Showing 27001 words to 30000 words out of 35032 words

Chapter 10 - NAGA TA KAINA 2&3 BOOK COMPLETE BY SODANGI.txt

25 Sep 2025

1346

fita sannan na bi bayansu na samu Muktar yana cevwa ato Umma ai laifin mamun nasun ne da ta haifo na ce guda daya da biyu ne kinga da bata hadasu rigima, na ce to ai sai ta karo daya kafin badi su zama 'yan mata biyu Nuwaira ta galla mun harara akwati na uku shake da kayan jarirai ya kuwa yiwa Nuwaira na kyautar mota Honda Prelude sabuwa dal mai Rofa daya a Sakkwaton ma ya sayeta kwananmu biyu muka dawo Abuja, watanni biyu da dawowar Muktar ina dakinshi ina shirya mishi jakar da zai yi tafiya da ita shi kuwa yana kokarin karasa kwalliyar shi takalmi black mocasin ne a kafarshi farin wando chınnose poduct din D.K.N.Y ya sanya rigar T. shirt baka nike ya dora shirt akanta short sleave beach wear milk clour agogon hannunshi kuwa rolex sai daukar ido yake yi ya kammala ta je gashin kanshi ya ce ya ya dai Madam na cinye? na kalleshi na yi murmushi kafin in yi magana ne jero atishawa har sau biyar ya kalleni cikin tausayawa 'yar hamakillah, na amsa mishi. Ta hanyar rama mishi addu'ar da ya yi mun yace an ya Badi'atu wannan. murar taki banine sanadinta ba kuwa? Na kalleshi.
kamar yaya? ya yi murmushi ya ce to naga taku karewa duk magungunan da kika sha ko a jikinta na yi kamar ban gane abinda yake nufi ba na ci gaba da kokarin rufe mishi jakar, kwanan Muktar hudu a Lagos kan wani aiki da aka turashi inda zai yi sati guda ni kadaice a falo sanda aka yi sanarwar shugaban kasa mai ci wanda yake soja ne mai mukamin General wanda kuma yake da matukar larin jini wurin talakawa don shirye-shiryen da ya gabatarwa na kawowa talaka sassauci zai gabatar da jawabi na mika hannu na dauki remot na kara maganar daidai an soma kada taken Nigeria ya soma jawabinne da gaisuwa ga yan Nigerna sai ya Ci gaba yana gaya mana halin da kasamu ke ciki matsayin tattalin arzikinta a jiyarta a bankin duniya abinda ake binta bashi da abinda ta biya tun hawanshi kan karagar mulki nasarori da kurakurai daya samu tun hawanshi ya kuma rokijama'ar Rasa da su kara hakuri da juriya don gwammanti ta samu ta ida manufofinta don samun cimma bukata cikin gaggawa majalisar koli ta soja tayi taro inda ta zartar da yin wasu canje-canja a jihohi an canzawawasu gwamnoni wuraren aiki yayin da aka nada wasu sabbi ya soma fadin wadanda aka yiwa canji yana kammalawa sai ya shiga fadin
sabbin gwamnonin da aka nada "Col Muktar Zubair is the new military administrator of Adamawa State" Abidna na ji shugaban kasa ya fadi kenan kan in yı komai da gudu Joda ta fito daga dakinta inda take nata kallon Badi' atu na ji kamar shugaban kasa ya kra suna maigidannan me ya y1? Na ce an nada Muktar Joda ya zama gwamnan Adamawa, Joda ta kidime cikin farin ciki gida ya kaure da sowar murna da gudu Hari ta shigo ta rungumeni tana murna ta ko ina makobta sai shigowa suke yi na ce Hári ki lura dasu a raba musu lemo su sha akwai fivealive a sito, ta ce to ni kuma na amsa wayar dake ta kara, muryar Gali na juyo daga London Your Excellency Congratulations" na ce kai Gali ni ce ma your excellency din? Ya ce e, mana gashi kuma an kaishi jiharku ta Adamawa ina ganin ma da biyu aka yi hakan na yi dariya na ce na rasa dalilin da kullum kuke turawa mutanen Adamawa ni bari zage-zagi su ji ku tunda Adamawa dai garin kawunnai na ne Gali ya kyalkyale da dariya kafin yayi magana sai na ce to ga nauyi yana shirin hawa kanku ya ce e, wallahi na ce to Allah ya layaku rnko ya ce to amin amin ni ma gani nan zuwa yana Legos ko? Na ce e, ya ce toina jin zamu iso tare na ce Allah ya kawoku lafiya, ina ajiye wayar Gali sai ga su Nafi'u Congratulations Anti na ce kaima haka Nafi'u ya ce yanzu zani Zaria in yiwa su Baba murna gobe sai mu iso ABuja cikin kungiyar abokanshi da kuma mutanen Zaria da za su zo taryen maigirma gwamna na ce to Nali'u saikun zo, ina ajiye wannan sai ga wayar Asma'u Adam ihu take yi har na hangoki a Government House,.na ce ai sai ki yi na katse layın don ganin shigowar lambobin Wasila har cikin dare jama'a isowa suke yi ban samu sassauci ba sai da dare ya yi nisa na yi maza na yi alwala na yi nalila na gabatar da addu'ar godiya ga Ubangiji da ya ni' imta mijina da zama gwamnan Adamawa na kalli agogo dare ya riga ya yi nisa, ban samu wayar Muktar ba a yau na Kuma san jama'a ne don haka nima ban nemeshi ba washe pgari da asuba ina idar da sallah Zaria na yi waya don in yiwa iyayenmu murna Innasu Wasila ce ta dauka na gaishesta cikin girmamawa na ce inna kunKuma Muktar ya zama gwamna ce e, haka al'amarin Allah yake ta Ko ina in ya ga dama sai ya jarrabeka na tausaya muku kwarai ganin yadda ake cincirindon tayaku murna alhalin hatsarin da kuke shiin Shiga a yanzu ya fi hatsarin da ya fada sanda yake jeji mulki da kuke gani in ka samcshi ba abin ayi la tsalle ana murna bane shugaba a ranar alkiyama zai zo gaban Ubangiji ne a daure cikin sarkar wuta sai
adalcinsa ne kawai zai iya kwanceshi ku yi kokari ku yi abinda aldalcinku zai kwaceku a wannan ranar in ba haka ba kuwa to kua ga ta kanku, ta katse layin ni kam ajiye wayar na yi na shiga kuka saboda taysayi, tun daga ran nan kuwa kullum na yi sallah ga addu;ar da nake yiwa mijina "Ubangiji kaine ka baiwa Muktar mulki shi bawankane mai tawali'u a gareka ka fini sanin tsakaninka dashi Allah domin kaine ka halicceshi na rokeka ka kara mishi jin tsoronka ka kara mishi karfin zuciya da jaruntakar tsayawa kan gaskiya ka kurna bashi mafita kan nauyin jama'a bayinka da ka dora mishi" wurin ran nansu Wasila da Asma'u Adam da Barira da Hari da su Nuwaira sune suka yi ta kula abincin da ake shiryawa don baRi masu zuwa mana murna da kuma Isowar mai girma gwamna, Muktar ya iso bayan La'asar cikin tawagar.Jama'a masu dimbin yawa da suka tareshi dakuma wadanda suka rakoshi daga can cikin masu rakoshin kuwa har da ya'yanshi guda uku da amininshi na kut da kut wanda ya zama danuwa a gareshi Gal AbdulWahab, ban samu ganin Muktar ba har na hakura na kwanta barci cikin barcinane kawai na ji kara waya na yi kokarin dauka na kei kunnena muryar Muktar na ji barci kike yi Badi'atu? Na ce, nauyin jama'a.yana shirin hawa kanmu kina irin wannan barcin Badi'atu? Ban zama abin tausayi a gareki ba? Bann taba sha'awar mulki ba, bana son shi saboda na san hatsarinshi tausayin Muktar ya kara kamani cikin sauri na ajiye wayar na ja mayafi na rufe jikina na nufi dakin Muktar
yana zaune kan dardumar da ya idar da sallolin nafila yaran kuwa ya kwantar dasu kan gadonshi su dukansu barci suke yi durkusawa na yia gabanshi ya jawoni jikinshi ya kankameni Badi'at nafi sha'awar zamana soja kawai a maimakon a dora mun nauyin jama'a akaina na sassauta murya a hankali na ce Muktar godiya ga Ubangji ya kamata ka yi ba ka shiga damuwa ba yada sbugabanni ke saurin kai shugabannin da basu da adalci wuta hakannan yake saurin samarwa shugaban mai adalci matsayi mai girma a wurin Ubangiji samina da kai din jarumine mai gaskiya da rikon amana har kullum a cikin taimakon na kasa da kai kake aka da kishin kasarka a ganina shugabanci a wurinka alheri ne don kuwa zaka yi abinda in Allah ya yarda zaka samu mafita a gobe kiyama ya zuba mun ido yana kallona sai na ce da zaka bar abu guda daya Muktar ina ganin da baka da sauran matsala a hankali ya kalleni.menen shi Badi'atu? Na ce ka bar barasa Muktar ko da kake cewa baka sha ka bugu anya Muktar ana yiwa Allah hikima ne kan abinda ya ce kar a yi? A hankali ya ce na barta Badi'atu na daina shanta fitar mun da.kwalbar dake dakin nan kar su Abba su tashi su ganta, a fadar.shugaban kasa ina tare da Muktar lokacin da aka rantsar dashi a matsayin gwamnan Adamawa daganan kuwa bai dawo gida ba airport ya wuce tare da yan rakiyarshi mutum biyu ya hau jirg1 Zuwa Yola headkwatar Adamawa, nima na dawo gida na shiga shirun taliya Yoola kafin in tafin kuwa sia da na kaiwa iyayenmu ziyara Zaria soba da hunkurn wurin iyayen Nuwaira na isa Yola sati biyu da isar Muktar na.samu iyalina da suka rigani zuwa kalau dinsu sai dai Muktar yana cikin matsanancin aiki saboda yanda al'amura suka cabe ga dimbin bashin da ake bin jihar ga yajin aikin malaman makaranta da malaman unguwar zoma ga yan kwangila sunyi aiki ba abiyasu ba, farkon abinda Muktar ya yi sbi ne zabge kudaden da ake baiwa matar gwamna a matsayin kudin aiwatar da hidimar gida abina ya shali har gidajen manyan ma'aikata a jawabinsa na farko ga al'ummar jihar ya gaya musu halin da jigar ke ciki ya yi alkawarin yin aiki tukunu don ganin ya fitar da jihar daga halin da take ciki, sai ya nemi hadin kai a wurin sarakuna wadanda suke sune iyayen kasa da kuma sauran jama'a baki daya, a lokacin da Muktar yake cikin wannan aikini kama gida harkata bude mun kyaututtuka ta ko ina sai zuwa mun suke yi daga wurin jama'amasu kamun kafar abasu commisinoni wasu kuwa yan kwangilane dake son Muktar yana Zama sosai ya bada izinin biyansu kudadensu cikin kwana asbirin da zuwana Adamawa dukiyar dana tara ba kadan bace matsalar kawat bar yanzu ban samu zama da Muktar ba ballc in gayaa mishi mutanen la nake so ya baiwa commisinoni don wani tokacin kusan kwana a 0flice yake yi ran nan dai na jira dawowarshi wajen karfe daya da kwata na dare na shiga dakinshi cikin kwalliya sosai don ya san da gaske na zama matar gwamna sai a na fara mishi mita kan rashin ganinshi ni da yara da bama y ya bani1 hakuri ya ce shima abin ya fi karfinshi ne, na auna na bashi bayanin irin alherin da nake samu tun zuwana da sSunaye mulanen da nake so ya nada commisinoni tagumi ya yi dla hannu biyu ya ce ni Muktar naga ta kaina gani gareka Allah ka taimaken1 na kalleshi fuskata a daure na ce me Kuma ya samcka., ya mike tsaye ya nui can cikin dakinshi ba tare da ya ce min komai ba kusan miinti talain ina zaune anan wurin na mike na bishi dakin yana kwanc akan gadonshi ya yi rigingine yana kallon sama ya dora hannayenshi guda biyu kan cikinshi daya kan daya haushi ya kamani yanda har na shiga dakın bai motsa ba, na ce wani sabon wulakancinne kuma haka? Ka san kwanciya zaka yi ba zaka gaya min ba sai ka barni ina zaman jiranka? Na soma zazzago mishi tsiya yana kwance bai ce min komai ba har na gaji da magana na koma kuka da dai na ga ba zai yi magana ba na fita na nuti sashina ina tunanin zaman Muktar gwamna ya soma canza hali tunda gashi ya soma wulakantani kwana biyu da faruwar wannan al'amarin ina kallon talabijin tashar N.T.A. Yola naga sanarwa daga gidan gwamnati Muktar ya harantawa masu zuwa gidanshi yin hakan wadanda suke son ganinshi ko bashi shawara su yi hakan tahanyar samunshi a office daga.karshe aka ce yana fatan za a kiyaye don kiyaye bacin ran hukuma, ina zuane ina tunanin manufofin Muktar a kaina na kasa ganewa gani dai.da ilimi har na digiri amma yayi kememe ya ki yarda in zama shugaba a kungiyar mata kamar yadda sauran matan gwamnoni suke yi, tsawon lokaci muna zaman tsama ni ashi abinda bai taba faruwa ba tun bayan shiryawarmu shekaru uku har da watani ina kwance a dakina a lokacin nan cikina wata bakwai ne gashi dai an gaya min 'yan tagwaye zan sake haifa amma ban gayawa Muktar ba saboda ni dashi kowa harkar gabashi yake yi har na soma gundura da zamanshi gwamna tunda dai canza min hali zai yi na shiga tunanin kan karar Muktar wurin baba babba kanabubuwan da yake min sia gashi ya shigo Badi'atu yaya dai? Na kalleshi a lalace na ce kamar yaya kuwa? ya ce wai lafiyarki nake tambaya na ce kalau dina ya ce to Alhamdulillahi dama zuwa na yi in rokeki ki taimakeni ki tsaya ki ga su Halima sun kintsa akan lokacin don yau su Abba zasu koma Kaduna gidan nafi'u da zama za kuma su tafi tare a masu kula dasu Halima da goggo Uwalc, ban san lokacin da na mike daga kwanciyar danke yi ba, na ce amma tun ran nan da ka gaya min na ce ban yarda ba, ya kalleni cikin nuna alamar mamaki ya Ce ni fa bana ganeki Badi'atu wadannan yaran naki ne? Da zan gaya miki kanina ya roki in bashi su ki ce min baki yarda ba? Nac in ba nawa bane ai kuma ba amansu ka yi ba nina haifesu, ya ja min kofa ya fita na bi bayanshi zuwa dakinshi ban ganshi ba na konna wajen yaran na sameshi ya tarasu dukansu ukun akan cinyarshi yana gaya musu yau zaku konma gidan babanku Nafi'u ba sai na gaya muku yana sonku ba Kuma kun sani shi ne yake kaiku Legos ku je ku ga beach, shi ne ya Kaiku Daura kuka ga rijiyar kusurgu, shi ya kaiku Sakkwato wajen Nana Fatima da maminku Nuwaira, Ummu ta yi maza ta ce e, baba yama kaimu Zaria da Soba Muktar ya yi maza ya ce yawwa Ummu kema kin tuna ba. 1a ce e, su Umar da Usman suma suka yi ta Iisšafi abinda Suke rike dashi na alherin nafiu a garesu da suka yi shiru sai ya ce to zaku koma gidanshi ku zauna zaku yi karatu a can Adamawa ba garina bane Umar ya ce amma garinsu maman mune, Muktar ya dan sha mur garın mamanku bashi ne garinku ba babana ka jiko? Usman ya ce e, babamu Zaria ne garinmu Muktar ya ce very good, baba ya jawoshi jikinshi in kun je can akwai Anti Safiyah matar babankuce ku yi mata ladabi Ummu tace bata..shiii ya katseta ku yi abinda nace muku gaba daya suka amsa to baba ina Halima? Cikin sauri ta zo cikin ladabi ta ce gata ya ce maza ku j ku gama karfe goma direba za1 kaiku airport Nafiu zai tareku a Kaduna, ta cc to ta kama hanounsu da gudu suka tali tana zolayarsu don ta iya kula da yara, na kalieshi cikin bacin rai na ce wai kai kana nufin dolc sai ka bayar dasu nc? Ya ce ki yi hakuri kar ki biyoni gaban ya yana ki zageni yafita ga zatona dakınshi zashi in bishi can mu yi wacce zamu yi sai kawai naga yayi waje yana tita na ji a. tayar da jiniya alamar office dinshi zai tafi na dawo dakina na rasa abin yi sai kawai na jawo wayana buga zuwa Zaria don in gayawa Baba babba 1rin kama karyar da Muktar yake min sai na samu Antina sai dana gama gaya mata komai Sai na ji ta ce yaran da kuke rigima ke dashi akansu nakinc? Ko dasu kika je mishi gidan? Ke Badi'atu bana son rashin kunya da dibar albarka ya'yan larin kike yiwa tashin hankali? Haka kika ga iyayenmu sun sa ido akanmu? To kar ki ji dawai zan je Soba in gayawa Inna abinda kike yi na ce Anti ba haka bane ni zamansu da Safiyan ne ki duba ki gani fa manya ma in suka je gidan nan in dai ta ga zasu dade sai ki ga zaman bar yi dadi ba balle 'yan yara haushi ga kara kama Antina ta ce in su je gidan kaga zamansu ya isheta ta hura wula ta jefasu a ciki ina abinda ya dameki? Sakarya mara kunya in yaran nan basu iso Kaduna yau ba ni da kene da yau zani Soba na fasa Kaduna zani in ga zuwan yaran ta, katse layin na kwanta ina kuka Anti kullum a bayan su Muktar take share hawayena na yi nuka yi Sallama dasu suka tali, kwana bi1yu ina zazzabı na kuwa san bakin cikin rabani da 'ya'yana da aka yi ne, tun ranar dana biyo Muktar ya fita ba are dana samu na gaya mishi abinda zan gaya mishi ba ban sake ganinshi ba sai a talab1jin na ganshi wai yana rangadin jihar Adamawa don saduwa da jama'a ya gama rangadin da sati daya a labaran N. T.A. Yola na ji sunayen sabbin commissinoni da Muktar ya nada babu ko cdaya cikin sunayen dana bashi haka nan bai saka ko daya cikin dangina ba abinda nake ganin akalla ya saka kawunaina biyu na kara kulewa da Muktar bai dai ce mishi komaiba to ina na n aganshi balle in ce mishi? Muna nan ahaka har ran nan na wayi gari ina nakuda e lokacin nan kuwa wata shida ne da hawan Muktar gwamnan Adanawa ya shigo dakin kafin ya fita dama kuwa kullum haka yake yi ina kwana Badi'atu? na ce lafiya ba tare da na kalli inda yake ba, ba dai matsala ko? Na ce babu ya juya zai fita ya ce to ni na tafi office zani wurin kaza da kaza zan kaddamar da rijiyar burtsatse a wuri kaza da kaza na ce sai ka dawo bai yi minti talatin da tafiya ba na baifi'yan tagwayena macee da namiji, Joda da sauran mutancn dake gidan suka yi ta tsalle suna murna nan da nan tunda lafiyata kalau ni da yarana ga kuma kulawar likitoci muka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login