Showing 15001 words to 18000 words out of 41435 words

Chapter 6 - NAMIJIN DARE Hausa Novels Complete.txt

dauriya Alh Tanko yace

"me ya kawoka gidana a halin yanzu! Sannan ma ta ina ka shigo?, Bayan na rufe ƙofar, kodai can dama da kai na rufe...?”
Haidar fuskarsa babu alamun rahama yace

"kaga nayi ma kama da wanda in zai shigo wuri sai yabi ta ƙofa, ta kowani yanayi nakan iya riskar mutum a duk inda yake.."
Alh Tanko yace
"to mai kake nufi da haka, ko kana nufin kai al'jani ne..?"
Tashi Haidar yayi cikin isah da ƙasaita, yayi taku biyu zuwa uku, yace

"naji daɗi da ka fuskanci hakan, ashe dama kai ba daƙiƙi bane, to ma'u ita ɗin mata tace, kuma bazan taɓa barin wani ya aureta ina kallo ba, saboda haka kaje ka janye aurenta da ka nema, inba haka ba zan salwartar da rayuwar ka.."
Alh Tanko kuwa kawai binsa da ido yake Sa'annan kuma ya bushe da dariya yace "oh ni ɗan babana! yau wai ni akewa barazana, dan zan auri ƴar baiwar Allah ma'u, to bari kaji in gaya maka wani abu, na daɗai da sanin irin ku a gari, sai kunga yarinyar kirki kyakkyawa kuma mai nasibin samun manyan mutane, sai ta samu mijin aure saiku bi duk hanyar da kuka ga dama, kuyiwa wanda yazo neman aurenta barazana dan ya fasa ko, to kasani ni ba irin barazanar da zakamin wacce zata yi tasiri a gareni ba, kuma banga wanda ya isa ya hanani auren ma'u ba, ba aljani ba ko sarkin aljanu ne kai sai na auri ma'u kayi duk abinda zakayi.."
Haidar da ya matuƙar fusata ya jiyo ga Alh tanko ,wata kalar girgiza yayi wacce lokaci ɗaya, halittun sa suka sauya izuwa abin tsoro, yace

"dama nazo maka da aminci ne, a tinani na zaka amsawa buƙata ta, amma tunda kace haka bari kaga ƙarfin ikon aljani.."
Alh Tanko da ya raɓe jikin bango, ko cikakken motsi ya kasayi, shidai kawai bin Haidar yake da kallo, yana so ya buɗi baki dan yayi magana, amma ya kasa cewa uffan..
Yana ji yana gani Haidar yasawa gidan sa wuta, sannan ne ya samu kƙarfin tashi ya fita da gudu dàn tàimaka ma iyalen sa,
da ƙyar suka samu suka fita daga gidan basu cire komai ba..

Da asuba kuwa Haidar ya sake dawowa wajen alh Tanko yace "kaga bala'i na farko kenan, sauran kuma duk baza suma dad'i ba, amma wata alfarma da zan iya ma shine, idan ka janye daga aurenta, kaga wannan gidan naka da ya ƙone zan mallaka maka wani wanda ya fishi sannan na dawo maka da linkin abinda ka rasa.."
Shidai alh Tanko shiru kawai yayi, zuciyarsa cike da tausayin ma'u da iyayen ta, haka ya kira su yace ya fasa auren ta.
aransa yana mata fatan alheri da kuma fatan Allah ya rabata daga tugun wannan azzalumin shaiɗanin aljanin, da yake iƙirarin cewa shi musulmi ne......








*KWANA BIYU KUNJI NI DAN ALLAH KUMIN AFUWA, NI KAINA BANSO HAKA TA FARU BA SAIDE KOMAI SAI ALLAH YAYI, AMMA INA TARE DAKU MASOYA BOOK ƊIN NAN*








*MORE COMMENTS*
*MORE TYPING*
*PLS KU RIƘA MIN SHARE DAN ALLAH*







~MRS KHAMIS CE~😍💃
[6/5, 10:24 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*24 & 25*




__________Washe gari kuwa da yamma, Ma'u ce tsaye ɗauke da botikin wanka, da dukkan alamun bayi zata shiga...
Kai tsaye bayin ta shige, ba tare da tayi addu'ar shiga nan ɗaki ba, bayan ta cire kayan tane, fara wankan ta ke da wuya, taji wani sihirtaccen ƙamshi ya cika gurin, sanin mamallakin ƙamashin da tayi ne yasa ta juyo da sauri, hango shi tayi tsaye a jikin bañgon bayin, ya naɗe hannunsa a ƙirjinsa, haɗe da ƙurawa halittun ta ido kamar zai cinye ta, dan ko ƙiftawa ba yayi....
Ganin haka da Ma'u tayi sai tasa hannunta, tana kare ƙirjinta, harararsa take ta ƙasa ƙasan ido, sannan tace "shine ina cikin wanka zaka shigo min ko! ni gaskiya ka juya ka daina kallonsa.."
Murmushi yayi,. yana cigaba da kallon nata, matsowa ya fara yi kusa da ita, yayin da yake cigaba da yi mata wani mayen kallo, turo baki Ma'u tayi tana ɗan diddira ƙafafuwan ta, da hanzari ya ƙara so, tare da janyo ta jikinsa, ido cikin ido suke kallon juna kamar ko wannensu zai cinye ɗan uwansa....

Haidar kuwa da yayi nisa a cikin shauƙin begen masoyiyar tasa, yatsa yasa yana ɗan zagaye leɓenta, da suka fi komai jan hankalinsa, da matuƙar birgewa a garesa, a hankali yace

"Ina son wannan leɓen! kuma ina kishin su, shiyasa banso inga yana wa kowa magana."

Turo leɓen kuwa Ma'u ta ƙara yi, sannan cike da zallar shagwaɓa tace .

"Uhmm! Ni ka barni inyi wanka na."

Cikin wasa da kwaikwayon muryar ta yace,

"Naƙi wayon! saide muje na miki da kaina."

Ido Ma'u ta fiddo waje tace
"ah ina kuma .?"

Yadda ta fiddo idon sai hakan ya burge shi, cikin raɗa-raɗa yace

"Ah gida na mana!."

Da sauri Ma'u tace

"To idan innarmu ta nemeni bata ganni ba fa?."

Rungume ta yayi tsam a jikinsa yace

"Inna bacci zata yi! Kuma kan ta tashi zan dawo dake.."

Ya ƙare maganar yana hura mata iska a kunnenta, lumshe idanunta tayi saboda daɗin hakan da take ji, jinta tayi an tsoma ta a cikin wani ruwa mai daɗin ƙamshi, ga wasu fulawoyi da suka bai baiye saman ruwan, cikin natsuwa da kuma salo yake mata wankan, yayin da Ma'u take jinta kamar wata sarauniya...
Haka aka gama wankan nan cike da soyayya, na ɗo ta yayi a towel, ya fito da ita daga bathroom ɗin, shimfiɗeta yayi akan bed ɗin dake cikin ƙayataccen ɗakin, shafe jikinta yake ta ko ina, a haka wani ɓarawon bacci mai ɗan karan daɗi yayi awon gaba da ita....
Bayan Haidar ya samu mutsuwar da yake so ya samu da ita, sai ya mirgina gefen ta yana ƙare mata kallo, cike da tsantsan so da ƙaunarta...

Koda Ma'u ta tashi, idonta da Haidar ya fara tozali, murmushi ta sakar mai, shima martanin murmushin ya mayar mata, sa'annan yace

"Fatan kin tashi lfy! Gimbiyata kuma sarauniyar da take mulkar zuciya ta."

Murmushi Ma'u tayi ta sunkuyar da kai, matsowa Haidar yayi kusa da ita yace
"Meye matsalar ki! Yanzu na miki maganin ta, dan zan iya komai akan ki hasken idaniyata.."
Ɗagowa Ma'u tayi sannan tace

"babu komai! Kawai na tuna mafarkin da nayi jiyane, kana sawa wani gida wuta, kuma da safe a kace gidan Alh Tanko ya ƙone, shin hakane da gaske kai kasa! Ko kuma mafarkin ne kawai..?"

Gira ya ɗaga mata alamar eh hakane, sannan yace

"Tabbas ni nasawa gidan sa wuta, kuma da ace bai janye maganar aurenki ba, to yau da shi zan ƙona, saboda danni kaɗai aka halicceki, ina ji ina kallo bazan taɓa barin wani namijin bil'adama Ya raɓeki, ke ko al'jani ne ya zo wucewa ta inda kike muduk ya kalleki, to sai na hukunta shi ko waye shi ɗin, kuma ko ɗan waye acikin jinsin al'janu....✍️





*Ina jin koken ku na cewa ya kamata akawo, wanda zai yi maganin haidar*

*To koken ya iso gareni amma saide fa kusani Haidar shine lbrn in ba haidar to ba lbr*👌😄





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING AKAI AKAI*✍️👌

*PLS SHARE*











~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/7, 12:41 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*26 & 27*




____________Zuba masa ido kawai Ma'u tayi, tana matuƙar mamakin furucinsa da yake cike da alwashi....
San sanyar ajiyar zuciya Ma'u ta saki a hankali tace
"To meyasa zaka aikata hakan..?"
Saida yaja dogon numfashi sannan yace

"Saboda ina sonki kuma ina ƙaunarki, Wallahi duk duniyar nan babu wanda ya kaini sonki da kishin ki, shiyasa ban ƙaunar inga ko wani ɗa namiji naga ya raɓeki koda kuwa shi waye.."

Ita dai Ma'u ido kawai ta zuba mai tana mamakin son da Haidar yake mata, gashi kuma wani ɓangare na zuciyar ta, yana kwaɗaita mata son yin aure ko dan hankalin innarta ya kwanta...
Haidar kamar yasan abinda take ayyanawa a ranta, hannunta ya kamo sannan a hankali yace

"Husnah ni ban isheki ki ƙare rayuwar ki dani ba?, Zan baki duk wani farin cikin da bil'adama bazai iya baki shiba, zaki kasance a cikin zuciyar da bazata taɓa yi miki kishiya ba, zan nuna miki soyayyar da ba'a taɓa yiwa wata ƴa mace ita ba a cikin duniyar masoya, ki cire tunanin auren wani bil'adama, ni nan kaɗai na isa na baki farin cikin da babu wani mahaluki da zai iya baki shi..."

Lumshe ido Ma'u tayi yayin da hawaye yake kwaranyowa daki daki, rungume ta Haidar yayi, yana bubbuga bayanta a hankali alamar rarrashi...
Cikin raunin murya Ma'u tace.
"Haidar nasan kasan cewa, innarmu bata da wani buri da ya wuce taga nayi aure, kuma gashi.....
Yatsar sa yasa a leɓenta yace
"Shishhht! Nasan komai basai kin gayamin ba, amma ga tambaya ɗaya zuwa biyu da zan miki, idan na samu amsar ta dai-dai yadda nake so naji to zan yanke hukunci da ya dace.."
A hankali Ma'u ta ɗago tana kallon cikin idonsa, duk da dai har yanzu bata iya kallon cikin idonsa, sunkuyar da kanta tayi tana kallon ƙasa....
Ɗago da kanta Haidar yayi sannan yace
"ki kalli cikin idona mana, pls mana masoyiya ta."
Kallo shi take cikin ido, yayin da take ji duk tsigar jikin ta tana tashi, yanayin salon kallon da Haidar yake mata, sai ya jefata cikin wani yanayi jinta take kamar ba ita ba, Saida ya ɗau wasu ƴan sakanni sannan yace,

"Kina sona! Kuma zaki iya rayuwa dani.?"

Girgiza kai Ma'u tayi alamar eh, hannunta Haidar ya kamo sannan cikin wani irin salo yace.
"Da bakinki nake so naji kin amsa min."
Eh kawai Ma'u tace a taƙaice .
Cikin murna da zumuɗi Haidar yace
"Da gaske! Kuma kinyi alƙawari.?"
Ma'u tace "eh mana." Ta faɗa tana murmushi..
Rungume ta Haidar yayi, yana jin farin ciki marar misaltuwa, a ganin sa tunda Ma'u itama tana sonshi to dukan matsalolin sa sunzo ƙarshe..
Haidar bai maida Ma'u ba sai gabda magribah, kai tsaye ɗakinta ya ajje ta...

Bayan ta gama shiryawa tsakar gida ta fito, samun zahrah tayi har ta gama girkin dare, kasancewar inna gwana ce wajen koyawa yara girki, ko kaɗan bata so taga yaro ya taso bai iya girki ba...
Dundu Ma'u ta kaiwa zahrah a baya, sannan tace
"autar mu! ina innarmu take ne".
Inna dake fitowa daga cikin ɗaki, fuskarta da alamun bacci tace

"Gani wake nema na?".

Ma'u tace
"nice innarmu."

"Ohh Wllhi nasha baƙuwa nayi,"
Inna ta faɗa tana ɗaukar buta...
Zahrah dake durƙushe tana dariya tace "innarmu ina ga baccin bai isheki ba."
Guri Ma'u ta samu ta zauna tana cewa
"da alama kuwa gaskiya."
Haka rayuwa tayi ta tafiya kullum soyayyar Ma'u ƙara lunkuwa take a zuciyar Haidar, musamman yanzu da yake ganin bashi da wani abu da ya shige masa gaba.....

Ta ɓangaren Ma'u kuwa saide muce subhanallah, Dan yanzu babu wanda yake zuwa yace yana sonta, ita dama ko a jikin ta dan duk namijin da ta kalla, saide taga ya zaman mata abin tsoro ko taga muninsa, Haidar shi kaɗai take ganin farinsa a doron duniyar s nan, sai ƴan uwanta maza wanda suka kasance muharramanta, amma sauran maza ita dasu *hai hata-hai hata*.......✍️






*More comment*
*More typing*
*Pls share*








~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/8, 8:48 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*28 & 29*




____________Haidar ne zaune a cikin wani lambu mai cike da furanni, iskar dake kaɗawa agurin da ƙamshin furannin sai suka haɗu suna bada wani ni'imtaccen yanayin dake sanya nishaɗi....
Babu abinda zuciyar sa ke hararo masa irin masoyiyar sa Ma'u, hannunsa ya shafa abun mamaki sai ga ma'u ta bayyana, ajikin hannun nasa kamar tv, kallon ta yake cike da shauƙi yana murmushi, gani yayi tana cokano baki kamar wata ƴar ƙaramar yarinya, hakan kuma yana matukar birge Haidar, sumbatar ta yayi ta jikin hannun nasa yana cigaba da kallon ta...
Ma'u kuwa da taji an sumbaceta sai ta ƙara cunno bakin nata kamar wacce take jiran tsammani.......

Haidar da yake kallon ta yana ƙara faɗaɗa murmushin sa, jinsa yake yafi kowa Sa'a a duniya, dan idan yana kallon ta mantawa yake da komai, jin motsi a ta bayan sa yasa da sauri ya shafi hannun sa, tuni hoton Ma'u ya ɓace a hannun nasa....
Abokinsa ne I'liyas, ya ƙara so yana cewa

"Toh Mijin bil'adama ashe kana nan! Ko bil'adamar taka kake tinani?."
I'liyas ya faɗa cike da
tsokana da kuma shaƙiyanci......
Haidar dake kallonsa yana hararar sa yace

"Mai zai sa inyi tunanin ta bayan ko da yaushe ina tare da ita, yanzu mah ina cikin ganinta, kazo ka katse min jin daɗi na.."
Baki kawai I'liyas ya saki yana kallon sa sannan daga bisani yace

"Ni ba wannan ba! ko zaka iya nuna min masoyiyar taka, naga wani irin kyawu gare ta da har ya ja hankalin ka."

Shiru Haidar yayi kamar mai tunanin wani abu jim kaɗan kuma sai yace

"Gaskiya bazan nuna maka ita ba.."
"Saboda me?."
I'liyas ya tambaya cikin mamaki,
Haidar yace "Saboda ina matuƙar kishin ta sosai, banso inga kowa yana kallonta indai namiji ne.."
I'liyas yace "lalle abin naka azimin ne, amma har ni da nake a matsayin abokin ka, baza ka nuna min ba.."
Tashi i'liyas yayi zai bar gurin kamar yayi fushi, ganin haka da Haidar yayi sai ya riƙo hannun sa yace
"yi haƙuri abokina zo in nuna maka ita."
Dawowa i'liyas yayi ya zauna, hannunsa haidar ya shafa sai ga ma'u ta bayyana, sakamakon ɗazu tana bacci yanzu kuma idonta biyu kawai dai tana kwance ne, kamar yadda yace kallo ɗaya i'liyas zai mata, hakan kuwa ta kasance yana kalla Haidar ya janye hannunsa....
I'liyas a ransa yace ba laifi tana da ɗan kyau, amma a fili sai yace wa Haidar
"Gaskiya na yarda da ake cewa so makaho ne, to tabbas haka ne! So babbar makanta ce, na farko ni banga wani kyawun da zaija hankalin ka zuwa gare ta ba, wanda har ace babu matan da suka fita kyau ba acikin jinsin al'janu, sannan ƙari wata makantar shine da har idonka ya rufe, ka kasa sanin dai-dai da kuma akasin haka.."

Haidar da izuwa yanzu ya fara fusata da abinda I'liyas yake ce mai, cikin fushi yace
"to ai bakasan wani abu ba! duk duniya babu wanda nake so yace Nurul aini tana da kyau, hakan da ka faɗa shine daidai, dan da ace cewa kayi tana da kyau to Wallahi da zan iya jin haushin ka, amma da ka faɗi akasin haka naji daɗi sosai, ni kaɗai nake so in yabeta kuma naga kyawunta.."

I'liyas yace "lalle kam."

"To da kake cewa ma na kasa sanin dai-dai da rashin sa kuma, to ai saika faɗa min mai na aikata na rashin daidai ɗin.."
Numfasawa i'liyas yayi sannan yace
"Gaskiya baza ɓoye maka ba, kai abokina kuma mai faɗa min gaskiya idan nayi kuskure, ka auri jinsin da ba naka ba kuskure ne abokina, ka killace ta, ka hanata kula kowa, ka ƙi bari jinsin ta ya aure ta, ya kamata kasan cewa hakan da kayi kuskure ne abokina, lokaci yayi da zaka farka daga barci da kake ka fita a rayuwar ta haka nan, ka barta tayi au...."
Wata gigitarciyar tsawa da Haidar ya daka mai Saida gurin ya amsa haɗe da bada wata iriyar girgiza, ba shiri, i'liyas yayi shiru daga nasihar da yake mai, wanda hatta tsuntsayen dake gurin Saida suka tsorata da sauran wasu halittu da ke gurin....
Cikin tsantsar fushi Haidar yake cewa
"Ba ina sonta bane dan in cutar da ita, ina sonta ne da in bata da farin ciki, kuma ba ina sonta bane dan in haɗa soyayyar ta da kowa ba, haka kuma bazan taɓa jurar na ganta ta haɗani da wa ni ba..."
Idanun sa ya Lumshe da suka rine suka koma baƙiƙirin, cigaba yayi da cewa "I'liyas ina so kafin na kefta idanuna, ka ɓacemin da gani, kayi nisa da inda zan iya hangowa, muduk ka bari na ganka sai nama lahanin da har ka ƙare rayuwar ka bazaka manta da shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login