Showing 9001 words to 12000 words out of 24397 words

Chapter 4 - TUKUNYAR MAYU Book Complete By Mrs Sadauki.txt

na soma jin muryoyi na kawo mini farmaki yayin da kuma wani iska ya soma kaɗawa mai mugun ƙarfi ,ga wasu inuwoyi da suka soma yin rawa a jikin bangon ɗakin.Yadda ake mini raɗa haɗi da yi mini dariya duk sai na ruɗe na ƙwala ƙara haɗi da janye hannuna daga jikin fitila,nan take ɗakin duhu ya ziyarce shi.Wani ihun na sake yi a karo na biyu jin an jawo ni an matse ni ga bango,zan sake buɗe baki na ji yatsansa a ciki haɗi da sautin muryarsa “shuuut!” tsit na yi ina sauraren bugun zuciyoyinmu da suke gudu a tsiyace lokaci guda........
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________


05

Da sauri na lumshe ido haɗi da jan ajiyar zuciya jin yana busa mini iskan bakinsa a fuska.Murya can ƙasan maƙoshi ya ce “faɗa mini me ki ka gani?”

Tambayarsa ita ta hararo mini abu na ƙarshe da ya razana ni,da wani mugun sauri na jimƙe gefen cikinsa ina jin wani tsoro na sake riskata.Kuka na soma yi ƙasa-ƙasa ina jin duniyar ta ishe ni,a hankali ya ɗan janye daga gare ni tuni kuma na buɗe idona ina kallonsa.Kamar wata mahaukaciya na ce masa “don Allah wace ce ni ? Ita kuma wannan budurwar da na gani daidai can tana kukan jini?”

Bai bani amsar tambayoyin ba,sai ma hannunsa da ya saka ya cire nawa da ke gefen cikinsa.Gadon da na tashi akai ya je ya kwanta tare da kiran sunan Jabeer,shi kuma kamar mai jira ya shigo yana wani kallona kafin ya nufi Mu'azzam da ke faman kama kansa.Magani ya shafa masa mai wani mugun ƙarfi kamar na aljanu sai na ga ya miƙe daram yana wani hararena kafin cikin masifa ya ce “matsala ce ke! Duk in mun haɗe sai kin tono mini masifa,gaba ɗayanki matsala ce fita ki bani wuri” ya ƙarashe cikin tsawa,duk kuma sai na tsorata jikina ya soma rawa.


“Haba Mu'azzam ka yi haƙuri mana,tun da ka soma wannan aikin ai dama dole ka dinga samun matsaloli a rayuwarka kuma ma ai ba ita ce farkon patient ɗinka da ka fuskanci makamanci haka ba” Jabeer ya faɗa cikin rarrashi.

A zafafe ya ce “don Allah fitar mini da ita malam kai ma ai har da kai ake saka mini ciwon kan”

Jabeer ya ɗan yi murmushi kafin ya ce “zo mu tafi” sai ya yi gaba na take masa baya ina mai waiwayen Mu'azzam wanda ke aiko mini harara.Muna fita daga ɗakin na ja ajiyar zuciya,sai na ji numfashina ma ya fi tafiya daidai in ban tare da shi.Har muka sauko ƙasa Jabeer na bani labarin Mu'azzam ɗin yadda yake da saurin fushi da kuma kirkinsa,ni dai iyakata saurare amma ban ce komai ba.Muna saukowa Maryam ta zo da sauri ta rungume ni tana mai shafar fuskata ta ce “fatan ba ki yi kuka ba?”

Kujerun na duba sai na ga an mayar da su yadda suke tun farko,dama can masifarta ce ta sa ta tado mu.Murya a raunace na ce “don Allah Maryam mu koma gida”

“Za mu koma har lokacin tafiyar ya yi,kin ga zo mu koma ɗaki” ta faɗa tare da jan hannuna.Ko da muka isa sai na ji hancina na fizgo mini irin ƙamshin nan da na ji a ɗakin sirri na Mu'azzam tamkar kuma ana ankare da ni haka nake jin ido na bin duk illahirin jikina.Banda tausayin kaina babu abin da nake yi,sam na kasa yarda Maryam ta gusa ta bar ni ko toilet in zan shiga sai ta je kusan ƙofa ta yi tsaye kuma ba na saka key.A wunin dai cikin ɗaki muka yi shi,hatta abincinmu Joy ne yake kawo mana shi.


A washegari sai wani sabon al'amari ya riske ni shi ne kasa riƙe kaina.Kwaɗayi kawai nake ji yawuna suna tsinkewa,amma sam banda tabbacin mene ne nake so.Da abin ya dame ni haka na fita na nufi kitchen,har tuntuɓe nake yi jin ƙamshin nama na tashi ina shiga kuwa na tarar babu kowa sai ƙatuwar tukunyar da ke kan gas.Sam ban damu ba haka na buɗe ta na soma tsamo naman,da zafi da komai haka na dinga ci ina haɗiyewa kafin na farga na cinye nama tasss sai ruwan romo kawai su ma haka na soma lasarsu ina siɗar hannu kafin na gaji na bari na koma ɗaki.Da na shiga na tarar da Maryam na aiki da system,ban tambaye ta ina ta same ta ba kawai na haye bed na soma lumshe ido ina son yin baccin gajiya saboda gudan aikin da na yi na cinye naman ƴan gida.


Babu jimawa kuwa na faɗa duniyar mafarki,kamar kullum yau ɗin ma mutane ne na gani masu yawa sun saka ƙatuwar tukunya a gaba suna rawa da juyi haɗi da waƙa.Wutar murhun sai ƙara ci take yayin da naman mutanen da ke cikin tukunyar sai tafasa yake yi.Kamar mai neman wani abu haka na soma dube-dube ina kallon ko ina na wurin har idona suka sauka kan Dr Bilal yana zaune daga gefe duk alamomin damuwa sun bayyana a gare shi.Ina dab da na yi masa magana na ji wata mahaukaciyar tsawa wacce ta yi silar fizgo ruhina daga waccan duniyar zuwa wannan.Dakyar na iya buɗe idona da suka yi mini nauyi na zube su kan turɓunaniyar fuskarsa mai cike da masifa.Har na buɗe baki zan tambaye shi lafiya amma ya wani fizgo ni a tsiyace,babu shiri gangar jikina ta rabu da gado na zo na faɗa kan ƙirjinsa.Wata irin muguwar matsa ya yi mini yana mai cewa “wato bacci ma ki ke yi saboda kin raina ni ? ”

Ƙoƙarin ƙwace kaina na soma ina mai yin nishin azaba “washhhh! Ka bari don Allah ” ya nuna mini yatsa kenan zai ƙara yi mini wata masifar muka jiyo muryar wani babban mutum na kira sunansa,haka ya wani ja ni ƙiiii har muka fito babban falon nan na tarar da kowa na gidan tun daga ƴan aiki har wani dattijo da nake kyautata zaton mahaifin Mu'azzam ne saboda yadda suke mugun kama da juna.


“Ke muguwa mayya uban wane ne ya baki izinin shiga kitchen ki cinye dukkan naman da ake soyawa Yayana? To yanzun nan zan sa ki amayo shi”Goggonsa ta faɗa tana mai nufo ni amma shi Daddyn ya dakatar da ita “Kabira ki bar maganar nan. Mu'azzam faɗa mini wace ce wannan?”


Maimakon ya bai wa mahaifinsa amsar tambayar sai kuma ya soma yin masifa,“ Daddy yanzun nan ka gama masifar kan sai an nemo wanda ya cinye naman kajinka yanzu kuma da aka fito da ita ka koma yin magana cikin ruwan sanyi kana tambayata cikin sanyin murya”

Daddy ya dubi kowa ya ce su watse kafin ya ce “zo nan ƴata”

Mu'azzam na duba ina son ya sakar mini hannuna,sai da ya murɗe shi kafin ya sake sa shi ɗin ma saboda Daddy ya ce ya yi.Kamar mai tsoron taka ƙasa haka na je na yi tsaye gaban Daddyn na kasa ɗaga kai na dube shi.

“Faɗa mini ƴata ke ce ki ka cinye naman kajin?” ya tambaye ni,da yake ban san kunya ba na girgiza kai na ce “ba ni ce ba Daddy kum...” da sauri Mu'azzam ya katse ni yana cewa “ke maƙaryaciya don Allah ki yi wa mutane shiru don kowa ya san ke ki ka cinye shi”


Na girgiza kai ina kallon Daddy na ce “da gaske ban ci ba Daddy kar ka yarda da shi ƙage yake yi mini saboda ya tsane ni” ina rufe bakina Mu'azzam ya wani dungure mini ƙeya yana cewa “dubi can” ya nuna mini tv,ina dubawa kuwa na hangi kaina a ciki sai fizgar naman nake yi ina yarfa hannu.


Wata irin kunya ce ta luluɓe ni da sauri na sunkuye kai,ina mai cewa “Daddy ka yi haƙuri!”

Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce “zo ki zauna nan ki faɗa mini irin muguntar da yarona ke yi miki ” inda ya nuna mini ɗin na zauna shi ma ya zauna yana mai kallona tare da jefo mini tambaya “a ina kuka yi haɗuwarku ta farko ke da my hero?”

Da sauri na ɗaga kai na dubi Mu'azzam wanda firgici duk ya bayyana a fuskarsa,da wani mugun sauri ya ce “haba Daddy mene ne na wani tambayarta? Ke tashi ki koma ciki”


Dariya ya bani wannan yasa na toshe bakina, wato yana tunanin zan sanar da Daddy na ce a cikin toilet ne.Lura da ba zai so hakan ba yasa cike da tsokana na ce “Daddy mun haɗu ne a cikin ...” yadda ya wani zo shuuu ya kai hannunsa ya toshe bakina shi ya haifar masa da faɗuwa ƙasan capet kusa da ƙafafuna.



Na fiddo ido waje ina kallon tsakiyar nasa idon da suke ɗauke da wani irin ƙwarjini da razani.Tsawon lokaci muna kallon junanmu kafin Daddy ya yi gyaran murya,da sauri ya janye hannunsa tare da tashi tsaye ya wani cabki kafaɗata ya miƙar da ni tsaye ya soma jana.


Banda kallonsa babu abin da nake yi,yadda sumar kansa ke wani tashi cikin iska jijiyoyin gaban goshinsa na daɗa fitowa da alamu ransa ya ɓace ne.Sai da ya kai ni har bakin ƙofa sannan ya tura ni gefe,bayana ya mannu da bango yatsa ya nuna mini yana gangame fuska,tsabar masifar tasa ta kai ƙololuwa bai iya furta komai ba.


Da dukkan hannuwana na dafe ƙirjinsa don tunkuɗe shi amma ko gezau haka yake currr kan ƙafafunsa,sai na janye su da sauri tare da sunne kai .Can ƙasan maƙoshi na furta “ka yi haƙuri ni ma ba zan iya faɗawa Daddy irin halin da na ganka ba a haɗuwarmu ta fark...” ban ƙarashe faɗar kalmar ƙarshe ba ya shaƙe mini wuya,duk idona suka fito sai da ya kusa sheƙa ni lahira sannan ya janye hannunsa tare da tafiya ya bar ni ina faman tari.Dakyar na ƙarasa ɗakinmu,na ɗauki ruwa na soma sha ina bubuga ƙirjina da nake jin tamkar numfashina zai ɗauke.


Da na gama shan ruwan na yi tunanin Maryam za ta tada mini zancen kaji da na cinye amma shiru ta yi sai alamun damuwa da na ga dai a fuskarta.Haka na raɓa gefenta na zauna ina kallon system ɗin,sosai abin da na gani ya ɗauki hankalina.Ba komai ba ne sai hotunan wasu cover masu ɗauke da abubuwan ban tsoro da kuma firgitarwa.A duk cikinsu babu wanda ya fi ɗaukar hankalina sai na wani da aka yi zanen harshe da kuma takaitaccen bayani.Ban yi nauyin baki ba na ce “Maryam wannan ɗin duk na mine ne?”

“Bincike nake yi” ta bani amsa tare da rufe system ɗin,ina shirin yin wata tambayar Joy ya yi sallama tare da cewa “Daddy na kiranki” a yadda ya kalle ni yasa na fahimci ni ce ake kira,da sauri kuwa na tashi saboda haka kawai na ji Daddy ya kwanta mini a rai ko don ban tashi na ga mahaifina ba oho.

A falo na tarar da shi ya saka tv yana kallo,sai da na rusuna sannan na ce “Daddy ga ni”

Remote ya ɗauka ya ƙara sauti,ya yi mini alama da hannu na matso.Ƙasan capet na zauna,murya can ƙasa-ƙasa ya ce “faɗa mini daga wane gari kuke?”

“Kibri!” na basa amsa ,sai ya washe baki ya ce “ni ma asalina can yake,aiki ne ya kawo ni Yawunde.Faɗa mini a wacce unguwa kuke a Kibri?”

Ina shirin yin magana Mu'azzam ya ratso falon kamar wanda aka jefo daga sama, remote ya ɗauka ya kashe tv sannan ya wani zubo mini mugayen idonsa,da sauri na sunne kai ina turo baki gaba.


“Daddy me ka ke yi haka? Wannan ɗin patient ɗina ce,kar ka soma jawo ta a jiki kawai don larurarku ɗaya da ita.Kuma ka bar ƙoƙarin cusa mata wasu abubuwan a kanta sam ban son haka” Mu'azzam ke faɗa yana wani kumbura kamar fulawar da ta ji yis.

Shiru Daddyn ya yi na wani lokaci kafin ya ce “babu ruwanka don na yi hira da ita ,kai da ita duk matsayi guda ki ke a wurina ita ma kamar ƴata haka na ji Allah ya ɗora mini ƙaunarta”

Mu'azzam ya waro ido yana mai cewa “daga ganinta yau shi ne har ka yi mata matsayi irin nawa? Ke taso mu je” ya faɗa a tsawace har sai da na zabura.Ina kumbure-kumbure na bi bayansa har muka isa bakin mota,shi ya buɗe mini murfi na shiga na zauna yayin da shi kuma ya zauna mazaunin direba.Gudu ya soma yi kamar zai tashi sama har muka isa wata asibiti,ko ta ina mahaukata ne ke shawagi duk an ɗaure musu ƙafafu da kaca.Tsoro ne na ji ya saukar mini ganin ya zagayo ya buɗe mini tare da bani umarnin na fito,idona da suka cika da ƙwalla na sauke cikin nasa sai na hango zallar ƙiyayyata a ciki.Finciko ni ya yi yana masifa,“saboda wannan shegen kallon da ki ke yi mini sai na ƙwaƙwule miki shegun idon nan naki masu kama da na mujiya” haka ya dinga jana har muka shiga wani sashe,cike da girmamawa likitan ya zo ya gaishe shi tare da basa kujera tsabar tsiya irin tasa ƙin zaman ya yi sai ni ya zaunar tare da canza harshe zuwa English ya soma yi masa bayanin da ban san na mine ne ba amma lokaci zuwa lokaci likitan yana ɗan dubana.

Can ya ɗauki waya ya yi kira ,babu jimawa kuwa sai ga wata mata ta shigo da hannu ya yi mata nuni da ni ita kuma ta kama hannuna.Kai na soma girgizawa ina mai kallon Mu'azzam,yayin da hawaye suka soma yi mini ambaliya.Wata irin wawar runguma na yi masa tare da ƙanƙamesa na fasa kuka mai tsuma rai,duk yadda ya so ya fincike ni kuwa ya kasa don ba ƙaramin riƙo na yi masa ba.


“Kar ka bari su tafi da ni wallahi ni ba mahaukaciya ba ce” shi ne kawai abin da nake nanata masa,daga bayana na ji shigar tsinke a damtsena wanda ko tantama babu allura ce aka tsira mini.A nan take na ji duk jikina ya saki,doli dangin naƙi tasa na saki Mu'azzam yayin da nurse ɗin ta tallabo ni ta ɗora kan weelshair.Wani bacci-bacci nake ji ,shi ne ya gyara mini zaman kaina yana mai cewa “ki kula da ita sosai sannan ki tabbatar kin yawata da ita duk wani sashe da lungu na cikin asibitin nan” yana gama faɗar haka ta soma tura ni,haka na dinga binsa da ido har muka fice daga ɗakin.Ta wata doguwar hanya ta bi da ni mai shegen duhu da kuma kukan tsuntsaye haɗi da ƙarar faɗuwar matattun ganye da ƴaƴan bishiya.Jin wannan abu sai ya soma hasko mini wani baƙin al'amari da ya taɓa faruwa a shuɗaɗiyar rayuwata.....
[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪


*FCWA*☀️

________________________


06

Tana daɗa tafiya da ni cikin duhun hanyar ina kuma daɗa samun wankin ido game da rayuwata.Tun abin yana zuwar mini da sauƙi har ya kai kaina ya soma matsanancin ciwo tamkar zai tawartse yayin da kuma dukkan illahirin jikina ya soma yin ƙaiƙayi haɗi da motsi.Ba tare da na shirya ba na ƙwala wata gigitaciyar ƙara,daidai nan kuma hancina ya soma ambaliyar jini sai kuma numfashina ya soma barazanar ɗaukewa.Da bala'in sauri ta ida ƙarasawa da ni wani ɗaki wanda ƙwayaƙwayin lantarki suka haska.Taimakon gaggawa ta soma bani don tsayar da jinin da ke zuba,yayin da ni kuma hankalina da tunanina ya soma shawarar ta wacce hanya zan bi na damƙe kurwarta.Haka kawai na samu maƙogorona da soma yin rawa yayin da idanuna suka soma juyawa suna kaɗawa kamar garaya,cikin abin da bai fi minti biyu ba na ci galaba kan nurse ɗin na damƙe kurwarta sai dai fa haɗiye ta ya gagare ni.Baya da baya na ga ta soma yi tare da danne ƙirjinta da ya yi mata nauyi,da gudun bala'i ta fice.


Idonta kamar za su rufe haka ta ƙoƙarta ta koma can ofis ɗin babbansu,tana kawowa ta zube ƙasa idonta na juyewa. Hankali tashe ya soma ambaton sunanta,ganin ta kasa cewa komai ya je bakin ƙofar toilet wacce Mu'azzam ya nemi a barsa ya shiga don juye larurarsa ta yawon fitsari.
“Dr Mu'azzam Please ka yi sauri ga nurse ɗin da na wakilta don kula da patient ɗinka nan ta dawo cikin mawuyacin hali”


Cikin azama kuwa ya fito,kallo guda ya yi wa nurse ɗin ya fahimci abin da ke faruwa.Maimakon hankalinsa ya tashi a'a sai ma wani murmushin gefen baki da ya yi,sannan ya ƙarasa ya taɓa goshinta ya soma karanto wasu addu'o'i nan take ta soma yin gumi sai kuma bacci ya ɗauke ta.

Mu'azzam ya ce “a kaita wani keɓaɓen wuri,kar wanda ya tayar da ita zan kula da komai” yana gama faɗar haka ya fita,idonsa ya lumshe ya soma jefa ƙafafunsa ruhinsa na yi masa iso izuwa ɗakin da nurse Fateema take .Yana ƙara matsawa yana kuma ƙara jiyo hargowar baƙin ruhin da ke mallakar gangar jikinta sai cika yake yana batsewa,yana isa kuma ƙofar ta buɗe da kanta.


Tun bayan fitar nurse ɗin nake ta ƙoƙarin haɗiye ruhinta amma tamkar an yi wa maƙogorona dabaibayi haka nake ji.Yana shigowa ɗakin na tsaya cak da abin da nake yi,na zuba masa idona da suka rikiɗe suka zama tamkar wuta.

Cikin wata murya da ba tawa ba na ce “Agent Mu'azzam ko kuma na ce Dr hahaha!”

Sai a lokacin ya buɗe idonsa yana mai yin murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa ya ce “ban san wace ce ke ba! Haka kuma ban buƙatar sani,sai dai da dukkan alamu abin harina tuni ta san da zamana ”

Wata dariya na ƙara jin na yi kafin na motsa bakina “zai fi kyautatuwa ka fita daga hanyata don ni ɗin ba ire-iren ruhikan da ka saba cin karo da su ba n...” ban ida rufe bakina ba Mu'azzam ya ɗaga hannunsa na dama yana mai cewa “daga Allah muke,gare shi za mu komawa,sannan a gare shi muka saka dukkan yardarmu ” tamkar feshin wuta haka kalamansa suka samu tasiri a gangar jikina,wata irin banƙarewa na yi ina zalzalo harshe yawu suka soma zuba.Cikin hargowa na buɗe bakina na soma yin magana wacce ainahi ba daga tunanina take ba.“Kar ka sake ambaton sunan Allah a inda nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login