Showing 24001 words to 27000 words out of 41435 words

Chapter 9 - NAMIJIN DARE Hausa Novels Complete.txt

kowa yazo da matsalar shine dan ya samu waraka idan Allah ya yarda, samun guri kawu Salisu yayi ya ɗan raɓe anan, da haka har layi yazo kansa, Shiga cikin shagon da mai maganin yake yayi, bakinsa ɗauke da sallama......
Wani babban mutum ne a zaune mai cike da kwarjinin da kamala, da ka gansa kaga malamin addinin saboda yanayin sa kaɗai ya isa ya nuna haka, bayan sun gaisa ne kawu Salisu ya zayyane masa dukkan abinda yake tafe da shi, gama maganarsa ke da wuya malamin yace
"Ya Salam! Inalillahi wa ina ilaihir raji'un, haƙiƙa kuma kuna da naku laifin, yarinya taƙi samu mijin aure, ko kuma sai an zo yin aure abu ya lalace, ko manemin aure ya gudu, ko wani abu ya faru dashi, ko kuma ita tace bata sonshi ga alamomi nan da yawa wanda kace duk suna faruwa, to ku meyása baza kusa ayar tambaya ba.. "
Numfashi malamin yaja yana girgiza kanshi domin yaji matsalar da bai taɓa jin irin ta ba, cigaba yayi da cewa
"Kafin a raba wannan yarinyar da mugun AL'JANIN SOYAYYAR sai an sha wuya, saboda ya daɗai tare da ita, kuma ya kamata ita kanta yarinyar tasan da wanda take mu'amala, dan zata iya yiwuwa yayi amfani da ƙarfin su na al'janu yasa mata soyayyar sa, dole sai kunyi ƙoƙarin sanar da ita abinda ya aikata mata, inba haka ba abune mai wuya aci galaba akan shi.."
Haka malamin nan yayi tawa kawu Salisu bayanin yadda za suyi, da kuma basu shawarwari akan yadda za'a taimaki Ma'u, daga ƙarshe kuma ya bashi maganin da za'a ba Ma'u, nasha daban na wanka ma daban, har da wanda zata turare jikinta......
Bai iso gida ba sai wajen la'asar, kai tsaye gidan inna ya shige, inna dake zaune tsakar gida, jin sallama yasa ta amsa tana bada izinin shigowa, ganin kawu Salisu ne ya shigo a sukwane, da mamaki inna take tambayar sa "daga ina haka! Naganka kamar a gajiye."

"Hmm kede bari! Wallahi wani ƙauye naje, tun asuba sai yanzu na dawo, gashi ko abinci ban iya zama naci ba... Ina Ma'u take ne?.."
Kawu Salisu ya ƙare maganar yana tambayar.
Inna tace
"kasan ta ita ƴar ɗaki ce, ko gajiya da zama ita kaɗai a ɗaki bata yi, ni Wallahi da ma zafi bai damun ta.."

"Ai kuwa lokacin daina zama ita kaɗai a guri yazo, dan yanzu ko kwanciya zatayi da dare ku riƙa haɗuwa duka a ɗaki ɗaya kuna kwana, sannan ki riƙa sata a koda yaushe ta kasance cikin tsarki, da yawan karatun Alkur'ani, da kuma yin addu'a idan zata kwanta bacci, yanzu ga magani nan na karɓo mata, malamin yace INSHA ALLAHU za'a dace..."

Cikin murna inna ta karɓi ledar magani, yayin da take ƙara ganin girman kawu Salisu a idanun ta, dan shi ɗin mutum ɗaya ne tamkar da dubu, yasan takan riƙe zumunci da amana a zuciyar ta kawai addu'a take ta faman zuba masa......
A fili kuwa rasa maima zata ce mai tayi dan ta rasa da wani harshe zata mai godiyar abinda yake musu, a hankali inna tace
"Salisu a koda yaushe kana kula dani da ƴaƴana kuma hakan bai taɓa gajiyar da kai ba, na rasa da wata kalma zan yi ma godiyar abinda kake mana, koda mahaifinsu yana raye iyakar abinda zai mana kenan, Allah ya jiɓinci lamarinka a ko ina..."

Girgiza kai kawai kawu Salisu yayi sannan yace

"Adda Hajara kenan! Ni kaina nasan ina da tabbacin cewa, da ace nine na mutu yaya yake raye to zai yiwa iyalaina fiye da abinda kike ganin ina muku, ƴaƴan ki ƴaƴana ne suma babu wani bambanci, dan haka ki daina damuwa..."

Bayanin yadda za'ayi amfani da maganin ya mata, sannan yayi kiran Ma'u yana ce mata "ki tabbatar duka wannan maganin kiyi amfani dashi Yadda ya dace, kuma wallahi naji labarin ba kyasha, ko akasin haka sai ranki yayi mummunan ɓaci.."
Amsawa da "to kawu." Ma'u tayi tana mamakin maganin meye kuma aka kawo...
Yana fita inna ta jiƙa maganin da Za'a sha a kwano, bayan ya jiƙu taba Ma'u tasha tana
cewa
"kiyi bissimillah.."
Karɓar maganin Ma'u tayi takai bakinta tana ambaton sunan Allah....

Haidar kuwa! A daidai lokacin da Ma'u zata sha maganin nan, lumshe idonsa yayi, dan ganin wani kalar maganine ake bata, dama aduk lokacin da yake so yaga wani abu, da ya lumshe idonsa zai gano ko meye...
Ya ɗauki ƴan sakkani idonsa a rufe, daga bisani ya buɗe su cike da ɓaci rai, dan gaba ki ɗaya idanuwan sun canza kala, da niyar zubar da maganin ya tankwaɓi hannun Ma'u, kufcewa kwanun maganin yayi daga hannun Ma'u, da sauri inna tasa nata ta tare, tana aikawa da Ma'u wata iriyar harara tace

"Da mugunta zubar da maganin zakiyi koh, bayan kina kallo duka na jiƙe, to ai saiki tashi ki ɗauko ƙaramin kofi na ɗiban Miki Kisha.."
Tashi Ma'u tayi ta ɗauko kofin, zuba mata inna tayi ta bata, Sha take tana ya mutsa fuskarta, kwata kwata maganin bai mata daɗi ba, kawai dan ba yadda zata yi ne dole sai tasha, ko minti ɗaya batayi da sha ba ta amayar dashi, inna tace ajedai tunda kin sha....


Shi kuwa Haidar da shi yasa Ma'u ta amayar da maganin, amma duk da haka Saida wani ya tsaya a cikin ta, tashi tsaye yayi ciki fushi yana ambatan sunan i'liyas, a cewar sa shi ya jamai wannan bala'in, gashi ana banka mata wasu banzayen magani, rufe idonsa yayi yana binciken inda i'liyas yake, da ƙyar ya gano asalin inda i'liyas ɗin ya ɓoye, ware idanuwan sa yayi yana murmushin mugunta, sannan ya furta a fili "I'liyas gani nan zuwa gare ka.." ya faɗa yana ɓacewa......
Bai bayyana a ko ina ba sai a wani tsaunin fararen duwatsu, gaba ki ɗaya gurin cike yake da wasu duwatsu manya manya manya, wanda yafi ko wanne girma HAIDAR ya nufa kai tsaye, ko da yazo bakin ƙofar wasu samudawan dakaru na gani tsaye a bakin ƙofar, suna gadin ta babu wanda ya isa ya kyata wannan gurin sai wanda suka aminta dashi.....
Wannan gurin kuwa ya kasance mallakin Sarkin malamen al'janu, dukkan wani ilimi na addini da na rayuwa har ma da dubarun da al'janu, suke dashi shi yake koya musu haidar ya kasance ɗaya daga cikin ɗaliban wannan malamin aljani, wannan dalili yasa i'liyas yayi tinanin zuwa gurin, dan Haidar yana matuƙar jin kunyar aikata wani abu a gaban malamin, kuma yana jin maganar sa fiye da iyayen sa.......
Shiga gurin yayi kai tsaye ba tare da sun ce mai komai ba, kasancewar shi ɗin sananne ne a wajen, haƙiƙa zan iya cewa cikin yafi waje girma dan halittun dake gurin nan Allah kaɗai yasan yawan su, hango iliyas yayi zaune yana koyawa wasu yaran al'janu karatun Alkur'ani, kasancewar malamin baya nan ya tafi umara, ganin Haidar da i'liyas yayi ba ƙaramin tsorata yayi ba, baisan lokacin da ya miƙa tsaye ba yana kallon sa, rai a haɗe Haidar yace
"ina so zan yi magana da kai, inda halin haka.."
Haidar ya faɗa yana yin gaba i'liyas da gabaki ɗaya ya gama tsorata da lamarin Haidar, da ƙyar ya aro jarumta yasa wa kansa, gudun kar Haidar ya gano ya tsorata da shi, binsa yayi a baya yana addu'ar Allah ya kuɓutar dashi daga sharrin Haidar........
Wani guri da babu kowa nan HAIDAR ya tsaya tare da juya bayansa, iliyas da ya ƙara so cikin ƙarfin hali yace
"gani.."
Saida Haidar ya daɗai bai ce uffan ba, sannan yaja numfashi yace
"I'liyas...! Me na aikata maka, kuma meye ribarka, da har zaka je kaci amanata..."

Shiru i'liyas yayi yana girgiza kai dan bashi da bakin da zaiwa Haidar magana kuma duk abinda zai cemai, bazai taɓa fahimtar saba.....

Cigaba Haidar yayi da cewa
"Gashi a dalilin maganar da kaje ka faɗa, sun fara ɗura mata wasu banzayen magunguna, nidai nasan wannan maganin da suke bata babu abinda zai sauya Dan yanzu ma na fara sonta, amma abinda nake so kasani, Ma'u tana da cikina, na tsawon wata ɗaya da sati biyu, kuma muduk suka ci gaba da bata wannan maganin, zai iya barar mun da cikina, kuma na rantse da Allah cikin nan ya bare kayi kuka da kanka, domin duk abinda nama kai kaja, kuma shi kanshi wanda ya bada maganin ma bazan ƙyale shiba, bare kuma kai da ka kasance kaine sila..........✍️








*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*











~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/15, 1:46 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*41 & 42*







_____________I'liyas kuwa dake tsaye yana kallon Haidar, kasa furta komai yayi, dan yana da tabbacin indai yayi magana, to zai iya ƙara tunzura Haidar, shiyasa yayi shiru, har ya gama banbamin sa ya tafi.....


★★★
Yau Suraj tun safe yake shirye-shiryen zuwa batsari, kasancewar Daddynsa yace yana son ayi auren akan lokaci, kawai idan zai koma U.K sai ya wuce da matar sa....
Cikin wani yadi fari ya shirya, kayan sun matuƙar karɓar sa, dan ba ƙaramin kyau yayi ba, wata baƙar hula ya ɗora a kansa, kasancewar sa fari, sai hakan ya ƙara fito da asalin kyansa, gaba ki ɗaya shigar baƙi da fari yayi dan hatta takalmin sa da agogonsa baƙaƙe ne.....
Fitowa yayi yana zuba ƙamshi, kai tsaye gurin mommy ya nufa dan ya sanar da ita tafiyar sa, mommy dake zaune tana kallo a T.V, hango Suraj da mommy tayi addu'a kawai take a zuciyar, bata son lokacin da a fili ta furta

"fa subhanallahi ahassanal kali qin."
Ƙarasowa yayi haɗe da tsugunnawa, mommy ya yiwa sannu sannan yace

"Na shirya mommy! Ni zan wuce, sai na dawo..."

Mommy da fara'ar ta tace
"to Allah ya kai ka lafiya, Allah ya kare ka daga sharrin masu sharri, kuma Allah Ubangiji ya baka nasara akan duk abinda ya kasance alkairi a gare ka.."
Amsawa yayi da ameen yana matukar jin daɗin addu'ar da mommy tamai, har ya tafi yana jin nishaɗi a zuciyarsa.....
Saida sukayi tafiyar waje awa ɗaya da rabi sannan suka ƙarasa, kasancewar akwai ƴar
tazara sosai tsakanin cikin Katsina da kuma ƙaramar hukumar ta batsarin.......
Darek wajen aikin su kawu Salisu yayi, nan suka taho tare zuwa gidan su innan...
Kawu Salisu ne ya fara shiga yana cewa
"bari nama iso koh.."
Ya faɗa yana shigewa, samun inna yayi a ɗaki a zaune, labarta mata zuwan Suraj yayi, sannan yace mata
"yana zaure ma a tsaye.."
Riƙe haɓa inna tayi tana cewa
"Wallahi har ga zuciya ta, ina farin ciki da zuwan Suraj! Saidai wani ɓangare na zuciya ta yana fargabar abinda zai iya faruwa dashi, sakomakon auren Ma'u da yake son yi, wallahi ina tsoron wani abu ya sami wannan ɗa.."
Jan numfashi kawu salisu yayi sannan yace "Haba adda Hajara! Komai fa kika ga ya samu bawa, to dama rubutacce ne a wajen Ubangiji, karki jingina hakan da wani abu kedai kawai kiyi fatan alheri.."

"Uhmm! Uhmm!! Uhmm fa, Salisu ina ga kawai ka shigo da yaron nan, in mai cikakken bayanin abinda ke akwai, in yaso sai muji daga bakinsa..."

Fita kawu Salisu yayi ya shigo da Suraj ɗakin inna, bayan sun gaisa ne inna ta fara mai bayanin abinda yake wakana.....
Ma'u dake tsugunne tana wankin under wear's, ganin omon da take wankin ya ƙare ,sai tazo wajen window inna, dan ba'a rasa omo ko sabulu a gurin, jin da tayi inna ta ambaci masoyinta yusif, yasa ta tsaya taji mai ake cewa.....
Dafe ƙirji Ma'u tayi tana magana a hankali, "Haidar dama kai ka kashe min Yusuf ɗina,? dama kaika Hanani nayi aure kamar yadda kowa yake yi,? mai na aikata maka?...."

Shi kuwa Suraj ganin inna ta gama bayanin ta, yasa ya saki murmushi yace.
"Babu wani halitta da ya isa ya cutar da wani halittan, face Allah ya riga da ya rubuta a kundin ƙaddararsa, so! ni abinda nake so kusani, suma sauran Allah ya rubuta ƙaddarar cewa a ta dalilin haka, wani abu zai faru dasu, wallahi inna! Yanzu da kika bani labarin abinda ke faruwa da Ma'u, sai naji duk duniya babu macen da nake so sama da ita, ada na zone saboda umarnin mahaifina, amma daga yanzu duk zuwan da zanyi zazone bisa matuƙar son da nake mata, kuma insha Allahu nine mijin ta, inna ki daina damuwa, Allah ba zai taɓa barin wani ya aikatawa bawansa wani abu ba, kuma idan wani abu ya faru dani ki ƙaddara Allah ne ya ɗoramin....."


Inna kawai murmushin su manya tayi, tana wa suraj fatan samun nasara a rayuwar sa...

Ma'u dake tsaye a bakin window, kasa motsawa tayi musamman da taji kalaman da suke fitowa daga bakin suraj, wani girman sa da ƙimarsa taji suna shiga cikin zuciyarta, a ranta ta ayyana.
"lokaci yazo da zan rabu da kai Haidar, in fuskanci rayuwar da ta dace dani, in rabu da zalunci da kake min, kuma kana fakewa wajen cewa kana tsananin soma.."
Ɗaukar omon tayi ta ƙara gaba abin....

Fitowa inna tayi tsakar gida, tabar kawu Salisu da suraj a ɗaki, suna cigaba da tattaunawa sai da suka gama sannan kawu Salisu ya fito yana ce mai
"bari a turo maka da ma'u.."
Ya faɗa yana fita daga ɗakin......
Inna kuwa dama tunda ta fita ta samu ma'u, akan taje ta ɗan kimtsa ga baƙo tayi, babu wani musu ko ɓaci rai Ma'u ta shiga ɗaki dan kimtsa wa, ba ƙaramin daɗi inna taji ba, har tana cewa lalle maganin malamin nan yana aiki, har an fara samun sauyi....

Ta ɓangaren Ma'u kuwa, abin ba haka yake ba, dan har wani duhu duhu take gani, ga wani azababben ciwon kai dake sauko mata lokaci ɗaya, kawai dai dauriya take dan yanzu tana jin lokaci yayi, wanda zata yi fito na fito da haidar......
Ɗaukar hoda tayi da niyar ta shafa a fuskarta da ɗan man leɓe, madubi ta ɗauka, maimakon taga fuskar tata ko hasken madubin, sai taga gaba ki ɗaya yayi baƙiƙƙirin, ajje shi kawai tasa hijab ɗin ta....
Tana fitowa inna tace ki ɗan shigan mai da ruwa ko, da to ta amsa, sannan ta ɗauko wani sabon jug da inna ta siyo, ruwan randar inna ta zuba mai sanyi, ta wuce ɗakin da yake a zaune.......

Shiga tayi ɗakin bakinta ɗauke da sallama, samun sa tayi zaune a kan dardumar tsakar ɗakin inna, kansa sunkuye yana daddanna wayar sa, Ma'u a ranta tace shi kullum yana danna waya ko gajiya ba yayi, ɗagowa yayi suka haɗa ido, da sauri Ma'u ta sunkuyar da kanta tana ambaton sunan Allah, jin jikinta yana karkarwa, bata san meyasa ba ko sunan Suraj taji an ambata, sai taji jikinta yana tsuma.....

"Are you ok?."

Muryar sa Ma'u taji tana huda dodon kunnen ta, cikin in ina Ma'u tace

"yeh... Yeah.."

Yace "kin tabbatar.."

Girgiza kai Ma'u tayi, sannan ta ajje ruwan haɗe da tsiyaya mai a ƙaramin kofi, ganin hannun ta Suraj yayi yana rawa, dan saura kiris ta zubar da ruwan, karɓar yayi ya ƙara sa zubawan, yana kai ruwa bakin sa, kaɗan ya kurɓa ya ajje kofin....
Sautin siririyar muryarta ya tsinkaya tana cewa

"ina yini..!"

"Lafiya ƙlau.." Suraj yace a taƙaice .
Shiru ne ya ratsa gurin kowa yana tinanin mai zaice, can kuma sai Ma'u tace

"Ya su inna.."

Dariya Suraj yayi sannan yace

"Mu bamu da inna saide mommy.."

Taɓe baki Ma'u tayi tana cewa

"Amma ai duk ɗaya ne ko.."

"Eh mana! Sosai ma."

Shiru ne ya ƙara ratsa gurin, dan har Ma'u ta gundura da zaman kawai Allah Allah take ya bata dama ta wuce, ji take kamar tana zaune a kan ƙaya, bata yi aune ba taji muryarsa yana cewa

"Shekarar ki nawa..?"

Ƙara maimaita tambayar Ma'u tayi a ranta, tana cewa ko ina ruwansa da shekaru na, ciki ciki tace

"Ashirin da tara.."
Gyaɗa kai Suraj yayi yana cewa
"Anya kin kai haka kuwa, Ni kallon ƴar 19 nake.."

Ma'u kuwa da take da shegen son girma, jin ya maidata ƴar sha tara, a zuciyar ta tace ji kuma wani ranin hankalin, amma a fili sai tace

"Uhmmm!."

Cigaba yayi da cewa

"matakin karatu fa! Ina nufin a ina kika tsaya.."

Cikin gajiya da amsa tambayoyin nasa ma'u tace

"Secondary school.."

Yace "kuma kina da buƙatar ki cigaba ko kuma kawai hakan ma ya isa.. "

A hankali Ma'u tace "ina so mana.."

Cigaba yayi da janta hira tun Ma'u tana ɗan nuna rashin sabo, har tazo ta sake dashi.....
Dazai tafi kuwa ɗayar wayar dake hannun sa, ya bata a cewar zasu riƙa gaisawa ta cikin wayar......✍️








*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*











~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~




[6/17, 10:54 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login