Showing 27001 words to 30000 words out of 41435 words

Chapter 10 - NAMIJIN DARE Hausa Novels Complete.txt

NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________






*43 & 44*



_____________Ƙin karɓa ma'u tayi tana mai godiya, hakan ya ba suraj mamaki dan shi a rayuwar sa, babu abinda yafi ƙi irin yama kyauta kaƙi karɓa, ƙyaleta yayi kawai ya fita daga ɗakin....
Tsakar gida ya samu inna a zaune nan ya mata sallama akan zai wuce, inna tace
"bari na baka saƙo ka kaiwa Momyn ka.." ɗaki inna ta shiga ta fito da leda ɗauke a hannun ta, ganin baya tsakar gidan yasa inna tayi kiran ma'u da sauri...
Fitowa ma'u tayi tana zumɓura baki kamar wata ƙaramar yarinya, lallashinta inna ta fara, dan yanzu inna ta daina jin haushin ma'u, tunda tasan lalurar da take damunta, janta take a jiki haɗe da kuma nuna mata soyayya...
cikin rarrashi inna tace
"Ma'un inna! Ungo nan kai masa yana waje yana jiranki, in mutum yayi baƙo in zai tafi rakashi ake kinji koh.."

Amsawa da "to." Ma'u tayi tana karɓar ledar hannun inna, tana fita ta same shi zaune a bayan mota da dukan alamun dama ita yake jira, dan hatta mirfin motar a buɗe ya barshi, ƙarasawa tayi tana tuttura baki, wai ita a dole an takura mata....
Alama ya mata da ta shigo cikin motar, ba haka ma'u taso ba dandai kawai bata san yi mai musu ne, zaunawa tayi kan kujerar amma ƙafafuwan ta suna daga waje, miƙo masa ledar da inna ta bata tayi tana cewa
"Gashi inji inna tace kaba momy.."
Ƙin karba yayi yana binta da wani irin kallo, ita kanta Ma'u sai da taji kunyar kalar kallon da yake mata, cikin sanyin murya Ma'u tace

"Lafiya..!"

Murmushi Suraj yayi sannan yace
"ba komai! Kawai naga kin min kyau ne.."

"Uhmm! Ina so in shiga gida pls.."
Ma'u ta faɗa cike da shagwaɓa
Cikin nuna kulawa Suraj yace
"Kodai kin gaji dani ba! Shiyasa kike so in tafi.."
Dariya Ma'u tayi tana cewa
"Ah ah wallahi! Kawai dai ina da ɗan wani aiki ne a cikin gida.."
Murmushi yayi kawai, sannan ya ɗauko wata ledar shopping yana miƙo mata, tsayawa Ma'u tayi tana kallon sa, Suraj kuwa ganin bata karɓa ba, yasa cikin tsare gida yace
"Karɓi mana!" Ya faɗa yana ƙura mata ido...
Kwarjinin da ya mata ne yasa ta karɓa tana yi mai godiya, tashi tayi a sanyaye sannan tace
"Allah ya tsare hanya! A gaishar da mutanen gidan.."
"Ameen." Yace yana Binta da kallo, Saida yaga ta shige gidan sannan yawa direban sa magana suka wuce......

Ma'u kuwa tana shiga cikin gidan wajen inna tayi, tana miƙa mata ledar da Suraj ya bata, karɓa inna tayi tana cewa
"Na miye wannan ɗin."
Buɗe wa Ma'u tayi, nan taga kayan lashe lashe ne da kuma na tanɗe tanɗe, sai kuma wayar da ya bata, bata karɓa ba. Ɗauka tayi tana jujjuya wayar cike da mamaki ganin wata ƴar takarda a jikin wayar, yasa da sauri ta buɗe, ƙaramin note ne kamar haka

*"Pls Husnah ki ɗauki wayar nan! Zan kira ki anjima, in na koma gida.."*

Ɗaukar wayar tayi tana murmushi, taji daɗin kiranta da Husnah da yayi, sai hakan ya tina mata da yayanta yusif, dan shi kaɗai ke ce mata Husnah...

★★★

Da misalin wajen ƙarfe tara na dare, Ma'u taji wayar da Suraj ya bata tana ringing, saida kiran ya katse sau wajen uku sannan Ma'u ta ɗaga kiran, cikin zazzaƙar muryarta tace

"Assalamu alaikum."

"Wa'alaikis salam! Ranki ya daɗe fatan dai kina cikin ƙoshin lafiya.."

Jin satin muryarsa da ma'u tayi yasa ta gane shine, da sauri tace

"Lafiya kalau! Ya kaje gida lafiya.."

"Alhamdulillah! Sun ce ma suna gaishar dake.."

Dariya Ma'u tayi mai sauti sannan tace
"Ina amsawa.."

Nan Suraj yaja ta da hirar soyayya, ita dai Ma'u saide kawai ta bishi eh ko ah ah, bai kawo komai ba tunda yasan harda rashin sabo da take da shi akan al'amarin...
Cikin farin ciki da jin daɗi suka gama wayar, dan ita kanta Ma'u baza ta iya cewa bata sonshi ba, haka kuma bazata iya cewa ba ta fara sonshi, ita dai kawai yana burgeta ne ga rayuwar sa yana tafi da ita yadda Yakamata, ko kaɗan baya da girman kai, ko jin shi ɗin wani ne, ita dai rayuwar sa ta mata.....

Tana cikin wannan tunanin ne, taji wayar tayi ƙara alamar shigowar saƙo, tana dubawa taga an rubuta
*"Matata insha Allah!*
*Ina so ki tashi kije kiyi al'wala, kizo kiyi sallah koda raka'a biyu ne, sannan kiyi mana addu'a sosai, INA SONKI..*

Murmushi Ma'u tayi tana maimata saƙon, kallon su inna tayi, nan taga inna har ta fara bacci ita kuma zahrah tana chart da wayar ta, dama yanzu tunda inna ta san lalurar Ma'u, suke kwana tare a ɗaki ɗaya, duk dan ta gujewa mu'amala da Haidar.....

Saukowa daga kan gadon inna Ma'u tayi a hankali, fita tayi tsakar gida dan ta ɗoro al'wala, har ta tsuguna da niyar al'walar sai taji tana jin fitsari, da sauri ta shige toilet ba tare da tayi addu'a ba, tana tsugunnawa taji motsi a bayanta, da sauri ta juya cikin tsoro, ganin wajen tayi wayam alamun ba kowa, da hanzari tayi tsarki tana shirin barin bayin, dan Allah Allah take tabar gurin, gaba ki ɗaya ta tsorata da yanayin, ji tayi anyi sama da ita, kama akan iska haka take jinta, lokaci ɗaya ta fita a hayacinta Bama tasan inda kanta yake ba, Saida ta ɗauki tsawon lokaci, sannan ta dawo hayacinta, samun kanta tayi akan wani ƙayataccen gado yayin da haidar yake zaune a gefe ya juya mata baya, yana kallon tarin hannunsa....

Cikin tsiwa da rashin kunya Ma'u tace

"Meye na kawo ni nan! Ni ka mai dani inda ka ɗauko ni..."
Ganin ya mata shiru kamar ba da shi take magana, hakan sai ya ƙara ƙule Ma'u, cikin fushi Ma'u tasa hannu da niyar fisgoshi, ko gezau bai yiba asali ma yana nan a yadda yake kamar ba wanda ya taɓa shi, sai ita da tazo fisgoshi sai taji kamar ita aka fisgah, ta sowa tayi ta zagayo ta gaban shi, kallon shi take tana jin zuciyar ta kamar zata fashe da tsoron shi, ita wallahi ko can dama da tasan haidar al'jani ne, bata ji tsoron shi ba kamar yadda take ji a halin yanzu, bin hannun nasa tayi da kallo, ganin ya ƙura mai ido ko ƙiftawa ba yayi, yasa ta leƙa kanta abinda ta ganine yasa ta zaro idonta.........✍️













*MORE COMMENT*
*TYPING*
*PLS SHARE*
















~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/18, 9:51 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


__________________________________________________




*45 & 46*







_____________Ba komai ta gani ba illah, Suraj zaune kan dadduma sai ƙur'ani mai girma da ke gaban shi da dukan alamun dai karantawa yake...
Da sauri Ma'u ta buɗi baki da niyar yin magana, amma sai Haidar yasa yatsan sa a leɓenta yace

"Shishhht!! Kar inji bakin ki yanzu, a gaba in dawo ta kanki.."
Allah sarki Ma'u sai ta koma gefe ta zauna, yayin da ta rafka uban tagumi wani tsoron Haidar take ji, yana shiga lugu da saƙo na zuciyar ta, cigaba yayi da kallon Suraj ta tafin hannunsa..

Saida ya ɗauki tsawon lokaci sannan ya ɗago, kallon Ma'u yayi fuskarsa ɗauke da murmushi yace

"Masoyiyata taho gareni.."
Shiru Ma'u tayi tana binsa kawai da ido a zuciyar ta kuwa, sunan Allah kawai take ambato dan shine kaɗai zai kawo mata ɗauki, game da azzalumi HAIDAR..
Tsinkayar muryar sa tayi yana cewa "baki ta so ba fa.."
A hankali Ma'u ta so har ta ƙara so gaban shi, tsugunnawa tayi a gaban shi cikin kuka Ma'u tace

"Haidar! Dan girman Allah karka cutar da sur...."

"Shishsht! Bana ce Miki ba kar inji bakin ki anan ba, kiyimin shiru.."
Ido kawai ta zura mai tunda ya hanata tayi magana da bakinta...

Janyo ta jikinsa yayi ya rungume ta tsam, kamar za'a ƙwace masa ita sai faman jera ajjiyar zuciya yake kamar wanda yayi tseren gudu, magana ya fara cike da rauni yace

"Wallahi Ma'u! Badan sonki da ƙaunar da nake Miki ba, wallahi banga dalilin da zai hana na miki hukuncin abinda kika min a yau ba, meye shi wannan bil'adama yake da shi wanda ni bani dashi, ki duba fa na fishi kyau nafishi sonki ke na fishi komai, meyasa lokaci ɗaya zaki sauya ra'ayi,? meyasa..?"

Ya ƙare maganar yana ƙura mata ido..
Shiru Ma'u tayi haɗe da sunkuyar da kanta, a zuciyar ta kuwa nemon temakon Allah take ta kowanne yanayi...
Cigaba Haidar yayi da cewa
"Ko kin manta alƙawarin ki a gareni, na zaki kasance tare dani a kodayaushe..?"
Nan ma shiru Ma'u tayi me, sai kuma can ta saki kuka tana cewa
"Ni ka maidani gidan mu bansan ganinka, na daina sonka ɗin, kawai ka maidani inda ka ɗauko ni.."
Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka....
Sakinta haidar yayi, yayin da idanunsa suka rine baƙiƙƙirin, dan ɓacin ran da yake ciki, komawa gefe yayi ya zauna yana kallon Ma'u da take kuka, kamar ance mata uwarta ta mutu....
Jin kukan nata yake har cikin ƙoƙon zuciyar sa, saidai bazai iya hanata yiba, saboda ko da wasa baijin zai iya rabuwa da ita ba....

Ta ɗau tsawon lokaci tana kukan har Saida ta gaji dan kanta, sannan ta taso..
zuwa tayi gaban Haidar ta durƙusa, kama ƙafafuwan sa tayi tana cewa
"Ina mai haɗaka da Allah da Annabi Haidar ka fita daga rayuwata ko na samu salamah, kabarni in auri jinsi nah, nayi rayuwa ta kamar yadda kowa yake yi, Haidar pls kaji tausayina....."
Ta faɗa tana haɗa hannayen ta......
Kauda kansa Haidar yayi yace
"Bazan iya ba! Saboda ina sonki, in na rabu dake ni kuma sai inyi yaya da rayuwata..."
"To kabarni in auri jinsi na! Kodan farin cikin iyaye na.."

"Shima bazan iya ba! Saboda ina matuƙar kishin ki, kuma ma naga ai yanzun ma kina da aure, tunda kina dani, ko akwai wani abu da na tauye miki a rayuwar mu ta aure ne..?"

Ihun baƙin ciki Ma'u ta kurma, da kuma na rashin sanin madafa......

★★★
Ɓangaren su inna kuwa da inna ta tashi da asuba, ganin bata ga ma'u ba hakan yasa tayi tunanin ko tana bayi, jiranta tayi akan in ta fito itama sai ta shiga ta kama ruwa, shiru shiru Ma'u bata fito ba, hakan yasa inna fitowa tazo wajen bayin tana kiran Ma'un....
Jin shiru bata amsa ba, yasa inna ta fara sababin ta
"Waike Ma'u uwar mai kike yi a bayin da har baza ki fito ba, na hanaki daɗewa a bayi, amma kinƙi ji ko Allah yasa na shigo na sameki anan ciki wallahi sai ranki ya ɓaci..."
Jin shirun yayi yawa gashi kuma bata jin motsin kowa, sai ta tura ƙofar bata ga komai ba, saima butar da ma'u ta shiga da ita jiya da dare, bata kawo komai ba, tayi abinda zata yi ta fito tayi al'walar ta, ta shige ɗauki abinta....
Saida inna ta idar da sallar tukunan ta tashi, zahrah tana ce mata
"Maza tashi kizo kiyi sallah, daga nan ki tashi Ma'u ina ga ɗakin can ta koma ta kwanta, tashi zahrah tayi ta fita, Saida ta kammala al'walarta, sannan ta tunkaro ɗakin ƙwanƙwasawa tayi tana kiran sunan Ma'u, shiru bata amsa ba, hakan yasa zahrah tura ɗakin, wayam babu Ma'u cikin tashin hankali zahrah ta ƙwalawa inna kira....
Da hanzari inna ta fito tana cewa
"Lafiyar ki kuwa zahrah da sanyin asuban nan, zaki riƙa wa mutane ihu.."

"Wallahi innarmu adda Ma'u bata cikin ɗakin nan.."

"Kamar ya bata ciki! Inba ta ciki ina zata shiga to..?"

Saida suka leƙa ko wani lungu da saƙo dake cikin gidan, amma basu ga ma'u ba, cikin tashin hankali inna tasa zahrah ta kira kawu Salisu, shima da yazo ya shiga cikin tashin hankali, ace babban mutum a neme shi an rasa to ina Ma'u kuma tayi......
Sosai hankalin su ya tashi, dan sun rasa ta ina ma zasu fara neman ta...

★★★
Suraj kuwa tun da asuba da ya tashi ya kira wayar hannun Ma'u, jin ba'a ɗaga ba yasa yayi tinanin ko bata tashi ba, ko kuma bata kusa da wayar ne....

Duka iyalen gidan Daddy zaune suke suna breakfast, bayan sun kammala ne Daddy ya kira Suraj yana tambayar sa yadda suka yi da ma'un, nan Suraj ya labarta mai komai ciki kuwa harda lalurar da aka ce Ma'u tana da ita, kawai abinda ya ɓoye mai shine bai bashi labarin cewa AL'JANIN Ma'u yana kashe mata samari in sun nace sai sun aureta, kuma ko su su inna ya riƙe su akan subar wannan abun a matsayin sirri, bai so su ƙara gayawa kowa...
Nan Daddy yace

"Gaskiya wannan yarinya tana da babbar lalura, Allah Ubangiji ya zaɓa mana abinda yafi alkairi, amma Salisu bai taɓa gayamin ba wallahi.."

Suraj yace "ai da yake suma kwanan nan suka fahimci tana da NAMIJIN DAREN, amma yanzu sun fara nema mata magani..."

Daddy yace "to Allah ya kawo mafita insha Allahu, anjima zan kira shi salisun mu tattauna akan maganar auren.........✍️








[6/17, 7:27 PM] Matar Khamis,: Haidar Wallahi duk nacinka Sai ka rabu da Ma'u.haka kawai ka hanata Aure,Ina ake aure tsakanin mutum da Aljan indai ba Mugunta ba,to wannan Karon dolenka ka hakura.muna gdy sosai Allah ya Kara basira yasa kifi haka.much love for you Sis.🥰🥰👍


[6/17, 7:29 PM] Matar Khamis,: [6/17, 11:17 AM] Marichou: Kai Masha Allah Allah ya kara basira
Ko meye Ma'u ta gano😳😳😳😳


[6/17, 11:41 AM] +234 906 547 6395: Nashiga fargabar abinda ma'u tagani


[6/17, 11:41 AM] +234 906 547 6395: Allah y kara basira d alama haidar bacin ransa na rashin nasara ne


[6/17, 11:48 AM] +234 816 328 3548: Masha Allah matar khamis Allah yakara basira dakarfin ido dazakin hanu munagodiya Allah yabarki da khamis har aljanna🤣🤣🤣🤣💃💃💃


[6/17, 12:16 PM] Ummu Khalid: Da alama soyayyar Suraj tayi nasara haidar kowa ya hango faduwa! Hmmm kishi da mutum ya Kare balle halittar da baka gani! Ga Dan Adam da shagala! Kishi tsakanin Suraj da Haidar! Bafa sai na fada muku duk Kan ahli biyu suna farinciki ba 😁domin Suraj mutum nai da matar sa ta mutu Yan gidan su suna ta so suga yayi aurai😄ma u ta Jima Bata shiga daga ciki ba😄 Ga haidar Aljanin soyayya!!! Haidar zaka Bari muji yadda yadda a Yi kayataccen biki 💃💃💃😁 ko aa? Da alama fa Suraj dan soyayya nai😍 shin Mai haidar yake so ya nunawa mau? Mrs khamis muje zuwa Allah ya kara fasaha👍🏾


[6/17, 1:25 PM] Fateemah Adam: Muna gdy Allah yakara basira kifi yadda kike yanzu yabiya maki bukatunki na alkhairi damu baki daya
[6/17, 2:21 PM] +234 916 233 5086: Toh me taga ni ?
Munje zuwa...muna godia Mrs khamis


[6/17, 7:30 PM] Matar
Khamis,: [6/17, 12:03 PM] Ummu Abno: Allah ya qwaci Suraj yau a hnnun haidar ita kanta ma'u tashiga taskun shi Allah y qwacesu 🤲🏻



[6/17, 2:10 PM] Maman Khairat: Allah yakara basira da zakin hannu to ma'u kema Allah ya qwace ki


[6/17, 5:48 PM] +234 806 548 4348: Tab🤔narasa me dance dan tsoro



[6/17, 6:30 PM] +234 913 122 9563: Dakyau soRaj ka iyaya soyayya tunda gashi ma'u tafara manta haidar matar khamis Allah y Kara zakinhannu tareda basira






_comment ɗin ku fa yana ƙara fasamin kai, ku taimake ni kar kan ya dagargaje😹_



_yan facebook groups Ni daku akwai amana cau cau💪💃_




_Ƴan group dina na Whatsapp ina yinku over kunfi kowa búrgeni yacin🥰💃😹_

*ALLAH DAI YA BARMU TARE*







*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*









~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/20, 4:18 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________










*47 & 48*






______________Suraj ya kira wayar hannun Ma'u sau ba adadi, amma shiru ba'a ɗaga ba hakan ya matuƙar ɗaga mai hankali, kawai sai ya yanke shawarar kiran kawu Salisu dan yaji ko lafiya, shima Saida ya kira shi sau wajen uku sannan ya ɗaga.....
Bayan sun gaisa ne kawu Salisu yake sanar da shi abinda ke faruwa, cikin kiɗimewa Suraj yace

"Yaushe kuma aka sace tan! Ko jiya da dare fa munyi waya da ita...."

Kawu Salisu yace

"Wallahi kuwa dai!
Saida safe muka nemeta muka rasa, amma muna tunanin ko ƴan kidnaping ne suka ɗauketa ..."
Cikin damuwa Suraj yace
"Tabbas haka zata iya faruwa, kasan yanzu yadda ƙasar tamu take, Allah dai ya kawo mana ɗauki..."

"Ameen ya Allah! Insha Allahu muna nan, muna tayin addu'a da yardar Allah Ma'u zata bayyana.."
Kawu Salisu ya faɗi haka cikin rauni, a sanyaye Suraj ya ajje wayar zuciyar sa cike da damuwa, a iya jiya ne kawai ya keɓe da ma'u, amma ba ƙaramin jinta yake a zuciyarsa ba, ta riga da ta zama shi ya zama ita, sosai ya damu da ita da al'amarin ta, hakanan yaji Allah ya sa mai tausayinta da kuma tsantsar ƙaunar ta acikin zuciyar sa...
Dogon numfashi yaja yana jin ransa yana ƙuna, ayyana abubuwa da yawa yake a ransa, ganin hakan bazai fushshe shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login