Showing 45001 words to 48000 words out of 59012 words

Chapter 16 - THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA) by Queen Mahirah.txt

24 Sep 2025

2146

ji dashi ya hanashi ko bude lumsassun idonshi,

bare yaga malamin har ayi tunanin ya gyada shi,

kuma bawai wai gurin shi na mishi ciwo ba a'a kawai hali da miskilanci irin nashi,

shi maganan nasu ba takura masa sukayi jinsu yake kamar stustu na yawo a brain dinshi,

maganan Fareed ne yasa shi bude idonsa dake alumshe

" ya jikin naka Tweeny "

gyada mishi kai kawai yayi, "wani guri yana maka ciwo ne ,"

still kan ya kara jijjigawa alaman ba abinda yake damunsa ,

"zaka ci abinci ,"

" tohhh mamansa kabi ka isahi mutane da iyayi ka damu dashi shine kaje kayi zamanka ka barshi shi kadai"

murmushi yayi yace " kai da kake baban shi ai gaka tare dashi ko,

tohh mai ne ne damuwarka da inda na staya ya fadi haka yana zabga masa harara ,

mutum sai shegen hancini na fada maka uziri na amma gaba daya kanka ya gagara dauka stabar dusa yayi yawa aciki,"

Fudhal stabar bacin rai idonshi har kan kancewa yayi yace

" ani kake cewa dusa yayi yawa akaina "

murmushin ya kara sakewa yace "a'a dana bayanka nakeyi "

"you are trying me Fareed wallahi kamai da hankalinka dani ko in fasa kanka da bindiga"

"bismillah Captain Fudhal ga fili ga mai doki ,

dan renin wayo kai daa kake sojan ruwa ma akwai kaskan cecce irinka,

kasan ni ba sa'anka bane dube ni dakyau soja ne ni bama na kasa ba na sama inka manta da COMMANDORE FAREED kake magana bama commander ba commandore,

ba kuma captain ba in maganan bindiga kake kasaan ni ba staran ka bane awannan fannin ka mai da hankalin ka ko insa a ma ruwan alburushi daga sama,"

awannan lokacin Fudhal ya yayi zafi harya tafasa har ma yafara konewa 😠 har wani jaa fuskanshi yayi abinka da mai saurin fushi,

har wani hayaki ne yake fitowa daga hancin shi ya mike a fusace yace

" zaka san daawa kake yau, irrrr in ka isaaa yi mu gani sojan ruwa kawai,
Fahreen yace "

"will you 2 shut up please,"

stittt sukayi hankalinsu ya dawo kanshi "why are always acting like small children,

sai yelling kukeyi a kaina so kuke ku kashe nine, eyyahh,"

" sorry Tweeny baza mu karaba kayi hakuri, ,"

stuka Fudhal yaja yace "sai ka tashi kaje ka shirya kayan da za'ayi tafiyan dasahi ai "

harara ya wulla mishi yace ""dama ko baka fada ba zanyi ai,

kuma karkayi expecting zan hada da kayanka wallahi,"

Fudhal yacea "inka kuskura dirty hand dinka ya taba cloth dina wallahi sai na fasa maka kai"

"michewww karyar banza "

ba tare daya staya ya saurari abinda zai ce ba ya mike ya shiga yayi hanyan wani stairs ya hau wani daki ya shiga wanda shima black and white ne komai na dakin ,

directly gaban wardrobe ya wuce ya bude ya dauko wani travelling bag ya rufe ya kara bude wani drawer inda kaya ne kala kala ko wanne da ban garensa inner wears ya fara diba kafun ya dawo ya dauki kayan sawa,

yawanci jallabiya da 3quatre ya diba masa da t-shirt mara nauyi sai da half jamfa wanda basu ma kai kanan kayan yawa ba,

bayan ya gama da nan perfumes ya koma dibowa sanda ya dibo akalla kala biyar masu masifaffen kamshi kafun yazo gun foot wears shima ya dauka wanda za'ayi amfani dasu,

cikin kankanin lokaci ya gama hada kayan tasss ya dawo farlo ya samesu yadda ya barsu bai ce kala ba ya nemi guri ya zauna,

wani dan madanni ya lasta cikin kan kanin lokaci sai ga wani soja ya shigo cikin farlon cike da girmamawa yayi saluting nasu, Fareed yace

" gobe zamuyi tafiya inaso ka hada mana convoy cikin sirri ,

bana so kowa na garin kano yasan zamu bar gari kamar yadda ba wanda yasan muna nan,

kuma ko bayan mun tafi kar ko da wasa kowa yasan mun zauna a gidan nan "

okayy sir angama

" send me your account number"

washe baki yayi yace okayy sir bai dena washe hakora ba har ya baro farlon don yasan ba karamin abin alkairi zai samu ba shiyasa yakeson Commandore Fareed akwai kyauta gashi faram faram bashi da girman kai,

yana da mutun ta kowa yana ganin girman dan Adam duk da sun kasance yan uku ne wato TRIPLET,

amma sam halayyar su ya ban ban ta kaf cikinsu Fareed ya fisu mutunci duk da shima Fudhal yana da mutunci kuma bayaa rena dan Adam dukan suma basa rena na kasa da su,

sai de suna da ban bancin halayya shi Captain Fudhal yana da saurin fushi kuma bashi da fara'a sanan bayason reni,

baya ga wayanan bashi da wani aibu in zaka bishi ayadda yake tabbas zaka more shi sosai don bashida kyashi,

shiko MAJOR GENERAL FAHREEN shi miskili daya fi mahaukaci ban haushi ,

shi zama dashi sai mai hakuri da juriya sanin halinsa sai makusancinsa duk bala'inka baka isa kasan mai ne ne halinsa ba,

shi tamkar maciji yake yana da wiyan sha'ani da rashin yadda,

shiyasa ake masa lakabi da SNAKE EYES,

idanunshi kaifi garesu yakan rudar da makiyansa dasu ya gigitar dasu da zaran ya shiga taro tohh hankali duk kansa yake komawa,
. ya stole idanun mutane dayawa duk da shi bai damu da kowa ba baya shiga sabgar kowa,

sai de mutane kullum cikin kawo mishi hari suke daga gida da waje kasancewar matashi mai babban makami gabaa daya shekarunsu 29 ne aduniya amma ya taka hanyan da manya dayawa basu taka ba,

ya shiga inda manya da dama basu shiga ba ya samu nasarori da dama a rayuwarsa bashi kadai ba hatta ga yan uwanshi haka ne sai de shi ya fi stole idon kowa ,

kasancewar sa wanda zai gaji sarautar masarautar kano wanda yake daya daga cikin manyan masarauta a fadin duniya.


washe around 7:30 suka kama hanyan Rugar hardo bello a bangaren Fahreen ya gagara misalta awani yanayi yake ciki,

yau wani irin farin ciki yakeji da anna shuwa da bai taba ji irin shi ba har wani annuri ne na farin ciki ke tashi daga ko ina na jikinshi,

su kansu sunyi mamakin ganin shi ayau ganin da karfinsa don shi yayi wa kanshi komai hatta abinci yaci sosai,
sunyi mamaki kwarai da ganin yanayin nasa suna de fatan Allah sa hakan ya daure Allah kuma ya bashi lafiya,

don su kansu sun gamsu sun kuma aminta da malami duk da basu san shiba.

karfe 8:00 suka isa Rugar Hardo Bello.



RUGAR HARDO BELLO { KANO STATE, NIGERIA]




QUEEN MAHIRAH




🧚THE TWO LIGHT ✨{RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰}🧚
BY;QUEEN MAHIRAH
?Saturday, ?17 ?February, ?2024
10:11:24 PM

Follow this link to join my WhatsApp group and shower 🚿 me with comment and react 😁😍🤩

https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9

🧚22🧚

RUGAR HARDO BELLO {KANO ,NIGERIA}

Yau tun tashi na, na tashi cikin wani yanayin dana gagara misaltawa gaba daya bana jin dadin zuciyata wani kunci nakeji dana rasa gane na mai ne ne,

sai de na ta'allaka hakan da batar yar uwata kasance warta yau sati biyu da kwana 3 da bata amma haryanzu ba labarinta,

hmmm mikewa nayi staye dama fitowa na kenan daga bathroom nayi wanka shine na zauna na fara karanta wasikar jaki.

dressing room na nufa bayan daukan kayana danayi kamar kullum sanda na kashe time dina wajen feshe ko wani lungu da sako na jikina da humra da kuma kuleccham mai stananin kamshi,

na kuma turara jikina da hadaddiyar turaren wuta mai bala'in kamshi,

haka tulin gashina ma sanda na turare shi da turaren wuta bayan hadaddun mayukan gashi dana shafe shi dashi,


sannan na shirya cikin wani light blue jeans da white top sai kimono white da blue touches ajiki,

daure igiyan kimonon nayi sai ya bada wani ma'ana na musamman ya fidda asalin shape dina nayi das dani nayi kyau,

kaina kuwa turban nasa light blue sai white veil dina dana yafa nayi masifar kyau,

fitowa nayi daga dressing room din na wuce directly inda shoe rag yake na dauki wani hadden white designer sneakers dina nasa,

masha'Allah godiya da yabo sun tabbata ga wanda yayi wannan kyakyawan halittan ba karamin kyau nayi ba duk da banyi kwalliya ba abinka da fara kuma kyakyawa ga wani tashin kamshi da nakeyi .

Farlo na fito anan na samu Islam na jirana itam cikin nata shigar mai daukan hankali mikewa tayi tace

" muje kar muyi latti"

kai kawai na gyada mata don sam yau ban tashi da son yin magana ba,

tare muka fito harabar gidan muka wuce side din Jaddi don musu sallama shi da Innani.

da sallama muka shiga farlon muka yi sa'a mun samesu a farlo,

Innani tace a'a shalelena har kun fito" ban iya cewa komai ba sai Islam ne ta gyada mata kai,

Jaddi yace " Allah kare ya kuma dawo daku lafiya"

da Amin Islam ta amsa niko a kasan makoshina na amsa,

bayan dogon addu'a da Innani ta surfo mana kamr yadda ta saba muka kama hanya.

mun fito muka samu Auwal har ya fito da mota,

ta bangare daban kuwa sai gyara guest room akeyi duk da dama agyare yake,

haka kawai na stinci kaina da stinkewan zuciya da bansan name ba.

school ya kaimu kamar yadda ya saba muka shiga tun daga gate din school din muke kwasan gaisuwa ta dalibai da wassu malamai da ma'aikata har muka isa staff room,

bance kala ko gaisuwan ma sama sama nake amsawa,

koda muka je staff din ma ban kula kowa ba,

haka ko da na shiga class yau ba walwala su kansu daliban sun sha jinin jikinsu da ganin yanayi na duk sai suka subure.

Innani ne ta zubawa Chief ido na yan sakanni kafun tace "Sheik,"

yace na'am "Nana,"

wani dogon numfashin ta kara saukewa kafun tace " niko ka kula da yanayin Noor yau gaba daya ta subure,

ni wallahi gaba daya a storace nake da wannan lamarin kana ganin baza a samu mastala ba,

anya baza mu kware ta da yawa ba, ni inaga kamar mu mai da can Iraq din ta cigaba da zama zaifi,"

murmushi Jaddi ya sake yace " ba yadda muka iya da abinda Allah ya kaddara,

ko bangon duniya zamu kai Noorul Huda bazai hana ta shiga wannan yanayin ba sabida kaddaran tace,

ba'a ja da ikon Allah namu addu'a da fatan alakairi,

sannan kasancewar da zasuyi a tare shine kadai hanyar war ware wannan mastalan,

in ba haka ba daga shi har ita ba wanda rayauwar zata mawa dadi."

dogon numfashi Innani taja tace to "Allah zaba mana abinda yafi alkairi,"

Amin shine abinda Jaddi yace.

Wasu hadaddin mota ne na bugawa jarida sukayi parking akofar gidan Chief Imam,

motoci ne na alfarma wanda sai wane da wane ke hawanta mota biyar,

hudu daga cikinsu bakake ne daya ne kadai fari wanda yake a stakiya,

ajikin ko wani plate na motan an rubuta COMMANDORE AJ sannan ko wanne da tambarin masarauta ajiki,

ban gama ankarewa ba saida naga dan dazon soldiers sun fito sun yi kawanya a motan stakiyan,

suna cikin haka aka bude musu gate din gidan tare da basu izinin su shiga nan kuwa wannnan farar motan ta danna kanta cikin gidan bata staya a ko ina ba sai a parking space,

nan yayi parking sojojin ne suka dawo cikin gidan suka kara yiwa wannan motan rumfa suka bude cab din motan na both hannun hagu da dama cike da takama da mazan taka suka fito su biyu daga motan,

suna sanye cikin half jamfa daya fari daya kuma sky blue,

ya matukar amsar su ya fidda zallan mazantakarsu da kwarjininsu hadi da haiba,

Captain Fudhal ne ya taimakawa Major General Fahreen ya fito daga motan,

Masha'allah yana sanye cikin dakakkiyar yadi black colour wanda ya fidda zallan kyansa da kamalansa,

fuskarsa tayi fayau da ita sai lumlumshe ido yakeyi kamar mai jin bacci,

Fudhal ne ya kama hannunsa suka fara tafiya kafun Commandore Fareed ya jera musu,

suna tafiya cike da izza da mazantaka hakika Allah yayi halitta anan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login