya rufe fuskarsa da wani ƙyalle sannan ya ɗauki gorar ruwa ya fita ni dai ina kallonsa har ya shiga banɗakin.
Mu'azzam na shiga toilet ya ga hannunsa da kumfan jini har ya bushe,ya ja tsaki ya fi sau goma yayi ta wankin hannunsa a zuci yana cewa ‘ tun da ta shigo rayuwata muka ƙulla alaƙa da matsala,in ba masifa ba mene ne abin yin sakaci har ƙunzugunta ya faɗi ƙasa’ kusan ruwan a wankin hannu suka ƙare,yana gama fitsarin ya fito ya yi cilli da gorar yana hararen nurse Fateema da ke can zaune cikin mota.
A yadda ya rufe murfin da mugun ƙarfi na fahimci cewa yana cikin fushi,sai na ƙara kama kaina da tunanin ta ya zan shiga cikin gidansu da wannan rigar wankan? Me ƴan aikin gidan za su ce waɗanda har zuwa yanzu ban san adadinsu ba tsabar yawansu? Tamkar ya shiga tunanina kuwa sai na ga yana satar kallon ƙafafuwana da suke a fili,wani ƙaton mall ya tsaya ya saya mini doguwar riga ya cillo mini yana wani haɗe rai amma ban damu ba na kuwa saka har da ƴar guntuwar godiya na yi masa.
Muna isa sai na tarar da Ammynsa ta shigo,wani irin farin ciki ne na ji ya mamaye ni har ban san lokacin da na je a guje na rungume ta ba.
“Har kun dawo? Ban jima da shigowa ba ni ma,ina shi Mu'azzam ɗin?” Ammy ta tambaya.Daga can baya ya ce “ta ya za a yi kin ganni tun da kin canza yaronki da baƙuwa” a sautinsa za ka iya tsinkayo tsantsar kishi.Sai kuma ya tako inda muke tsaye yana mai cewa “malama matsa daga nan na ji ɗumin mahaifiyata ” da mugun sauri kuwa na je zan jaye jikina daga na Ammy amma ta dakatar da ni tana mai cewa “rabu da shi ai saboda ke na zo garin,ina can ina tunanin halin da kike ciki da na kasa jura shi ne na zo ”
Wasu yawu na haɗiye na tsoro ganin yadda Mu'azzam ke ƙara gangame fuska, murmushin ƙarfin hali na yi ina mai cewa “Ammy zan shiga daga ciki in kun gama gaisawa sai na fito”
“To Fateemana ki je zan zo da kaina na same ki” Ammy ta faɗa tana murmushi kafin ta kama hannun Mu'azzam kamar wani yaro su haura sama.Ni ma can ɗakinmu na wuce ,abu na farko toilet na shiga na haɗa ruwan ɗumi na yi wanka sannan na zo na kimtsa.Wata irin yunwa nake ji hakan yasa na fita a tsorace zuwa kitchen,Maryam na tarar da Joy suna hira kuma da dukkan alamu gulmata suke yi.
Ya ɗan sunne kai yana mai cewa “ga ma ta nan ta shigo Please ki sanar da ita”
Maryam ta yi ɗan murmushi tana mai cewa “kar ka damu Joy zan yi mata magana,ungo wannan ka kai kan dianing” ya karɓa tare da ficewa.Sai a lokacin ta dube ni tana gimtse dariya,na ce “ni dai yunwa nake ji ki fara bani abinci kafin wannan shirmen ”
Ta ce “ban ƙarasa ba amma ga snack ki ci” ta zuba mini shi cikin plate jikina har rawa yake na karɓa,ina shirin fitowa muka yi karo da Joy ina shirin faɗuwa ya kamo hannuna yana wani murmushi haɗi da bani haƙuri.
Wata mahaukaciyar tsawa muka ji ,da mugun sauri ya saki hannuna jikinsa ya soma yin ɓari yayin da shi kuma shugaban ƴan tsamin rai ya ƙaraso yana zuba masifa har da cewa in iskanci Joy ya sa gaba zai kore shi daga aiki,bawan Allah shi kuma har da hawayensa.Bayan ya gama yi wa Joy bala'i ya juyo kaina,plate ɗin hannuna ya karɓe ya miƙawa Joy kafin ya damƙi hannuna ya soma jana.
Tsabar masifa bibiyu haka yake taka step ɗin har muka isa can sama,wanda yake tamkar wata fadar sarki.Yarɓi ya yi da ni yana mai nuna mini hannu,sai dai kafin ya yi magana Ammy ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunan da ke jere tana mai tambayar “meke faruwa a nan? ”
“Ki tambaye ta! ” ya faɗa cikin ɓacin rai,haka kawai na ji kuka ya zo mini na je bayan Ammy na ɓuya.
“Kaf patient ɗin da na taɓa samu babu wacce ke caza mini kai irinta,banda wahala da matsala babu abin da take kawo mini” ya faɗa kamar zai fashe.
“Ka yi haƙuri Mu'azzam ba ka ganin har yanzu ita ɗin yarinya ce?” Ammy ta faɗa .
“Babu wata yarinta kawai mahaukaciya ce,ina ce Maryam ƙanwarta ce amma kin taɓa ganin ta yi shirme irin nata? Yanzu fa don sakalci a tsaye na ganta tare da Joy yana yi mata murmushi har da wani riƙe hannunta,amma da yake ita sokuwa ce ko kaɗan ba ta damu ba”
Ammy ta yi murmushi tana shirin yin magana Joy ya zo yana cewa “yalaɓai ka yi baƙuwa ta ce na baka wannan ”
Karɓa yayi ya karanta sai na ga ya dube ni kafin kuma ya fice.Zuciyar Mu'azzam har wani dokawa take da sauri,a can bakin ƙofar shigowa ya je ya tsaya a daidai lokacin kuma mai gadi ya yi masa da nuni da hannu sai ya nufi ɓangaren.
Daidai tsohuwar motar da ta kawo su Fateema ya ja ya tsaya yana kallon matar wacce take duƙunƙune cikin wani tsohon bargo.
“Taso mu shiga daga ciki” ya faɗa ,Mama wacce jikinta yake cike da rauni ta yi ƙarfin halin tashi tsaye.Bargon ta jawo ta rufe fuskarta da shi sannan ta take masa baya suka shiga daga ciki,suna tafe yana addu'ar Allah sa Ammy ta ja mahaukaciyar yarinyar can sun bar sashensa ai kuwa ba su nan.
Wani ɗaki ya kai Mama,wani haɗin magani ya yi mata mai kyau ta sha sai kuma ya je ya shiga toilet ya yo fitsari ya dawo ya zauna ya tisa ta a gaba.
Cikin rauni ta soma yi masa magana “sunana Halimatu,na fito daga garin Kibri a wani ƙauye da ke nan kusan rugar farko ta Fulani .Ƴata guda Maryam,sai kuma Fateema wacce ta kasance ƴar kishiyata ” tana kawowa nan sai ta yi shiru.Mu'azzam ya ce “kenan ba ke ce ainahin mahaifiyar Fateema ba?”
Ta jinjina kai kafin ta ci gaba da cewa “Hindu ta kasance kishiyata amma sam ba mu yin irin wannan mugun kishin,hasali ma tamkar ƴar uwa haka ta ɗauke ni.Mijinmu malam Abdu ya kasance manomi sannan makiyayi,a kullum cikin kawo mana kayan lambu da sauran abubuwan masarufi yake da kuma kawo ciyawa wa dabbobinsa hakan yasa gidanmu bai rabo da macizai kusan kullum sai ya fitar mana da su.
Wata ranar Alhamis ina madafa ina tuƙa tuwo sai na ji ihun Hindu tana cewa “na shiga uku maciji ! Maciji a shimfiɗar Fatee” a daidai lokacin da nake fitowa a wannan lokaci ne kuma da idona na ga Hindu ta saka wani mashi ta tsire macijin tare da cilla shi can cikin ciyayi sai kuma ta ɗauke ƴarta Fateema wacce a lokacin ba ta fi wata shidda ba da haihuwa.
Na ƙarasa tare da yi mata jajaye kafin na koma madafa na ci gaba da yin girki.Bayan na gama ne na kira Hindu don cin abinci,a nan ne fa muka ga wani sabon al'amari hannun Hindu ya kumbura ya yi suntum ya cika da ruwa” Mama na kawowa nan sai ta yi shiru tana goge ƙwalla,yayin da Mu'azzam ya ce “jira na shiga banɗaki na dawo” sai ya je ya shiga toilet cak ya tsaya saboda inuwar mutum da ya gani a tsaye cikin ɗan madaidaicin madubin da ke manne da bango.......
Ga masu son fara yin payement,regular group 500, VIP group 1k via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪
*FCWA*☀️
________________________
07
Kafin Mu'azzam ya yi wani motsi madubin ya yi wani irin motsi yana bado haske mai ƙuna,ya kai tafin hannunsa ya kare fuskarsa.Ƙarar tarwatsewar madubin shi yasa ya maido dubansa ga bangon,a gaban idonsa inuwar ke ƙara nitsewa tana shigewa cikin bango har ya bar ganinta.Fitsarin yayi sannan ya fita ya samu Mama wacce har yanzu ba ta bar hawayen ba,ya nemi wuri ya zauna yana mai cewa “ina jinki”
Sai ta ci gaba da cewa “wani irin matsanancin kuka ne Hindu ke yi Fateema na taya ta,duk sai na rikice na rasa da wanne zan ji sai kawai na fita ƙofar gida a guje.Cikin sa'a kuwa na ci karo da malam ya shigo layin.“Lafiya meke faruwa Halimatu?” ya tambaye ni,na basa amsa “Hindu ce babu lafiya hannunta sai ƙaba yake yana tara ruwa” hankali tashe ya yi gaba muka koma can gida.Tuni Hindu ta fita hayyacinta,haka na goye Fateema na nemo maƙwabta suka taimaka muka kai ta asibiti. Da isarmu kuwa a fara yi mata aiki,ba a ɗauki lokaci ba kuma aka bamu result wanda ya nuna tana ɗauke da cutar suga ne.Kuma kar ka ji wani abu dukkanmu mun yi amanna da hakan hatta ita Hindun,sam ko da wasa ba mu kawo a ranmu wai macijirin da ta kashe ne silar ciwonta.Kwana uku muka yi asibiti kafin a sallamo mu,sosai hannun nata ke daɗa yin sauƙi haka na dinga girka mata duk wani abu da mai cutar suga zai ci.Cikin abin da bai fi wata biyu ba Hindu ta rame sosai,sai dai hannun nata tuni ya kame har ma ta kama aikin gida mun dawo walwala kafin kuma wata rana da dare muna tsaka da cin abinci ta miƙe tana cewa dukkan jikinta ke ciwo .Shimfiɗa ta yi ta kwanta,ƴarta Fateema sai ta je gun mahaifiyarta tana kuka ita kuma sai ta soma shayar da ita wacce wannan shayarwar ita ce ta zamo ta ƙarshe a rayuwarta don kuwa washegari da ciwon nono Hindu ta tashi.Malam ya nemo mata magani ta shafa sai dai tamkar wacce aka shafawa acid haka abin ya ƙara ƙamari,ka ji dalilin da yasa Fateema ta dawo hannuna na ci gaba da kula da ita.A cikin ciwon Hindu babu sauƙi ko kaɗan,kullum cikin ƙara ƙaruwa yake,tun muna zuwa asibiti mu dawo har ta kai da an riƙe mu can.Ba mu taɓa sanin ciwonta ba na asibiti ba ne sai wata rana da muka fito waje a farfajiyar asibiti don shan iska,wata mata bararoji irin masu bayar da magani ta zo ta yi tsaye tana kallon Hindu.
“Ke kam me ya kai ki shiga hurumin da ba naki ba? Kin tayar da mugu yana bacci shi kuma ya baza miki guba a duk illahirin jikinki.Ki koma gida shi ya fi don kuwa maganin asibiti ba zai yi miki komai ba sai ma ƙara cutar da ke” shi ne abin da matar ta faɗa tare da yin gaba,sai Hindu ta dube ni a galabaice ta ce “kar dai a ce macijin da na kashe ne matar nan ke magana?”
“Tabbas da ƙamshin gaskiya a maganarta amma bari malam ya zo” na faɗa ,ai kuwa da Abban Fatee ya zo muka shaida masa sai ya nemi a sallame mu muka koma gida muka soma yin maganin gargajiya.Sannu a hankali ciwon ya fara sauƙi sai dai kuma Allah ya hukunta shi ne silar mutuwarta ” tana kawowa nan sai ta yi shiru, Mu'azzam ya yi ƴar gyaran murya kafin ya ce “Allah ya jiƙanta ya yi mata gafara! Haƙiƙa ta yi babban kuskure na kashe maciji a tashin farko saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce *Macizai da ake samu a gidaje ana kashe su ne bayan an kira su sau uku su fita, saboda tsoron kar da su kasance cikin Aljanu, sai dai (nau'i biyu): Al-abtar da dhut-Tafifatan waɗanda ake kashe su koda a gidaje ne saboda Annabi (SAW)kawai ya haramta shi ga sauran macizai. _Al-Bukhari, babin farkon halitta n°3297 da n°3298 da Muslim, babin aminci, n°2233._ *- Al-abtar (الأبتر) shine wanda wutsiyarsa ta yi gajere,* *- dhut-tafifatayn (ذو الطفيتين) shine wanda yake da zane biyu a bayansa.*
Wajibi ne a kashe waɗannan macizai guda biyu a kowane hali, saɓanin sauran da ake kashewa sai bayan an kira su su fita har sau uku, ta hanyar cewa misali: "Na kira ku ku fita daga gidana" ko kuma wani hukunci da zai yi gargaɗi ne kuma ya na nuna masa cewa an hana shi zama a gidan.
In duk mutum ya yi haka amma macijin bai fita ba,hakan na nufin ba aljani ba ne,in ma shi ɗin ne to bai cancanci darantawa ba a kashe shi.
Amma idan maciji ya kai masa hari, sai a bar shi ya ture shi, ko da a karon farko. Idan har hakan ya haifar da kashe maciji ko kuma a iya daƙile harin ta hanyar kashe shi, to a nan muna da hakkin yin hakan, kare kai ne. _Fatâwa Islamiyya juzu'i na 4, shafi na 450 da 451._ _Sheikh Muhammad Ibn Salih Al-Utheymine(r)_
To amma ni ban san wane irin nau'i ne ta kashe ba ko kin gansa da idonki?”
Mama ta jinjina kai ta ce “ni kuwa na gansa,a hannun Fateema amma lokacin tuni ya bushe gawarsa ce ta tono bayan wani lokaci ”sai ta soma yi masa bayanin yadda macijin yake.
Mu'azzam ya waro ido yana cewa “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” da sauri kuma ya tashi ya buɗe wani akwati ya ciro wani ɗan ƙaramin littafi ya shiga dubawa zufa na karyo masa.Cikin hukuncin Allah ya samo ainahin zanen macijin,jikinsa har rawa yake yi ya nunawa Mama ya ce “shi ne wannan?” ta jinjina masa kai,ya ce “ki kwanta ki huta zan fita ”
Mama ta ce “ina son ganin Fateema”
Ya ce “abu ne da ba zai yiyu ba,saboda a halin yanzu dodon da ke jikinta tuni ya farfaɗo ya fara mallakar tunaninta har ya yi nasarar kwantar da wata baiwar Allah,har yanzu kuma ban yi mata magani ba”
Wasu sabbin hawaye suka zubowa Mama ta ce “don Allah ka yi ƙoƙari sosai ka tabbatar ta samu lafiya,ita ɗin amana ce mai matuƙar girma a gare ni ”
Mu'azzam ya ce “kar ki damu wannan shi ne aikina shekara da shekaru ”
“Na gode” ta faɗa tare da yin kwanciya,yayin da shi kuma ya fice.
★FATEEMA
Sosai na ji daɗin yadda ya yi saurin tafiyarsa da aka ce ya yi baƙuwa.Ammy ta kama hannuna muka sauka ƙasa,can ɗakinmu muka je na nuna mata inda muke bacci sai kuma ta soma yi mana tambayoyi in ba mu fuskantar kowacce irin matsala.Ina shirin bata labarin abin da Goggo Kabira ta yi mana sai kuma Maryam ta katse mini hanzari tana mai cewa “Ammy me yasa kika zaɓi ki zauna can Duwala madadin nan?”
Ammy ta yi murmushi ta ce “saboda kasuwancina,sannan Mu'azzam na yawan samun baƙi a can fiye da nan.Amma kar ku