Showing 21001 words to 24000 words out of 41435 words
Chapter 8 - NAMIJIN DARE Hausa Novels Complete.txt
 ta baro baƙin ta, tana tinane-tinane a zuciyar ta....
Koda Ma'u ta fito samun Suraj tayi a zaune akan dan damalin ƙofar gidan na su, kasancewar kansa a sunkuye yake yana ɗan duba wani abu a wayar sa, bai ji matsin fitowar ta ba shiyasa ma bai ɗago ba, samun guri Ma'u tayi ta tsaya ƙiƙam kamar sojan da yake shirin fareti, kicin-kicin tayi da fuskarta kamar bata taɓa dariya ba, yayin da idonta yake kallon wani gurin daban....
Saida ta ɗauki wajen minti biyar sannan Suraj yaji jikinsa yana basa akwai wani a gurin, ɗagowa yayi a hankali daga kallon wayar da yake, tozali yayi da kyakkyawar fuskanta da take a cirɓine, a ransa ya ayyana cewa da ace zatayi murmushi da sai tafi haka kyau, kawar da tunanin yayi da sauri haɗe da ɗaga kafaɗarsa alamar ko a jikin sa, kallon ta yake tun daga sama har ƙasa haƙiƙa ta haɗu iya haɗuwa, dan bata da makusa ko kaɗan, ta ko ina tayi saide ace masha allah cigaba da kallon ta Suraj yayi baice da ita uffan ba, yana jiran kawai yaga iya gudun ruwan ta, na ƙin mai magana har wani lokaci zata kai a haka...
Gajiya da tayi a tsaye yasa ta ɗan jiyo kaɗan, da niyar taga mai ɗan rainin hankalin nan yake, da har yanzu bai ma san da tsayuwar ta ba, idanuwan su ne suka sarƙe da na juna, lokaci ɗaya Ma'u jikinta ya fara karkarwa, baya tayi luuu zata faɗi, wata sufah Suraj yayi ya riƙo hannun ta yana mamakin komai yasa zata faɗi, ganin da yayi kamar bata cikin hayacinta, sai ya ɗauki waya ya kira Daddynsa, sheda masa abinda ke faruwa yayi, cikin al'ajabi dukkanin su suka fito waje ganin halin da Ma'u take ciki sai abun ya basu mamaki...
Alhaji Ibrahim yace "Lafiya son me ya faru da ita ne?.." 
Suraj yace 
"Wallahi Daddy nima bansan meya faru ba kawai tana tsaye naga zata faɗi."
Kawu salisu yace "to kamota mu shiga daga ciki." 
Ɗaukar ta Suraj yayi cimak kamar wata ƴar baby suka shige gida...
Fifita kawai suke mata dan su a tinanin su suma tayi, nan ko basu san kaɗan daga cikin kaidin Haidar ne ba....
Haidar kuwa dake zaune a inda yake yana kallon su, dukkan abinda ke faruwa da saninsa, asalima shi ya bugar da Ma'u a cewar sa bazai lamunci yaga tana yiwa wanin sa magana ba....
 Babu abinda yafi komai ɓata masa rai da ɗugunzuma mai hankali, sai yadda yaga Suraj ya haɗa jiki da matarsa, ji yayi wata zazzafar tsanar Suraj tana shiga ta ko ina a jikin sa, kawai tinanin irin hukuncin da zai shiryawa Suraj yake, na taɓa mai masoyiyar sa da yayi, rumtse idanuwan sa yayi, yayin da zuciyar sa da jikinsa yake jin su kamar ana zuba masa ruwan zafi.....
Ɓangaren su inna kuwa! Babu abinda ba su yiwa Ma'u ba amma bata tashi  ba, hakan yasa momy tace wa inna 
"Ko asibiti zamu kaita ne! tunda kinga bata tashi ba.."
Kawu salisu yace "Ni gani nake kamar abun ba na asibiti ba ne.."
Nan dai kowa da abinda yake cewa, Daga ƙarshe dai suka yanke shawarar ayi mata rukiya, ruwa Suraj yasa aka ɗauko a kofi,  nan ya karanta ayatul kursiyu da ayoyin farko na suratul bakara, cikin ikon Allah ana shafawa Ma'u sai gashi taja ajiyar zuciya daga bisani bacci yayi awon gaba da ita, sauran ruwan tofin kuwa Suraj yace a ajje mata idan ta tashi sai a bata tasha......
Haka suka zauna har lokacin tafiyar su yayi Ma'u bata tashi ba, tafiya suka akan bayan kwana biyu Suraj ya dawo ya duba ta....
 tafiyar su kuwa ko minti biyu ba'a yi ba, sai gashi  Ma'u ta tashi daga baccin da take, cigaba tayi da al'amuran ta kamar komai bai faru ba, yayin da inna ta shiga cikin damuwa da kuma rashin sanin madafa........✍️
*More comment*
*More typing*
*Pls share*
~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/11, 12:26 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄
*NAMIJIN DARE*
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
____________________________________________________________
*36 &. 35*
____________Bayan isha'i kuwa inna ce zaune tare da iyalen gidan ta, Zahrah da Ma'u suke hira suke kaɗan kaɗan, ita dai inna saide ta bisu eh ko ah ah, kasancewar jin da take kanta yana matukar mata ciwo, kuma ba komai bane yasa mata ciwon kan, illah tinanin da ta sawa kanta......
Numfasawa inna tayi sannan ta kira sunan zahrah tace 
"Zahrah kiramin yayanku a waya ince mai in zai biyo ta nan, ya taho min da maganin ciwon kai."
Amsawa da "to" zahrah tayi sannan ta ɗauko wayarta dake ɗaki, yaya Auwal ta dannawa kira, bugu ɗaya ya ɗaga haɗe dayin sallama,  miƙawa inna wayar zahrah tayi tana cewa "gashi ya ɗaga.." karɓar wayar inna tayi tana karawa a kunnen ta.......
   Inna kuwa bayan ta gama wayar da yaya Auwal, miƙewa tayi tana ce musu "bari in shiga ciki na kwanta! Kafin yayan naku ya ƙara so."
 Ta faɗa tana shigewa ɗaki.....
kwanciya tayi tana maida numfashi a hankali, da haka har ɗan gyangyaɗi ya fara ɗaukar ta, bata daɗai da fara gyangyaɗin ba, taji kamar motsi a cikin ɗakin, idon ta rufe tace  "zahrah kema kwanciyar zakiyi tun yanzu.."
Jin shiru ba'a bata amsa ba yasa ta buɗe idonta, taga waye ya shigo cikin ɗakin, maimakon taga zahrah ko Ma'u sai taga akasin haka, dan wani mutum ta gani tsaye a saitin inda take kallo, yanayin halittun sa sun bata tsoro sosai, dan komai nasa ya linka da na bil'adama da ta saba gani ba yau da gobe, inna da take cikin yanayin tsoro da firgicin ganin sa, kawai dauriya take wajen riƙe ihun da take so tayi na akawo mata ɗauki...
   Kunnuwanta suka jiyo mata awon Muryar sa da tasa saura kaɗan ta saki fitsari, ji tayi yana cewa
"Ki kwantar da hankalin ki! Ni banzo dan na cutar dake ba, ko na tsoratar dake, asalima Ni nazo ne dan na tinatar dake, abinda kika kasa fahimta  tun da daɗewa..."
 Inna kawai kallon sa take yayin da tsoron ta yake daɗa ƙaruwa, cigaba yayi da cewa 
"Ni sunana I'liyas! Kuma Ni al'jani, shin kin taɓa tsayawa kiyi tinanin me ya hana ƴarki Asma'u aure har izuwa yanzu.."
  Girgiza kai inna tayi, yayin da kanta yake ƙara ɗaurewa...
"Nasan kun daɗe kuna tinanin lokacin auren nata ne baiyi ba ko! To abinda baku sani ba shine Akwai wani al'jani, wanda ya kasance daga cikin mu, sunan sa *HAIDAR* shine ya auri ƴar ki Asma'u, kuma ya hana ko wani namiji kusantar inda take, kuma duk wanda yayi gangacin haka yakan sashi cikin bala'i koma ya rasa rayuwar sa gaba ki ɗaya...."
Nan dai I'liyas ya kwashe komai tun daga lokacin da Haidar ya kashe Yusif, har izuwa gobarar da Alh Tanko yayi, sannan ya ƙare da cewa "Haidar yafi kowa dake cikin al'janu taurin kai da kafiya, idan yana son abu komai yakan iya aikatawa, abune mai wuya Haidar ya rabu da yarinya ki, Ni dai taimakon da zan iya muku shine kuyi kokarin raba yarinyar nan da wannan *AL'JANIN SOYAYYAR,* idan ba haka ba! ba zai taɓa bari wani namiji ya raɓi inda take ba..."
I'liyas yana ƙare maganar da yake, ya ɓace ɓat kamar bai wanzu a gurin ba.....
Inna da take cikin tashin hankali da kiɗimewa, sanƙarewa tayi guri guda ko cikakken motsi ta kasa ai watarwa, kawai zufa take keto mata yayin da ta rasa mai ma zata yi, tana cikin wannan halin Auwal ya shigo ya sameta......
Ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki abin ya matuƙar ɗaga mai hankali, gaba ki ɗaya jikinta karkarwa yake, tana so tayi wa Auwal magana amma bakinta yaƙi sarrafuwa, da gudu Auwal ya fita daga ɗakin dan kirawo mota, su kuwa su Ma'u ganin yaya Auwal ya fita hankali a tashe, yasa sukayi cikin ɗakin da inna take da gudu, suma halin da suka ganta ya matuƙar basu mamaki, duk da dama ance yanzu yanzu sai Allah....
Kwantar da ita sukayi akan gadon da take suna jera mata sannu, inna kai kawai take ɗaga musu, tana bin Ma'u da idonta, yayin da take jin tausayin Ma'u yana ratsa dukan jijiyoyin jikinta, suna haka ne yaya Auwal ya dawo, kamo inna sukayi suka miƙar da ita tsaye, fita da ita sukayi dan kaita  asibiti........
Ɓangaren I'liyas kuwa! bayan ya bar inna tafiya yayi, yana tinanin inda zai iya ɓoyewa azabtarwa da muguntar Haidar, dan yana da tabbacin cewa! Indai Haidar ya gano abinda ya aikata masa, Allah kaɗai ne zai iya karesa daga sharrin Haidar.....
Tunowa da wani malamin su dake cikin wani tsibirin dutse da yayi, yasa ya yanke shawarar zuwa can, dan nan gurin ne kaɗai! Haidar bazai iya zuwa ba dan ya cutar da shi...
Nufar gurin yayi a zuciyar sa, yana wa Ma'u da iyayen ta fatan samun nasara akan Haidar..........✍️
*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*
~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/12, 9:51 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄
*NAMIJIN DARE*
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
____________________________________________________________
*37 & 38*
_____________Ɓangaren su Suraj kuwa! Tunda suka tafi daga batsari babu tinanin da yake sai na Ma'u, haka kurum yaji Allah ya same matuƙar tausayin ta, bai san meyasa ba Amma sai yabar hakan a matsayin, ƙila dan tana da matsalar jinnu ne, har Allah Allah yake ya sake zuwa ko dan ya ganta, a da ya cirewa kansa son yin aure tunda matar sa ta mutu, amma yanzu yana jin lokacin da zai kawowa jiddah uwa yayi, dan yana kallon Ma'u zuciyar sa ta aminta da ita, a matsayin 
ta kasance uwar ƴaƴan sa na har abada.....
               
                 ★★★
Likitoci Saida suka duƙufa akan Inna, sannan ta dawo hayyacinta, sosai ina ta tsorata! dan abu biyu ne suka haɗan mata, ga ganin al'jani da tayi kuma ga lamarin da yazo mata da shi kunnuwanta sunyi rauni da sauraron abun, da zarar ta tuno abin sai hankalin ta ya matuƙar tashi, Saida likita ya mata allura sannan ta samu yin bacci.....
 Yaya Auwal kuwa ganin an kwantar da inna a asibiti, yasa yace 
"Zahara ke ki zauna a wajen innarmu da goggo ( matar kawu Salisu kenan), ke kuma Ma'u sai mu wuce gida da safe kyadawo.."
Ba haka taso ba! amma ba yadda zata iya, dole tabi yaya Auwal da kawu Salisu suka wuce gida...
     Ba yadda kawu Salisu da yaya Auwal basu yi da itaba akan taje gida kawun su kwana da yara, ko kuma su suzo su tayata kwana, amma taƙi  acewar ta zata iya kwana ita kaɗai a gidan, ƙyaleta suka yi ta shigewar ta, su kuma suka ƙara gaba abinsu......
Tana shiga tasa sakata a ƙofa,  jin gidan shiru babu motsin kowa, hakan baisa taji tsoron komai ba kai tsaye ɗakin ta nufa da niyar kwanciya, samun Haidar tayi zaune akan katifar ta, ya tanƙwashe ƙafafuwan sa, wani sihirtaccen murmushi yake aiko mata dashi, tare da buɗe hannuwansa alamun ta taho gare shi, da gudu Ma'u ta taho tayi kamar zata faɗa jikinsa, sai kuma ta juya masa baya, táshi yayi ya rungumota ta bayan, haɗe da ɗora kansa a kafaɗarta, cikin kunnenta yace 
"meye kuma ya faru!  Masoyiyata, ko baki yi farin ciki da ganina ba." 
Cikin sanyi murya Ma'u tace 
"ah ah innarmu ce bata da lafiya, hankali na ya matuƙar tashi wallahi, saboda innarmu itace komai namu.."
Juyo da ita Haidar yayi ta gabansa, ganin tana hawaye sai yasa hannu ya share mata shi, rungume ta yayi yana ɗan buga bayanta a hankali, sannan yace
"Ki kwantar da hankalin ki, inna zata samu lafiya insha Allah, kiyi shiru ki daina kuka kinji..."
Girgiza kai Ma'u tayi tana cewa "to" 
Shi kuwa zaunar da ita yayi akan cinyar sa yace 
"Ina so ki kasance cikin farin ciki a koda yaushe, dan kiyi farin ciki zan iya sadaukar da komai nawa a kanki, wallahi ina sonki kamar bugun numfashi, ina ji rayuwa ta baza ta iya tafiya daidai ba idan ba ke a cikin ta...."
Haka yai ta gaya wa Ma'u, kalamai masu tsayawa a rai da ratsa zuciyar mai sauraro, daga ƙarshe kuma ya ɗauketa suka tafi yawon shaƙatawa, bai dawo da ita ba sai gab da asuba, wani nan nauyar bacci yayi awon gaba da Ma'u, cike da mafarkin Haidar masoyin ta, sai ƙarfe takwas saura ta tashi, ganin yadda lokaci ya ƙure gashi ko sallar asuba bata yiba, da hanzari ta tashi tayi bayi tana sauri sauri ta gama abinda take, tana idar da salla ko tsayawa tayi addu'a bata yiba, ta tashi tayi waje tana buɗe ƙofa, tayi karo da yaya Auwal dake ƙoƙarin shigowa tare da anti mardiyya (matarsa kenan) gaishe su tayi tana karɓar kwadon abincin dake hannun anti mardiyyan, wucewa suka yi cikin gidan inda yaya Auwal yasa Ma'u ta ɗaukowa inna wasu kayan, da zata canja sannan suka wuce asibitin......
      Koda suka isa asibitin samun inna suka tana bacci, sai kuma zahrah da goggo dake zaune suna karyawa kasancewar kawu Salisu yazo har ya siyo musu abin kari ya tafi wajen aikin sa.....
Nan suka zauna aka suna gaishar da gaggo haɗe da tambayar ta ya mai jiki, amsawa tayi tana cewa "da sauƙi! Har ta tashi da asuba tayi Sallah, sai kuma ta koma baccin, Amma likita yace baccin da take shine sauƙin a barta tayi abinta.."
Yaya Auwal yace "to madallah bari naje naga likitan, daga nan zan wuce idan kuma ana buƙatar wani abu sai a kira Ni.."
Amsawa da "to." Suka yi gaba ɗayan su, sannan shi kuma ya fita dan zuwa ganin likitan.......
      Alhamdulillah jikin inna yayi sauƙi, kwanan ta biyu aka sallamai ta yayin da kawu Salisu da yaya Auwal suke ta hidima da ita, kasancewar likita yace a daina barinta cikin tinani da damuwa, shiyasa suke ƙoƙarin kulawa da ita yadda ya kamata......
Bayan kwana biyu inna ta kira kawu Salisu da manyan ƴaƴan ta maza yaya Auwal da yaya Sani, 
Nan ta zayyane musu dukan abinda i'liyas ya gaya mata, game da aljani da yake auren Ma'u, da kuma yadda yake korar mata samari, har idan sun mai gardama yake kashe su ta ƙare da cewa "gobarar ma da Alh Tanko yayi, ashe shi ya assasa komai.."
Dukkanin su shiru suka yi sun ma rasa ta inda zasu fara, kawu gumi ya share inda yayi ta maza yace "ba shakka! Lalle biri yayi kama da mutum, wallahi tunda nake ban taɓa jin labari mai kama da irin wannan ba, haƙiƙa al'janin nan ya zalunci Ma'u, da ace anyi wa Ma'u aure akan lokaci, da yanxu ina da tabbacin idan Allah ya bata tana da yara huɗu, tunda gashi yanzu sa'aninta da ƙawayenta daga me yara huɗu sai mai uku, amma yanzu da yardar Allah Ma'u sai ta rabu da wannan azalimin AL'JANIN SOYAYYAR..."
Kawu Salisu ya ƙare maganar cike da san kwantar musu da hankali......
               ★★★
Ɓangaren HAIDAR kuwa! Duk abinda I'liyas ya sanar da inna, da kuma shirin raba shi da Ma'u da suke, duka yana sane da faruwar hakan, asalima a jiya da i'liyas yazo gidan ya ga zuwan shi, dan ya sawa gidan tsaron da duk abinda ake zaiji kuma zai gani, a duk inda yake, kawai ya ƙyale I'liyas ne dan bai ɗauki hakan a wata matsala ba, kuma shidai abinda ya sani babu wanda ya isa ya raba shi da Ma'u koda kuwa waye a doron kasar nan........✍️
*_Niko nace akwai Allah Haidar saide in bamu haɗa ka da Allah ba_*😒🙄
*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*
~MATAR  KHAMIS CE 🥰💃~
[6/13, 10:59 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄
*NAMIJIN DARE*
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
____________________________________________________________
*39 & 40* 
______________Yau kawu Salisu tun asuba da ya tashi ya shirya, dan zuwa wani ƙauye da yaji ana labarin wani malami da yake bada maganin al'janu, tafiyar sa yayi ko inna bai gayawa zai je wani gurin ba, dan ya ɗauki aniyar nemawa Ma'u magani koda Kuwa nawa yake....
Wajen ƙarfe 12:00 daidai ya ƙarasa cikin ƙauyen, tambayar gidan da mai maganin yake yayi, nan ya samu wani yaro ya raka shi har inda mai maganin yake, mutane ya samu da yawa kuma dukkanninsu









