Showing 3001 words to 6000 words out of 41435 words
Chapter 2 - NAMIJIN DARE Hausa Novels Complete.txt
 taɓa zuciya......
 ita ba komai bane, yafi ɓata mata rai, irin yadda inna take cewa, wai taimaka mata ake so ayi, sai kace wata al'majira....
  *WAI SHIN MEYE HAƊIN MA'U DA HAIDAR* ?
inna Hajara itace mahaifiyar su Asma'u, inda take da ƴaƴa shida maza biyu sune Auwal da Sani sannan Asma'u  sai ƙannanta mata, Aisha da Safiyya, sai kuma auta zahra...
Ma'u tunda ta tashi, ta tashi cikin soyayyar iyaye, kasancewar inna, tunda ta haifi Auwal da Sani sai haihuwar ta tsaya mata, saida ta ɗauki shekaru har bakwai, sannan Allah ya bata cikin Ma'u...
   a lokacin tayi matukar murna sosai, da ɗin daɗin ma, da ta haifi ɗiya mace abinda take matuƙar sha'awa.
    haka tai ta rainon ɗiyarta yadda yakamata,  cikin lokacin ne inna tayi baƙi, sai ta shimfiɗa musu tabarma a tsakar gida, nan suka zauna suna ta hira, yayin da ta kwantar da jaririyar ta Ma'u a cikin ɗaki.. 
   Haidar yazo wucewa ta gurin kenan, sai ya hangi wani kafirin aljani yana ƙoƙarin cutar da ita, kasancewar sa musulmi kuma mai tausayi, yasa yazo ya taimake daga cutarwar wannan kafirin aljanin, tundaga wannan lokacin Haidar ya kasance tare da Ma'u........✍️
   *HATTARA IYAYE ANAN YAKAMATA KUSAN CEWA, DUK LOKACIN DA MUKE DA ƘANANAN* *YARA, MUDAINA AJJE SU, A GURI SU KAƊAI BA TARE DA MUNYI MUSU WATA ADDU'A BA , KAWAI MUN BARSU ADUK YADDA MUKA GA DAMA.*
  *SHIYASA ZAKUGA IYAYEN MU NA DA MUSAMMAN IRIN NA ƘAUYE IN ZASU AJJE JARIRI, SAI ANSA WANI YA ZAUNA A GURI SANNAN UWAR YARO ZATA TASHI, KO KUMA A AJJE MAKAMI KUSA DA JARIRI, WAI DAN YAZAMA KARIYA A GARESHI..*
    *TO AMMA A GANINA HAKAN DUK BAI YIBA* KAWAI KIYI ADDU 'A
KI TOFE YARKI, KO ƊANKI, SHI YAFI ALKAIRI BAMAKAMI BA KO AJJE WANI
 AKUSA...☹️
*_sannan ina matuƙar godiya da yadda kuka karɓi wannan littafin nawa, jiya da aka jini shiru hakan ya faru ne bisa hutun sati dana keyi na gode_*
*more comment*
*more typing*
*pls share fisabilillah🤩🙏*
~MRS KHAMIS CE🥰💃~
[5/10, 1:19 PM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄👄
 🥺 *NAMIJIN DARE*🙆♀️
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
________________________________________________________________
*page 6*
Tunda ga wannan lokacin, Haidar ya kasance, tare da Ma'u, yana bata kariya...
Ko su kansu shaiɗanun, idan suka ga Haidar tare da ita, ko tunkarar inda Ma'u take ba suyi..
Haka Ma'u ta taso, yarinya kyakkyawa, fara doguwa, gata da gashi, kamar ƴar buzuwa, son kowa ƙin wanda yara sa, gata dasan kwalliya gwanin sha'awa, duk wanda yaga Ma'u sai ta burge shi, saide hassada ta mutane..
A lokacin ne Haidar, zuciyarsa ta fara kamuwa da son Ma'u, domin duk abinda take burge shi take, musamman idan tayi kwaliya..
Hakan yasa Haidar yin tinanin bari ya ƙauracewa rayuwar ta, ko ya manta da wata soyayyar ta..
     Haka rayuwa tai ta tafiya, abubuwa da dama sun faru, masu daɗi, da marassa dad'i, ciki kuwa harda rasuwar mahaifin su Ma'u..
  A lokacin Ma'u an zama ƴan mata, dan tana da shekaru sha bakwai cif cif, komai de na cikakkiyar matashiyar budurwa, ya bayyana gareta..
  Dama lokacin, mahifinta yana raye, ya haɗa auren da ɗan ƙanin sa, wato kawu salisu, Ma'u ita da yusif suna soyayyarsu sosai, domin suna matuƙar son juna, dan har lokacin da za'ayi bikin nasu ansa, kawai ana jiran ya gama ginin sa ne sannan ita kuma tayi, Candy....
          ★     ★      ★
Ɓangaren Haidar kuwa, tunda ya tafi bashi da wani aiki sai tinanin Ma'u, tun yana daurewa, har ya kai yanzu, baya iya daurewa, dan kullum ciki begen ta yake, kamar yau ma yana zaune shi kaɗai, akan wani tsauni dake tsakiyar ruwa, yanayinsa kaɗai ya isa yasa a gane bawane dake cikin shauƙin soyayya...
    Ya ɗauki tsawon lokaci agurin, kuma duk abu ɗaya yake wato tinanin bil'adama, ji yayi anda fa sa ta baya, murmushi ya saki ba tare da ya juya ba yace "Iliyas mai kake yi anan! a daidai wannan lokacin?."
   Dawowa yayi ta gaban sa, haɗe da maida mai martanin murmushin sa, yace   "wllhi nazo wucewa ta ƙarshen tsaunin nan, sai na shaƙi kamshin turarenka, kuma nasan bbu mahlukin dake amfani da wannan kamshin, in ba kai ba, shiyasa na zagayo tanan sai gashi na ganka, amma mai kake yi anan!, ka zauna kai kaɗai! lafiyar ka kuwa?.."
   Numfasawa Haidar yayi, haɗe da  sakin wata ajjiyar zuciya mai zafi, yace
 "wallahi matsalar soyayya ce abokina,  wllhi dukan bugun numfashina, da begenta yake bugawa, ji nake bazan iya rayuwa batare da ita ba."
  Ya ƙare maganar sa, cike da rauni.
  Da tsantsar tausayi, Iliyas yace  "ita ko wannan mace da kake so wace ce, a cikin jinsin jinni ƴar wane haka mai sa'a."
  Girgiza kai Haidar yayi yace  
    "Ba a cikin ko wani jinsi take ba, face bil'adama."
  Da mamaki Iliyas yace "bil'adama! bil'adama fa kace, haba Haidar,. mai zakayi da bil'adama, ga jinsinka nan, akwai mata kala-kala, kuma masu kyau, kawai ka rabu da ita.."
    "Uhmm Iliyas kenan, wannan ba macen da zan iya rabuwa da ita bane, kuma ina sonta kamar numfashi na, zan iya komai akanta."
  Haidar ya faɗa har cikin ransa...
 Bushewa da dariya Iliyas yayi, sannan yace 
 "to ita masoyiyar taka tana ina.?" 
 Ya faɗi maganar nan, yana ƙunshe dariyar sa.
  Ajjiyar zuciya Haidar yayi, yace "yanzu tsawon shekara huɗu rabona da inganta, amma fa ina azabtuwa wllhi abokina."
  Ƙara kecewa da dariya Iliyas yayi yace "to kai kana nan, kana haukan sonta, wata ƙila ita tana cen tayi aurenta.?
    A fusace Haidar ya ɗaugo, fuskarsa ta sauya, ta koma wata kala dan ɓacin rai, yace "wllhi duk wanda ya auri masoyiyata, hmm!! sai na ɓatar da rayuwar sa, ta har abada."
  Miƙewa yayi da sauri, riƙesa Iliyas yayi yace "ina zuwa kuma?. Haidar yace "gurinta zanje naga meke faruwa a rayuwar ta."
      Da sauri Iliyas, yace "ah ah Haidar! karfa ka manta, cewa ita ɗin bil'adama ce, kuma tana da rauni, kai kuma bil'jinnu ne, kuma kana da ƙarfi, dan Allah! dan Allah! Haidar ka rabu da ita, ka samu wata a jinsinka ka aura, kada ka cutar da ita, kaji tausayin ta Haidar.."
    A fusace Haidar ya juyo yace " da ace wani ne yake min wannan maganar, da sai ya ɗan ɗana kuɗarsa, kai abokina ne idan baza ka goyamin baya ba, kada ka ƙara min magana mai zafi irin haka, in ba haka ba zamu samu saɓani da kai,.."
  Haidar ya faɗi haka yana ɓacewa...
 
    ★     ★      ★
Acan ɓangaren su Ma'u kuwa, ana ta shirye-shiryen bikinta da Yusuf, dan yanzu haka ma ta dawo daga wurin gyaran jiki, tayi wani fresh da ita, tafito a matsayin ta na amarya, sauri-sauri take ta shiga wanka, kasancewar ana zafi sosai..
   A gurguje ta faɗa bayi, dan yin wanka ko taji sauƙin zafin da take ji, Haidar kuwa da ya bayyana a gidan , ganinta cikin bayin tana wanka yasa ya shiga cikin bayin, tsura m halittar ido yayi, yana jin kamar ya haɗiye ta, dan son da yake mata, yayin da ita Ma'u wankanta take cikin kwanciyar hankali, dan har wani lumshe ido take idan ta zuba ruwan ajikin ta, cikin shauƙi da salo take wankan, kamar tasan akwai wata halitta da take kallonta..
  Shi kuwa Haidar da ya ƙura mata ido ko ƙiftawa ba yayi, wani yanayi ke fisgarsa, yana jin zai iya kasancewa da ita na har abada........✍️
*ina ta gani ƙorafe-ƙorefen ku dan allah ku riƙamin uziri abubuwa da yawa sunmin yawa ne shiyasa amma insha allah zan ƙoƙarta, ina jin dadin comments ɗinku ina godiya sosai..✍️*
*more comment*
*more typing*
*pls share*
~MRS KHAMIS CE🥰💃~
[5/11, 4:12 PM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄👄
*NAMIJIN DARE*
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
____________________________________________________________
*page 7*
________Da wajen magribah, Ma'uce zaune cikin ɗakin inna, tana cin kazar amare, da inna ladidi ƙawar inna ta aiko mata da ita, ci take amma badan ranta yana so ba, asalima ji take kamar zatayi ame..
     Yusuf ne ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, guri yasamu kusa da ita ya zauna, leƙa cikin kular yayi haɗe da sakin murmushi, yace  "gaskiya ne ƙanwata, ashe ki nan kina cin daɗin ki, kin barni da sanƙamar tuwo."
   Ya faɗa cikin sigar tsokana, murmushin mugunta tayi tace    "bismillah yayana" ƙwace kular yayi yace "saide in cinye duka! dan kede kam kin ci rabon ki."
 Ido Ma'u kawai ta zuba mai, tana so taga yadda fuskar sa zatayi, yayin da ya fara cin naman kazar, yago wata tsoka yayi ya kai bakinsa, har wani lumshe ido yake, kasancewar nama yaji dahuwar daddawa, yana sawa baki maimakon yaji daɗi, saima wani mugun bauri da ya ziyarci bakinsa, da sauri ya furzar, yana ya mutsa fuska.
  Ɗagowa yayi, ya kalli Ma'u "sannunki da ƙoƙari, da wani kalar kayan ɗaci aka dafa kazar nan, ya faɗa yana goge bakinsa da hand kichef..
  Ma'u kuwa dariya take iya san ranta, sai  da ta tsagaita da dariyar, sannan tace ai wllhi yaya Yusuf kwaɗayinka yawa ne dashi, yanzu inda nace bazan baka ba, wallahi sai kaci, shiyasa na bar ka bakinka ya hanaka.
 Ta ƙare maganar, tana ƙunshe dariyar ta,  shagala Yusuf yayi da kallon ta, dan  yana matuƙar son Ma'u, kamar ransa.
  Matsawa kusa da ita yayi, cikin raɗa raɗa yace "na miye ! pls faɗamin ƙanwa ta"?  sai da ta ya mutsa fuskarta, sannan tace nima bansan ko na miye ba, kuma inna kusan kullum, sai ta bani irinsa..
  Fahimtar ko na miye da yayi ne, yasa ya miƙa mata sauran, yace "gashi ki cinye duka, ai abun na taimakon kaine..."
 Ya faɗa yana sakin ƙayatacen murmushin da shi kaɗai, yasan ma'anarsa...
        ***
Haidar dake zaune cikin wata sahara, iskar dake kaɗawa, da kuma yanayin ni'imar dake sauka agurin, sai suka haɗu suka saukar mai da shauki, da kuma begen masoyiyar, abin ƙaunar sa...
   Shafa tafin hannunsa, abun mamaki sai ga Ma'u da Yusuf, suna hirar su ta masoya, cikin kwanciyar hankali, gwanin ban sha'awa..
  Wata kururuwa Haidar yayi, haɗe da sakin wani raza nan nan ƙara, wanda ya haddasa wata firgitacciyar guguwa lokaci ɗaya, ɓace yayi ɓat, cikin ƙanƙanin lokaci ya bayyana ɗakin inna, dai-dai lokacin kuma Yusuf ke cewa Ma'u "kinga rana ita yau kina gidana, ba damar ki kore ni, ko kice min bacci kike ji, ya faɗi haka cikin wasa..
  Haidar dake tsaye zuciyar sa tana ta tafarfasa, ji yake kamar ya bayyana a garesu, kodan yawa  Yusuf lahanin da bazai taɓa moruwa ba.....
*_dan Allah kuyi hakuri da wannan ba yawa sakomakon banjin dadi kuma shi jiki da jini sai mun haɗu gobe in Allah ya kaimu_*
*more comment*
*more typing*
*pls share*
~MRS KHAMIS CE~🥰💃
👄👄👄👄
*NAMIJIN DARE*
         _aljanin soyayya_✍️
  ```story and writing```
      
          *by*
  *_ummy mrs khamis_*
     09137879957
________________________________________________________________________________
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
  _(Domin Marubuta Mata)_
    
   ✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*short story*
*TSOKACI* :
 ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁♀️```
```bissimillahir rahamanur rahim``` 
*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a )  aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*
______________________________________
SADAUKARWA!!
 ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃
 
*bissimillahir rahmanir rahim*
____________________________________________________________
*Page 8*
_________Shirye-shiryen biki yana ta kan kama, inda yau biki ya rage saura kwana ɗaya, sosai ake shagali baka ma hannun yaro, amarya ansha kyau sosai, kasancewar yau suka yi walima, duk tabi ta gaji, tana gabatar da sallah isha'i ta shige ɗakin inna wanda babu mutane da yawa sosai, hayewa can ƙuryar gado tayi, nan ta ƙundundune tuni wani nan nauyan baccin gajiya yayi awon gaba da ita..
     zaune suke cikin wani ƙatataccen lambu, cikin nishaɗi da annushuwa, suke hirar su irin ta masoya, wani mutum ne yazo inda suke, kallon yusuf yayi yace "kaide ka nace, sai ka mallaki abinda bai dace ya zama mallakin wani ba, to kasani yau ce rana ta ƙarshe, da zan ƙara ma kashedi akan ka rabu da masoyiyata,  idan ba haka ba, zaka tafi inda ba'a dawowa"..
    Murmushi Yusuf yayi haɗe da kamo hannun Ma'u, ya riƙe shi gam a hannun sa, yace "Babu wanda ya isa ya rabani da Ma'u, sai Allah n da ya halicce mu." 
  Mutumin ƙafa yasa ya hauri Yusuf a ƙirjinsa, tuni ya faɗi ya fara aman jini, Ma'u da take kallon ikon Allah da gudu ta tashi da niyar taje gurin yusuf, amma mai sai mutumin ya riƙe ta, ɗayan hannunsa kuma ya shaƙe Yusuf dashi tun yana motsi har ya daina, kallon ƙasan gurin yayi tuni wani ƙaton rami ya bayyana a gurin, tana ji tana kallo mutumin, ya jefa masoyinta Yusuf a cikin ramin, ita kuma ya wuce da ita yana cewa "keɗin mallaki nace, duk wanda yayi gigin mallakarki, ga irin sakamakon sa.."
  A firgice Ma'u ta farka daga baccin da take, sakamakon wannan munannan mafarkin da tayi, jiki na karkarwa ta lalabi wayarta da ta kashe lokacin da zata kwanta, gudun kar a dameta..
  Number Yusuf ta lalubo, kira take wayar tana ta ringing, amma ba'a ɗaga ba, kira ta sake yi amma still ba'a ɗaga ba, saida ta kira yafi sau bakwai amma shiru, ƙara gigicewa tayi haɗe da sakin kuka tana cewa, "Allah kasa mafarkin nan kar yazama gsky", ta ƙare maganar tana haɗa hannuwanta biyu...
     Shi kuwa Yusuf a dai-dai lokacin da Ma'u take kiransa, shima yayi mafarki sak irin wanda tayi, amma saide shi ba yau ya fara ba, ya kai sati ɗaya yana irin wannan mafarkin, kuma duk akan barazana ne na ya rabu da Ma'u..
  Tashi yayi yaje ya ɗora al'wala sallah yayi raka'a biyu, tare da yin addu'a da neman tsari akan duk wani abin sharri..
Bayan ya gama ne yazo zai kwanta, wayarsa ya ɗauka dan yaga ƙarfe nawa, abin mamaki sai yaga kiran ma'u, da sauri yabi kiran bugu ɗaya ta ɗauka, fashewa da kuka tayi, sannan tace "shine sai kiranka nake, amma kaƙi ɗauka, wllhi kaban tsoro." a kiɗime yace "lafiya! mai ya faru kike kuka!, faɗa min tunkan zuciyata  ta buga?."
  "uhm wllhi yayana ina cikin fargaba, wani mugun mafarki nayi, wai nida kai...." katseta yayi da sauri yace "ba'a faɗan mugun mafarki, saide mafarki na jin daɗi ko na farin ciki, kawai kedai kiyi addu'a, kinji ƙanwata.." 
   Saida ya mata nasiha sosai, tare da nuna mata shi mafarki ba gsky bane, yawanci duka sharrin shaiɗan ne, bai bar ta haka ba, saida ya tabbatar da hankalin ta ya kwanta..
  sannan ya ɗora da tsokanarta, duk yawanci wasan da yake mata kunyar sa takeji, hakan yasa ta kashe wayar , haɗe dayin addu'a ta tofa a hannun ta, shafe jikinta tayi sannan ta kwanta abinta.
      *ASUBA TA GARI MA'U AMARYA*
Shi kuwa yusuf kasa komawa yayi, dan jin shi yake kamar bashi da cikakkiyar lafiya, kawai daurewa yake a matsayinsa na namijin gaske, kuma mai dauriya.
  Yusuf kuwa dake zaune sai gumi yake, ga wani zafi da jikinsa yayi, dan duk wannan shaƙar da Ma'u ta gani acikin mafarkin ta, azahiri yana kwance kan kadon sa, amma a baɗini abinda Ma'u ta gani ya faru da gaske..
   Sosai yusuf yake shan azaba a jikinsa, bacci kawai yake so yayi, amma saide bazai samu ba..
A haka har akayi kiran sallar asubar farko, tashi yayi ya ɗora al'wala, fara gabatar da nafilfili yayi,  kan ayi kira sallahr shiga Masallaci..
  Kafin gari yayi tangararo, ixuwa yanzu yusuf ya jigata ko fita ya kasayi, turo ƙofar akayi , Auwal ne ya shigo wanda ya kasance babban yaya ga Ma'u, hararar Yusuf yayi sannan yace "wato ka barni da wasu shashashan abokananka, shine kazo nan ka kwata, to wllhi maza tashi muje kaji dasu, dan ni nagaji.."
 Ya ƙare maganar yana cigaba da harararsa, ɗago kai Yusuf yayi yana murmushi yace "kasan wani abu Bros wllhi jiyan ne, in na zauna a wajenku surutun ku yawa zaimin, gashi na dawo nan ɗin ma, amma duk da haka zazzaɓi nake ji." dariya Auwal ya saki yace  "to kai gashi baka san surutu, kuma gashi zaka









