Showing 18001 words to 21000 words out of 24397 words

Chapter 7 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt

da lalacewar motarmu wacce Abba ya aro.Muna tsaka da tafiya ta tsaya cak, Abba ya fita yayi ƴan taɓe-taɓe kafin ya ce “ku fito ina ga sai na nemo mai gyara” Mama ta buɗe murfi muka fito tana mai cewa “a ina za a samu mai gyara cikin wannan dokar dajin?”

“Zan dubo! Bari na fiddo muku tabarma ku zauna kafin na dawo” ya faɗa tare da buɗe Boot ya ciro mana tabarma.Mama na karɓa sai ya tafi,yayin da ta ja hannuna muka ƙetara can gaban wata inuwar bishiya.Tabarmar ta shimfiɗa tare da yin zaune ni kuwa tsaye na yi ina kallon wata mata mai fararen kaya hannunta na riƙe da ƙwaryar nono.

“Fatee zo ki zauna” cewar Mama tana nuna mini gefenta.
Na maƙe kafaɗa saboda hasken idon matar ba za su barina har na samu damar isa can ba,ban san dalili ba amma ƙila saboda ruhin dodon da ke kwance a jikina a dabaibaye.

“Zo ki zauna” ta sake faɗa tare da miƙo mini hannunta,na girgiza kai na ce “ki cewa wannan macen da ke bayanki ta bar kallona”

A tsorace Mama ta juya sai dai da dukkan alamu ita ba ta ganinta,jikinta na ɗan rawa ta miƙe tare da cewa “don Allah ki yi haƙuri kar ki cutar da mu motarmu ce ta lalace shi ne muka zo mu zauna kafin a gyara amma za mu gusa ” wani murmushi na ga matar ta yi kafin ta ce “haƙiƙa ko a bil'adama akwai masu kyakkyawar zuciya, waɗanda suke ɗaukar ƴaƴan kishiyoyinsu tamkar nasu.Allah ne kaɗai ya san dalilin da yasa motarku ta lalace a daidai kuma bakin ƙofar gidana,ƙila don na tura motar kyakkyawan burinki ta kai ga ci” da dukkan alamu hatta Mama ta ji wannan furicin don kuwa sai da ta mayar mata da amsa inda take cewa “na gode sosai da kika fahimce ni,kin ga ni ma daga yau na yarda cewa har a mutanen ɓoye akwai na kirki na bar ki lafiya” sai ta naɗe tabarmar,sai dai fa matar ba ta bari muka gusa ba sai da ta zo ta ratsa gangar jikin Mama ta shige tamkar yadda ruwa ke huda ƙasa su nitse haka na gani.Ina shirin yin magana Abba ya dawo shi da mai gyara,sai kawai muka tafi wurinsa.Ba a ɗauki ko da minti biyu ba motar ta tashi wanda na yi imani cewa ƴar bafulatanar nan ta jikin Mama ce ta warware sharrin da yasa motar ta tsaya.Ko da muka shiga ciki sai Mama ta jawo ni ta rungume a ƙirjinta,tamkar ana gasa ni haka nake ji sai dai na kasa kubcewa haka na daure har muka isa wajen wani mai bada magani.

Duk da mun tarar da jira haka ya sa aka zo aka ja mu,da muka shiga ciki sai da ya dubi Mama na wani lokaci kafin ya ce “duk da na ga kun samu wacce za ta taimaka muku sai dai ku sani ruhin dodon Jinniya nada mugun ƙarfi saboda zaluntarta da aka yi,sannan kamar yadda na samu labarin zuwanku tun kafin ku zo to haka na ga mummunar ƙaddarar da za ta faru da ku nan gaba.Amma babu komai,zai zo da sauƙi ku tashi ku nemi wuri ku kwanta kun yi doguwar tafiyar zan sa a kai muku abinci ita kuma wannan ku bar ta nan” haka kuwa aka yi a bai wa su Abba masauki bayan sun ci sun sha ni kuwa kasa ci na yi,a wannan daren ne Mama ta samu cikin ƙanwata Maryam wacce zaɓi ce daga ƙaddarar rayuwata.

Bayan tafiyar su Mama wankan magani ya yi mini sannan ya ɗaura mini wata laya a wuyana wacce shigarta kenan na ida jin komai da ya danganci ɓoyayyar duniya ya tsaya mini cak na dawo normal yarinya ƴar shekara biyar.

Washegari kafin mu tafi mai bada magani ya shaidawa iyayena kar su bari layar nan ta bar wuyana.Daga nan muka ɗauki motarmu ta komawa can gida,a nan ne wani mummunan hatsari ya same mu.Cikin irin soyayya ta uwa Mama ta ƙanƙame ni gam,tare da buɗe motar muka fito daidai nan kuma mota ta soma ci da wuta alhalin Abba na ciki.Muna kuka muna kallo motar ta toye ƙurmus a dokar daji,faɗar tashin hankalin da muke ciki ya fi gaban misali.Haka Mama ta goya ni muka soma tafiyar ƙasa,wacce duk tako ɗaya da za ta yi ya fi taki ɗari da wannan muka isa gida a wannan dare.A washegari Mama ta sanar da rasuwar Abba aka yi masa zaman makoki mai cike da tsiyar gumi ana cewa ita mayya ce ta kashe kishiyarta yanzu kuma ta damƙe mijinta.Surutun mutane yasa ta sayar da ɗan abin da dangi Abba suka rage mana,ta haɗe kayanmu muka bar gidan muka koma can cikin ainahin birnin Kibri inda muka fara rayuwa mai cike da ƙalubale.Sana'ar ƙosai Mama ta fara haka da haka har cikin jikinta ya tsufa ta haifo Maryam ,wacce zuwanta duniya shi ya yaye ƙuncin rayuwarmu wanda kuma ba kowa ya kawo canjin nan ba sai ƴar bafulatanar nan ta jikin Mama.A ranar suna Mama ta samu kyaututtuka da dama wanda yasa bayan arba'in ta fara sana'a mai gwaɓi har ta saya mana gidan da muke zaune ciki .Haka rayuwa ta shuɗe na tsawon shekaru har na gama karatuna na soma fafutukar neman aiki,wanda a ƙarshe wata asibiti ta yarda na je na dinga yin aiki amma albashin ba wani ba.Mama ce da Maryam suka ƙarfafa mini gwiwa kan na je na soma yi wanda da ace sun san cewa asibitin nan ita ce mafarin tono baƙin sirrina na tabbata ba za su yarda ba.

A ranar farkon zuwana wuraren ƙarfe shidda na yamma ne,komai na tafiya daidai ina duba patient har zuwa dare.Inda gizo ya fara saƙa shi ne wani ɗan yaro da ya mutu tsakiyar dare,wanda tun zuwana na ji mugun sonsa.Wannan soyayyar tasa ta haifar mini da ƙawa zuciya har na yi masa rakiya zuwa MUTUWARE,tamkar ni ce uwarsa haka na rungume gawarsa ina kuka daga bayana na ji an dafana da wani irin hannu wanda ba zan iya misalta yadda na ji ba,amma da na juyo sai na ga babu kowa.Wani tsoro na ji har zan fita sai kuma wani akwatin gawa ya buɗe.Kamar wacce ake tatsowa ruhi haka na ji ana fizgata a haka har na isa kusan akwatin .Gawar wani kyakkyawan saurayi ce a kwance,sai dai da dukkan alamu ba mutuwa ya yi ba saka shi aka yi a ciki.

“Ki taimaka mini na fito” ya furta,na waro ido jikina na soma rawa.Ya ci gaba da cewa “kar ki ji tsoro kina iya taimakona,ban mutu ba sharrin maƙiya ne suka saka ni a nan.Sunana Dr Bilal shararren likitan nan na garin Kibri...” ina jin abin da ya ce sai na zuba da gudu a guje sai dai ina zuwa bakin ƙofa sai ta dantse......
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________

09

Ko da na juya akwatin gawar na ga yana fitar da wani haske.Jikin ƙofar na jingina tare da rumtse idona ko zan ji sassauci,ashe ma ƙaimi na ƙara don kuwa tamkar fitar iska haka na samu ruhina ya fice daga gangar jikina ya isa can bakin akwatin gawar.Hannu na miƙa masa ina mai cewa “ka zo na cece ka amma da sharaɗin za ka yi mubaya'a kai da sauran doctor's na asibitin nan” na yi wannan furicin ba tare da ni kaina na san me hakan ke nufi ba.


“Na amince” Dr Bilal ya furta,yayin da kuma na kai hannu na jawo shi na fitar da shi daga akwatin,kafin ruhina ya zo da wani bala'in gudu ya koma cikin gangar jikina.Wani irin shock na ji ya shige ni tamkar na kama da wutar lantarki daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gadon asibiti.


Na tashi dakyar ina dafe kaina da ke yi mini azabar ciwo,sam kuma na kasa tuna abin da ya faru.Haka shugabanmu ya ce na tafi gida sai na huta,godiya na yi masa na dawo gida.Ina shigowa Maryam wacce a lokacin ba za ta wuce shekara sha huɗu ba ta zo ta rungume ni sai kuma ta yi baya tana ƙare mini kallo.Yanayinta na ga ya canza kafin ta ce “anty Fatee me ya faru ki ka dawo gida tun asubar farin? Ba sai ƙarfe goma za ki sauka ba?”


“Ni ma ban sani ba Maryam,kin ga banda lafiya ne” na faɗa tare da raɓawa gefenta,sake da baki take kallona tana mai hana ni wucewar har za ta yi magana Mama ta leƙo daga kitchen tana mai cewa “ki barta ta huta mana,in ta tashi sai ku yi magana”

“Amma Mama yanayin ƙamshin jikinta ya canza daga wanda na sani kuma ma ...”

“Ya isa Maryam!” Mama ta katse ta tare da ce mini “je ki Fateena ki kwanta” kai na jinjina mata tare da wucewa da sauri na shige ɗaki.
Ko kaya ban rage ba na haye gado na soma lumshe ido,a can cikin ɓargon zuciyata ina jin cewa da akwai wani abu da ya faru da ni amma na manta .Da na ga kamar ina son jawowa kaina matsanancin ciwo ne sai na ture tunanin na soma sauke ajiyar zuciya ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.Tsawon lokacin ina baccin kafin na farka,wanka na soma yi na canza kaya sannan na fito falo.

Zungum na tarar da su kamar ba su cikin walwala,Maryam ta taso da sauri za ta soma yi mini tambayoyi amma Mama ta dakatar da ita sai ma abinci da aka ce ta ɗebo mini.Bayan na ci na ƙoshi sai na je na kwanta kan kujerar da Mama ke zaune,kaina na ɗora kan cinyarta sai da ta ɗan buɗe rigata ta taɓa ƙatuwar layar da ke wuyana sannan ta ce “Fatee ya aikin fatan komai ya tafi daidai?”

Na yi murmushi mai sauti na ce “eh alhamdullah,sai gobe kuma zan koma da safe” sai na ga ta kalli Maryam tare da sakin ajiyar zuciya.

Wunin ranar dukkan motsina akan idon Mama yake da muka zo kwanciya sai da ta shafa mini wani mai marar daɗi.
Washegari haka na shirya na tafi asibiti,sai dai tun daga bakin ƙofa na ga canji saboda yadda kowa ya sha jinin jikinsa.Ina isa na samu abokiyar aikina Farida,cikin sakin fuska na soma yi mata magana amma sai na ga tana haɗe rai ina shirin tambayarta lafiya ai kuwa sai ga wanda ya ɗauke ni aikin ya shigo tare da miƙo mini takarda.
Da na duba sai na ga ta sallama ce,na ɗaga kai ina shirin yi masa magana ya nuna mini ƙofar fita cikin tsawa yake cewa “ki fita” babu yadda na iya na fice ɗin.


Idona tab ƙwalla haka na soma tafiyar ƙasa ina tunanin me zan cewa su Mama,kawai sai ji na yi na faɗi ƙasa.Na maido hankalina jikina,wani mai mota ne ya kaɗe ni,idona kansa har ya fito ya miƙar da ni tsaye.

Cikin sanyin murya yake cewa “fatan kyakkyawa ba ta ji ciwo ba? ”
Kai na girgiza masa,murfin motarsa ya buɗe mini tare da cewa “da dukkan alamu akwai abin da yake damunki mu je na rage miki hanya” kamar wacce ya yi wa asiri haka na shiga kuwa.Ya zagayo ya zauna,ya soma driving yana mai cewa “sunana Dr Bilal”
Da sauri na dube shi sai na ji tamkar na san sunan da kuma fuskar,sai dai ban iya tunawa ba sai murmushin yaƙe da na yi.
Takardar hannuna ya karɓe ya karanta bai ce komai ba haka ya ajiye ta yana ɗan haɗe rai,ni ma sai na sunne kaina.Ban ɗago ba sai da na ji yayi parking,ido na shiga ƙyaftawa ina kallon wata haɗaɗiyar asibiti wacce ta fi waccan girma da kuma kyawu.

Fita ya yi,ya buɗe mini ƙofa haka ni ma na fito kamar wata doluwa na take masa baya har muka shiga ciki.Likitoci na tarar birjit,duk suka miƙe tsaye tamkar masu zaman jiranmu.Cike da girmamawa suka gaishe shi kafin shi kuma ya ce “ina mai gabatar muku da nurse Fateema,daga yau za ta fara aiki da mu a wannan asibitin ” duk sai suka shiga taɓa mini suna murmushi,a dole ni ma na murmusa ɗin ina kallon Dr Bilal ina mamakin ta ya aka yi ya san sunana .Nan ya bar ni tare da su,suka soma gabatar mini da junansu a nan ne na haɗu da ƙawata Rahinatu mace mai sauƙin kai da tausayi.Ita ce ta nuna mini ko ina na asibitin,a cikin zagawar da take yi da ni ne take ce mini “kina da matuƙar sa'a tun da har ki ka samu Dr Bilal shi ne da kansa ya kawo ki asibitin nan,a kaf manyan likitocin asibitin nan masu faɗa a ji duk ya fi su tsatsauran ra'ayi kusan saboda kafiyarsa ne akan ra'ayinsa yasa ya shiga komar maƙiya.Tsawon lokaci yana hannunsu sai jiya ne ya dawo”

Na ce “ni kuwa ban ga wani zafin kai a tattare da shi ba” . Tana shirin yin magana wata nurse ta zo da sauri tana mai cewa “ Dr Bilal na neman nurse Fateema a ofis ɗinsa” wata irin faɗuwar gaba ce na ji wacce ban san dalili ba,nurse Rahinatu ce ta yi mini rakiya har zuwa bakin ƙofa.Bayan ya bada izinin shigowa sai na tura ƙofar tare da yin sallama,bai amsa ba ya dai zuba mini idonsa masu kashe ruhi da mugun sauri na sunne kai tare da ja na tsaya.Ya taso ya yi tsaye a gabana yana mai kamo dukkan hannuwana,murya kamar mai yin raɗa yake furta mini “ina sonki ƴar cikin Fateema ”yana gama furta haka babu zato babu tsammani na ji bakinsa kan laɓana yana mai tura harshensa....” yadda na ji an fizge gilashin da ke manne a idona haɗi da hullar kaina su suka tsayar da labarin rayuwata da nake gani ana hasko mini.


Cikin zafin rai na ga Mu'azzam ya finciko ni da mugun ƙarfi daga kan kujerar,ƙirjina ya bugu da nasa na yi baya kamar zan faɗi amma yadda ya riƙe hannuna gam ya hana faruwar haka.
Tsabar yadda yake wani tamke fuska dukkan illahirin jijiyon kansa suka fito,cikin masifarsa da nake mugun tsoro ya soma yi mini ihu.

“Wato da yake ke ballagaza ce shi ne daga baki aiki har da yi masa sumbata,ke jarababiya ƙanwar ayyu”

Idona suka fara zubar da hawayen azaba,cikin rawar murya na ce “sumbata kuma? Ni ban sumbaci kowa ba”

Tamkar wanda ya fita hankalinsa haka ya wani tura ji jikin bango tare da kama wuyana ya ce “in ina magana kina ƙaryatawa sai na shaƙe miki wuya ki mutu kowa ya hutu da fitinarki,ke yanzu ko kunya ba ki ji ni kike faɗa wa Dr Bilal ya sumbace ki? ” muƙut ! Na haɗiye yawun tsoro ina son ƙaryatawar amma ina jin tsoronsa,ni ban ma san taƙaimamai abin da yake magana a kai ba.

Hawaye ne suka soma yi mini zarya ina mai kallon tsakiyar idonsa waɗanda masifa ta saka su yin ja sosai.Tsawon lokaci muna kallon juna kafin ya janye daga kusa da ni ya juya mini baya,can kuma ya ce “fita” furucinsa ya tuna mini dagar da na sha da mahaukacin ai kuwa da mugun sauri na koma gabansa ina mai girgiza masa kai.Tsakiyar idona ya duba,kafin ya kawar da kai ya je ya buɗe wata ƙofa ya shiga.Kamar jira take ya gusa haka ta bayyana gare ni tana mai kallona da idonta masu matuƙar firgitarwa.Da wani irin bala'in gudu na bi bayansa,sam ban yi tunanin toilet ce ya shiga ba.Jikina na mugun kyarma na juya masa baya,tsorona na daɗa ƙaruwa ido kawai na rumtse ina jin yadda zazzaɓi ya soma kawo mini farmaki.
Ƙiiii haka ya jawo ni waje ,a dole na buɗe idona nan na yi arba da ita fatalwar ya buɗe baki zai yi masifar na ƙanƙame shi tare da yi masa magana cikin fitar hayyaci “fa..tal...ta..talwa ” yadda numfashina ke ta ƙoƙarin tsinkewa yasa a dole na yi shiru.

Ina jin lokacin da ya saɓe ni ya fito da ni,wani ɗaki ya kai ni ya kwantar kan gado yana son ɓanɓare ni amma na ƙi sakinsa don har ga Allah tsoron budurwar nake yi wacce ban san wace ce ba.

“Ki nutsu ta tafi” ya faɗa cikin taushin murya,jin yanayin da ya yi maganar yasa na sake shi tare da buɗe ido a hankali.Cikin nasa idon na sauke nawa,babu laifi ya saki fuskarsa duk da babu wani annuri.Hannuna na duba sai na ga ashe bottle ɗin rigarsa ne na tsinke,ya juya mini baya kafin ya fiddo waya a aljihu ya yi kiran Jabeer .Babu jimawa ya shigo riƙe da akwatin likitoci.

“Ka duba ta sai ka yi mata allura ” Mu'azzam ya faɗa yana mai waigowa ya dube ni,shi kuwa Jabeer ya matso kusa da gadon da nake kwance.Da sauri na tashi zaune ina mai cewa “wallahi lafiyata lau ban so” Jabeer ɗin bai saurare ni ba ya soma ƙoƙarin yi mini allurar,ban kuwa yi wani tunani ba na gantsara masa cizo a dole ya yi baya yana kallona yayin da shi kuma Mu'azzam yake wani murmushi mai fitar da tsantsan kyawunsa.

Kamar wata yarinya na dire daga kan gado na je bakin ƙofa ina rarrabar ido, Mu'azzam ya kalli Jabeer ya tuntsire da dariya kafin ya ce “zan wuce gida sai mun yi waya” sai ya zo gabana ya buɗe ƙofar,na take masa baya har mota.Wannan karon ni na buɗewa kaina can gidan baya,na takure wuri guda.Shi ma a slow ya soma tuƙin har muka iso gida yana satar kallona ta cikin madubi.Kusan a tare muka shiga falon sai kawai duk muka yi tsaye saboda yadda aka ƙawata shi ,goggonsa Kabira ta zo da sauri ta kamo hannunsa tana cewa “Zeezi ki sauko ga angonki ya ƙaraso” Daddynsa ne ya soma yin taɓi shi da sauran dangin da aka tara a wurin amma banda Ammy wacce ke kallon fuskar ɗanta.


Ƙarar saukowarta yasa na ɗaga kaina sama,budurwar da muka fara cin karo ce a can Duwala gidan Ammy.Ta sha kyawu har ta gaji,kuma babu ƙarya ta haɗu sosai don sai da ta burge ni.Tana isowa falon jikin Mu'azzam ta je ta faɗa ,da dukkan alamu kuma ba wannan ne farkon yin hakan ba duba da ko kaɗan bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login