Showing 15001 words to 18000 words out of 59012 words
Chapter 6 - THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA) by Queen Mahirah.txt
ita gida take son zuwa har suka isa Fatima ta sauka tashiga inda gonan da taimakon driver suna cikin ciran masaran ne suka hango wani mota nayin hayaki da alama ma hastari tayi ba bata lokaci driver ya karasa don bada agajin gaggawa,
suna zuwa ya bude motan ya ciro wani daga ciki wanda su kansu sanda suka razana ganinshi kamar balarabe amma sun danne hakan suka sashi a mota suka kaishi hospital na cikin rugar,
aka shiga bashi agajin gaggawa , cikin kan kanin lokaci suka dukufa akansahi don ceto rayuwarsa Allah ya yadda ya kuma basau daman hakan kasancewars mutummai sauran numfasahi adoron duniya, dakyar Fatima ta koma gida gani take kamar wani abu zai sameshi,
sanda ya dauki kwana 5 kafun ya farfado bude idonsa na fari da Fatima yayi tozali kasncewar tazo duba shi nan ta sanar wa Dr cewa ya farfado aka kuma yi masa chakeup da ikon Allah ya ware sumul sai de yaki cewa komai sai ido shima bai fiye stay wa kallon mutane da ita ba lumshe ta yakeyi yi kamar dan cordaine,
akalla ya kai 2 weeks ahalin Malam Umar na dawainiya dashi a hospital inka caire Zainab da bata kallonsahi da idon rahama karsahe saallamrsa akayi suka waucae gida dashi daki na musamman aka bashi suka cigaba da kula dashi shi mamaki suke bashi ganin basu san komi akan shi ba amma suna ta faman hidima dashi,
ya kai wata kafun akarshe a ya sanar da Malanm Umar wane ne shi da abinda yasa ya baro gida har yayi accident, Malam yayi mamaki sosai sai dea ba abun mamaki bane hasalima kadan ne daga cikin RIKICIN GIDAN SARAUTA
sunnrike shi hanu bibbiyu ya zame a musu kamar na miji da Allah abi basu ba bayan wani lokaci aka hadasahi da Fatima aure dauk da irin kananun magana da aka ringa yi agarin hatta familyn sanda aka samu mastala dasu amma Chief yayi burus da lamarin su,
nan ya nemi daya koma kasar Iraq basu hanashi ba dama acan yayi karatu kuma yake cigaban karatunshi na matakin Hand,
ya koma can da zama da Fatima har yasa ta a makaranta dama shine burinta AAllah ya azirtasu da 'da namiji suka mawa malam takwara suna kiransa da Imam ko little Imam ko kuma Faruq.
WANNAN SAHINE TAKAICECEAN TARIHIN ASALIN CHIEF IMAM DA RUGAR HARDO BELLO
Follow this link to join my WhatsApp group and 🚿 me with comment and react 😁😍🤩😘
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
END OF PAGE 7
BY ; QUEEN MAHIRAH
comment and share
🧚THE TWO LIGHT✨ [RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰]🧚
By;Queen Mahirah Idriss
?Tuesday, ?09 ?January, ?2024
11:07:10 AM
Follow this link to join my WhatsApp group and 🚿 me with comment and react 😁😍🤩😘
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
🧚8🧚
BACK TO LABARI
"Wannan shine takaiceccen tarihin asalinmu,"
inji Chief Imam yana magana ne yayin da yake fuskantar Zulaihat
"ina fata ayanzu kinsan suwaye mu da kuma yanda akayi muka hadu da dan uwanki,"
kai ta gyada alaman ehh to
"Alhamdulilah haka ake so yanzu ina bukatar sanin mai ya faru dake don tabbatar da abinda nake zargi,"
dogon numfashi taja ta sadda kanta kasa wassu hawaye masu zafi na bin kuncinta tace
"sunana ZULAIHAT BINT SULTAN IBN MUHD HABIBULLAH IBN ABDULMALIK IBN ABDULFATAH IBN ABDULJALAL,"
ahankali ta sauke wani ajiyan zuciya
[ hmm ba dole ba irin wannan suna haka kamar ana kiran register akiyama]
"sunan mahaifina SULTAN IBN MUHD HABIBULLAH IBN ABDULMALIK IBN ABDULFATAH IBN ABDULJALAL IBN ABDULJALIL wanda ya kasance sarkin kasar EGYPT,
na kasan ce 'yaaa kuma sirka ga Masarautar SUHATAJ ABDALLAH IBN MUHD KAHTER IBN ABDULMALIK IBN ABDULFATAH IBN ABDULJALAL IBN ABDULJALIL,
kuma halitta mafi soyuwa agaresu kafun faruwar wannan lamarin dayasa har iyayen dasuka haifi kyamatata suka kuma yankemun hukunci mafi muni ba tare da yin kwakkwaran bincike ba akan lamarin,
wanda azahiri kana gani kasan zancen ba haka bane ko makaho ya laluma yasan wannan abun babu kanshin gaskiya aciki,
fashewa tayi da kukan 😭daya ci karfinta rintse idonshi Othman yayi don yana shakkan jin abinda zai fito daga bakinta,
hankali ta stagaita da yin kukan da ba wanda ya hanata dan kallo daya zaka mata ka hango irin zallan kunan da take ji azuciyarta,
wanda bazai misaltuba "sun yanke mun hukuncin kisa ta hanyan jifa sun kuma yanke hukuncin kai 'yaa'yaana gidan marayu daya fi kowanne rashin galihu,"
ware manyan lulu eyes 😲nashi yayi in disbelive yana jijjiga kai dan hankalin shi ya gaza daukan abinda take fadi
"tayaya Zulaihat??
mai ma ya faru daya janyo hakan??
mai kikayi??,"
"sunyi mun auren dole auren ko kin ki ko kin so sai kin zauna dashi,
sun auradda ni a mutumin da ko a mafarki akace na aureshi sai nayi sati ban koma bacci ba,"
dan jimm tayi ta goge hawayen fuskanta ta lallausan tafin hannunta kafin ta cigaba da cewa
"bayan lokaci dana dauka atare dashi wanda ba komai acikin zaman sai bacin rai da tashin hankali,
mun dau lokaci muna wannan zaman kafun na Allah ya faru akanmu,
muka fara son junan mu Allah ya azirtamu da samun karuwa na haifi dana na farko MUBARAQ,
bayan wassu shekaru Allah yakara azirtamu da wayannan yaran dan,".
murmushi tayi ta cigaba da cewa
"alokacin da na haife su an nuna musu soyayya kamar zaa maidamu ciki,
hatta daki da gurin zama sanda aka canja mana an yi sadaka da kyaututtukan da baa taba yiba a wannan ranan idan kashigo cikin masarautarmu zaka ranste nadi akeyi dan yadda masarautar ta cika da shige da fice na jamaa,
zan iya cewa baa taba irin wannan cikan ba don wassu na cewa har da aljanun masarautar,
sun samu kyaututtuka marassa adadi da addua,
duk wannan ya faru ne aranar da suka shigo duniya ranar suna kuwa munga abin alajabi wanda ya storatar damu,
jamaa ne suka ringa tururuwan zuwa ina da tabbacin ba mutane ne kadai ba suka halarci wannan biki,
a wannan ranan aka dau ALKAWARIN AURE stakanin yar dana haifa da dan yayata,
yara sunci suna MAHNOOR DA MEHNOOR bayan suna da kwana 10 wani kishin kishin ya fara tashi wai yayan dana haifa baa gidan aurena na haifa ba,
wai su din shegu ne,"
fashewa tayi da wani mastiyacin kukan da tunda abin ya faru bata yi irinshi ba Othman kam daskare wa ma yayi azaune don he is totally speechless shi sam baya ma fahimtar abinda take fada kokadan,
" waye babansu??
waye kuma mijin da kika aura??
ya san abinda ya faru ne,"
da saninsa aka yanke wannan hukuncin????,"
Inji chief a ahankali ta stagaita da kukan nata tace
" mijina shine baban su bai san abinda ya faru ba baya ma kasar gaba daya,"
dogon numfashi chief yaja Innani tace
"to yar nan waye mijin naki a ina yake rayuwa,"
" yana rayuwa a Masarautar Suhataj Muhd Habibullah hasalima shi dan masarautar ne cikakken jinin sarauta ne,
mai ji da karfin iko ya kasance makami mai stole idon makiyansa mutum ne shi mai kwarjini baya storon kowa,
yakan taka kowa kuma ya kwana lfy dan lelen Fulani da Baba sarki fari kuma mai farin aniya ga wanda yaso mai kuma bakin aniya ga wanda ya bukaci hakan,
kallo daya zaka mata ka fahimci irin zallan kaunan data ke mishi don tini duk wni damuwa dake fuskanta ya kau sai sakin murmushi☺️☺️ takeyi akai akai
"ya kasance mutum mai zafin kishi wanda ko fita baya son nayi shi hatta mata ma kishi yake dasu muddin suka kusanci inda nake,
kaf masarautar babu wanda ya isa ya kalli koda yastan kafa na ne duk girmanka kuma duk stufanka muddin ka kasance namiji to ya haramta maka kallona,
ciki da waje ba wanda baya storonshi baa hada hanya dashi inyace zaiyi to zai yi shi soja ne mai babban makami MAJOR GENERAL MUHD KAHTER IBN ABDALLAH IBN MUHD KAHTER IBN ABDULMALIK IBN ABDULFATAH IBN ABDULJALAL,"
da sauri Othman ya dago rinannun idonshi ya zuba mata su akaci saa suka hada ido da ita murmushin karfin hali ta sakar mishi tace
"kana mamaki ko,"
gyada mata kai yayi kamar sabon wawa murmushin ta kara sakewa tace
"nima haka nayi lokaacin da akace zan aureshi i was totally speechless wanda ko hawaye na gagara yi awannan lokacin,
hadiya raina ne kawai banyi ba awannan lokacin,
amma sunce nayi musu biyayya zanga da kyau rayuwar mu zatayi albarka sun hango hakan sunce tarayyar mu zata kawo karshen abubuwa dayawa dake faruwa a wannan masarauta da yardar Allah,
sun zuri'ar mu zata kasance hasken da zai haskaka duhun daya mamaye wannan masarautar ko Mai daren dade wa sai komai ya canja,
babu wani sauyi acikin wannan tarayya ba sauyin data kawo illa tashin hankali data jefani aciki da tarin danasani na bin umarninsu danayi, wanda shi ya janyo faruwar haka,
kuka ne yaci karfinta Innani ta koma gefenta ta rungumo ta jikinta ta hau lallashinta shiko Othman yama rasa inda zai stoma ransa yaji dadi guda daya
"yahh Allah wannan wane irin iyaye ka hada mu dasu wanda basu damu da farin cikin 'yaa'yaan su ba akullum damuwarsu shine masarautar su da yadda zasu fada data,
kullum suna mana huknci batare da bin sassala ba sun manta cewa mu 'yaa'yaa ne agaresu,
sun manta cewa muna da hakki akansu amastayin su na iyayen mu suna mana hukunci kamar yadda suke wa alumman dasuke shugabanta,
suna manta cewa mastayi biyu suke dashi agaremu iyaye da shuwa gabanni,
wannan wani irin kaddara ce mai zafi haka,"
dafa kafadanshi chief Imam yayi yace "karka ga laifin su basu manta daku ba wannan kadan ne daga cikin kalubale da RIKICIN GIDAN SARAUTA fatan shine Allah ya raya haske biyu [ TWO LIGHT] ina da tabbacin su zasu yaye wannan duhun da hasken su da baya gushewa,
ku kwantar da hankalinku kuyi rayuwarku Allah yana sane daku lokaci nanan zuwa lokacin da saa zata bar hannun makiyanku ya dawo hannun ku fatan shine Allah bawa haske biyu [ TWO LIGHT] ikon cinye jarabawansu,"
Amin shine abinda kowa yace
"zan baki wassu addua ki tabbatar kina musu shi kullum da dare da safe da kema kanki akwai kuma rubutun da zansa amiki na kariya daga miyagun jinnu dan su ke bibiynki ayanzu ina da tabbacin turo su akayi su haukata ki saide Allah yafi karfinsu zamu yake su da Ayaarr Allah,
Nana kaita ciki ta huta ko sai akawo mun mahnoor da mehnoor din namusu addu,"
" Tohh"
shine abinda ta amsa dashi ita da Fatima suka taimaka mata suka kai daki aka hada mata ruwa mai dumi ta wasta tasa kayan bacci tasha magani mintina kadan ya dauketa bacci yayi awaun gaba da ita don akwai maganin bacci aciki,
suka kai yaran falon daya othman ya karba daya chief ya karba da kallo othman yake bin babyn ko baa fada ba yasan wannan jinin Kahter ne don yanayin kama na jini da sukeyi bugu da kari wannan tabo da yar keda shi a dansten hannunta wanda yake kamar gadon masarutar su ne wannan tabon don dukkansu nada shi,
to abin mamakin 🤔mai ya shiga kan Baba Sarki na yanke wannan danyen hukuncin bayan ga shaida na zahiri wanda ke nuna su cikakku yayan Kahter ne,
chief ya musu adduan neman stari ya kuma sa aka maida su suka kwanta don tunda suka tashi suka sha nono shikenan suka koma bacci abinsu,
Fatima de atakure take koda so daya tana son su hada ido ko su kebe don ta gyara kuskurenta sai de ba dama dan ta fahimci sam hankalinsa baya jikinsa ana shi bangaren kuwa bawai fushi yake da ita ba aa kawai de yana bukatan keban cewa shi kadai ne,
tabbas yana tausayin dan uwanshin
shin wani hali zai shiga idan ya dawo ya tarar da danyan aikin da iyayensu suka mishi🧐🤔??
chief ne ya kaste mishi tunaninshi da cewa
"Hamma idan sunyi arbain inaso ku koma can IRAQ da zama gaba daya dasu ko zata ji saukin abinda ke damunta muddin tana nan kuma baza su taba barinta ba tayi nisa da kasar na tabba insunga bata nan zasu sarara da abinda suke Yi ,
shine kadai hanyar samun lfy su ita da 'yayanta,"
kai kawai ya gyada mishi a wannan ranan kowa da abinda yake sakawa aranshi game da abinda ya faru kowa da abinda yake hasasowa musamman chief da ya hango abubuwa dayawa game da yaran wanda shi kanshi sanda ya girgiza da ganin hakan tabbas ya tausaya musu tun suna yan kanana sun fara fuskantar jarabawan rayuwa,
dole su dage akan yaran nan wajen musu tarbiya mai kyau da daura su akan tafarki na islama da steratar da kansu daga faduwa halaka.
wannan daren kowa ya kwana da abubuwa aranshi musamman chief da yaga abubuwa dayawa game da wayannan yaran yasan zasu tara makiya na gida da waje sai de Allah kare ya basu ikon cinye jarabawan su.
Ameen inji ni Queen 👑 Mahirah
Ku cugaba da biyoni don warware wannan kulkin Mai wiyan kulli😁
20 YEARS LATER
Assalamu alaikum sallama sallama wai ba kowa ne agidan nikam ehyehhh,
wata hadaddiyar budurwa ne ke magana cikin siririyar voice nata mai daukan sense,
tana sanye da atamfa fitted gown wanda ya amshi jikinta ya zauna a kyakkyawar surarta mai daukan hankali da nutuwar Mai kallonta da Mai karatu,
ya kuma fitar da zallan kyau da haduwa da hasken fatarta mai daukan eyes👀 da imanin Mai kallonta kasancewar sa creamy colour,
kare mata kallo nayi don ganin ta inda zan fara zayyano kyawu da Kuma zallan stari da kyan halittan da Allah ya mata,
doguwace tana da stayi saide ba zololo ba baza kuma mu kira ta siririya ba, ba kuma katuwa ko narkekiya ba zamu ce da ita yar das das mai daukan ido da sense,
fara ce sai de farinta ba irin namu na husawa ba tafi kama da na larabawa musamman na kasar Egypt ba ko digon baki ajikinta kala ce Wanda take daukan hankali ba Mai haska ido ba ko konasu, kala ne kamar Madara Wanda baka gajiya da kallonta sa kasancewarsa Mai sanyin tashi da haskaka idon Mai kallonta da Mai karatu ya Kuma Kara masa karfi don samun daman karatu ba kakkautawa👀😁,
fuskarta dauke yake da kyawawan eye balls nata masu daukan hankali wanda suke kalan toka wato grey colour suna Kuma dauke da zararan eyelashes nata Wanda which is moist as always Wanda ke lumsar da idon making them to look so damm hot and sexy,
ga pointed nose nata Wanda yake sai dai face nata👃,
da cute small pink lips 👄, that are so fetching musamman I tana magana da husky voice nata ko tana shagwaba,
wuyanta sanye yake da kyakkyawan sarka mara nauyi wanda ya kwanta a fatar wutanta ya haska sosai,
starin surar ta ko baa magana sai de muce mashaa Allah starki da yabo sun tabbata ga Allah ubangijin talikai da yayi wannan halittan, ta kasance irin matan da ake kira masu coca-cola shape kasancewarta Mai cika daga sama ga hips nata da kamar zan su akayi suna tamkar suyi magana,
halittan ne da ita Wanda ke rikitar da mata ya sasu kishi😡,
kara rankada sallama tayi ta fashe da kuka kamar wata yar shekara uku taba buga kafa akasa yayi da ko komai na jikinta ke jijjiga Yana mosti da fusga,
wata stohuwa ne ta fito daga daki har zanin ta na neman faduwa tana waya taba uwarsa Sheikh Fetel kaine ko nasan kai zaka iya turus tayi ganin ba kowa a stakar gidan da sauri ta karasa gunta tace tana zaro ido MAHNOOR 😲😲
END OF PAGE 8
QUEEN MAHIRAH IDRISS
Follow this link tojoin my WhatsApp group and 🚿 me with comment and react 😁😍🤩😘
https://chat.whatsapp.com/EPeM4KtGCoJ9mrYw1Avfow
👇
Comment and share 😁
🧚THE TWO LIGHT✨ [RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰]🧚
BY;QUEEN MAHIRAH IDRISS
?11 ?January, ?2024
12:46:55 PM
Follow this link tojoin my WhatsApp group