Showing 21001 words to 24000 words out of 24397 words

Chapter 8 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt

yi ƙoƙarin ture ta ba.

Taɓi aka shiga yi a karo na biyu,ni ma haka na samu kaina da taɓawar sai dai fa a can ƙasan zuciyata haka nake jin wani abu kamar ban murna da hakan.


Goggo Kabira ce har yanzu ta ƙara yin magana “kamar yadda kuka sani an daɗe da ɗaura auren Mu'azzam da Azeeza a yau kuma mun shirya ɗan ƙaramin shagali domin tarewarsu” wata irin langwaɓewa ita Azeezar ke sake yi a jikin Mu'azzam wanda har zuwa yanzu bai nuna farin cikinsa ba,muna haɗa ido da shi sai na ga yana aiko mini wani kallo ya tsayar da dubansa kuma a kaina.Na shagala sosai cikin kallonsa na ji muryarta kusa da ni,“ungo wannan furannin je ki ƙawata ɗakin da za a tarbi amarya”goggo Kabira ta faɗa tana mai miƙo mini wani basket mai furanni sai wani gangame fuska take.Na karɓa tare da juyawa na haura can sama,tsaye na yi ina tunanin to wanne ne daga ciki ɗakin amaryar? Daga bayana na ji motsi ko da na waiga sai na ga ita ce ƴar masifar ta biyo ni.


“Zo na nuna miki yadda komai zai tafi” ta faɗa tare da shiga ɗaya daga cikin ɗakunan,tun daga falon wani sihirtacen ƙamshi ne ke tashi ko ina an gyara shi tsaf,ina biye da ita har muka shiga can bedroom nan ne ƙamshin Mu'azzam ya farmaki hancina ban san lokacin da na lumshe ido ba saboda a ɗan zaman da muka yi da shi na fahimci na fara son ƙamshinsa.


“Ki canza wannan zanen gadon ki shimfiɗa ɗaya daga cikin waɗannan ” furucinta yasa na buɗe ido na ga zannuwan gadon da pink da kuma fara.Da ɗan murmushina a fuska na ce “ina ga a shimfiɗa pink ɗin za ta fi kyau”


“A'a farar za ki shimfiɗa ita wannan gobe sai a shimfiɗata in an cire wannan ” ta miƙo mini farar.Ni kuwa da yake sokuwa ce sai cewa na yi “kamar farar za ta yi saurin ɗaukar dauɗa”

Ta langwaɓar da kai ta ce “dama iya daren farko kawai ake buƙatarta” da sauri na sunne kai don zuwa yanzu na fahimta,ina jin lokacin da ta yi murmushi mai sauti kafin ta ce “kin san daren nan ya fi komai muhimmanci a rayuwar ma'aurata,za su san junansu kuma duniya za ta shaida sun zama ɗaya” tana gama faɗa ta fice.


Wani irin zafi ne na soma jin yana taso mini daga ƙasan zuciya,ban san na mine ne ba haka na soma gyaran kamar yadda ta buƙata .Bayan na gama sai na koma gefe ina kallon yadda gadon yayi tsaf,wata guntuwar ƙwalla ta zubo mini na yi saurin goge ta kafin na fito.

Daga nan saman bene nake kallon yadda dangi ke ta yin hidima,shi kuwa gogan sai faman danna waya yake yi amarya kuwa tana can tsakiyar danginta.A gaban idona Jabeer ya shigo,sai kuma a wannan lokacin ne Mu'azzam ya miƙe ya tarbe shi ina ganin sun tunkaro bene na yi saurin rugawa a guje na shige ɗaya daga cikin ɗakunan .

Wani irin duhu ne ke da ɗakin, amma kamar daga sama na soma hango wani haske wanda ya ja ragamar ruhina izuwa gare shi.Ina isa na zube gwiwaina ƙasa tare da kai hannu na buɗe wani ɗan ƙaramin akwati na ƙarfe,da sauri na rumtse ido saboda yadda hasken ya dalle mini ido.Duk da idona a rufe suke hakan bai hana ruhina gane mini wani ɗan mitsitsin littafi ba wanda duk yayi ƙura,page ɗin farko ce ta buɗe kanta harufan da ke rubuce a ciki suka soma karanta mini kansu ba tare da ni na karanta ba,duk wani sirri kuma da ya ambaci kansa haka zuwa cikin kwanyata ya zauna a daidai lokacin da na buɗe idona kuwa wani irin yanayi ne ya riske ni na ƙarfin power......
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________

10

Cikin riga na ɓoye littafin kafin na miƙe na je bakin ƙofa,ganin babu kowa yasa na fice da sauri .Kai tsaye ɗakinmu na wuce ban bi ta wani shagalin biki ba,gudun kar Maryam ta zo ta tarar da ni ina karatun littafin yasa na shige toilet tare da buɗe page ta biyu sai dai tamkar an kunna fanka haka dukkan pages ɗin suka dinga buɗe kansu harufan ciki na tashi sama kamar wasu ledodi.Banda idanu babu abin da na zuba musu ina kallo,pages ɗin na gama idawa littafin ya ɓatan dabo daga cikin hannuna.

Wani irin nauyi na ji kaina ya yi mini,kamar makauniya haka idona duk suka disashe.Da lalube haka na samu na fito na kwanta kan bed,gurnani haɗi da nishi nake ji a cikin kwanyata yayin da kuma matattun idona ke nuno mini wani ƙasurgumin daji mai albarkar ruwa masu gudana.A cikin yanayin da ya riske ni sam na kasa sanin taƙamaimai halin da nake ciki.




★MU'AZZAM


Tun da suka shigo gidan aka tarbe shi da zancen tarewarsa da Azeeza ya ji zuciyarsa na tafasa.Ji yake kamar ya yi ihu amma ya daure ya ɓoye damuwarsa har abokinsa Jabeer ya ƙaraso.


Ƙofar ɗakin ya rufe ko kafin ya ce wani abu Jabeer ya furta “ ya kamata ka nutsu domin kar ciwonka na zuciya ya tashi ”

A hasale ya ce “na nawa kuma? Ka duba fa ka gani babu shawara ba komai ake yin walimar nan,Ammy kuma na tsaye ba ta ce komai ba ita kuma mahaukaciyar yarinyar nan har da wani taɓa hannuwa take yi tana murna da kuma zuwa ta gyara gado hum! Ji nake kamar na kama da wuta” Mu'azzam ya ƙarashe faɗa yana mai kawai bango naushi.


Jabeer ya ce “kar fa ka manta kai ne da kanka ka ce kana son Zeezi ba haɗa ku aka yi ba”

“Amma ai soyayyar ƙurciya ce,ni yanzu ban sonta ” cewar Mu'azzam.

“In ba ka sonta wa kake so kenan? Don dole akwai wacce ta canza maka ra'ayi” Jabeer ya faɗa yana mai dafa kafaɗarsa.
Shiru ya ɗan yi kafin ya ja tsuki ya ce “ni babu wacce nake so,kawai dai yanzu Zeezi ba ta gabana ” Jabeer ya ɗan yi murmushi mai sauti ya ce “to kawai ka yi haƙuri ƙila ta sake dawowa gaban naka in wacce ta tare mata ƙofa ta gusa”

Da wani mugun kallo ya kalli Jabeer kafin ya ce “kar ma banzan tunaninka ya baka wai ni Mu'azzam zan iya son wannan mahaukaciyar ”

Yayi ƴar dariya ya ce “ni ai dama ban ce ba kai ne ka furta da kanka hakan na nufin dama tana cikin ranka”

Mu'azzam ya haɗe rai ya ce “na kira ka don ka yi mini maganin damuwata amma kana daɗa mini wata”

“Abokina kai ne ba ka son gaskiya in kana cikin wata matsala maimakon ka duba gaskiyar lamarin amma sai ka bari ego ɗinka ya rinjaye ka.Da ka ƙi da kaso kana son Fateemah,tun ranar da ka ganta ka kamu da sonta a kallon farko amma saboda girman kai gani kake ka fi ƙarfin ka so mace kamar ta.Ka sani yanzu duniya ta ci gaba ba wani abu ba ne don ka so macen da ba ta waye ba,kai ne za ka wayar da ita ta zama classic.In ka ɗauki Azeeza da Fateema banbancinsu ƙalilan ne,ka ga....” cikin tafasar zuciya Mu'azzam ya dakatar da shi yana mai cewa “kai ka ga ban kira ka nan don ka zo ka yi mini surutu ba,in ba za ka bani shawara ka tafi kawai”


Jabeer ya dube shi da kyau kafin ya ce “yanzu ya kake so a yi?”

“Inda na san yadda za a yi zan kira ka ne?”

“Kana ganin fatalwar Nadiya ba za ta iya kai wa Azeeza farmaki ba?”

“Inda za ta yi da tun tuni ta yi,amma ko sau ɗaya ba ta taɓa yi ba.Kaf cikin waɗanda take fito ma irin patient ɗina ne da aka kawo masu jinya”

Jabeer ya ce “ka yi wa kanka tambaya don me sai waɗanda kawai suka zo neman magani wurinka?”

“Ban san dalili ba Jabeer amma tabbas da akwai shi,amma mene ne?”

“Ya kamata mu je wurin teacher shi kawai zai bamu amsa ”

“Mu je” ya furta tare da buɗe ƙofar suka fito,har za su sauka idonsa ya kai ga ƙofar rufaffen ɗaki wanda tsawon shekaru ba a taɓa buɗe shi ba.

“Mu tafi ba mu da sauran lokaci ” Jabeer ya faɗa .Haka Mu'azzam ya bi bayansa,da suka sauko sosai Goggo Kabira ta so tsayar da su amma ya ƙi saurarenta.A motar Jabeer suka tafi gidan teacher,wani tsohon mutum ne mai farin gashi ya tsufa sosai sannan makaho ne.
Amma duk makantarsa ya san ƙamshi dukkan ɗalibansa, wannan yasa su Jabeer na isa ya ambaci sunansu.Gaishe shi suka yi a mutumce kafin su faɗi abin da ya kawo su,teacher ya yi murmushi yana mai cewa “maɗaukakiyar littafin tsira tuni ta bayyana a gidanku,tana ɗaya daga cikin baƙinku.Haƙiƙa mawallafin littafin taswira ya yi gaskiya,kamar yadda ya ce ba za a iya ɗaukar littafin sirri ba sai a ranar da ake gudanar da wani taro a cikin wannan filin gidan.Mu'azzam matarka ta gaskiya ta bayyana,matar da a kullum fatalwar Nadiya ke shakkar zuwanta wannan dalili ne yasa take farmakar patient ɗinka don ta san cewa a cikinsu ne za a samu wannan Goddess ”

Kallon juna suka yi kafin Mu'azzam ya ce “kenan tuni an ɗauki littafin sirrin? To amma ta ya za a yi na gane ita wannan Goddess ɗin?”

“Ita ɗin ta fita daban da saura! Kammaninta sun banbanta da na mutane,in tana tafiya iska ne abokin tafiyarta zai dinga kaɗa gashin kanta yana haskaka idanunta.Saura ƙiris ta mallaki dukkan wasu sirrika na tafiyar da aikin prophecy,muddin ta mallake su a yau to akwai yi yiwuwar gidan gawa ya ɗauki fasanja ”

Ran Mu'azzam ne ya sake ɓaci,da wani irin sauri ya miƙe tsaye yana mai cewa “muddin ina numfashi ba zan taɓa barin hakan ta faru ba.Mu je Jabeer,teacher mun gode sai mun sake dawowa”

Teacher ya ce “ Mu'azzam ka kula da kyau,sannan ina so ka sake yin bitar darussan da muka yi a baya sannan ina so ka sani fansar Aljani ba ɗaya take da ta ɗan Adam ba”

Ba tare da ya ce komai ba suka fito shi da Jabeer,tsabar yadda yake jin zuciyarsa na tafasa shi ne ma yayi tuƙin ya dinga gudu kamar zai tashi sama.Shi kuwa Jabeer sai ƙoƙarin dannar ƙirjinsa yake a haka har suka isa gida, lokacin tuni an shiga sallar asar dakyar ya yin alwala suka shiga masjid.Bayan sun fito suka wuce can cikin gida,kamar wani zararre haka yake kallon duk baƙin da suka zo amma bai ga alamomin nan ba da teacher ya shaida masa.


Ammy ta zo ta ja hannunsa ta soma nuna masa wasu dangin da suka zo bayan fitarsa,sama-sama suke gaisawa sai faman baza ido yake kuwa.Lura da hakan yasa Ammy ta ce “lafiyarka kuwa Mu'azzam? Ko dai patient ɗin da aka kawo ɗin ce aikin ya fi ƙarfinka?”

“An kawo wata patient ne?” ya tambaya da sauri.
Da mamaki Ammy ta ce “au dama ba a sanar da kai ba? Oh! Ƙila aiki ne yasa na sha'afa suna can ɗakin waje” yana gama ji ya bar Ammy ya nufi ƙofa,Jabeer ya take masa baya.

Tun da suka doshi ƙofar suke jin wani irin ɗohi,amma a haka suka shiga.Turus suka yi suna kallon wata matashiyar budurwa wacce jikinta yake da shegen datti ,idonta jawur suke kamar barkono kammaninta kuwa kamar wata halitta daga wata duniya .Sun ƙure ƙarshen fanka sai gudu take wannan ya saka figagen gashin kanta damar kaɗawa.

Mahaifiyarta na ganin Mu'azzam ta taso ta gaishe su,ya ce “tun yaushe ku ke nan? ”

“Jiya cikin dare”

Mu'azzam ya kalli Jabeer kafin ya ce “amma ya aka yi ba ku neme ni ba?”

“Wata mata ce ta ce mana mu zauna a nan” ta basa amsa tare da zayyano masa siffar Goggo Kabira.

“Tun da kuka zo kenan a nan kuke?”

“A'a ɗazu Kando ta fita har zuwa can cikin gidan shi ne na je na nemo ta har muka haɗuwa da wata mata mai kirki ta zubo mana abinci” tana faɗar haka ya gane Ammy ce.


Hannun Jabeer ya ja suka ƙara komawa can ciki,sai dai wannan karon can saman bene ne suka haura.Sawun taku ya gani masu cike da dauɗa ,zuciyar Mu'azzam ce ta soma tsinkewa yana addu'ar kar dai abin da zuciyarsa ke raya masa ya zamana gaskiya.


Idonsa ne suka kaɗa suka yi ja lokacin da ya shiga rufaffen ɗaki ya tarar da babu wannan littafi na sirri wanda aƙalla ya gwada ɗaukarsa ya fi cikon casbi amma ya kasa.



Jabeer kamar ya shiga zuciyar Mu'azzam ya ce “tana iya yi wa kuma ba Kando ba ce ta ɗauki littafin wata ce daban”

Jin abin da Jabeer ɗin ya ce sai ya tuna da Mama wacce ya rufe a wani ɗakin kuma.Da sauri ya tafi can sai dai kuma ita kanta ta yi ƙasa ko sama da dukkan alamu ma ba ta cikin gidan,kai ya dafe ya rasa abin da ke yi masa daɗi.

Haka suka zauna shi da Jabeer suna ta saƙa da warwara yayin da kuma gefe guda ake ta tsara yadda diner ɗin da za a yi a yau za ta tafi.



★FATEEMA


Ban san tsawon lokacin da na ɗauka ba cikin wannan yanayin kafin na samu kaina.Toilet na shiga na tsarkake jikina na zo na yi sallolin azahar da asar kafin na gabatar da magarib.Ina nan zaune kan sallaya aka kira isha'i na miƙe na mayar kafin kuma na yi zaune ina lazumi,a haka Maryam wacce yanzu ta zama ƴar gida ta same ni.


“Ga kayanmu waɗanda za mu saka Ammy ta bamu,ki gwada ki gani ko za su yi miki ” shi ne abin da ta faɗa tana mai cillo mini wata doguwar riga pink an yi mata ratsin fari haka kuma an zuba mata duwatsu masu shegen kyawu.


“Ina za mu je?” ita ce tambayar da na yi mata.Sake da baki take kallona kafin ta ce “wajen diner na Mu'azzam ko?”

Na ɗan taɓe baki don har ga Allah duk na manta abin da ya faru,tashi na yi tsaye na gwada rigar ta kuwa yi mini daidai sai dai ta wurin tsawo ta yi mini tsayi.Sai da Maryam ta gama yaba kyawun da na yi kafin ta shiga toilet ta yo wanka,ni ma sai da na sake yin wani kafin na zo na shafa mai da kwalli sai man leɓe.


Da na saka rigar sai na soma dubarar yadda za a yi ta bar jan ƙasa,Maryam da ta lura da haka sai ta ce “ko na karɓo miki takalmi masu ɗan tudu wurin Goggo Kabira?”

Kamar na shaƙe mata wuya haka na ji,na ce “matar da ta nuna tsantsar tsanarmu ita ce za ki je ki nemi alfarma ai gwara na fasa tafiya”

Ammy ta shigo tana cewa “ya aka yi har yanzu ba ku fito ba?” gaishe ta na yi yayin da Maryam ke shaida mata matsalar da aka samu,“ok ina zuwa.Maryam yi mata kwalliya kafin na dawo” Ammy ta faɗa tare da ficewa.

Maryam ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “don Allah anty ki bari na yi miki kwalliyar nan kar Ammy ta ga kamar ba mu yaba da auren ɗanta ba” na buɗa baki zan yi magana kenan sai Maryam ta kamo hannuna,haka na yi shiru kamar kullum na yi zaune ta soma tsantsara mini kwalliya.Tana cikin yi ne wayarta ta yi ringing wacce ban san yaushe ta same ta ba,lambar ƙafata ce Ammy ta tambaya.Har sai da aka kawo mini takalmin Maryam ba ta gama mini kwalliya ba, lokacin da muka ɓata yasa Maryam ba ta tsaya yin tata kwalliyar ba ta saka kayanta ta fice.


Jiƙaƙen gashina da ta ɗaura a tsakiya na baje ina turo baki tare da cewa “salon ya yi mini wari ta wani ɗaure mini gashi” mayafin rigar na ɗora a sama sannan na saka takalmi masu tsinin sai na fita ni ma .Tsit falon yake babu kowa amma ina jin ɗan sautin music daga can waje,hakan yasa na yi saurin fita ina tafe ina ɗan riƙe rigar kamar mai koyon tafiya haka nake takawa gudun kar na faɗi sam ban yi tunanin salon tafiyar zai jawo hankulan mutane a kaina ba.


Idona banda ɗan ƙyaƙyafta su babu abin da nake yi,wani irin iska ne ke kaɗawa wanda ya yi sanadin faɗuwar mayafina daga saman kai zuwa kafaɗa nan take gashina ya soma tashi sama har yana rufe mini fuska.Baza ido nake yi ina son hango Maryam sai dai ban ganta ba,ina juyawa na hangi Jabeer da sauri na nufi can.Sam ban yi lura da tawowar Mu'azzam ba wanda shi ma hankalinsa yake kan waya sai ji na yi na kai masa karo.Na yi baya zan faɗi amma kuma sai na yi saurin cabko hannunsa hakan yasa na dawo gaba sai dai fa tsayuwa kan ƙafafuna ta gagara.Ga mahaukacin ƙamshin da yake zubawa ya fi na kullum,ga kayan jikinsa waɗanda faɗar tsadarsu ɓarnar baki ne ga kuma rikitatun idonsa da ya tsoma cikin nawa.Duk suka taru suka ruɗa ni,hasken cameraru ne ya dawo da ni daga kogin kallonsa da nake yi ,shi ma da dukkan alamu ya shagala da kallona.


Wasu daga cikin waɗanda aka gayyato ne suka soma yi masa congratulations da samun kyakkyawar mata irina.Maimakon ya ce musu ba matarsa ba ce a'a sai ma dai idonsa da yake ci gaba da kallona da su,daga bayana na ji muryar Maryam da sauri na tafi na bar shi har ina shirin faɗuwa.


“Shi ne kika wani tawo kika bar ni can ɗaki” na faɗa ina mitsike mata kumatu,ta yi murmushi kafin ta ce “ki yi haƙuri anty Fatee zo mu je ki zauna” haka ta ja ni muka zauna kan kujerun da aka tanada don zama.Maimakon ta zauna ita ma sai ta tafi ta bar ni,duk sai na soma jina a takure ina jin kaɗaici na mamaye ni.Kamar walƙiya haka na soma ganin wani abu mai ƙyalƙyali na wasa da hankalina,a hankali na miƙe tare soma dosar can cikin shuke-shuken .Sam ban farga da na bar cikin gidan ba sai da na soma jin ƙarar ruwa,da na duba da kyau sai na ga ashe ƙasurgumin dajin nan ne na ɗazu.Ina shirin takawa baya don komawa kawai sai ji na yi na rumza ƙafata ta maƙale a cikin wani rame.Daidai nan wurin ya ɗauki matsanancin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login