Showing 33001 words to 36000 words out of 41435 words
Chapter 12 - NAMIJIN DARE Hausa Novels Complete.txt
 jajantawa juna akan ɓatan Ma'u, Suraj kuwa yanzu da yasan komai, shiru yayi yana nazarin yadda zai sanar da kawu salisu, abinda ya faru dashi tsakanin sa da Haidar, ga kuma Daddy yana gurin, cigaba yake da saƙa da warwara, sallama akayi da kawu Salisusai ya fita yaga waye, fitar sa ke da wuya Suraj shima ya tashi yana cewa Daddy.
"Bari na amsa waya! Naga kamar ɗakin ba network.."
  "Ok." Kawai Daddy yace
Fita Suraj yayi! Nan suka ci karo da kawu Salisu yana ƙoƙarin dawowa, da sauri Suraj yace
"Am...! Kawu ina da magana.."
 Amsawa to kawu yayi, Sannan suka raɓe gefe yana sauraren abinda Suraj ɗin yake gaya mai, sosai kawu Salisu ya firgita da jin abinda Suraj ɗin yace , cikin ɗimuwa kawu Salisu yace
"Gaskiya Suraj wannan ba abu bane, wanda za'a ɓoye ma iyayen ka ba, idan wani abu ya same ka baza yafewa kaina ba, dan kaima Tamkar ɗa kake a wajena..."
Kawu Salisu ya faɗa yana jan Suraj cikin gidan..
Ta ɓangaren Suraj kuwa tsoro yake kar iyayen sa,  su tsorata da lamarin Haidar, su hana ya auri Ma'u, shi kuma abinda bazai iya ba kenan, dan ji yake kamar idan bai aureta ba mutuwa zai yi...
Suna shiga ɗakin kawu salisu ya zayyanewa, Daddy dukan abinda ke faruwa harda wanda aka ɓoye mai, sannan ya ɗora da cewa abinda yasa ba'a faɗa maku ba, Suraj ne ya nemi alfarma akan abar wannan abun a matsayin sirri, kar a sanar daku...
Kallon Suraj Daddy yayi sosai sannan yace 
"Anya Suraj kasan wace alaqa ke tsakani na da mutanen nan kuwa, da har kake ganin akwai wata lalura da zata sa in guje su, Nima Asma'u ƴata ce! Kuma duk inda magani yake, dani za'a nemo mata.."
Sunkuyar da kai Suraj yayi yana cewa 
"Daddy kayi haƙuri insha Allahu bazan sake ba.."
Gyaɗa kai kawai Daddy yayi yana maida kallonsa ga kawu Salisu yace.
"Yanzu shi wanda ka karɓo mata magani kwanaki a ina yake..?"
Kawu Salisu yace
 "Nan wani ƙauye ne ba nisa..!"
Daddy yace
"Ai kawai tashi zaka yi muje wurin malamin.."
 Kawu Salisu yace
"Tun Yanzu kuma..?" 
"Ƙware kuwa! Kasan da zafi zafi ake kunna wuta.."
Daddy ya faɗa yana miƙewa tsaye...
Mota suka shige dukan su, Suraj shi da direba a gaba, sai kuma Daddy da kawu Salisu a baya, tafiya suke suna cigaba da tattaunawa akan wannan matsalar, da Haka har suka iso gidan mai maganin....
Bayan an musu isone suka shiga daga ciki, samun mai maganin suka yi kwance bayada lafiya, dan ko tashi baya iya yi, Saida wani yaronsa ya ɗago shi daƙyar, Yana ganin kawu Salisu ya saki murmushi yace
"Bawan Allah kaine ka dawo! Gaskiya naji daɗin zuwanka, kullum addu'a ta kan Allah ya karɓi raina ka dawo, dan in sanar ma da wani abu.."
Cike da ruɗewa kawu Salisu yake kallon mai maganin, yayin da ya kasa furta komai..
Daddy ne yayi ƙarfin halin cewa
"Malam fatan dai lafiya! Kaike neman shi gaggawa haka..?"
Cikin Muryar wanda yake jin tsananin ciwo malam ya cigaba da cewa
"Lafiya ba lafiya ba! Wato kam bayan zuwan ka da kwana uku, misalin ƙarfe sha biyu na dare, sai ga wannan AL'JANIN da ya auri yarka ya zo min, a tunani na aikina ne ya fara cin nasara akan sa, shine yazo ya bani haƙuri bisa abinda ya aikata, ashe abin ba haka bane yazo dan ya min kashedi akan inbar yin aiki akan saina raba shi da ƴarka, idan ba haka ba kuma zai illatani..."
Numfashi yaja sannan ya cigaba da cewa
 ''Nan muka fara jayayya dashi, har ina tilasta masa sai ya rabu da ita, bai cemin komai ba sai murmushi da ya saki, sannan ya fesamin wani abu a jikina, yana cewa wannan hukuncin da nama, nayi maka ne saboda maganin da ka bada ake bawa matata, yana barazanar zubar da cikina da ke jikinta, kuma wallahi idan cikin nan ya zube saina kashe ka..."
Sai da ya kuma jan doguwar ajjiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa
"To kunji abinda ya faru tsakani na dashi, kuma tun daga wannan Lokacin nake kwance bani da lafiya, shima bai ƙara dawowa gare ni ba...."
Dukkanin su tsuru tsuru suka yi suna kallon  malam ɗin, fuskar su shanye da mamaki, cikin sanyin murya kawu Salisu ya kwashe dukan abinda ya faru ya gayawa malam ɗin har da ɓatan Ma'u da kuma zuwa da Haidar yayi gurin Suraj ya mai barazana...
Girgiza kai kawai malam yayi yana murmushi yace
"Tabbas wannan anyi shaiɗanin al'jani, wato kam da yaga rashin nasara a tattare da shi sai ya ɗauke yarinya, amma insha Allahu sai anci nasara akan sa, yanzu taimakon da zanyi muku, zan haɗa ku da wani ɗan uwana cikakken mafaraucine yakan iya ganawa da ko wani irin al'jani, kuma duk hatsabibancin al'jani yana iyawa Dashi..."
  Kiran wani yaro yayi yana ce mai,  
"malam muddasir kuwa yana gida..?"
 Shiru yaron yayi can kuma sai yace
 "eh ɗazu kamar naga ya dawo daga farauta..."
"Yauwa!! Yi sauri ka raka bayin Allah nan wajen sa, kace mai ni na turo su gurin sa.."
Tashi suka yi suna mai godiya, Daddy kuwa rafar yan dubu dubu, guda biyu ya ajje mai yana cewa gashi kayi hidimar gida..."
Godiya sosai malam ya mai haɗe da nuna mai jin daɗin sa, fatan Samun nasara ya musu, sannan suka mai sallama.....
Basu daɗe suna tafiya ba, suka ƙaraso gidan malam muddasir ɗin, kasancewa babu wani nisa sosai tsakanin gidan sa da gidan wancan malamin...
   Yaron da ya rako sune ya shiga gidan, can kuma sai ya fito yana cewa "yace ku shigo.."
Shiga sukayi bakin su ɗauke da sallama, wani dattijo ne da yake sanye Da Kayan farauta, ya amsa musu sallamar tasu, Izini ya musu da su shigo daga cikin ɗakin, bayan su zauna ne yake tambayar su mai ke tafe da su, dukkanin su mamakine kwance a fuskar su don basu yi tunanin shine mai maganin ba, dan Ko kaɗan baiyi kama da mai farauta, bare ace yana magana da aljanu ba, komai nasa a natse yake yinsa.....
Kawu Salisu ne yamai bayanin dukan abinda yake tafe da su, cike da mamaki malam muddasir yace
"A gaskiya tunda nake ban taɓa haɗuwa da matsala irin wannan ba, amma da yardar Allah bazata gagareni ba...."
 Kallon Suraj yayi yace "kaine wanda kake son yarinyar ko..?"
 "Eh ." Suraj yace
Ɗauko wani abu yayi a cikin kwalba ya miƙawa Suraj yana cewa "karɓi wannan maganin ka shafa a jikin ka, insha Allahu babu abinda zai iya maka saidai ya ganka ya barka, yadda ka dogara da Allah, da kuma zikirorin da kake a kodayaushe, bazai taɓa tashi a Banza, insha Allah ita ma yarinyar yanzu za'a san yadda za'a kawo min ita nan...........✍️
_Wayyo mura nake😤🤧 sosai, jiya naso inyi muku post, saidai hakan bai yiwu ba, amma insha Allahu zaku jini zuwa yamma_
*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*
~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/23, 7:46 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄
*NAMIJIN DARE*
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
__________________________________________________
*53   &.   54*
______________Rufe idanuwan sa yayi yana karanta wasu  ɗalasimai, da in yana son ganawa da aljanu yake karanta su, ya ɗau tsawon lokaci yana wannan abun, daga bisani kuma ya buɗe idon sa yana kallon su yace  
"A gaskiya samun nasara akan Haidar, abu ne mai wuya saidai mubi hanyar ta cin amana da kuma yaudara..."
Kawu Salisu yace 
"Kamar ya kenan.?"
Malam muddasir yace 
"Dole in Muna so a ɗauko Ma'u daga inda Haidar ya ɓoye ta, to sai mun nemi taimakon abokin sa i'liyas, dan ina da tabbacin shi kaɗai ne yasan inda Haidar yake..."
Daddy yace  "indai hakan ba zai yiwu kawai ina ga ayi..."
Kirari malam muddasir ya fara yi, wanda zai isa ga iliyas da sauri kuma aduk inda yake zai san ana buƙatar taimakon sa...
               ★★★
I'liyas kuwa dake zaune a cikin tsanin farin Dutse, tun laifin da ya aikatawa Haidar, har yanzu ya kasa fita daga cikin gurin, dan yana da tabbacin Haidar bazai taɓa ƙyalesa ba, abisa cin amanar da ya mai, wannan dalilin yasa ya ƙi fita daga wajen dan gujewa cutarwar haidar a gare shi....
Ji yayi ana kiran sa da gaggawa, alamar ana buƙatar taimakon sa, tashi yayi daga inda yake, wajen wani tsohon aljani dake zaune yana karatun Alqur'ani mai girma yazo, durƙusawa yayi yana miƙa mai gaisuwa cike da girmamawa, amsawa al'janin yayi fuskarsa cike da kamala yace.
"Yadai i'liyas!! Lafiya naga kamar kana cikin damuwa.."
  Cikin girmamawa i'liyas yace
"Wallahi yallaɓe!! A wani wajen ne, na duniyar bil'adama ake da buƙatar taimako na, kuma gashi ba zan iya fita ba dan taimaka musu..."
"To me yasa baza ka iya fita ba..?"
Duƙar da kai iliyas yayi sannan yace
 "Allah ya gafarceka!. A gaskiya ba wai nazo nan bane dan ɗaukar darasi ko wani abun, illah nazo ne dan na gujewa Haidar daga laifin da na aikata masa, nan i'liyas ya kwashe dukan abinda ya faru ya faɗa wa wannan tsohon, girgiza kai kawai tsohon nan yake har I'liyas ya dasa aya a maganar sa, cikin fushi wannan tsohon aljanin yace
"Lalle Haidar ya tafka babban kuskure, sa'ar sa ɗaya da bansan wannan lamari tun fari ba, kuma Wallahi sai ya fuskanci hukunci na, yanzu zan je a madadinka dan in taimaki waɗanda suke neman ka......
       
            Ɓangaren malam muddasir kuwa, sai faman kiran iliyas yake amma shiru bai bayyana ba, dakatawa yayi da kiranyen da yake mai yana mamakin meyasa bai zo ba, zai ƙara yi kenan yaji wata guguwa tana doso inda suke, lokaci guda ɗakin ya rune da duhu ba'a ganin komai, cikin ƴan sakanni komai ya lafa, saiga wannan tsohon aljanin ya bayyana a dakin, tsorone ya kamasu gabaki ɗaya, dan hatta shi kanshi Malam muddasir saida ya tsorata da ganin wannan tsohon aljanin, cikin san kwantar musu da hankali yace
"Sunana Shaikh ibn muzzafar! Kuma nine Sarkin malamain aljanu na musulmi,  Nazo ne dan na taimaka muku, abisa neman taimako da kukayi a wajen I'liyas, saidai shi yana cikin wani uzuri ne da bazai iya zuwa ba, amma gani nazo a madadin sa.."
cike da girmamawa malam muddasir ya farawa ibn muzzafar kirari, dakatar da shi yayi yana cewa 
"Bana buƙatar wannan abun, kawai ka faɗi wani kalar taimako kuke da buƙata a gareni, yanzu inyi muku shi.."
Nan malam muddasir ya kora masa dukkan abinda yake wakana.....
Cike da mamakin abinda suka faɗa mai, dan yayi daidai da abinda I'liyas ya sheda masa, da sauri yace
 "Insha Allahu yanzu zan kawo ƙarshen wannan lamarin.."
Ya faɗa yana ƙesta Yatsun sa, kafin ƙiftawa da bissimillah, sai ga wasu samudawan aljanu su uku sun bayyana, hannun ɗaya ɗauke da wata kujerar zinare, ajje ta yayi kusa da ibn muzzafar dan ya zauna, zama yayi yana kallon wannan samudawan aljanu, cikin bada umarni ya kalli guda biyun yana ce musu 
"Kuje duk inda Haidar yake ku kawo min shi nan..."
Cikin girmamawa suka ce "angama ya Shaikh..."
Suna faɗin haka suka ɓace ɓat..
Kallon ɗayan yayi shima yace mai
"Kaje gidan Haidar! dake ƙasan ruwa yarinyar da ka gani a cikin gidan ka ɗauko mini ita.."
Duƙar da kai yayi yana cewa "an gama ya Shaikh.."
Ya faɗi haka shima yana ɓacewa...
 Sudai su kawu Salisu zubawa sarautar Allah suka yi ido, dan wannan lamarin yafi ƙarfin su, hatta shi kanshi Malam muddasir shiru yayi yàna mamakin abun kamar a Film, ga shi dai cikin sauƙin shugaban malamain aljanu zai magance wannan matsalar koya zata kaya..............✍️
_zanso inga ko Haidar zai rabu da ma'u,🤔🤔_
*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*
~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/24, 10:19 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄
*NAMIJIN DARE*
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
__________________________________________________
*55     &     56*
______________Ma'u kuwa dake zaune tunani ne fal a ranta, musamman yanzu yadda Haidar ya killace ta a guri ɗaya, babu motsin wanda take ji bare taji sanyi a ranta, kullum sai ya mata alƙawarin maidata gida amma sai ya saɓa mata alƙawarin da ya mata, a fili ta furta "Haidar yaushe ne zaka maidani cikin ƴan uwana.."
Ta ƙare maganar tana sakin kuka gwanin ban tausayi....
Tana cikin wannan tunanin ne taji anyi sama da ita cikin iska, kasa tantance a wani yanayi take, cikin firgici take Ambaton sunan Allah dan neman tsarinsa, daga dukan wani abun halitta, cikin ƙanƙanin lokaci taji an ajje ta akan doron kasa, ƙara tsorata tayi sosai hakan yasa ta rumtse idanuwan ta.....
       Su kuwa su kawu Salisu ganin an ajje Ma'u, hakan ba ƙaramin basu mamaki yayi ba, cikin zumuɗi da murna kawu Salisu yace
"Ma'u kece...!?"
Da sauri Ma'u ta buɗe idonta tana binsu da kallo, ganin kawu Salisu da kuma Daddy har ma da Suraj, sai kuma wasu da bata san ko su waye ba, cikin jin daɗin Ma'u ta ƙarasa kusa da kawu Salisu, hannunsa ta riƙo tana ƙara fashewa da kuka, cikin gunjin kuka Ma'u tace
"Wallahi kawu haidar azzalumi ne shi ya hanani in kula kowa, kuma ya hana kowa ya raɓe ni....."
Lallashinta kawu Salisu ya fara yi, amma kamar ba da ita yake yiba..
Kallon Suraj Ma'u tayi, cike da fitar hayyaci ta faɗa jikinsa, tana cewa 
"Yace  kaima sai ya kashe ka! Kuma wallahi idan ya kashe ka Nima mutuwa zanyi, dan wallahi ina sonka..."
 
    Allah sarki Suraj! Da yaga kamar bata cikin hayacinta, sai ya rungumo ta jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta, a hankali ta fara yin shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa akai akai.......
 Haidar ne tare da waɗanda Shaikh ibn muzzafar ya aika su kawo shi suka bayyana a gurin, idon haidar bai sauka akan kowa ba, sai kan Ma'u da take rungume jikin suraj, cikin fushi da tsananin kishi haidar ya tunkare su, hannu yasa da niyar ya funciki Ma'u daga jikin suraj, bai kai ga ƙara sa hannun nasa ba yaji andaka masa tsawa da sauri ya juya, ganin ibn muzzafar ne yasa ya duƙar da kansa alamar girmamawa, amma duk da haka zuciyar sa da tunanin sa, yana gurin Ma'u dake jikin suraj, magana ibn muzzafar yake mai amma ko kaɗan baya jin sa, asali ma idonsa ya rufe ba abinda yake gani sai ma'un sa dake jikin wanin sa wanda bashi ba.......
Yadda yake jin zuciyar sa tana suya, yasa ya kasa haƙuri, Ɗayan hannun Ma'u ya kama ya fisgota, Suraj kuwa da yake ankare da shi, sai shima ya riƙe hannun nata ɗaya,  idan Haidar ya jata, sai shima ya jata, aka rasa waye zai haƙura ya sake ta, Ma'u kuwa kuka kawai take tana so ta ƙwace daga riƙon da Haidar ya mata amma yaƙi sakinta.....
Ibn muzzafar kuwa dake zaune yana kallon yadda  Haidar yake ja inja da bil'adama, sai abin ya matuƙar bashi mamaki, lalle Haidar ya daɗe da makancewa a soyayyar bil'adama, wata tsawa ya sake daka mai a karo na biyu, da sauri Haidar ya sha jinin jikin sa amma bai saki hannun Ma'u ba, cike da isa ibn muzzafar yace
"Haidar!!!! Ina mai umartarka da ka sakin mata hannun ta..."
   Sakin hannun Ma'u haidar yayi yana aikawa da Suraj wani irin mugun kallo, mayar masa da martani Suraj yayi a ransa yana ayyana
 "ai ba tsoron ka nake ji ba.."
*Kai Suraj kodan kaga da ibn muzzafar ne a kusa🤔dan shi kanshi haidar ba kanwar lasa bane😹*
Gyaran murya ibn muzzafar yayi Yana kallon haidar daga bisani kuma yace 
"Nasan izuwa yanzu ka fahimci cewa, nasan komai kuma nazo ne dan na kawo ƙarshe al'amarin..
Haidar yaushe ka zama mai zalunci.? Yaushe ka zama mai tauye haƙƙin rai.? Shin ko ka manta cewa hakan da ka aikata ya saɓawa al'adar mu da addinin mu, kuma sai ka fuskanci hukunci na dai dai da abinda ka aikata, saboda haka ina mai umartarka a karo na biyu, da ka rabu da wannan bil'adamar tayi rayuwar ta cikin salama, kazo cikin jinsin ka nama alƙawarin duk wacce kace kana so, ko ƴar waye acikin duniyar aljanu zan nema maka auren ta..."
 Durƙusawa haidar yayi cike da rauni yace 
"Allah ya gafarceka! Na yarda da duk hukuncin da zaka min, amma dan Allah kar kace sai na rabu da ita, wallahi ina sonta fiye da rayuwa ta, bazan taɓa barinta ba koda da daƙiƙa ɗaya ne..."
Ibn muzzafar yace
"Ba wai na tambaye ka abinda ke cikin zuciyar ka bane, umarni ne na baka ba shawara ba, ina so ka furta da bakin ka cewa ka rabu da ita.."
 Cikin dagiya da taurin kai Haidar yace
"Allah ya gafarceka! Ban fara sonta ba dan in rabu da ita, na fara son tane dan in dauwama da sonta na har abada...."
Fusata ibn muzzafar yayi da yadda Haidar ya ke mai jayayya, cikin tsawa yace
"A karo na ƙarshe haidar Ina umartarka da ka rabu da ita..."
Miƙewa tsaye Haidar yayi ido cikin ido yake kallon ibn muzzafar yace
 "Gaskiya bazan rabu da ita ba, kawai ka cire kanka a wannan al'amarin,









