Showing 3001 words to 6000 words out of 24397 words
Chapter 2 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt
kallon motar sai ya buɗe mana ƙofa muka wuce ba tare na san dalilinsa ba,nan ne na ga ainahin kyawun gidan.Tsoro ne na ji ya kama ni,ko kafin mu ƙarasa a babbar ƙofar da za ta kai mu ainahin falon gidan tuni jikinmu ya jiƙe.
Muna yin tsaye ƙofar ta buɗe da kanta,Maryam na gaba riƙe da hannuna muka shiga sai kuma na ja na tsaya cak saboda ƙatoton hotonsa da na gani manne a bangon da ke saiti da ƙofar shigowa.
Ƙarar sautin takalmi masu tsini shi ya maida mini kallona ta ɗaya ɓangaren,wata matashiya ce ta fito tana tafiya kamar za ta karya ƙasusuwanta.
“Wa kuke nema?” ta tambaye mu cike da wulaƙanci,kafin mu kai ga cewa komai kuma wata dattijuwa ta fito tana cewa “Sarah ki iya bakinki” ta yamutsa fuska kafin ta yi gaba,ni kuwa tambayar kaina nake ko ina za ta je cikin wannan daren a yayin da ake ruwan sama kuma.
“Sannunku da zuwa kun sha hanya,ku zo ku zauna” matar ta faɗa tana sakin wani murmushi.Ita ce ta yi mana izinin hawa kan kujeru kafin ta saka masu aiki su kawo mana Coffe ,kasa sha na yi sai raba ido nake ina jin tsoro na sake shigata ga hotunan mutumen da har abada ba zan manta da kalmar da ya faɗa mini ba duk ko ta ina su ne manne da bango.
“Ki ɗauka ki sha anty Fatee ” cewar Maryam ƙin kula ta na yi sai ma jikina da na dinga ƙanƙamewa.
“In babu damuwa ina son sanin daga wane gari baƙinmu suke” dattijuwar ta faɗa tana mai yin zaune tana kallonmu.
Maryam ta soma kame-kame kafin ta ce “wurin mai gidan muka zo”
Ta saki ɗan murmushi ta ce “shi ɗin ɗana ne ,ina son sanar da shi ne saboda gudun ya yi faɗa an bar baƙinsa ba tare da ya sani ba”
Maryam ta buɗe aljihun rigarta ta ciro wata tsohuwar fatar rago wacce aka yi wa rubutu a jiki ta miƙawa matar,ita kuma ta karɓa tare da soma karantawa tana yi tana ɗagowa tana kallonmu har ta gama.
“Ke ce Fateema?” ta tambayi Maryam,ta girgiza kai ta ce “a'a antyna ce” sai ta yi mata nuni da ni.Kallona ta yi na wani lokaci kafin ta miƙawa Maryam fatar wacce take tamkar takardar wasiƙa,sai kuma ta ɗauki waya ta yi danne-danne kafin ta kara a kunne.
“Mu'azzam ka zo gida ka yi baƙi daga masu muhimmanci ” shi ne abin da ta faɗa kawai ta kashe kiran,sai kuma ta dube mu ta ce “in ya zo sai ki basa takardar ” sai kuma ta ƙwala kiran sunan mai aiki ita ce ta nuna mana ɗakin da za mu kwanta wanda babu abin da babu hatta gado da frigine.
Muna shiga na fizge hannuna cikin masifa nake cewa “sai wani jimƙe mini hannu kike yi kamar ƙaramar yarinya,ina ne kika kawo ni ? Za ki faɗa mini abin da ke faruwa ko kuwa sai na bi dare na tsere?”
“Kin ga zo ki cire kayan jikinki ki sauya wasu kafin mura ta kama ki” cewar Maryam.Ji na yi kamar na ƙurmar ihu tsabar takaici ,wai ƙanwata ce ke bani umarni .Na yunƙura zan shaƙe ta sai na soma atishawa,babu jimawa kuma zazzaɓi ya kama ni sai na soma gangame jikina a dole na cire kayan jikina na ƙudundune da zanen gado.Maryam ta saki murmushi ta ce “bari na je na ɗauko kayanmu” tana fita na ƙara ƙanƙame jikina ina jin tsoro.
Idona na rumtse gam daidai nan kuma na soma jin wata irin tsawa da cida,babu shiri na diro daga kan gado ina shirin fita wutar ɗakin ta ɗauke daidai nan kuma aka turo ƙofa.Na saki wata irin razananiyar ƙara a sa'ilin da na kai masa karo,na yi baya zan faɗi ya taro ni tare da maido ni kan ƙirjinsa yana wani matse ni.Cikin tsoro ni kuma na gantsara masa cizo haɗi da tura shi sai muka yi baya muka faɗi,na faɗa kan ƙirjinsa.
Ido na waro jin sautin muryarsa da ya fitar da “washhh!” ni duk a tunanina ɓarawo ne,ƙoƙarin ƙwace jikina nake yi hakan sai ya bai wa zanen gadon da na yane jikina damar soma walwalewa iska ya kaɗa shi ya rufe idona yayin da nake jin ƙirjina duk a buɗe sam ban san hasken wuta ya dawo ba sai da ya hankaɗe ni na faɗi,ina jin lokacin da yake jan tsuki.
“Me kike yi kuma a nan?” sautin muryar Maryam ya daki kunnena.Na tashi zaune ina turo baki tare da gyara zanen.
“Anty Fatee ki zo ki kama mini kin tsaya kuma kallona” ta faɗa tana mai jan trollynta,a dole na miƙe na ja ɗayar na kai can ɗaki.
Har na buɗe na zaɓi kayan da zan saka tunaninsa bai bar zuciyata ba,babu abin da ya fi damuna irin ƙamshin jikinsa mai kashe ruhi.Cikin kaya masu ɗan nauyi na shirya sannan na haye bed,ina shirin lumshe ido matar gidan ta shigo tana murmushi.
Cikin sigar bayar da haƙuri take cewa “halin Mu'azzam ne sai shi,abu kaɗan ke saka shi fushi amma kar ku damu na san da sannu za ku saba.Me ya ce muku?”
Maryam sai ta dube ni,tana mai cewa “a'a ni bani nan ya shigo anty Fatee me ya ce?”
Rikecewa na yi na soma kame-kame,sai ita matar ta yi murmushi ta ce “kar ki damu yi kwanciyarki”
A ɗan rikice na ce “hajiya halan ce miki yayi na...naaa ”sai kuma na yi shiru.Ta ƙaraso ta zauna gefena ta ce “bai ce mini komai ba,sunana Ammy ba Hajiya ba ki kira ni da haka don haka kowa ke kirana da shi” sai kuma ta taɓa goshina da sauri kuma ta ce “zazzaɓi ne ya sauko muku bari na kira Mu'azzam ya zo ya duba ki” tana gama faɗar haka ta fice.
★MU'AZZAM
Shararren likitan abin da ya shafi ƙwaƙwalwa ne,bayan haka kuma yana taɓa wasu ɓangarorin aikin jinya da dama.Ƙwarewa a fannin aikinsa da kuma yadda mahaifiyarsa ta tsaya masa shi ya ƙara fito da tauraronsa yake haskawa a ƙasarsa ta haihu Kamaru da kuma sauran ƙasashen ƙetare irinsu Nijar,Tchadi da Nigeria .Bayan aikin likitanci yana kuma taɓa siyasa wacce yake da kujera mai girma ta ministan lafiya, wannan yasa shi yake zaga garuruwan da suka kewaye Kamaru don samo bakin zaren abin da ya adabi nahiyarsu wato ta mace-macen mutanen da kullum farashinsa ke ƙara hauhawa.Sai dai duk wannan ƙwarewa ta Dr Mu'azzam har izuwa yanzu ya kasa nemowa kansa lafiyar cutar da ke uzura rayuwarsa,wato matsalar fitsari.A ƙalla yana yin fitsari kusan duk bayan minti ashirin wasu lokutan in ya kwanta bacci ya kan tsinci kansa tsamo-tsamo cikin fitsari.Duk wani gwaji an yi masa amma babu wata alama da ta tunana mafitsararsa nada rauni,maimakon kuma ya ɗauki ƙaddara sai kuma ya kasa jurar haka kullum cikin tunani yake wanda hakan shi ne silar mutuwar annurin fuskarsa.A irin yawan shiga banɗakin da ya saba yi ne ya haɗu da Nurse Fateema wacce yake jin in akwai wacce ya tsana to bayanta yake,saboda in banda likitocin da suka taɓa duba lafiyarsa babu wanda ya taɓa ganin sirrinsa.
Tun bayan da aka gama meeting ɗin da ya je ya shigo jirgi ya koma can babban birnin tarayyar Kamaru Yawunde,kiran mahaifiyarsa ne yasa ya ƙara shigowa jirgi aka kawo shi Duwala cibiyar hadadar kasuwanci.
Yana zuwa Ammy ta shaida masa inda ta sauke baƙinsa,yana shiga kuma aka rashin sa'a ya ci karo da Fateema duk abubuwan suka faru da shi.Ganin cikar ƙirjinta har ya fi yi masa ciwo kan buguwar da yayi a kai, wannan yasa ya cilla ta gefe.Yana fitowa daga sashen ya ci karo da Ammy,cikin halin nasa na masifa yake cewa “ban san kuma daga ina bagidajiyar nan ta fito ba mtwsss!” bai kuma ya tsaya ya saurari Ammy ba ya haye can saman bene inda sashensa yake.
Duk wasu kayan da ke kan teburi ya shiga zubar wa yana jan tsuki duk don hana ƙwaƙwalwarsa tunano masa abin da idonsa suka gane masa....
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪
*FCWA*☀️
________________________
03
Duk wata tsikar jikinsa sai da ta tashi duk da kuwa yadda yayi ƙoƙarin hana faruwar hakan.Ido ya soma ƙanƙancewa yana ja da baya yayin da kuma tunaninsa ke basa tamkar ga surar fatalwar budurwarsa nan na tunkaro shi.Kan bed ya zube ita kuma ta yi tsaye tana kallonsa tana yi masa dariya,cikin fitar hayyaci ya jawo inda yake ajiye alluransa dakyar ya iya yi wa kansa allurar.A take zufa ta karye masa sai ya soma maida numfashi,ya jawo blanket ya rufe kansa babu jimawa baccin wahala ya ɗauke shi mai cike da mafarkin nurse Fateema.
Lokacin da Ammy ta shigo ɗakin don kiransa tana ganin yana bacci sai kawai ta ƙyale shi ta fita ta sa a haɗa wa Fateema shayi mai kauri sai ta sha magani.
★FATEEMA
Ina nan kwance Ammy ta dawo ita da ƴar aiki,har sai da na ja ajiyar zuciya jin wai yayi bacci.Hakan yasa na karɓi shayin na sha shi da maganin,babu jimawa kuma na ji duk zazzaɓin ya sauka.Tunani na ta yi barkatai har ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.
Washegari ko da na farka tuni duk an kawo trollynmu,ban ga Maryam ba sai kawai na shiga toilet na yi wanka na fito na kimtsa sai na yi zaune gefen gado ina tunanin Mama ga shi ban zo da waya ba ballantana na kira ta.
Ina nan zaune mai aiki ta shigo ta ce “hajiya ta ce ki fito” da sauri kuwa na miƙe na bi bayanta,a falo na tarar da su idona kuma kansa ya fara sauka yana zaune cikin baƙaƙen suit hannunsa riƙe da wasiƙar jiya yayin da kuma Maryam ke gefensa ta wani sunne kai.
“Kin fito? Ƙaraso mana” Ammy ta faɗa tana murmushi,na ɗan sunne kai tare da cewa “ina kwana?”
Ta ce “lafiya lau alhamdullah ! Na shiga ɗakinku na tarar kina bacci har Maryam za ta tashe ki amma na hana ta na ce ta bari ki huta.Ɗauki plate ga shi can kan table”
Jikina na ɗan rawa na nufi dianing na ɗauko plate ɗin,na dawo ina shirin wucewa ta gabansa ya ɗago ya dube ni da shegun idonsa nan take ƙafafuna suka harɗe na yi kamar zan faɗuwa yasa ƙafarsa ya taro ni,cikin masifa yake cewa “ki kalli gabanki kin wani tawo kina rawar jiki” masifarsa ta saka na saki plate ɗin hannuna ban shirya ba,abin da ke ciki duk ya zube .
“Ka bi ta sannu mana Mu'azzam ,kana yi mata tsawa me zai hana ta rikice? Kin ga zo ki zauna nan inda ma can kika zauna kika ci abinki duk da bai takura ki ba” Ammy ta faɗa tare da kamo hannuna ta zaunar da ni,na ɗaga kai a hankali na dube shi sai na ga ashe hararena ne yake yi kamar idonsa za su faɗo.Wani irin tausayin kaina ne na ji,sai na dubi Maryam ina shagwaɓe fuska sai ta kawar da kai.
“In ta gama ta same ni a mota” ya faɗa tare da miƙewa ya fice.Wani abincin aka kawo mini sai rarrashina Ammy ke yi a haka dai na samu na ci,sai kuma na ji wani batu wai zan bi Mu'azzam zuwa asibiti.
“Wurin me Ammy ?” na samu kaina da tambayarta,sai na ga Ammyn ta dubi Maryam da sauri ta ce “zai duba ki ne”
Na ce “ai na warware”
“Kin ga don Allah ki tashi ki tafi,ba ki da lafiya shi ne dalilin zuwanmu nan”Maryam ta faɗa tana kamo hannuna a dole na miƙe sai ka ce wacce ta yi wa asiri.
Ammy ce ta yi mana rakiya har bakin motarsa,a baya muka zauna direba ya ja mu bayan Ammynsa ta yi masa nasiha da tuni game da girman amana.Ta cikin madubi muke ɗan haɗa ido da shi a haka har muka isa wata asibiti mai kyau.Cike da girmamawa ake gaishe shi har muka isa ofis ɗinsa,wata kujera ya nunawa Maryam ya ce ta zauna ni kuma ya tisa ƙeyata gaba muka shiga ciki.
“Ki je ki hau gado” ya faɗa dakyar kamar wanda bai son yin magana.Tsoronsa ya yi mini jagora har na je na hau na kwanta,sai da ya ɗora farar riga sama sannan ya saka safar hannu sai ya zo ya duba idona kafin kuma ya ja kujera ya zauna ya ce mini “wace ce ke?”
Da ɗan mamaki na dube shi kafin kuma na ce “Fateema”
Ya haɗe rai cikin masifa ya ce “yaushe na tambaye ki sunanki? Cewa na yi wace ce ke?”
Tuni idona sun kawo ruwa,na tsani tsawa ko kuma yi mini magana cikin ɗaga murya.
“Kin ga ba kuka na ce ki yi mini ba,amsa za ki bani wace ce ke?”
Cikin muryar kuka na ce “Nana Fateema Abdullahi ” ido ya ƙanƙance yana kallona kafin ya ƙwala kiran sunan“Maryam???” da sauri kuwa ta shigo tana mai cewa “ga ni ”
“Ki tambayar mini antynki wace ce ita” ya faɗa yana wani yin baya yana kaɗa ƙafa.
Maryam ta dube ni kafin ta ce “ɓoyewar me za ki ci gaba da yi anty? Kawai ki faɗa masa wace ce ke”
Cikin rashin fahimta na ce “Maryam me zan faɗa masa? Na faɗa masa Fatee ce ni,sai me kuma yake son sani?”
Wata irin dariya ya tuntsire da ita kafin ya ce “Maryam fita!” ai kuwa ta fice,tana fita sai ya miƙe tsaye yasa hannu ya kama hijabina da sauri na damƙe shi kuwa na ce “me za ka yi?”
Ba tare da ya dube ni ba ya ce “a asibiti in patient ya zo likita na duba bugun zuciyarsa ko ba a koya muku hakan ba?” da sauri na cika shi,sai ya yi sama da hijabina da kuma rigata.Safar hannunsa na ga ya cire,ya ɗora dukkan tafukan hannunsa a cikina “kin ga periode ɗinki a jiya ” ya faɗa mini sam ba wai tambayata yake yi ba.A hankali ya soma daddana wurin a nan take kuma na soma jin zafi ina jin kuma lokacin da wani abu ke fitar mini ,ido na rumtse gam a daidai nan kuma na ji ya sake maimaita mini tambayar cikin wani sauti marar amo.
“Wace ce ke?”
“Mayya ce !” na basa amsa kai tsaye.
“Me kike gani a kullum in kina bacci?” ya sake jefo mini tambaya.
“Mutane! Mutane zagaye da wuta!” na basa amsa cikin i'ina.
“Me suke dafawa?”
“Naman mutane”
“Su wane su? Faɗa mini fuskokinsu”
“A'a Bilal zai fasa aurena ina sonsa sosai ba zan faɗa ba”
“Ki faɗa mini fuskokin su wa kike gani”
“A'a ba zan faɗa ba hakan cin amanar ƙauna ce” na faɗa ina mai buɗe idona yayin da hawaye suka soma zubo mini ta gefe da gefen ido.A haka nake kallon Mu'azzam har zuwa yanzu hannunsa na kan cikina yana danna shi,a hankali na kai nawa na ɗora na ce “ban so ka bari”
Janye hannunsa ya yi ya je ya yi tsaye gaban window,murya a daka yake cewa “ban san mene ne so ba,ban san me ake ji ba in aka kamu da shi da har kuka yarda ku mutu kansa.A shawarce zan so ki amayar da baƙin sirrin nan ko ba komai wutar da ke tafasa TUKUNYAR MAYU na garin Kibri za ta daina ci amma kin zaɓi wanda kike so kan dubban al'umma ”
“Ni babu wani sirri da na sani” na faɗa ina tashi zaune.Cikin tsawa ya ce “tashi ki fice mini daga ofis!”
Na turo baki ina kallonsa ina shagwaɓe fuska,sam ban san mene ne ya shiga kwanyata ba da ke ta ƙoƙarin canza mini tabi'a.
“Ba za ki fita ba kenan?” ya faɗa yana mai nufo ni, da sauri na sauko har ina tuntuɓe kafin na je can inda Maryam take zaune.Tana ganina ta miƙe tana mai cewa “har kin gama basa labarin?” ban kai ga bata amsa ba ya fito yana mai cewa “ku je direba ya maida ku gida”
Kallonsa na yi na ga ransa a mugun ɓace duk sai na ji kuma babu daɗi amma sam ban ji zan iya faɗa masa ɗaya daga cikin sirrin Dr Bilal ba.Kamar wata ƴar yarinya haka ta ja hannuna muka fita zuwa can harabar asibitin,direban ne ya ɗauke mu zuwa gida.
★KIBRI
A daidai lokacin da motarsu Fateema ta tafi a wannan lokacin ne kuma mutane suka cika falonsu.Mama ta yi saurin komawa can tana fuskantar mutanen gari da kuma ɗaiɗaikun likitoci masu aiki a can asibitin da nurse Fatee take .
“Ina take ki fito mana da ita” muryar wata tsohuwa da ke nan cikin layinsu ta daki kunnen Mama,tsohuwa ce sosai ba ta da kowa a garin ita ke ciyar da kanta da kasuwar sayar da soyayyar gyaɗa da take yi.
Mama ta yi murmushi ta ce “Iya wa kike nema?”
“Mayyar ƴarki wacce ke kashe yaran maƙwabta yau dai asirinta ya tonu ” tsohuwa Iya ta bata amsa.
Cikin dakiya Mama ta ce “sanin kanku ne Fateema ba ta taɓa cin naman ɗan kowa ba,hasali ma ku ne kuka tunzura ta har ta kai da mayafin da ya suturta baƙin sirrinta ya yaye.Sannan abu na gaba da zan faɗa muku ta bar Kibri kenan har abad...” ba ta ida rufe bakinta ba ɗaya daga cikin likitocin ya ɗauke ta da mari hakan ya yi sanadiyar fashewar bakinta kan kace wani abu tuni sun rufe Mama da kuka,sai da suka yi mata lis sannan suka bar ta nan kwance rai hannun Allah.
Tana nan cikin mawuyacin hali Rahinatu ta zo,dakyar ta iya taimakon Mama ta miƙar da ita tsaye sannan ta ja ta suka fito ta saka ta a mota.Suna gusawa kenan aka cilla wa gidan wuta duk a tunaninsu har yanzu tana ciki.Gudu sosai Rahinatu ke shararawa har suka fita daga cikin gari,hanyar da babu kwalta ta rutsa suka fara shiga ciyayi.Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin ta tsaida motar,sai da ta haƙa wani ɗan ɗaki irin na zamani sannan ta taimakawa Mama ta fito.Wuta ta hura sannan ta gasa wa Mama fuska haɗi da yi mata magani,sai a lokacin ita kuma ta ce mata “na gode sosai Rahinatu ”
Shiru ta yi ita kuma tana kallonta,kafin ta ce “ina Fateema?”
“Su suka aiko ki?” Mama ta tambaya.
Rahinatu ta girgiza kai ta ce “a'a Mama ina son dai sani ne”
“Ni kaina ban san inda suke ba,abin da na sani shi ne kawai ruhin mahaifinsu ne ya tuƙa su izuwa maɓuya mai kyau”
Rahinatu