Showing 33001 words to 35032 words out of 35032 words

Chapter 12 - NAGA TA KAINA 2&3 BOOK COMPLETE BY SODANGI.txt

25 Sep 2025

1350

ta kawo mijinta don haka ina cikin matsanancin shiri ita kuwa Nuwaira 1ana zumudin innar zata aurar da yar autarta Hindatu, ni kam tun sati biyu kafin bikin zaman Bayelsa ya gagareni na koma zaryar Zaria, Soba, Yola da Kaduna a ranar daurin auren kuwa a gabansu baba babba Muktar ya daur auren 'yan mats shida don itama Dintadu babansu Gali Muktar ya baiwa waliccin aurenta don haka shi ya daura auren baba babba ya karbarwa Uzairu yana gama bayar da nashi kannen ya nufi Yola don karbarwa baban Anti auren Bintu yar kawuna Yero ya kuma wakilta Gali da Nafi'u suka je karbarwa sauran yaran maza guda biyu na dawo daga Kaduna inda aka yi budar kai Zainaba a gidan Dr. Mannir ina yiwa Antina bayanin abinda ya wakana Wasila ta leko tana cewa ina kirjin biki, na yi kamar ban ji a ba, sauran mutancn dake lalon Anti suka yi dariya Wasila ta shigo ana gaya min yaya Muktar ya yiwa Inna waya dazu ya ce ta gaya miki ki bar komai ki isa Bayelsa gobe don ki samu halariar bikin da matan kabilar wawan ke yi sbekara shekara wai sun roki ki zama musu babbar bakuwa a wurin, na ce irkashi to rakanı gidan su Luba in zaga su kafin in tafi goben.
Ina Bayelsa na haifi mai sunan Antina Shema'u, duk da a Zana aka yi suna liyala sosai matan garin suka shirya don tayamu murnar karuwar da muak samu, siyasa ta kankama sosai har an fara gudanar da za6a66uka yau ma ranar zabece da wurio Muktar ya tasani a gaba muka je muka jefa kuri'ar mu a mazaba ta 4 dakc garın ycnagua, indá aka yi mana rijista mun dawo gida ni da shi muna zaune a falonshi na yi waya Kaduna don taya su Abba murnar cika shekaru bakwai bakwai a duniya Ummuce ta fara magan da alama tana cikin farin ciki salamu alaikum baba abinda ta fara fada kcnan, amin wa alaikum salam Muktar ya amsa barka Ummu da cikarku shckaru bakwai ta ce yawwa baba mun gode, amma bakwai da yawa kuwa baba? Cikin sauri Muktar ya ce da yawa kai Ummu daga daya fa aka faro har kun zo bakwai ai Kun kama hanyar girma, ta cc to kai shckarunka nawa? Yace ni yanzu ina da arba'in da uku watanni kadan ne babu ibu ta saka mishi arba'in da auku fa ka ce baba muka yi tayi kara alamar an fige wayar daga hannunta, ni ne. soja baba na saramaka baka ganni banc Muktar ya yi maza ya sara cikin murmushi ya ce nima na sara maka baba don na yi yanda ka bugi kasa da kafarka sai dai mc yasa ka kwace waya a hannun 'yar uwarka? ya cc ta cika surutu baba zata bata mun lokaci Muktar ya ce to kun cika shckara bakwai yau ko? Ya ce e, amma ni zance babanmu ya kara mun nawa tunda Nafisu karfi dukansu na iya kayar dasu na kuma fisu iya gudu da tsalle, ni kam dariya nake yi Muktar kuwa ko a jikinshi sai ya ce yi hakuri ku tafi tare kawai baba hakan bawai yana nufinka fisu shckaru banc sai dai alamune na kai din sojane rikici ya kaure tsakaninshi da Umar akan karbar wayar Muktar ya ce kai soja baiwa dan uwanka wayar nan shima mu yi magana, Umar yana karba ya ce baba shi karfi da tsalle ya fini ni kuma na fishi kokari a aji na wuceshi a karatun Alkur'ani ni na yi haddar izufi goma sha bakwai shi ya yi sha biyar wel done babana to ai dama kaine babbain ji Muktar kuma yau da sassafe da babanmu ya kaimu gidan baban Sakkwato mu gaya mishi shekarunmu bakwai ni ya baiwa kyautar mu da ya bamu na rike to ai kaine babban Muktar ya sake fadi yanzu an jima zamu ziyarci gidan marayu babanmu zai kaimu da yamma zamu yi gasar karatun Alkur'ani kuma ni zan cinye gobe kuma za mu je Zana da Soba shi kenan jibi zamu koma makaranta Muktar ya ce na gode muku dukanku Allah ya yi muku albarka suka amsa amin, ya katse layin ni kam a yanzu nafi kowa murnar zamansu Abbawurin Nafiu gaba daya lokacin shi na yaran ne ga cikakkiyar tarbiyar da yake basu, sakamakon zabe ya fito jan'iyyarsu Gali batayi nasara ba sai dai sun samu gwamnoni goma sha biyu daga cikin talatin da shida jam'iyyar da ta yi nasarar tana a gwamnoni sha biyar nc sauran jam'iyyu biyun suka sauran gwamnonin a tsakaninsu talakawa Sun zabi wani raba, shugabane da ya yi alkawarin larlado da taltalin arzikin kasa, darajar naira la bunkasa ya wadata asibitoci da magunguna, kyauta ya magance matsalar dauke wutar lantarki ya bayar da ruwan sha mai tsafta kai alkawura dai masu dadin to Allah ya yi mun nikawa farar hula mulki mun dawo barikin soja da zama Muktar ya zama Bnigodicr Gencral ko wata shida bamu yi ba a Rukuba Barrack dake Jos aka turashi Bakassi cikin sojojin da aka dora musu nauyin lura da yanda za a mika wurin ga Cameroun, yana can bai dawo ba wani umarnin ya sakc fitowa cewar ya nuli kasar Indiya don yin kos na watanni shida kan aikinshi dai na soja, yana dawowa ya zama shugaban rundunar ta 4 ta askarawan Nigeria dake Bauchi mun sbekara a Bauchi aka cc ya nufi jaji ya zama shugaban makarantar borar da hafsoshin soja dake can muna jaji shekararmu daya da wata biyu a lokacin ina goton Muhd Gali, Muktar ya zama Major Gencral a duk lokacin a mukc cikin wadannan ayyuka da canjc-canjc Gali yana can yana fafatawa cikin harkokin siyasa, kasa tana ncma ta rikice al'amura sun cabe komai ya ta barbare Gali kullum yana cikin babatu a gidajcn jaridu da talabijin kullum cikin kushe yanda gwamnati take tafiyar da al'amuran kasa yake, tun jama'a suna ganin adawa ce tasa Gali iin wadannan maganganun har dai aka gano gaskiya yake fadi, gwamnati sai almubazzaranci da dukiyar kasa take yi cin hanci da rashawa ya yi katutu an kasa biyan ma'aikata hakkinsu, masu fansho kuwa tuni suka shiga halin ha'ula'i farashin man fetur sai tangal-tangal yake yi wai an bar yan kasuwa su yi yanda suka ga dama, gwamnati ta cire tallafin da take yiwa man, tuni talakawan kasa suka soma fadin sun ga ta kansu.
Ran nan Muktar ya dawo daga kasar Germany tafiyar shi ce ta kashin kanshi ya yi ind aya tafi da Ummi Nafisatu da Nana Fatima suka yi mishi rakiya ya dawo da sati biyu ina gida na amsa wayarshi daga office shirya maza Badi'atu gani nan zuwa zaki rakani Zaria yanzu sa ce lafiya ya ce lafiya mun isa Zaria kusan sallar La'asar ne yana cikin falonshi can muka sameshi ni dia Muktar mun nutsu sosai don oima maganar da Muktar din ke yi ta kashe min jiki kwarai baba babba ya gyara rikon da ya yiwa baban yara ko Gali ya ce amma a matsayinka na yanzu ka bar aikin soja Muktar? Ai na dauka zaka bari ka kai matsayin General tunda kana gab da kaiwa Muktar ya kara sunkuyar da kai ya ce burina kenan amma abinda nakc hange ya sanyani bakura da hakan in dai ba kainc ka ce baka amince da barin aikin nawa ba, don na shiga wani hali na canka-cakare, ko da Muktar bai furta ba daga ni har baba mun fabimci akwai wani abind aya hango nan da nan baba ya amince da barin sojan Muktar ya shiga yi mishi fatan alheri wata hudu kaca idan wannan maganar sai ganmu a sabon gidanmu na Kaduna Muktar ya zama ritaya Major General yan uwa da abokan arziki sai zuwa mana murna ake yi Muktar ya fita aikin soja lafiya, nan da nan ya shiga shirye-shiryen abinda zai yi cikin kankanin lokaci ya bude kamfanin sufurin jiragen sama mai suna ZU U MA AIRLINE, ina tare da Muktar a ranar da aka kaddamar da jiragen muna barin wajen Zaria muka nufa don shaidawa baba babba jirgin ZU'UMAN ya tashi na shiga dakin
Antina ina mata sallama zamu tafi, anti ta kalleni ta ce ke dai kullurm daga ciki sai goyo wahalar nakuda bata damunka nayi murmushi na ce Ant.i kowa da irin zuwanshi da kuma arzikinshi ni kuma kin ga wannan din London Muktar ya ce zani awonshi ta ce ai sai ku yi ta yi na yi dariya kawai na tafi muna kwance cikin dare ni da Muktar wasanninmu muke yi na farantawa juna rai rabon damu mallakawa juna kanmu irin na yanzu tun kafin Muktar ya zama gwamnan Adamawaa a yanzu ni dashi mun zama tamkar amare ko ina zashi ni ce 'yar rakiyarshi in kuwa kwanciya zai yi zai ce bar abinda kike yi ki zo ki mun tausa, in ce to, karar waya ce ta damemu Muktar ya mika hannu ya dauka, hello na ga alamar fuskarshi ta canza, na ji yana cewa yanzu? Wanc asibitin zaku kaishi? Ganinan 2uwa yanzu, da sauri Muktar ya dira daga gadon ya shiga bandaki wanka mai sauri ya yi ya fito yana sanya kayanshi yana bani amsar tambayar dana yi mishi babana bashi da iafiya Badi'atu, abinda babanlungu ya gaya min kenan wai yana ciwon habo, na ce irinshi ya taba yi Muktar sanda baka nan kana dajin nan biyo Muktar na yi ina mishi wannan bayanin don tuni har ya shige motarshi yana kokarin fita daga gidan ba zan iya jiranki ba da safe kawai ki zo na ce to Allah sawwake na dawo dakinshi na kwanta barcin da na yin ba mai dadi bane daga idar da salla ta na shirya cikin motata na nufi Zaria daga ni sai Gali karami mu biyu ina isa kofar gidanmu na ga motoci sai isowa suke yi na kauce don in yi parking gefe daya sai kawai naga Muktar kanshi babu hula kafarfshi babu takalmi shi da wasu mutane suna kokarin fito da makara daga ciki Tukuna
A ranar kaddamar da littafin a jihar bayelsa Wanda yayi daidai da ranar da mukhtar ke cika shekaru hamsin cif a duniya zan iya cewa gaba d'aya Nigeria ta taru a bayelsa, shugaban kasa da mataimakinsa suna can ministoci gwamnoni da sarakuna da duk wani mai fad'a aji ya zo uzairu na zab'a chief launcher don shi ke shagabancin zuuma airline, Alhaji Gali Abdulwahab uban taro, mai masaukin bak'i gwamnan bayelsa, Ina zaune cikin hijabi da bak'in madubi kusa da mijina masu jawabi suna ta yi, yabona suke yi suna fadin namijin kokarin da nayi wajen kammala tarihin da nayi da aka gama jawabai sai aka shiga lunching, Ni kam da naji abinda uzairu ya bayar rike baki nayi, jama'a suka yi ta fadin abinda suka bayar, jihar adamawa ce take fadin yawan littafin da ta saya akan miliyoyin nairori a lokacin da mukhtar ya juyo yana tambaya ta ranki ya dade wadanannan miliyoyin da ake Tara Miki me zaki yi dasu? Ko zaki ajiyesu ne ki yi ta shirya min gara Ina Sha , in yi ta cin Bean And meat casserole? Nayi murmushi nace your Excellency zaka Sha gara ne inka in ka warware bakin aljihunka, wadanannan makudan kudaden da kake magana a kansu zasu tafi ne wajen aiwatar da shirina na taimakon yara qanana masu fama da ciwon zuciya, samar musu magani kyauta da Kuma daukar nauyinsu zuwa kasashen waje in har hakan zai Zama shine hanyar warkewarsu. Mukhtar ya kama hannuna ya rike da karfi ya ce Badi'atu, a lokacin da Babana ya bani ke biyayya da gudun bacin Rai ne yasa na karbeki a yau Ina alfahari da kasancewata d'a mai biyayya ga iyaye don Kuma hakan ya sani na samu abunda nayi ta roko tun Ina d'an k'arami shi ne ubangiji ya azurtani samun mace ta kirki.
Shekaru hudun mulkin mukhtar sun kusa cika jama'ar k'asa sai Kira suke yi mukhtar ya sake fitowa su zabeshi ya ci gaba da mulkinsa saboda a zamaninsa kasa ta yalwata zaman lfy ya tabbata jama'ar k'asa sun samu kwanciyar hankali an raba su day talauci da wahala an rabasu da ambaton kalmar *NAGA TA KAINA!*
sai anjima
Taku
Hafsat sodangi
Sai mun sake haduwa a wani littafin.





















Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login