Showing 18001 words to 21000 words out of 41435 words

Chapter 7 - NAMIJIN DARE Hausa Novels Complete.txt

ba..."
Ɓacewa I'liyas yayi kamar yadda haidar ɗin yace, Saida yayi nisa daga inda haidar yake sannan ya bayyana a gurin, saƙa da warwara kawai yake can kuma sai yayi murmushi yace "Wallahi Haidar saina rabaka da bil'adamar da kake iƙirarin cewa matar kace.."

Shi kuwa Haidar ganin iliyas ya bar gurin, sai shima ya tashi da niyar barin gurin acewar sa iliyas ya ɓata mai rai bari yaje inda zaiji dama dama......


★★★
Ɓangaren su Ma'u kuwa zaune suke a tsakar gida, sun shimfiɗa tabarma suna ta hira abin su cikin kwanciyar hankali, kasancewar ƴan uwanta mata sunzo musu ziyara yau, sai hirar su suke gwanin birgewa, Ma'u dake tsakiyar su baza ka taɓa cewa itace yayarsu ba, zakayi tunanin duk sun girmeta...
Inna dake gefe tare da ƴan jikokinta, sai wasan su suke abinsu, ɗagowa inna tayi ta kalli Ma'u a ranta ta ayyana cewa Allah sarki kema da kinyi aure da kina nan da ƴaƴan ki, Allah ka dubi wannan baiwa taka ka fito mata da mijin aure nagari tayi auren ta....✍️










*More comment*
*More typing*
*Pls share*








~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/8, 7:45 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*30 & 31*



*KATSINA CIKIN GARI*

___________A wata ƙasaitacciyar anguwa da tafi kama da ta masu mulki, dukkanin gidajen dake jere a wannan anguwa gaba ɗaya su haɗaɗɗune, idan ka kalli wannan zaka yi tunanin wancan yafi wannan kyau da tsari, amma sai dai kana kallo zaka hango wanda ya fisu....
Wani gida da yafi jan hankali na shi naga an buɗe get ɗin gidan, yayin da motoci na alfarma ke shiga kamar an rako shugaban kasa filin jirgin sama...
Bayan motocin sunyi fakin a inda ya dace, ma'aikatan gidan suka taho da hanzarin su, har rige-rigen buɗe Bayan motar suke, wanda hakan ya nuna alamun suna farin ciki da zuwan sa, a hankali aka buɗe murfin motar, tare da zuro ƙafafuwan sa waje, sai ya ɗau wasu ƴan sakanni sannan ya fito gaba ɗayan sa...
Alhaji Ibrahim naga ya fito daga cikin tare da wata mata, da dukan alamun dai matar sa ce, sai wasu matasa guda biyu dake binsu a baya, tahowa suke cike da tsantsar farin ciki da murnar ganin juna...
Suraj kenan matashi kuma baƙin fata na farko da yake tuƙin jirgin sama, a ƙasashen ture, kyakkyawa ne shi ajin farko ga kuɗi ga jin daɗin duniya duka Allah ya bashi.....
Ganin iyayen nasa lafiya hakan ya sashi nishaɗi da farin ciki, jikin ladabi da biyayya ya tsugunna har ƙasa ya gaishar dasu, dan suraj akwai ɗa'a, ƙannen sa suma suka gaishe shi cikin girmamawa suna mai sannu da dawowa.....
Ɗunguma sukayi gaba ɗaya suka shiga cikin gidan, a falo suka yada Zango nan suka zauna aka sake wata sabuwar gaisuwar yaushe gamo, haɗe da ƴan hirarraki kaɗan kaɗan....
Momy ce ta kalli mubarak tace
"ka cewa yayan ku yaje yayi wanka sai ya fito muci abinci."
Shi kuwa Suraj jin tace haka sare yasan dashi take, kawai dai ta fake da mubarak ne, sai yaji bai ji daɗin hakan duk da cewa ya saba da wannan ɗabi'ar ta Hausa Fulani, ace wai uwa baza ta iya kallon ɗan ta na fari ba, bare har tayi doguwar magana dashi....
A sanyaye ya tashi ya shige ciki domin ya watsa ruwa, suma sauran tashi suka yi kasancewar magribah ta gabato, Alhaji Ibrahim ya kalli Momy yace
"Wai ina jiddah take ne! Bata zo taga babanta ya dawo bane.."
Momy tace "ni Wallahi nama manta in tashe ta Barci take, gashi yamma tayi yanzu, tun ɗazu take jiran dawowar tasa har ta gaji da jira bacci yayi awon gaba da ita.."
Daddy yace "to gaskiya je ki tashe ta, daga nan sai ki faɗa mata babanta ya dawo.."
Tashi Momy tayi tana dariya tace "yanzu kuwa kaga tsalle tsalle a wajen jiddah.."
Hayewa tayi saman bene da shi kuma Daddy ya fice masallaci...


★★★
Bayan magribah kuwa Momy ce ke ta ciku-cikun haɗa musu dinner akan darduma, dan Daddy baison hawa danning ya fison cin abinci a ƙasa wannan yasa har iyalen gidan sa sun saba da hakan....
Wata yarinya ce da baza ta wuce shekara biyar ba, ta fito daga cikin ɗaki da gudu, yarinya sak Suraj kamar yayi kaki ya zubar, cikin Muryar ta ta ƴan yara tace
"momy ina Daddyna yake! Kin ce inayi sallah zan ganshi yana ina..?"
Momy tace
"to Sarkin tambayoyi! Kije yana ɗakinsa, kuma ki tafi a hankali.."
Taku uku tayi a hankali sannan ta zuba da gudu. Ɓangaren Daddy nata tayi tana kiran sunan shi...
Suraj dake zaune kan sallaya yana zikirin yamma, dan suraj Masha Allah akwai son ibada....
Shigowa tayi da gudu ta, faɗa jikin sa tayi tana ihun murna, rungume ta yayi yana ƙara jin son ƴar tasa da kuma ƙaunar mahaifiyarta,
da ta rasu wajen tsawon shekaru biyar kenan, ranar da ta haifi jiddah Allah ya karɓi ranta tun daga nan Suraj bai ƙara yin aure ba, dan ko zancen auren aka mai sai yayi kuka, a ganin sa bazai samu mace tamkar mahaifiyar jiddah ba.....
Jiddah ce ta katse masa tinanin da yake wajen cewa
"Daddy ka taho min da tsaraba ta.?"
"Eh mana sarauniya ta! Yanzu muje gurin momy muci abinci sai mu dawo, na nuna Miki tsarabar ki.."
Ɗaukar ta yayi suka wuce babban falon gidan, kasancewar anan suke cin abincin.....
Bayan an gama cin abincin ne Alhaji Ibrahim ya kalli Suraj yace

"Am!! Suraj ya maganar mu da kai kan ka tafi U.S. , akan zuwa ganin ƴar aminina Salisu, fatan dai baka manta ba.."

"Eh Daddy ina sane! Amma yanzu ina ganin kamar za'a iya mata aure, tunda kaga yanzu shekara biyu kenan dayin maganar.."
Daddy yace "tabbas hakane insha Allahu gobe sai muje can batsarin, in yaso in an mata aure to dama can ba rabon ka bace ita..."
Suraj yace "to Allah ya kaimu.."
ya faɗa cikin ladabi, hira suka cigaba da yi ciki nishaɗi har lokacin sallar isha'i yayi, sallar isha'i kuwa kowa yayi nasa gun.....
Washe gari kuwa da shirin su, suka tashi sai ƙaramar hukumar batsari........


★★★
Ɓangaren Ma'u kuwa yau tunda ta tashi take jin faɗuwar gaba, tun tana daurewa har ta gayawa inna halin da take ciki, inna kuwa sai ta kwantar mata da hankalin cewa INSHA ALLAHU alkairi ne Ma'u karki damu kedai kiyi ta addu'a, nima ina miki fatan alheri.
A haka har bacci yayi awon gaba da ita, cikin baccin ne take mafarkin wani mutum ya ɗaure Haidar yazo ya jata sun tafi, shi kuma haidar dake ɗaure sai kiran sunan ta yake amma mutumin yaƙi sakar mata hannu, tayi ƙoƙari taga fuskarsa amma ta kasa, a daidai lokacin ne Ma'u ta farka a zabure, tana mamakin wannan mafarkin da tayi, a ko da yaushe saide tayi mafarkin Haidar yana cutar wasu amma yau shi aka cuta......✍️





_alhmdllh yau dai nayi post sau biyu a rana hakan ya faru ne sakamakon comment ɗinku musamman facebook ina yinku ƴan facebook da ace zan iya dana ambaci sunayen ku saide ba lokacin haka amma insha Allah zan ƙoƙarta hakan_





*More comment*
*More typing*
*Pls share*









~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/9, 12:37 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*32 & 31*




____________Haka ta tashi tana al'ajabin wannan mafarkin da tayi, ji tayi wani sanyi yana ratsa mata zuciyar ta, sakamakon ɗazu da gabanta yake faɗuwa...
Tashi tayi ta fito waje, samun inna tayi zaune tana gyara wake, sai kuma auta zahrah dake wankin uniform ɗinta, sannu da hutawa tayi musu sannan ta zauna, waken da inna take gyarawa Ma'u ta karɓa, cigaba tayi da gyaran suna ɗan taɓa hira jefi-jefi.......

Ƙarfe 12:00 daidai suka ji sallamar kawu Salisu da wasu baƙi, ganin Alhaji Ibrahim da inna tayi yasa da sauri ta tashi tana "lale marhaban! sannun ku da zuwa, ku ƙara so ciki.."
Cikin ɗakinta inna ta kaisu, tare da shimfiɗa musu ƙatuwar dadduma, nan suka zauna aka fara gaishe gaishe cikin mutunta juna, Alhaji Ibrahim ya gabatarwa da inna Momy da ƴaƴan sa maza guda uku, inna tace "masha allah! Allah yayiwa rayuwa albarka." Gaba ɗaya suka amsa da ameen....

Ma'u dake tsakar gida tana shirya abincin rana, sai kaiwa da komowa take, Dan ma'u gwana ce wajen girki, zahrah ce ta shigo da katan ɗin ruwan gora a hannun ta da ta siyo a shago, da hanzari Ma'u ta karbi ruwan ta ɗauki ƙaramin tire ta ɗora kofuna akai, ta shiga dashi ɗakin da suke......

Koda ta shiga cikin taga sun zuba mata ido, Ma'u dama gata da tsoron mutane Musamman ma taga akwai maza a gurin, a dabur ce ta tsuguna ta gaisher dasu amsawa sukayi gaba ɗaya, suna kallon ta...
Shi kuwa Suraj da bai ɗago ba kallon ta yake ta ƙasa ƙasa, idonsa ya faɗa kan ƙafar ta, da take fara sol, kamar bata taka ta a ƙasa, ji yayi ƙafar ta burge shi dan shi yana son yaga ƙafar mace kyakkyawa koda kuwa bata da kyawun fuska...
Sauri yayi ya kawar da tunanin da yake a ransa, yana fatan Allah yasa yarinyar da za'a haɗa shi da ita tana da hankali.....
Tashi Ma'u tayi ta fita daga ɗakin ta barsu suka cigaba da hirar su da su inna, ganinta da Alhaji Ibrahim yayi sai yaji daɗin hakan, dan haka kurum ta kwanta mai a rai, kuma yana da tabbacin zaman su zai zo ɗaya da Suraj....

Kiran sallar azzhar ne yasa kawu Salisu yaja su zuwa masallaci, a hanyar su ta dawowa ne Alhaji Ibrahim yake cewa kawu Salisu
"wannan yarinyar Asma'u! Da nagani yanzu shin maganar mu da kai ta kwanakin baya da suka wuce, tana nan Ko kuwa an mata miji..?"
Kawu Salisu yace
"ah ah! Ba'a yi mata ba."
Nan kawu Salisu ya kwashe dukan abinda ya faru bayan rabuwar su ya faɗa mai, shima Alhaji Ibrahim labarin dalilin da yasa ba su zoba yaba shi, sannan ya ɗora da cewa "yanzu haka ma a shirye suke, dan sunzo da Suraj ne yaga Ma'u, su shirya kansu in sun daidai ta ayi musu aure.....
Kawu Salisu yayi murna da hakan, har suka ƙarasa gida kawu Salisu yana murna, bayan sun shigo ne, sannan Ma'u ta gama girkinta zubo musu tayi a kula ta kawo musu, haɗe da kawo musu fulet ɗin da zasu ci tayi waje, zuzzuba musu abincin inna tayi ta miƙa musu, shi kuwa Suraj ganin alale da miya sai yaji bazai iya ciba, kasancewar bai taɓa ciba, amma ba yadda ya iya dole yaci dan yadda yaga mutanen suna da mahimmanci a idon Daddyn sa, idan bai ciba Daddy bazai ji daɗi ba, a hankali ya fara kaiwa bakinsa, yana tinanin yadda zaiji ɗanɗanon abin, amma sai yaji akasin haka za gewa yayi yaci sosai dan yafi kowa ci da yawa....

Kammala cin abincin da kaɗan, Alhaji Ibrahim ya kalli Suraj yace
"Son kaje daga waje! Kan mu fito, in yaso sai a turo maka yarinyar yanzu ku gaisa da ita.."
Amsawa yayi da " to." Cikin ladabi sannan ya fita daga cikin ɗakin, fitar sa ke da wuya kawu Salisu yace wa inna taje ta tura masa Ma'un...

Inna na shiga ɗaki ta samu Ma'u a zaune, dafa ta inna tayi sannan tace "kije daga waje akwai baƙon da zaku gaisa dashi.."
Ma'u kuwa jin abinda inna tace sai taji kamar an buga mata guduma, a tsakiyar kanta dafe kan Ma'u tayi sannan ta kalli inna tace
"wllhi innarmu kaina ne yake min ciwo bazan iya zuwa ba....."
Cike da mamaki inna take kallon ta tace "yanzu na sameki lafiya kalau amma daga yin maganar, kije kiga wani har kai ya fara ciwo, anya Ma'u lafiyar ki kalau kuwa?.."
Inna ta tambaye ta tana riƙe baki, cigaba da cewa inna tayi "zaki tashi ki wuce ne! Ko sai na ɓata ranki........✍️





*SHIN MA'U ZATA JE KUWA?*🤔

*WAI INA HAIDAR YAKE NE*😹








*COMMENT*💃❤️



[6/8, 10:30 PM] Matar
Khamis,: [6/8, 10:03 PM] +234 703 739 6908: Wow gsky matar khamis duniya ce munajin dadi sosai wlh naji dadin da Suraj yakasance me bautawa Allah akan lokaci naji dadi dayaxama Mai azhkar hakan xaisa ya ci karfin haidar me ikirarin yanason ma'u Allah yakara basira Allah yakaimu gobe muga posting dayawa Allah yakara xakin hannu

[6/8, 10:11 PM] +234 906 547 6395: Wayyo Allah alkadarin haidar y karye💃🏻

[6/8, 10:20 PM] +234 703 644 4508: Wow kadarin haidar hakusa karyewa Allah sarki ma'u Allah yakusa rabaki da ala kakai💃💃💃 matar khamis Allah yakara basira muna godiya

[6/8, 10:23 PM] +234 906 598 1474: Yau munzama yan gata 2pg arana gaskiya mungodefa matar khamis Allah yabiya muma munayinki over

[6/8, 10:24 PM] +234 706 058 4513: Allah ya karawa rayuwa albarka
[6/8, 10:31 PM] Matar Khamis,: Bayan Dade wa ta banyi karatun littafin hausa ba.yanzu da na Fara karanta wa ba wani littafi da ya ke min Dadi fiye da wan Nan labari da kike rubutawa some times na Kan rasa Mai zan Cai Miki fatan Alkhairi a ko da yaushai na ke Miki da fatan nasara acikin rayuwa

[6/8, 10:36 PM] Matar Khamis,: [6/7, 1:23 PM] +234 906 598 1474: Topah yanxu akafara wasan muna gdy Mrs khamis Allah yabiya
[6/7, 7:30 PM] +234 805 056 9109: Masha Allah matar khamis littafi yai Dadi Allah ya Kara basira👍🏾 lallle abun da zai raba ma u da haidar sai Allah!!!

[6/8, 9:13 AM] +234 803 777 8216: yau nice 1 matar khamis Allah yakara basira
[6/8, 11:30 AM] +234 805 056 9109: Yanzu aka Fara labari .Masha Allah .haidar bai kyauta .Allah sarki mahaifiyar ma u taban tausayi burin kowaccai uwa taga Auran yaran ta ! Shin dangin ma u ba wadda zai Kara tsayuwa akanta ? Ba wadda zaiyi tattamar Anya ma u Bata da wata matsala ? Ina nufin aljanu ko sihiri ko jifa ? Matar khamis Allah ya Kara basira👍🏾zan so jin karshe drama Nan . Lallai haidar shi nai shi nai babban tauraro Amma ya kamata ya samu Abokin gogayya ko da bai Kai shi ba .

[6/9, 10:44 AM] Matar Khamis,: Tofa anzo wajan haidar zaigamu da gamonsa

Mungode Allah yaqara basira da zakin hannu

[6/9, 10:45 AM] Matar Khamis,: Naji dadi ma,u zata fara samu cenji

[6/9, 10:46 AM] Matar Khamis,: [6/8, 11:21 PM] +234 803 152 3601: Masha Allah. Allah ya kara basira da hazaka. Ma'u kin kusa hutawa

[6/9, 8:53 AM]
Alhamdulillah: Wow yanzu akafara munagodiya Allah yakara basira da zakin hannu

[6/9, 9:43 AM] +234 916 233 5086: Wow , kai yayai dadi,ni dama naji acukina suraj sai dawo,wayyo haidar har ka ban tausayi,
Muna godiya ,Allah ya kara kaifin ido

[6/9, 9:59 AM] +234 816 823 8549: Lpy da nisan kwana matar khamis🥰
[6/9, 10:47 AM] Matar Khamis,: [6/7, 6:28 PM] +234 706 363 6092: Kae🙆‍♀️😭😭Allah sarki ma,u


Allah yakara basira


[6/9, 8:41 AM] +234 706 363 6092: 💃💃💃🤣🤣kae masha Allah da alama wadda xasu papata da hydar yaxo


Allah yakara basira



_______________________________


_ASHE DAMA HAKA HAIDAR YAKE DA MAƘIYA🤔 NIDAI MATAR KHAMIS BABU RUWA NA IN HAIDAR YA KAMA MUTUM😳🙆🏻‍♀️_
*NAYI NAN 👩🏼‍🦯👩🏼‍🦯*



*WALLAHI JIYA COMMENT ƊINKU YA SANI NISHAƊI SOSAI 🥰💃 ALLAH YA BAR ZUMUNCI*






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*












~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/10, 7:50 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*34 & 35*



_____________Shiru Ma'u tayi ta sunkuyar da kanta ko kallon inna bata yiba, ganin haka da inna tayi yasa ta fara mata magana cikin faɗa-faɗa, tashi Ma'u tayi hankali kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki, bata san mai yasa ba haka nan take jinta kamar ba ita ba, hijab ɗin ta tasa sannan ta fice daga cikin gidan.....
Bayan fitar ta kuwa inna wani dogon tagumi taja a ranta tana saƙa abubuwa da yawa, amma ta kasa samun mafita, tashi tayi ta koma ɗakin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login