Showing 6001 words to 9000 words out of 24397 words

Chapter 3 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt

ta ja numfashi kafin ta ce “ki kwanta ki huta Mama,daga baya za mu yi magana”

“A'a zai fi kyautatuwa da ki bar tarin tambayoyinki don kuwa ba zan amsa miki su ba” cewar Mama.

“Taimako ne za ki yi Mama,a halin yanzu rayuwar Dr Bilal tana cikin mugun hatsari nurse Fatee ce kawai za ta iya yi masa magani”

Mama ta yi murmushi mai ciwo kafin ta ce “sau ɗaya tak ake sarar mummuni,ki sani har zuwa yanzu Fateema yarinya ce ba ta da wayon sanin abin da idanun sauran al'umma ke gani.Duk wani taimako da ta yi wa Dr Bilal sam ba ta san ya danganci baƙin sirrinta da na yi ta ƙoƙarin binnewa tun tana yarinya ba.Shi kuma duk da irin hallacin da ta yi masa sai da ya watsa mata ƙasa a ido”


“Mama kin fi kowa sanin Dr Bilal shi ne farin cikin Fateema...” da sauri Mama ta katse ta da “shi yasa na nisanta ta daga garin Kibri,ba zan so ta ga yadda za a tsoma masoyinta a cikin TUNKUNYAR MAYU ba...” ita ma Rahinatu ta katse Mama da cewa “wannan babban kuskure ne wanda a gaba za ki yi da na sani”


“Kuskuren da zan yi shi ne barin Fateema a garin nan don ko shakka babu da naman Dr Bilal shi ne abu na farko da za ta fara sakawa bakin maitarta shi”ganin dai Mama ba za ta faɗa mata inda Fateemar take ba sai kawai ta haƙura ta bar ta a nan ta koma can cikin gari.



Ofis ɗin Dr Bilal ta shiga,har zuwa lokacin yana kwance tun bayan da aka shaida masa an basa hutun wuccin gadi wanda a cikinsa ba komai ba ne sai zallar azabar ruhi da hana masa abin da yake so.Sam bai yi tunanin yakice nurse Fatee a rayuwarsa shi ne babban kuskurensa sai yanzu.

Galabaitatun idonsa ya tsurawa Rahinatu wacce ita ma sai a yau ne ta yarda da cewa tabbas-tabbas da akwai TUKUNYAR MAYU a asibitinsu.

“An ƙona gidansu Fateema komai ya ƙone ban samu damar ganin mahaifiyarta ba kuma” ta shaida masa kafin ta fice.Shi kuwa wani irin kuka ne ya fashe da shi yana mai soma lissafin kwanakin mutuwarsa.....
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________

04

Dr Bilal na daga kwance yana tunanin abin da ba zai fishe shi ba kawai ya soma ganin inuwoyin baƙaƙen ruhika na ratso ofis ɗinsa.Kafin ƙyaftawar ido duk suka zagaye shi,yawun tsoro ya haɗiye kafin ya soma yin magana cikin rawar murya.“Zan so ku bani damar ƙarshe,na yi muku alƙawarin ba zan sake yin kuskuren da na aikata ba.Zan nemo nurse Fateema zan kuma damƙa muku ita matsayin sacrifice ɗin shagalin murnar cikar shekara ɗaya da kafuwar wannan daular tamu ta Mayu.Ku sani soyayyar nurse Fateema ba ta yi kamar raina ba,zan iya haƙura da ita domin tseratar da tawa rayuwar” yana gama dire kalamansa sai shugaban asibitin gaba ɗaya wanda ya kasance babban likita ne sai ya ce “za ka iya yi wa kowa ƙarya ya yarda amma banda ni,ka yi tunanin ban san cewa ka aika nurse Rahinatu zuwa neman Fateema ba? A tunaninka za ta iya taimakonka a wannan gaɓar? ”


Idon Dr Bilal na tsiyayar da hawaye ya ce “shugaba ina son ka yarda da ni Please ka bani wannan damar”

Sai da ya yi ɗan jimmm kafin ya ce “nan da watanni uku za mu cika shekara ɗaya a wannan tafiyar,zan so kafin wa'adin lokacin ya cika ka gurfanar mana da nurse Fateema ”
Cike da murna ya ce “an gama shugaba” kamar walƙiya haka duk suka ɓace daga ɗakin,a nan take kuma Dr Bilal ya nemi cutar da suka saukar masa ya rasa.Tashi ya yi ya soma binciken inda zai samu nurse Fateema sai dai da dukkan alamu wayarta na cikin gidansu kamar yadda aka nuna masa.





★DUWALA


Direba na ajiye mu duk sai muka doshi ƙofar da za ta kai mu cikin falon.Cak na tsaya jin tamkar ana ƙare mini kallo,wurin da nake jin kaifin idon na fitowa na duba sai na ga babu kowa sai motar da ta kawo mu jiya.

“Ni kam Maryam wane ne ya tuƙo mu jiya? ” na tambaye ta ina mai dubanta.

Ba ta bani amsa ba har muka shiga falon, Ammy ce ta tarbe mu tana tambayar jikina na amsa mata a takaice da “alhamdullah!”

“Fatan Mu'azzam bai takura ki ba?” ta tambaye ni tana mai kamo hannuna ta zaunar da ni kan kujera tana sakar mini wani murmushi.Sai da na kalli Maryam kafin na girgizawa Ammy kai,na buɗe baki da niyyar yin magana kuma ya shigo kamar an jefo shi daga sama.


Barina Ammy ta yi tare da nufarsa tana cewa “lafiya Mu'azzam?” bai ce mata komai ba sai matakala da ya soma takawa ita kuma ta take masa baya.Na ɗan taɓe baki ina jin haushinsa har cikin raina,Maryam ta zo ta zauna kusa da ni tana cewa “anty Fatee ya kamata fa ki saki jikinki ki...” da mugun sauri na katse ta “na saki jiki kamar yaya? Kin ga ni gida zan koma wurin Mama sam ban yarda da mutanen gidan nan ba,yo gida kamar na ƴan yankan kai dubi komai na gidan daban yake da na mutane”


Sai da ta yi ƴar dariya kafin ta ce “wallahi tunaninki ne ke faɗa miki banza-banza amma wallahi mutanen kirki ne,inda a ce mugaye ne da Mama ba za ta ce mu zo nan ba”


Shiru na yi ina nazarinta,wai ƙanwata da duka-duka ba za ta wuce shekara goma sha bakwai ba ita ce ke faɗa mini abin da ya fi dacewa da rayuwarmu.Cikin sanyi jiki na miƙe tsaye zan tafi ɗakinmu sai kuma ga su Ammy sun soma saukowa har da uban tsamin rai.


Da ido na ƙure shi ina kallon tamkakar fuskarsa wacce tsabar yadda ya haɗe ta yasa ba a iya ganin kyawunta.Idonsa ya sauko cikin nawa yayin da kuma laɓansa suka motsa,duk da ban ji sautin ba amma zan iya gane abin da bakin nasa ya furta.“Jarababiya!” shi ne abin da laɓansa suka ayyana,na waro ido tare da nuna kaina “ni?”


Har sai da ya sauko bai bani amsa ba sai kuma ya kawar da kansa gefe,tare da yin tsaye ƙiƙam.
Ammy ce ta yi magana,“Maryam je ki haɗa kayanku kamar kala biyar haka za ku wuce Yawunde”

“To Ammy ” ta faɗa kafin ta yi gaba,yawun bakina ne na ji sun ƙwafe na kasa furta komai sai sumar kansa da na kafe da ido ina kallo saboda yadda ya bani baya.

Babu jimawa kuwa Maryam ta fito jaye da ƙaramin trolly,yanzu ɗin ma hannuna ta kama ta jimƙe.Ita kaɗai ta san sirrin,amma ni dai nawa shi ne yi mata biyayya haka muka fita zuwa harabar gidan.Wannan karon da kansa ya tuƙa mu kuma wata motar ce daban,har muka isa wani tabkeken wuri wanda nake kyautata zaton filin jirgi ne Maryam ba ta sakar mini hannu ba.


Wasu sojawa ne suka zo suka tarbe mu,su ne kuma suka kai kayanmu har can cikin jirgin yayin da shi kuma gogan ya koma can gefe yana waya.

Wani soja ne ya zo ya ce mana “ku zo na nuna muku inda za ku zauna” haka muka take masa baya,karon farko a rayuwata da na shiga jirgi.Kusa da kusa muka zauna ni da Maryam abin sha aka kawo mana,ita kaɗai ta sha ni kuwa ta window nake leƙensa sai wani zagaye-zagaye yake yana waya.


‘Ko da wa yake waya?’ na tambayi kaina a zuci na kuma bai wa kaina amsa ‘ bai wuce budurwarsa! Baiwar Allah amma na tausaya mata da take son maloho irinsa’ sai kuma na saki murmushi jin sunan da zuciyata ta kirasa da shi.Daidai nan shi ma na ga ya juyo yana murmushi kafin ya nufo jirgin yana mai janye wayar daga kunnensa ya maida ta cikin aljihunsa.


Wata irin ajiyar zuciya ta tsoro na sauke jin ƙamshin jikinsa ya cika jirgin,ido na rumtse don ban ƙaunar ganinsa.Ina a haka na ji muryarsa yana cewa “ku saka belt!”


Maryam ta ce “ban san ya zan yi ba ”

“Ki jawo waccan sai ki manna shi jikin nan”ina jin ya faɗi haka sai na buɗe ido don ganin yadda za ta saka sai dai tuni ta saka ɗin.Fiƙi-fiƙi na yi da ido ina kallonsa,bai ce mini kanzil ba sai hannunsa da ya kawo ya jawo bel ɗin zai saka mini.Cikin sauri na ce “ban so ka bari zan yi da kaina” ina ƙoƙarin ƙwace belt ɗin ya buge mini hannu da ƙaton zobensa da ke babbar yatsarsa ta tsakiya.

“Baƙauya kawai!” ya faɗa bayan ya saka mini,sai kuma ya yi gaba.Haka kawai na ji zuciyata tana azalzala amma babu yadda zan yi dole na ja bakina na yi shiru,a haka jirgin ya tashi da mu sama bai sauka ba sai babban birnin tarayya Yawunde.


Yadda motoci suka zo tarbenmu sai abin ya bani mamaki,cike da girmamawa kuma aka ja mu izuwa motar da za ta ɗauke mu wacce iya ni da Maryam ne kawai.Wani tsoron ya sake riska ta na soma dube-dube ina waiwayen baya,sauƙinta da na ga sauran motocin na bin bayanmu wasu kuma a gaba amma sam ban wace ce daga ciki Mu'azzam ke ciki ba har muka isa masauki.Wani katafaren gida ne wanda har ya fi na can kyawu da girma,muna shiga da wata mata muka ci karo mai kama da waccan matashiyar ta gidan Ammy.Kamar ta ga wani kashi haka ita ma ta ɓata rai tana wani ɓoyewa alamun tsoro duk ya bayyana a fuskarta.


“Mu'azzam su wane ne? Me yasa ka tawo da su gida madadin asibiti?” ta faɗa tana toshe hanci.

Cikin zafin rai ya ce “saboda nan ɗin gidana ne! Joy? Joy?” ya shiga ƙwala kiran wani,babu jimawa kuwa wani inyamuri ya zo da gudu yana cewa “na'am yalaɓai”


“Ka kai su masauki sannan su faɗa maka kalolin abincin da suke ci daga yau za ka dinga dafa musu,in ka gama ka same ni a ɗakina” yana gama faɗar haka sai ya wuce can sama yayin da shi kuma Joy ya ja trollynmu ya kai mu wani ɗaki.Abin da na lura shi ɗin ma a ɗan tsorace yake yi mana magana,yana fita na cewa Maryam “wai kin lura tsoronmu yake ji?”

“Zan shiga wanka” shi ne abin da ta faɗa madadin amsar abin da na ce mata, sai bayan ta fito sannan ni ma na shiga nan ne na yi arba da wani baƙin jini da ya cika mini pad.Ido na lumshe ina tuna yadda yake danna mini ciki,na ɗauki tsawon lokaci a haka kafin na samu na yi wankan.Towel ɗin da na gani rataye na ɗaura sannan na fito,cike da mamakin yadda Maryam ba ta baƙunta na soma mita ina yi mata addu'a.Da na buɗe trolly sai na ga sam ba ta sako mini pad ɗina ko ɗaya ba,kaya na saka sannan na fito ina baza ido kamar marar gaskiya.


Babu kowa falon sai masifafiyar matar nan sai tsawa take yi wa ƴan aiki tare kuma da zaginmu ,duk ba wannan ba ne damuwata ba sai jin yadda take alaƙanta mu da mahaukata shi ya fi damuna.
Ina nan tsaye duk idona sun raina fata,sai duban hanya nake yi don ganin ta ina Maryam za ta ɓullo sam ban ga saukowarsa ba sai ƙamshinsa ne ya ziyarci hanci ne.


“Mene ne? Tsayuwar me kike yi a nan? Wuce ki zauna ki ci abinci ” ya faɗa fuskar nan tamau babu annuri,idona na shiga juyawa kamar an jefa ƙwarya a ruwa so nake na shaida masa ban cikin halin da zan zauna kuma ina son sanin inda Maryam take,sai dai ba ƙaramin kamu tsoro da shakkarsa suka yi mini ba.


Tsawa ya yi mini,sai kawai hawaye suka shiga zubo mini sai a lokacin kuma na ga Maryam ta fito daga wani wurin da nake kyautata zaton kitchen ce .Da bala'in sauri har ina yin tuntuɓe na je gare ta tare da ƙanƙame ta ina mai sakin wani marayan kuka.Sam na kasa fahimtar taƙamaimai ni wace ce,tun da ya shigo rayuwata komai nawa ya soma canzawa.


“Anty Fatee lafiya kike kuka me ya faru?” Maryam ta faɗa tana ɗan janye ni daga jikinta,ita ɗin ta fi ni tsayi sai ni kuma na fi ta ƙiba.Ɗan waiwayawa na yi na dube shi,sai na ga kuwa mu yake kallo.Cikin muryar kuka na ce “please kar ki ƙara tafiya kina barina tsoro nake ji a duk lokacin da kika yi nesa da ni ”


Hannuna ta jimƙe tana mai cewa “to ki yi shiru gani na zo” ta faɗi haka tare da jana muka koma can ɗakinmu,sai a lokacin take kwatanta mini ta shiga kitchen ne saboda Joy ya buƙaci haka.

Muna nan zaune sai ga shi ya shigo,fuskarsa ta ɗan sassauto da alamun kamar tausayi a shimfiɗe da ita ya miƙo mini wata leda.Ƙin karɓa na yi sai hannunsa da na kafe da ido wanda gashi ya kwanta luf sai sheƙi yake.Cillo mini kedar ya yi kafin ya fice,sai na buɗe nan na ga ashe pad ce sai pant amma da dukkan alamu za su yi mini kaɗan.Toilet na shiga,sai na ga ashe duk na ɓata jikina har a ƙafata ya ɓace sai da na sake yin wani wankan sannan na kimtsa.


Da na fito sai na ga ƴar aiki tana goge ɗakinmu,ashe duk na ɓata wurin ba tare da ni na sani ba.A kunyace nake kallon Maryam wacce na ga zuwa yanzu kamar ita ma tana son mu koma wajen Mama.



★MU'AZZAM


Sosai ya ji zafin irin yadda Fateema ta ɓoye masa sirrin Dr Bilal,har ya yi fushi sai kuma ya ga da buƙatar ya kaita can asibitinsu ta Yawunde inda za a saka ta yin magana da ƙarfin tsiya ba tare da ta shirya ba, wannan dalilin ne yasa shi dawowa gida cikin ɗayar motarsa da kusan kullum a asibiti take kwana.Tun daga balaguron da suka yi a cikin jirgi har izuwa yanzu da ya kawo mata pad idonsa na kanta,yana jin tsanar da ya yi mata zaune daram a zuciyarsa yayin da gefe guda kuma ya soma jin tausayinta musamman lokacin da ta ruga ta rungume Maryam wanda a nan ne ya fahimci har pad ɗin tana buƙata wannan yasa ya shiga ɗakin Zeezi ya binciko pad da pant ɗinta waɗanda ba ta yi aiki da su ba.


Tsuki ya ja a karo na barkatai yana jin zuciyarsa na azalzala game da abin da ta yi masa na ƙin karɓar ledar hannunsa.Wayarsa ta bado haske alamun shigowar saƙo,ya ɗauka ya duba sai ya ga abokinsa ne Dr Jabeer.Bayanan da ya turo masa ya karanta sai ya ajiye wayar ya shiga toilet,wanka ya yi ya shirya cikin kayan ƴan ƙwallo adidas baƙaƙe masu dogon wando.Sai da ya gyara sumar kansa ya bar ta a baje sannan ya fesa turare ya ɗauki wani ɗan ƙaramin littafi ya fito yana addu'ar Allah yasa kar ya gamu da ƴar matsalar can Fateema ai kuwa har ya fice ba su haɗu ba.



Can wurin da aka tanada wurin motsa jiki ya nufa,littafin ya ajiye kan ɗan ƙaramin teburi sannan ya soma zagayen tabkeken wurin.Sai da ya zagaya shi ya fi a ƙirga sannan ya tsaya don hutawa,da mugun sauri Joy ya zo ya miƙa masa gorar ruwa da kuma ɗan ƙaramin towel.Murfin ya buɗe ya soma wanke fuskarsa ,sai kuma ya cire rigarsa da duk ta jiƙe da gumi da kuma ruwa.Har zai zauna sai kuma ya ɗauki littafinsa ya ƙara gaba.



★FATEEMA

Muna zaune ni da Maryam masifafiyar matar nan ta aiko a kira mu,cikin masifa take bamu umarnin mu juya ƙattan kujerun da ke falon alhalin ga ƴan aiki nan maza.Banda masifa babu abin da take zubawa,raina ne na ji yana ɓaci yayin da kuma yawu suka soma cika mini baki idona kuma na wata irin rufewa kamar ƙwan lantarkin da yake gargadar mutuwa.


Da sauri na nufi ƙofar fita don tofar da yawun,gijifff na ji na kai wa wani abu karo na yi baya zan faɗi amma yatsunsa masu mugun sanyi suka cabko ni tare da maido ni gaba sai ga kaina kwance a ƙirjinsa.A hankali na ɗan ware idona na dube shi,wani irin jana ya yi waje ya duƙar da ni tare da kama mini wuya nan na soma kakari ina zubar da baƙaƙen yawu.Tsawon lokaci ina a haka kafin na soma jin sassauci,da kansa ya wanke mini bakina kafin ya kira masu aiki su tsabtace wurin.Ina ƙoƙarin tashi kawai jiri ya kwashe ni,cikin fitar hayyaci na ji ya sungume ni tare da shigar da ni can ciki na yi tunanin a falo zai ajiye ni amma sai ya haura da ni can sama.Wani ɗaki ya kai ni mai kamar asibiti ya shimfiɗe kan gado,agajin gaggawa ya bani na farko kafin ya ɗauki waya ya yi kira.


“Ki buɗe idonki kar ki rufe su” ya faɗa yana mai kama tafin hannuna na hagu ya soma mirza shi da ƙarfi,motsi na soma ji a cikin maƙoshina yayin da maduban idona ke hasko mini matar nan wacce na fi kyautata zaton goggonsa ce.


Ƙofa aka turo aka shigo,a ɗan rikice su biyu suka haɗu suka soma yi mini magani wanda ya sha banban da na asibiti.Sun ɗauki sama da minti talatin a kaina kafin na dawo normal,a yayin gudanar da agajin na ji abubuwa da dama a cikin jikina waɗanda ban san na mene ne ba.


“Ƙwayoyin sun fara bazuwa a jininta ” abokin nasa ya furta.
Shi kuma Mu'azzam ɗin ya ce “yau ne suka samu damar ɓallewa suka kutsi jininta ka ga muna iya yin wani abu.Please Jabeer ina son ka ƙara binciko mini wannan ƙwayar ”


Wanda ya kira da Jabeer ɗin ya ɗan dube ni kafin ya ce “me kike ji a yanzu?”

Shiru na yi ban ce komai ba sai Mu'azzam da nake kallo,shi kuma tsuki ya ja yana mai cewa “na faɗa maka taurin kan tsiya ne da ita,dole sai an saka mata hullar gaskiya” yana gama faɗar haka sai ya nufi ƙofar fita,abokinsa ya take masa baya suka bar ni a nan ni ɗaya.


Saukowa na yi daga gadon na soma ƙarewa ɗakin kallo,wani abu ya ja hankali shi ne fitilar ƙwai amma ba ɗaya take da sauran ba.Hannuna na rawa na kai shi na taɓa ƙwan,nan take ya kawo haske sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login