Showing 15001 words to 18000 words out of 24397 words

Chapter 6 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt

damu na kusa dawowa nan ɗin ko don saboda ku”

Na ce “Ammy ai mu mun kusa komawa gida,kin ga mun baro Mama a can Kibri ita ɗaya” na ƙarashe faɗa da alamun damuwa a fuskata.Ammy ma duk sai ta nuna rashin jin daɗinta kafin ta ce “ki sa a ranki tamkar Mamarku tana tare da ku,sannan ina ku ɗauke ni tamkar uwa ”

“To Ammy ” shi ne kawai abin da na iya cewa,kamar abin asiri haka Maryam ta zo ta shafi fuskata sai na soma gani dishi-dishi a dole na samu wuri na kwanta ina kallon lokacin da ta ja hannun Ammy suka fice.

Bacci ne ke ta kawo mini farmaki,har na lumshe idona sai kuma na ji motsin ziyara haɗi da kaifin ido.Ban sani ba ruhina ke magana ko kuwa mine ne amma tambayar da na yi ita ce “wace ce ke?” budurwar da ke tsaye a gabana wacce wannan shi ne karo na biyu da na ganta ta bani amsa da “ki tambayi Mu'azzam shi zai baki wannan amsar,ko da yake na san bai son a yi masa zancena saboda yana tsoron kar na ɓata masa shirinsa ”

“Wane irin shiri? ” na tambaye ta.Sai da ta yi wata gigitaciyar dariya kafin ta ce “duk wanda Mu'azzam ya kawo gidan nan saboda ya cutar da shi ne,ya yaudari ƴan mata bila'adadin da farko zai nuna miki yana sonki da zarar kin saki jiki sai ya miƙa ki izuwa TUKUNYAR MAYU ”tana gama faɗar haka ta ɓace a nan take kuma dafin da Maryam ta jefa mini ya saki jikina,da wani mugun sauri na diro daga kan gadon ƙofofin hancina na shaƙo mini warin fatalwa irin dai wanda na taɓa ji a ɗakin Mu'azzam.A tsorace na fita ina gudu sam ban ga tawowarsa ba sai ji na yi na kai masa karo,yayi baya da mu duk muka faɗi ƙasa sai dai ni a kan ƙirjinsa nake.A ɗan tsorace na ɗaga kaina ina kallon tsakiyar idonsa kamar yadda shi ma yake yi,na shagala sosai a kallonsa na ji ya yi cilli da ni gefe.Kaina ya bugu jikin bango,ban dawo daga cikin raɗaɗin da na ji ba ya soma yin masifarsa da ta zame masa sabo.


“Jarababiya kawai in ba ki taɓa jikina ba sam ba ki jin daɗi,shi yasa kike tafe ba ki kallon gabanki.Kullum cikin gudu kamar mahaukaciya mtswww!” ya ja tsuki.Na tashi zaune dafe da kai ina kallonsa,duk masifar nan da yake faman zazzaga mini bai hana ni yi masa magana ba.

“Fatalwa na gani cikin ɗaki” na faɗa tare da nuna masa ƙofa,shiru ya yi yana kallona kamar mai yin nazari kafin ya nufi ɗakin.Na take masa baya , dube-dube ya soma yi yana buɗar hanci can ya ce “me ta ce miki?”


Shiru na yi don kuwa na manta,ya matso kusa da ni cikin ɗaga murya ya sake cewa “me ta ce miki?”
Cikin rawar murya na ce “na manta” ya dungure mini kai yana cewa “saboda ƙwaƙwalwar kifi ce da ke shi ne ki ka manta abu mai muhimmanci mtswww sokuwa” sai ya fice tare da bugo mini ƙofa na zabura na je zan buɗe amma tamkar abin tsiya ƙofar ta ƙi buɗewa.Cikin kuka kuwa na soma jijiga ta ina kiran sunan Maryam,na fi minti biyar a haka kafin a buɗe ƙofar.Don mugunta ashe tun ɗazu bai tafi ba yana nan tsaye,wani murmushi ya saki yana mai jawo hannuna ya fiddo ni waje.Cike da jin haushi na soma kai masa duka shi kuma banda dariya babu abin da yake yi mini,wato burinsa dama shi ne na tsorata shi yasa ya rufe ƙofar.

Dukkan hannuwana ya kama ya riƙe gam,fuska shaɓe-shaɓe da hawaye nake kallonsa.Cikin taushin murya ya soma magana,“ban san me mahaukaciyar nan ta faɗa miki ba,amma ina so ki yarda da ni kar ki saki ki saurare ta ko kuma ki yarda da soki burutsun da za ta faɗa miki.Ita ɗin muguwa ce,ba mutumniyar kirki ba ce don haka ina so ki aje hankalinki wuri guda ki yarda ki gane ba ki da lafiya” yana gama faɗar haka sai ya sakar mini hannuwa ya tafi,na bi bayansa da kallo har ya fice.


Ko da na ƙaraso falo sai na tarar da Ammy da Maryam a zaune suna karatu,amma sam ba na Alkur'ani ba ne wani littafi ne daban .Gefen Maryam na zauna ina mai baza idona kan rubutun abin mamaki sai na ji wai zan iya karanta shi,amma sam ba da baki a'a ta ido kawai.Wani irin sanyi ne na soma jin jikina na yi kamar wacce aka saka a ƙanƙanra,yayin da kunnuwana suke tariyo muni wata murya wacce rabon da na ji ta tun ina ƴar shekara uku.Wannan murya ba ta kowa ba ce sai ta aljana macijiya,matar da take fito mini a zahiri ba wai cikin mafarki ba.Tunanina da lissafina ba su yi wani jinkiri ba suka ɗingiza ni izuwa shekaru ashirin da suka shuɗe a baya.



A tsaye nake gaban wutar da ake dafa tumu,Mama da Abba suna yin hira jefi-jefi yayin da kuma gefe guda Abba ke ƙara juyara zangarniyar gero wanda yake farkon fitowa wanda kuma shi ake kira da tumu.Daga cikin wutar nake hango wasu manyan idanuwa masu mugun haske suna kallona,sam ban ji tsoro ba kasancewar shekara ta uku kacal a duniya sai ma abin ya burge ni har ta kai da na sa hannu a cikin wutar na kamo su sai dai ba iya idanu ba ne har da wani dogon bindi wanda ya kasance na maciji.A jikin bindin gasashen tumu ne jere rasss,haka na sa hannu ina ɗebowa ina ci yayin da idanuwan nan masu mugun haske suke daɗa yi mini wani kallo .

Ina tsaka da morewa Abba ya ce “Fateema ungo wannan ki ci”

Mama ce ta ce masa “ai ba za ta karɓa ba sai ta cinye wanda ke hannunta” ta ƙarashe faɗa tana mai hasko mini fitila,sai na ga ta yi cilli da ita tana salati a nan take kuma abin da ke riƙe da hannuna ya sulɓe mini ya koma cikin wuta.Abba ya ce “lafiyarki?” muryar Mama na rawa ta ce “busashen maciji ne a hannun Fatee” sai dai da Abba ya haska fitila babu komai a hannuna,sai ya ce kawai don har zuwa lokacin Mama ba ta fidda zancen maciji a ranta ba.Haka dai muka ci tumun muka kwanta,sai dai nawa baccin sam bai yi wani nisa ba na farka saboda wata murya da ke kiran sunana.Haka na tashi na soma takawa har na isa inda sautin muryar ke fitowa,cikin ciyawa ne,sai na ja na tsaya.Fararen idanuwanta masu matuƙar haske su ne abu na farko da na fara gani kafin ta ida fiddo ainahin jikinta wanda shi ma yake walwali yana fitar da wani hasken wuta abin sai ya burge ni na duƙa na ɗauke ta.Sosai muka yi wasa da ita wanda a ƙarshe ta kai ni wata duniyar mai cike da macizai irinta tana nuna musu ni tana cewa ƴarta ce ni.····


Sanyin ruwan da na ji a jikina shi ya farfaɗo da ni daga duniyar wankin idon da ake yi mini na tuna rayuwata ta baya.Maryam na gani a tsaye riƙe da bokiti yayin da kuma Ammy ke faman busa wutar hayaƙi,a hankali nake ƙara ware idona ina kallonsu so nake na basu labarin abin da na gani amma tamkar an toshe mini maƙoshi haka na ji ba zan iya bada labari ba.Miƙewa na yi na fita harabar gidan ,wani irin canji na riskata wanda sam ban san farkon tono baƙin sirrina ne ba.Can cikin jardin na ja na tsaya tare da nutsuwa ina sauraren wani amon murya wacce ba ta ƴan adam ba,sai da na nutsu irin sosai ɗin nan sannan na fahimci cewa sautin na fitowa ne ta cikin ciyayi.Haka na zube kan gwiwana na soma buɗe korin shuke-shuken har Allah ya kai ni ga wata daula ta tsutsotsi......

Only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________

08


Tamkar yadda mutane ke kafa daula su yi gidan sarauta haka idanuna suka gane mini masarautar tsutsotsi.Kamar wata zararriya haka nake kallonsu suna ta hidindimu,abin da ya fi ɗaga mini hankali shi ne yadda aka yi har nake jin maganar da suke yi.


Jikina ne ya soma yin rawa jin topic ɗin da suke tattaunawa a kai ba na komai ba ne sai na yadda za su yi su kashe Mu'azzam.Ban gusa ba sai da na ji ta yadda suka tsara plan ɗin,na miƙe da sauri ina tafiya ƙafafuna na harɗewa na nufi can wajen direba . Kame-kame na fara kafin na ce “Mu'azzam ya ce ka kai ni can wurinsa” na faɗi haka ne sanin shi ne direbansa.Ba tare kuma da yin gardama ba kuwa ya buɗe mini mota,na shiga gidan baya na zauna muna tafe ina tunanin abin da na gani ɗin.



A can ɓangaren Mu'azzam kuwa yana fita direct babbar asibitinsa ya wuce.Bai iya duba kowanne patient ba ya dai samu wuri ya zauna suna hira da babban abokinsa Jabeer inda yake faɗa masa matsalolinsa shi kuma yana basa shawara.



“Wallahi abokina tun da yarinyar nan ta shigo rayuwata duk komai ya ida cakule mini,kana ga fa a yanzu ko minti ashirin ɗin ban yi haka nake zaryar shiga toilet.Abin da ma na lura kamar in na samu kusanci da ita matsalar ta fi saurin taso mini,ina ga saura ƙiris ni ma na dinga saka pad ɗin” Mu'azzam ya faɗa yana wani kama kai.

Jabeer ya ce “duk dai komai ya kusa zuwa ƙarshe tun da an samo bakin zaren ka gano kalar macijin da Ummarta ɗin ta kashe”


“Babu wani sauƙi don har zuwa yanzu ban samu na yi magana da ita Fateemar ba,kuma abin takaici abokina ta ƙi yarda ba ta da lafiya to ta ya za a yi mata magani? Kuma fa Nadiya ta soma yi mata fatalwa tana fito mata,kai abin dai sai godiyar Allah ” Mu'azzam ya faɗa yana tashi tsaye ya nufi toilet,jimmm kaɗan ya fito yana haɗe rai.


Jabeer ya ja numfashi kafin ya ce “amma me yasa da ka kai ta asibiti ba ka jona mata hullar gaskiya ba wacce za ta saka ta yin bayani don dole?”


Mu'azzam ya basa amsa da “ta ya za a saka mata hulla alhalin dodon jikinta har ya riga ya bayyana,ni babban tashin hankalina ma bai wuce kar ta ƙi sakin kurwar nurse ɗin”


Jabeer shi ma ya miƙe tsaye sannan ya buɗe wani ɗan ƙaramin littafi ya ce “ina ga kawai hanyar da ba ka son bi ɗin za mu ɗauka muddin muna son ceto kurwar nurse ɗin,ka ga masu amfani da maitar maciji abin da suka ƙi jura shi ne hayaƙi me zai hana ka ɗauko Fateemar a gwada yin haka ɗin ?”


Mu'azzam ya ce “wannan solution ce mai haɗari,don ana iya wajen ceto kurwar ita Fateemar numfashinta ya tsinke tun da ainahi ba ita ce ke yin maitar ba,saka ta ne ake yi” sai kuma duk suka yi shiru suna nazari.





Sosai direba ke sharara gudu har muka iso,shi ne ya yi mini jagora har zuwa ofishin Mu'azzam wanda a jikin ƙofar ma an rubuta sunansa.Ba tare da neman izini ko yin sallama ba na buɗe ƙofar da ƙarfi,a tare duk suka juyo suna kallona ni kuwa sam ban damu da irin kallon da suka yi mini ba na nufi Mu'azzam ina mai basa labarin abin da idona suka gane mini amma sai na ga suna kallon juna kamar ba su yarda ba.


Cikin son sai na sa sun gaskata na ce “wallahi da gaske nake,in kuma ba ku yarda ba ku zo na nuna muku” .Harshe Jabeer ya canza sai kawai na ga Mu'azzam ya kama hannuna yayin da shi kuma ya take mana baya,cikin wata mota ce daban muka shiga inda Jabeer ya tuƙa mu.Duk da ban san gari ba amma na gane hanyar asibitin nan ce ta mahaukata,ina ji ina gani kuwa suka shiga da ni.


Tamkar wata ƴar kaso haka Mu'azzam ya ɗaure ni jikin kujera,wanda kafin ya iya yin haka sai da ya sha fama da ni don har cizonsa na yi.

“Jabeer kunna hayaƙin” Mu'azzam ya faɗa,shi kuwa tamkar jira yake ya buɗe wani akwati da ke cikin ɗakin sannan ya fiddo komai tare da haɗa komai.

Ina ganin hayaƙi ya fara tashi na ƙara ƙaimin kuka ina mai ce masa “ina da cutar toshewar numfashi don Allah ku kash....” sauran maganar ce ta maƙale mini jin harshena ya soma zazzalowa yana ƙara tsayi har yana taɓo cinyata.Hayaƙi ya turniƙe mini hanci da maƙoshi,tamkar an zuba mini wuta haka gangar jikina ta ɗauki zafi.Ba a ɗauki lokaci ba kuma wannan abin da ke cikin jikina na ji ya soma yin magana,“in ma dai niyyarka ka kashe Fateema to ka makaro domin kuwa hatta cutar toshewar numfashin da take magana ni ce nan na haifar mata da shi,kuma ba zan baku abin da ku ke so ba yadda ka ƙulle hanyar da zan haɗiye kurwar nurse ɗin nan haka ni ma zan ƙulle maka ƙofar da za ka janye ta daga gare ni”


Mu'azzam ya ce “Jabeer miƙo mini ruwan floris sannan ka ƙara zuba turaren a ciki” wata gora ya miƙo masa ya buɗe ta sannan ya soma watsa mini ruwan ,nan take kuwa na soma yin ihu ina son kubcewa ruhin da ya ɗauki mallakar tunanina kuwa sai kuma ƙara nanata wa yake yi ba zai bayar da kurwar ba.

Tsawon lokaci da Lahaula Wala ƙuwata illa billahi sannan na ji wani abu ya gangaro maƙoshina ya fito da gudun bala'i.Tamkar dunƙulen gulusuwa haka yake,sai dai fari ƙal yake yana gama fitowa bakina ya fashe tare da yin sama cikin iska sai kuma a lokacin na dawo hayyacina.


Cikin wata irin muguwar tsana nake kallon Mu'azzam don ni sam duk abin da ya faru a yanzu na manta shi shaf.Da kansa ya kwance mini igiyoyin da ya ɗaure ni da su,ya ɗauki wani ƙyalle ya fara goge mini hijabina da duk ya ɓace.Cikin jin haushi na ture shi tare da tashi tsaye,ban kuma yi jinkiri ba na ruga a guje na ɓalle ƙofa na fita.

Yadda nake gudun da sauri yasa ban ɗauki lokaci ba na fito harabar asibitin sai kuwa na yi rashin sa'a a daidai wannan lokaci ne wani mahaukaci ya kubce.Cak na tsaya ina waro ido yadda ya nufo ni gadan-gadan,da wani bala'in gudu na yi baya zan koma inda na fito sai na ci karo da Mu'azzam.Banda wani zaɓi wannan yasa na nufe shi don tseratar da kaina sai dai ina tuni mahaukacin ya kwashe ƙafafuna sai da na yi sama kamar zan faɗi,amma wani irin haske ya fita idona ya daki ƙasa sai gani ina yawo cikin iska sam gangar jikina ta ƙi taɓa ƙasa.

Da yake mahaukacin nada rabon wahala haka ya ja ƙafata ta baya,wanda ban san a ina na samu ƙarfin buge shi ba sai ga shi ya faɗi warwas.


Daidai nan na yi tsaye kan ƙafafuna,yayin da kuma likitoci suka zo suka ɗauke shi.Ni kuwa sunne kai na yi ganin kallon da Mu'azzam ke aiko mini,kamar wata ƴarsa ya damƙi hannuna ya ƙara mayar da ni can ciki.Wani sashe na musamman muka shiga mai ɗauke da wasu zane-zane da ban san ma'anarsu ba.


Hannuna ya saki tare da cewa “zauna can” ya nuna mini wata kujera mai hoton zaki,na maƙe kafaɗa na ce “ni gidan zan koma” rikitatun idonsa kawai ya zuba mini babu shiri na je na zauna.
Wata hulla ya ɗora mini a kai sannan ya saka mini wani gilashi wanda ya kasar da duk hasken ganina.Tamkar makauniya haka na koma,abin mamaki kuma sai na ji na kasa yin motsi.Ina cikin sabon yanayin ne na ji tambayar Mu'azzam kamar daga sama.


“Nana Fateema ina son ki bani labarin kanki,sannan wace ce ke ? Wasu irin laifuka ki ka aikata tun ƙurciya zuwa yanzu da kike zaune a gaban dodon Mayu?” yana gama dire kalamansa haka na ga rayuwata a cikin idona kamar wacce aka kunnuwa tv.


“Kamar yadda ka sani sunana Nana Fateema a wannan duniyar,yayin da kuma a ɗayar duniyar ake kirana da Goddess/déesse.Rayuwata ta kasance ruwa biyu ,rabi ta normal mutum rabi kuma ta keɓaɓiyar duniya ta waɗanda ba su baccin dare sai na rana.Kamar yadda na gani a wani wankin idon waiwayen bayan rayuwata,a ranar da Abba yana gasa mana tumu a wannan ranar ce na yi gamdakatar da Jinniya wacce ta ɗauki matsayin uwa mahaifiyata sakamakon ɗanta da Momata Hindu ta kashe.Tun daga wannan lokaci sai ta soma zuwar mini a mafarki da kuma rayuwar zahiriya.Babban zunubin da na fara aikatawa shi ne na kashe matar Abbana wacce ya auro saboda jinkirin haihuwar da Mama ta samu .Tun daga ranar da ta shigo gidan Abba duk ya canza,ni kuma na kasa jura wata rana da dare na damƙe mata kurwar a cikin daren kuma ta mutu.Mutum na biyu kuma shi ne ƙanen mahaifina na kashe shi a lokacin da na cika shekara biyar a duniyar sakamakon zargina da ya soma yi ,duk wannan bai ishe shi ba ya soma bin didigina a garin nemo gaskiyar ni wacce ce na rikiɗa na zama macijiya na kashe shi har lahira” ina kawowa nan na yi shiru.

Mu'azzam ya sake cewa “amma ta ya aka yi aka toshe miki hanyar ci gaba da yin mugunta?”


“Mama mutum ce mai baiwa,tana ganin abubuwa a cikin mafarki wanda kuma ba kowa ke sanar da ita ba sai aljanunta.A cikin mafarki ta ga komai, amma da yake ta iya takun saƙarta sai ta yi shiru da bakinta ba ta sanar da kowa ba har Abbana.Ban san a ina ta samo maganin raba ni da ruhin dodon jikina ba kawai na samu kaina da rashin sinadarin.Sosai kuma na fahimci canjin da na samu, amma babu wanda zan iya yi wa magana sai dai abin yana damuna saboda kewar uwa Jinniya wacce ta ce ita ce mahaifiyata.Yawan tunaninta yasa na soma yin mummunan mafarkai na dinga zabura haɗi da yin suratai, wannan dalilin ne yasa Mama da Abba yanke shawarar kai ni wajen mai magani da ke can wani ƙauye mai nisa.Yayin wannan dogon balaguron mun haɗu da ƙalube da dama a bisa hanya,ciki kuwa har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login