Showing 6001 words to 9000 words out of 59012 words

Chapter 3 - THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA) by Queen Mahirah.txt

24 Sep 2025

2156

yamawa fatima ya jiki' tace

" Alhamdulillah yayi sauki gashi har na fito ma",

"little imam how are you?,

yace" am pretty fine,
Dr how about you ?,"

"am also fine ina Dad dinka, kunyi waya ne,"

"ehh munyi yace ma yana hanya ya kusa isowa rugar nan, zai zo yaga twins din mu ai nabashi labarin su,"

murmushi dr yayi ya shafa kan shi sannan ya karasa gaban gadon patient din ya dubata sannan ya juyo ya fuskan cesu with full of hope, Innani tace

" ya jikin nata",

yace "Alahamdulillah da sauki zata ma iya tashi nan da good 3 hours nan da wa uku kenan,

sai de zata iya tashi a firgice duba da irin yanayin data shiga a fari,"

"tohhh yayi kyau Allah tashi kafadunta,"

ameen kowa ya amsa dashi inji chief karasawa yayi gurin babies din yace

" mashaallah look at them they are so pretty just like egyptians,

kamar larabawa Allah de ya saka da alkairi gaskiya ba karamin kokari kuka yi ba chief da kuka cece su Allah saka muku da jannatul firdausi,"

murmushi chief yayi yace

"kuma ai kuna kokari sosai Dr, "

"ai bamu kai kuba kudin na daban ne, Allah de ya saka muku da alkairi,"

ameen suka amsa kafin ya fita ya je don duba sauran patient,

yabar kowa da abinda ke saka wa a heart nashi baya Fatima da abin duniya ya isheta,

. ba abinda ya kara daga mata hankali sai ganin matar datayi ganin irin zillan kyan da Allah ya mata, ga wani kwarjini na musamman da daukan ido da takeyi,

in tace bata storata ba tayi karya maganan zainab ne ya fara dawo mata karde ita ne dako ita ne data shiga uku,

tasan karshen zamanta da mijinta ne yazo muddin ya kasan ce abinda take storo ne,

tohh tagama aiki ajiyan zuciya tasauke, numfashinta har wani hardewa yakeyi,

jin an dafa kafadarta tane yasa tayi saurin daga idonta taga Abbanta dake gefenta fuskarshi dauke da smile, yace

"babu abinda zai faru sai alkairi,"

itama murmushin ta kakalo ta mishi bata ce komai ba.

.
wata hadadiyar car ce mai numfashi da keta hazo, ta keto cikin wannan rugar,

a back seat wani kyakkyawan halitta ne ke zaune yana sanye da Ralph Lauren brown suit da yayi masifar amsar jikinsa akalla zai kai 35years,

sai de sam shekarun basu nuna ajikinshi ba fari ne tas Mai daukan ido da hankali, kyakyawa ne Son kowa kin Wanda ya rasa,

Fuskansa zagaye yake da hadaddiyar man's pride dinshi Wanda da gani taji naira sai sheki take Tasha gyara haka sumar kanshi acike yake tamm dayawa baki wuluk dashi mai stansti,

Pointed nose nashi ya Kara kayatar halittansa Yana Nan zattt dashi ga small redish lips nashi masu ban shaawa, Eyes nashi are sexy kamar Mai Jin bacci haka suke ga zararan eyelashes nashi Daya Kara narkar da idon, eyebrows nashi tamkar shi yayi shaping kayanshi.

Yanayin kyansa da hasken sa yasani tan taman Anya bahaushe be kuwa ganin yanayin hasken fatar shi wanda azahiri yafi kama Dana larabawa.

Kai staye baza ka kira shi da balarabe ba sannan baza ka kirashi da bafulatani ba kai staye,

sai de kace dashi HALF CASS wato ruwa biyu,

kallo daya zaka masa ka hango zallan damuwan dake shinfide a kyakyawan face nashi ga wani stinkewa da heart nashi keyi,

duk da yasaba da hakan aduk lokcin da ya sako kafanshi a Nigeria hakan kuma nada nasaba da rayuwarsa na baya,

sai de yau stinkewan heart din na daban ne yarasa mai yakeji farin ciki ko aka sinsa,

sai de yana jin wani anna shuwa na daban yana jin tamkar zai hadu da wani abu mai mahimman ci to amma mai ye shi,???

shine amsan daya gagara bawa kanshi abu 3 ne masu muhimmanci a arayuwarsa,

daga inlaw dinsa sai wife nashi da children nasa Faruq da Islam,

sai kuma mai kankat wato FAMILY nashi,

tabbas yana farin ciki zai ga 'ya'yan sa da matarsa da inlaw dinsa,

saide akwai wani abu na musamman ayau to mai ne ne wannan???,

family dinsa yasan yayi ban kwana dasu badan baisan inda suke ba ko basa raye ba aa sai dan wani dalili mai karfin gaske,

dogon numfashi ya fesar 😤kafin cikin husky voice nashi yace

"bashir,"

da sauri ya amsa yace

"su ummin little sun koma gida ne ,"

"aa"

shine abinda bashir yace" okayy to kaini hosptal din ",

"tohh"

ya amsa masa dashi direct asibitn suka wuce basu wani dade suna tafiya ba suka iso,

parking yayi a harabar hospital din ya fito da wuri ya bude mishi cab din car din ya kai akalla 5 minute kafun ya zaro kafarsa ta dama bakinsa dauke da bismilla ya kara daukan lokaci kafin ya fito gaba daya,

wani irin bugu heart nashi yayi daya sa shi rinste idon shi da sauri,

ahankali ya fara taku cike da takama da mazantaka da izza, yana tafiya tamkar yana tausayin kasan kallo Daya zaka masa kanhango jinin SARAUTA dake yawo ajikinsa ga yanayin halittansa surarsa ya tabbatar mun da cewa ya hada da larabawa,

Yanayin halitta da girman gabansa ne yasa shi cikin jerin giant don a murde yake sanadin mosta jiki da yakeyi da Kuma yanayin halittansa,

bashir ya mishi jagora har dakin da su innani suke,

daga cikin dakin kuwa wannan baiwar Allah ta farka da salati abakinta kafin ta wani razana ta fara dube dube,

ganin mutane a zagaye da ita yasa ta kara rikicewa sosai ,ta fara ambaton sunan Allah,

Innani tayi kanta daniyan mata bayani amma ina ta dira daga kan gado tana yiin baya baya tana tambayansun abu daya cikin yare hudu,

na fari FULLANCI na biyu TURANCI na uku LARABCI sai na hudu HAUSA tambaya take ina

ya'yanta?,

suwaye su?,

kara yowa kanta Innani tayi kawai ta fasa ihuu tace

"don't touch me,"

ana cikin wannan hali sai wannan mutumin ya shigo dakin da sallama aba kinshi kanshi akasa,

jin wannan voice da ko daga bacci ta tashi baza ta taba mantawa bane yasa ta juya arazane sukayi 4 eyes 👀 dashi daga shi har ita suka staya cak kowa na nuna dan uwanshi baki dauke da zance da kyar yace

"keeeee ya akayi kika san inda nake,"

itako da gudu taje ta yi hugging nashi so tight aka bar su Innani da sake baki😲🤤



END OF PAGE 3
MU HADU A PAGE 4

Queen Mahira Idriss

Follow this lin to join my WhatsApp group and shower 🚿 me with comment and react 😁😍🤩

https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9

Comment and share 😁






🧚THE TWO LIGHT✨ [RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰]🧚
BY;Mahirah Idriss
Monday, 01 january, 2024
04:48:07 PM.

🧚4🧚

Da gudu taje tayi hugging nashi so tight as if like her life defend on him ta fashe da wani mastiyacin kuka mai cike da maanoni da yawa,

kan kameshi takarayi sosai tana cewa

"am i dreaming pls in mafarki nake kar atashe ni,

i cant blieve this akace wai you were dead ina kashiga for all this long?

kabarmu cikin tashin hankali tunda ka tafi komai ya lalace komai ya baci ,"

dago da kanta tayi daga broad chest nashi tana kallon fuskanshi kallo daya zaka mishi ka tabbatar da ya shiga wani yanayi,

his eyes turn red as if like an wasta masa pepper gaba daya mood nashi ya canja

kana kallonsa kasan an taba masa inda yake masa kaikayi hannu tasa ta tallafo face nashi

tace "kayi shiru say something,"

daga can baya ne suka ji anyi gyaran murya Innani ne data gagara hakuri tayi gyaran murya dan gaba daya ta rasa mai zata fassara abinda ido da zuciyanta ke gani,

ba ita kadai ba kowa dake wannan room din hakan yake agunshi kai hatta little ma kanshi ya daure,

bare Fatima da gaba daya komai na dakin ke juya mata maganan zainab ne yake dawo mata cikin kwanyarta a halin data ke ciki kadan yarage heart nata baiyi blowing ba,

numfashinta har harde wa yakeyi Innani ne ta kara breaking silence din da cewa

"ko zaku samu ku mana bayanin abinda ke faruwa anan Hamma,"


[ haka innani ke kiransa dashikasancear sunan su Daya da yayanta ]

kokarin raba ta da jikinsa yayi dan sai yanzu ma ya tuna a ina suke,

wani ihu ta kara yi ta kan kameshi tana

"wayyo Allah na zasu kasheni kasheni zasuyi AKHIE, kataimake ni,"

ganin yadda ta riki ce ne yasa Innani dafe kirji tace

" mun shiga uku daga taimako sai abu ya zama bala'i,

mai zan gani haka baiwar Allah,
wai mai ma yake shirin faruwa ne??,

mai ne ne hakan wacece ke kin wani tukuikuye shi,"

itako kara kan kameshi tayi dan gani take kamar zaa raba su tamkar zata shige cikinshi,

Innani ta rafka uban salati tace

"mun shiga uku mai zan gani ni khadijatu matar sheiky keta hakki haka agaban magabata da ranar🌞 Allah,

kai Hamma kayi mana bayani mana ka cire mu aduhu🌚,

wannan wani irin abune agaban sirkanunka da danka uwa uba harda matarka,"

tana maganan ne cikin kukan neman magana irin nasu na stofi da gefen mayafinta take goge fuskanta ko ince ta rufe fuskanta ta fashe da kukan neman sababi,

"haba kaikuwa kar kaban kunya mana agaban matarka,"

Chief imam bawan Allah wanda tun dazu baice komai bane yayi gyaran murya yace

"Nana ya isa yi shiru,"

batare da ta kara cewa komai ba tayi shiru sai sheshsheka take Fatima ko bushewa wa ma tayi ta nemi hawayen ma tarasa Allah kadai yasan irin azaban da takeji a zuciyarta,

Chief yace "bismillah Hamma ga guri zauna,"

yayi magana ne cikin nustuwarsa da kamala,

ba musu yasamu guri ya zauna itako tamkar jela haka ta ringa binshi a baya tare suka zauna ta rungume hannunsa sai zazzaro manyan eye balls👀 dinta takeyi kamar wanda tayi araba da malaikan daukan rai

wani dogon numfashi😤 yaja yana kokarin rabata da jikinshi ta kara fashe mishi da kuka😭

"Akhie were are we,??
su din suwaye su Akhie??

batare da tabari ya amsa mata tambayan ta ba ta wani zabura cikin kaduwa bakinta har rawan yakeyi wajen cewa,

"😱my twins ina suke??
ina twins dina??
my babies,"

tana magana tears 😭na wanke beatiful and shiny ✨face nata mai daukan hankali tana jijjiga shi

"na shiga uku sun 🤯 kashemun babies dina,"

cikin muryanshi mai cike da zallan nutsuwa izza bugu da kari mulki da takama yace

"ZULAIHAT ya isa ki nustu, lets talk ki kwantar da hankalinki kinji they wont hurt you impact they were your savior, they saved you and your babies calm down,"

ahankali ta stayar da kukan nata cikin larabci tace

" Akhie a ina muke??
suwaye su ??
katabbar baza su cutar damu ba??
kuma ina twins dina??,"

" ehh Zulaihat ba abunda zasu mana ki nutsu muji komai daga garesu i will introduce them to you ido tadan ware😲 tace so you knows them,"

kai ya gyada mata yace

" ehh nasan su they are my family,"

ahankali ta maimaita kalman

"family dama bayan mu kana da wassu family ne,"

" yess they are my family bayan anyi exiling nawa s, suka jawoni jiki they show me love they even gived me there daughter,"

dan daga giranta😕 daya tayi tace

" you means sun aura maka yarsu for what reason, zasu aura maka yarsu,"

ganin yadda yanayinta ya canja ne yasa yayi kokarin calming nata down dan tabar larabcin ma,

shiko ayanda yasan halinta ba karamin aikinta bane taci mutuncin ko wani daya daga cikinsu,

" ki kwantar da hankalinki i will explain to you later,"

" ohh haka zaka ce okay ask them where the hell did they kept my babies??,"


"you keep on saying your babies a ina kika samesu,"

wani kallon tara saura kwata ta bishi dashi tace

"kai daka cemun kayi aure mai nace maka sai nine zaka hau mun wani tambaayan renin wayo,

for good 9 years baka gida kana nufin zama zanyi tayi inyi ta jiranka kenan har sai ka dawo kazo ka aureni,

ko da ka tafi ka barni ai tohh ban mutu ba na yi aure na haihu,

bari ma kaji first born nawa ma is 9 years old ga kuma twins din dana haifa in kuma bukulu zaka mun tohh ,"

tunda ta fara zancenta a yaren hausa baice mata kala ba sanin halin abarsa murmushi☺️ kawai yayi dan ta tuno mishi da abubuwa da dama wato har yanzu bata canja ba tana nan da stiwanta

" i wonder who marry this naughty girl??,"

duk azuciyarsa yake zancen kama kugunta tayi tace

" heyy Mr ba cewa nayi ka zuba mun na mujiya kana kallo naba ask them ina yarana,"

tana maganan cike da stiwa

"ZULAIHAT!!!!!!,"

dan kaurara voice nashi yayi ya ambaci sunanta

"show some respect they are my in-laws,"

" and so what concern me ina ruwana dasu har wani zaka ce sune yan uwanka,"

yanzu dajin wannan zancen yasan haushin furucin nashi taji smirk😏 yayi kafin ya juya ya fuskanci su Innani ya sadda kanshi kasa yace

"dan Allah Abba kuyi hakuri da halinta rashi fahimta ne kar abinda ta fada ya dameku,"

innani ne tayi saurin cewa

"mu ba wannan muke son jiba fada mana wacece ita,"

dogon numfashi yaja yace

"kanwata ce,"

" kan warka,"

shine abinda Fatima tace tana saukar da dara daran eye balls 👀nata a cikin nashi wani dan rass yaji ganin yadda idonta ya sauya kala ga kuma kallon data ke binshi dashi na tukuma

"ehh kanwata ce nasan ba lalle ku fahimce ni ba ko ku yadda dani ba amma wannan shine truth din

ita yar uwata ce ta jini duk da ba uwa daya uba daya ne suka haife mu ba

saide iyayen mu sun kasance yaya da kani ne,"

murmushi chief yayi yace

"mashaallah tabbas magananka na akan gaskiya ga kaman jini daya bayyana karara duk wanda yaki yadda da hakan to tabbas akwai wani boyayyen manufa daya ke dashi,"
innani tace

"kuma fa haka ne haba shiyasa yaran suke kama da islam ashe jininta ne su ai da tun fari hakan ka fada mana da bamu muku mummunan fassara ba amma itan ya halin ku ba daya ba itan naga kamar rikicecciya ce,"

murmushi yayi yace

"haka take innani yar rikici ce kawai gata ne yamata yawa duk laifin fulani ne ita ta sangartata ai itace ma wanda na taba baki labarinta,"

"ohh ikon Allah itace yan biyun nan wadda dayan saliha,"

" ikon Allah ashe da rabon zamu gamu wallahi tunda hamma yaban labarinku Allah ya jarrabeni da sonki ashe kina nan tafe ma,"

itako ware idoo 😲tayi tana ganin ikon rabbi stohuwar har da guntun kwallanta ga yanda take maganan kallo daya zaka mata ka gane bilhakki da gaskiya take zancen har zuciyanta

nan da nan taji jikinta yayi sanyi lakwas tana jin wani iri sai wani kunyan muta nen ya dira mata lokaci daya ta sadda kanta kasa ta takure agu daya

innani tace "ya kaman naga ta takure hamma tambaya mun ita mai ke damunta,"

murmushi yayi yace "tun dzu take tambaya na ina yayanta,"

" ohhh ikon Allah ayyah baiwar Allah yi hkuri dole ki rikece bari akawo miki su inda gadon yaran yake ta karasa ta turo su har ga banta,

"da ikon Allah duk hayaniyan basu tashi ba kodan sunsha maganin muran ne dama likitan yace zai sasu bacci ,dama suna bukatar hakan,"

inji innani har gabanta ta kai mata yaran tozali tayi da yaran nata dake bacci hankali kwance da gani sun samu kyakkawar kulawa wani kwalla ne ya cika mata idonta,

hannu tasa ta dauko dayan ta kwantar a cinyanta ta dauki dayan ma ta fashe da wani kuka mai cin rai kukan mai ban tausayi wanda duk mai karatu da mai sauraronta sai ya tausaya mata ta rikesu gam gam tamkar za'a kwace mata su,

sanda tayi mai isanta ta dago kai ta kalli su chief tace

"Shukran lakum shukran jazilan bansan da wani kalma zan gode muku ba dan Allah kuyi hakuri da abinda nayi agareku dan Allah ,"

kokarin durkusawa takeyi innani ta tare ta tace

"ya isa ba sai kinyi hakan ba mun fahimce ki mun gode Allah ma da abin ya staya ahaka mun fahimci juna da wurri muma kanmu mun miki mummunan fahimta sai mu yafewa juna,"

murmushi tayi tace

"Akhie sirkanunka suna da kirki ba kaman nawa ba da suka koreni lokacin dana ke bukatarsu sun juya mun baya tamkar basu suka haifeni ba kamar basu suka rene niba suka mai dani shalele ba,

they aboundon me and my babies they kicked us out of there family,

they tried to kill us,
bansan mai na musu ba Akhie,"

fashewa tayi da mastyiyacin kuka mai cin rai shi kanshi da da hali da kukan zai mata dan ya tausaya mata matuka it was thesame thing daya sameshi they exile him and tried to kill him da badan chief da,da ya rasa ransa,

yarasa mai yake damun parent nasu

"Yaahh Allah ,"

shine abinda ya fada a zahiri innani da takejin kukan har ranta ne yasa ta cewa

"ya isa,"

tashiga lallabata kamar uwa da yatta duk da bata gama gane abinda suke fada ba dan turancin data cigaba dayi Fatima ko zuciyanta yayi sanyi ga tausayin ta daya dirar mata sabida staff taji abinda take cewa dan tana jin turanci haka chief ma yaji kai hatta little dake dakin y tausaya wa matar tun dazu ya makale wa umminsa dan yaga abin yafi karfin brain dinshi shiyasa ya kame agu daya,

innani bata barta ba sanda ta tabbatar tayi shiru kafin tace

" sheik yanzu kam ai yakamata mu koma gida ko tunda ta tashi tana da bukatar hutu,"

gyada mata kai yayi yace

bari ya kira likitan yazo ya kara dubata hakan kuwa akayi ba bata lokaci yazo ya dubata ya rubuta musu takaddan sallama da cewa karshen sati zaa kawo ta kara mata gwaje gwaje dan tabbatar da lafiyanta,

chief da kanshi ya kira zainab a waya yace ta daura ruwan wanka ta kuma shirya abinci ba musu ta amsa masa da to,

amma Allah kadai yasan mai take shirywa a zuciyarta

staf Innani ta gama shirya musu kayansu bashir driver ya kaisu mota

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login