Showing 39001 words to 42000 words out of 59012 words

Chapter 14 - THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA) by Queen Mahirah.txt

24 Sep 2025

2145

abun yazo da sauki,
don tana iya yin abubuwa daa yawa kamar su karatu cin abinci da kanta da sauransu...,
Dr yace brain din yana da bukatar hutu ne in akayi sa'a in just 5month memory dinta zai iya dawowa, 2 to 3 weeks kuma zata iya komawa kamar kowa,

sabanin yanzu da komai sai ance tayi kafun takeyi ayanzu bata da maraba da yarinya yar shekara 9,

kai zaka mata tarbiya ka daura ta ahanyan daya dace mastayinka na mijinta, kuma ban ce ka zalince taba dan ku maza sai ahankali"

shi de shiruu yayi kamar ruwa ya cinye shi, yana ta juya magan ganun nata a brain

dinshi maida kallonta tayi ga Zawjatul Ameer da tayi lubb ajikinta tana bacci kafin ta dago tace

" zo ka dauketa a hankali ka kaita dakina ka kwantar da ita, ka kuma rage mata wannan uban kayan da ka lafta mata ,"

bai ce komai ba sai mike wan da yayi ya zo ya dauketa in a bridal style yayi hanyan wani kayaceccen stairs mai shegen kyau wanda aaka shinfida masa wani hadadden carpet zaka ranste da zinare akayi stairs din stabar walwalin da yakeyi da daukan ido 👀.

tafiya yake cikin nutsuwa wani daki ya nufa wanda da alama shine dakin Sultana Najda da mamakina ni Queen Mahirah yana zuwa kofan ta bude da kanta ya shiga yana shiga ta rufe kiriff.

cikin hadadden dakin ya karasa wanda yasha Royal blue and golden furnitures, karasawa yayi gaban tafkeken gadon dake lullibe da labule ya kwaantar da ita,
ya kai akalla 2min yana karewa cute face dinta kallo maganan da Mima ta fada mishi ne yake dawo mishi brain dinshi,
har ya juya zai tafi ya tuno da abinda Mima tace sai ya fasa ya dawo,
zama yayi akusa da ita ya kai akalla 50sec yana tunanin ta inda zai fara cire mata wannan uban kayan jikin nata ganin yadda tayi cuddling a guri daya kamar cat,
dogon numfasahi yaja ya gyara zamansa akan gadon ya masto daf da ita yamika hannunshi ajikin ta yadan bude hannunta ya cire bottle din jacket 🧥 din wani dogon numfashin ya kara ja dan baisan ta inda zaai fara cire mata rigan ba

mastowa ya karayi daff da itaa ya dago kanta ya kwantar ajikinsa atakaice da kyar ya cire wannnan rigan dan ba karamin yaki suka yiba sai cukuikuyeshi takeyi kamar zata koma caikinshi,

yayi mamakin yadda bata tashi daga baccin ba kodai har da maganin bacci ake bata ne tunda yaji Mima tace anaso brain dinta ya huta,

ajiye jacket 🧥 din yayi agefe ya fara tunanin yadda za'a cire sauran,
veil din da aka mata rolling dashi ya fara cirewa gashinta da aka tufke ya ware wani sassanyar kamshi ke tashi daga ciki tsayawa yayi yana karewa tulin gashin nata kallo wanda yake baki wuluk dashi,
hannunsa yasa ya shafa gashin nadan wani lokaci kafun ya maida hankalinshi ga alkebban jikinta bai shaa wiya gun cire alkebban ba,

kyak'kyawan surarta ne ya bayyana wanda yasaa shi dauke wuta na wassu mintina, dakyar ya haadiye yawun wahala ya kauda kanshi gefe wani lallausa filo ya jawo ya dagota da niyan kwaantar da ita,
anan ne kidan ya canja salo don chakumoshi tayi ya fado kanta rufff
waani kukan wahala ta sake don ya mata nauyi aka,
jiki ba karfi ya mike da kyar ya jingina kansahi ajikin gadon ya lumshe idonshi.

a gaskiya an gama da rayuwarsa ayau kadai ji yake kamar kanshi yayi blowing, yanzu ahaka zai cigaba da zama da yarinyar nan yayi ta mata jegon jaka,
gaskiya ba'a masa adalci ba ya kai 5min yana ta karanta wsikar jaki kafun ya yayi kokarin jan kanshi ya sauka daga kan gadon,

ko juyowa baiyi ba bare ya yayi kuskuren ganinta ayanzu ma shi kadai yasan mai yakeji,
yana zuwa bakin kofa sai ga Sultana Najda na shigowa cak ta staya ta kare mishi kallo ganin yadda ya hargiste idonshi yayi jaaa gaba daya ya canja kaman ninshi wani dummm zuciyanta ya bada da sauri tayi cikin dakin
hango ta da tayi tana sharar baccinta tane yasa taji relief,

shiko kafun ta juyo ya fece dan ya stargu da kallon da take mishi, murmushi tasaake ta jijjiga kai ta karasa bakin gadon da kamar anyi yaki ahankali tace

"lalle ko gyara yayi kyau,"
saide tana mamakin yadda yarinyar take a gyare stafff don tun farkon zuwanta inka ganta zaka ranste amaryace don yadda fatanta ke glowing ta bangare da dama a gyare take hakan yasa tafara contemplating anya ma bata da aure,

bata yadda ba sanda tasa gyne Dr ta duba ta tabbatar mata da she is still virgin kaafun hankalinta ya kwanta.



NIGERIA {KANO STATE}

Wata hadaddiyar shararriyar farlo ce mai stari irin na turawa black and white ne colour combination din farlon,

ba wani babba bane dan dai dai ne mai cike da kayan alatu da more rayuwa ,
ba abinda ke tasahi sai wani sassanyar kamshi da sanyin A\C wanda ya kara kayata farlon,
babu karan abinda yake tashi a farlon sai na A\c da kamshin dake tashi,

wani halitta na hango zaune bisa daya daga cikin sofa na farlon ya jingene kanshi jikin sofa yana sanye da farar jallabiya,

fari ne tas babu digon baki ko kadan ajikinshi kyak'kyawane na ajin farko wanda ko kyau ya ganshi sai ya sara mishi ban cire stammanin ya hada jini da Annabi yusuf ba,

a iya tarihin rayuwata ban taba ganin halitta mai kyau irin wannan ba.

fuskarsa yana shinfide da hadaddiyar man's pride dinsa baki wuluk mai stansti da daukan hankali, wanda ya kara fidda stanin kyansa da kwarjininsa,

hancinsa tamkar kara aka staga yayi dai dai da face nasa sai kasancewarta ba katuwa ba siriri ne dan dai dai,

idonsa dake aalumshe da zararan eyelashes dinsa da kuma well shaped eyebrow dainsa wacce tamkar shi ya saita abunsa,

lip dinsa so cute dashi pink colour, hmmm abun sai wanda ya gani don ba'a cewa komai don Allah yayi halitta anan dana kare masa kallo na hango stanstan izza da kwarjini atattare dashi,

kirar halittan sa da surar sa yafi karfin yaro a murde yake gashi yana da stayi kana kallonsa kasan ba karamin dakakken namiji bane,

gashin kansa baki wuluk dashi mai tarin yawa da stansti.

lips nashi na mosti ahankali wanda da alama tasbihi yakeyi, zarazaran finger dinsa na aikin bautawa mahaliccinsa wanda ya zauba masa kyak'kyawan halitta,

karan takalmin dana ji ne yasa na maida hankali na kan mai tafiyan masha'Allah hakika babu abun bautawa da gasakiya sai Allah, godiya da yabo sun tabbata ga ubangijin da yayi wannan kyak'kyawan halittan.

wani hadadden Giant handsome ne fari tass,

yanaa sanye da unifoam na Navy wanda yake white colour ajikin rigar dagaa bangaren dama akwai inda aka rubuta CAPTAIN FUDHAL,

unifoam din yayi matukar amsar sa ya kuma fidda murdadden surar sa mai firgitar da abokan adawansa,

idonshi sanye da dark space cute lips dinsa sai kyalli yakeyi,
pointed nose dinsa ya kara wa face dinsa kyau,

face nashi kewaye da bakar sumarsa mai sheki,
{wanda aka fi sani da saje}
da daukan idon mai kallonta da mai karatu,
ya karawa face din nashi kyau sosai,

haka gasahin kansa yaa sha mayuka sai sheki yakeyi gashi dayawa ga stansti ,

hannunsa dauke da hulansa, ya cigaba da tafiyaa cike da isa da takama face nashi babu annurin fara'a ko kadan sai de hakan bai sa yayi muni ba sai wani kyau da kwarjini daya kara masa ,

tafiya yake tamkar zaki mai shirin baza taro har ya iso cikin farlon agefen wannan farin halittan ya zauna yaja dogon numfashi cikin husky voice nashi yace

" how are you feeling"

ahankali ya bude snake eyes dinsa ya zuba su a fuskan Captain Fudhal wanda shima alokacin ya cire dark space din sa ya zuba mishi lion eyes nashi,
bai ce komai ba ya lumshe idonshi,
daga fannin Captain bai damu da rashin amsan nashi ba don dama yasan ba lalle ne ya samu amsa ba,

alama yayiwa house maid da hannu daya ajiye tire din abincin dake hannunsa akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login