Showing 18001 words to 21000 words out of 35032 words

Chapter 7 - NAGA TA KAINA 2&3 BOOK COMPLETE BY SODANGI.txt

25 Sep 2025

1345

dai Badi'atu? Muktar ya Tambayeni na ce kalau ashe ango ya iso? Muktar ya yi murmushi ya ce ya iso har mun sanyashi a lalle, na ce haba gaskiya na ganshi yana kyalli. Gali ya dan yi murmushi ya sunkuyar da kanshi kasa kema wai sai da kika zo wannan bikin? Sai da suka jira ta dawo sannan suka yi mata sallama suka tafi. Washe gari tun sassafe na sha kwalliya cikin wani shegen leshi baki mai shara-shara da laushi ya sha duwatsu, gashibashi da nauyi ko kadan dinkin siket ne mai fadi da katuwar riga da aka yi ta tamkar malum-malum turmi biyu Muktar ya saya aka yi min amfani da yadi bakwai na baiwa 'yar gidan Wasila yadi ukun, na yi matukar yin kyau ga zinarai sun kama jikina sai walkiya nake yi ina gama karyawa na nufi sashin baba karama don a can ake aikin bikin, ita baba Sabuwa sashinta ya cika da'yan uwanta wadanda kuma sunc iyayen Nuwaira, ina gaida baba karama na nufi kicin don in sa ido kan aikin da ake yi hidimar aikin sosai na shiga tamkar ba tsohon cikine a jikina ba duk. lokacin da Baba karama ta zo wucewa zaka ji tana ce min ki fa rinka zama Badi'atu in yi murmushi in ce mata tio kafin karfe daya aikin ciccika manyan kuloli da abinci muke yi ana kai wa wajen mutane ana zuba musu na ware wasu manya guda uku na shakesu da farar shinkafa guda daya na cikashi da soyayyen naman saniya guda biyu na cikasu da kunun gyada sannan na kawo wata katuwar kwalla na cikala da miyar tumatur wacce baba damna ka sanya ludayi cikınta sai ka debo naman kaji na hada na ce a kaiwa angwayc kafin su nuf
wurin daurin aure na dawo sashın baba Sabuwa na tarar da su
Antina da Innarsu Wasila da Hajiya Murja har da Hari suna wajen
na cc lah kun zo ashe kuna nan na tsuguna na gaishesu na ce
gaskiya Anti ba bikin Gali kuka zo ba nan ai dangin amaryane gaba
daya aka yi dariya na ce zo mu je Hari, Wasila ma tana can muka
taho tare na zo na shirya abincin da muka yi har da masa da miyar
taushe ya kuma sha tantakwashi da naman rago na jera kan wani
katon tirc na dauka na je na kai musu na ce akwai fruit salad da

41


zobo da kunun zaki har ma da alala bari in je in kawo muku, Henya
Murja ta ce ke Badi'atu samu wuri ki huta kin ga yadda kike digar
gumi kuwa? Samu Wasila ki sata ta kawo mana na ce a1 tana cikin
kicin ne zan dai turo duk wanda na samu. Kawai Baba Sabuwa 1a ce
in banda karfin halima wannan ciki na Badi atu in ta zauna a1 sau au
dagata. anti ta ce itama bhaka take, na yi maza na bar wurın don ban
son jin tonon asirin da take shirin yi min. Wajen karfe uku da rabi
na fito daga wanka na sake wata kwallıyar want leshin na s ake
sakawa sky blue dinkinshi irin na safen ne yan kunnayen dake
Jikina ma ba sune na yi amfani dasu a safiyar ba. Saminu ya le:ko
ina Anti Badi'atu? Wuce tana can ciki Hajiya Murja ta bashi um rni
ya miko min wani kunshi mai girma na goro da dabino murza
murza wai gashi in ji Yaya Muktar an daura auren Yaya Gali da
Nuwaira gaba daya muka ce Allah ya sanya alheri na tire na zu ba
na fito dashi inda iyayenmu suke zaune na ajiye musu a tsakar gi da
ma sai raba goro da dabinon akeyi ana sanar da Jama'a an dau ra
auren Gali da Nuwaira tsofaffi kuwa sai rangwada guda suke y1
Saminu ya sake shigowa yana fadin akwai ltyafar cin abinci yanzt a
Zaria hotel duk mai son zuwa ga motoci nan a ko far gida da
daddare ni ban je daukar amarya ba, baba Sabuwa ce ta hana ta ce
wai in dai ba so ake in je in haihu a hanya ba Den haka na zauna
cikin masu tarbar amarya su Wasila da su Hari suka tafi amarya ta
1so bayan sallar 1shai ga alama kuwa'yar dangice don kuwa jama'ar
da suka rakote ba kadan bane ta sauka a sashinta wanda aka vi
matukar kayatar dashi aka kuma nuna mata gata ta wajen kayatar
dashi da kayan alatu ko da yake Antina ta ce min gaba duyan abiada
na gani a wurin aikin baba Sabuwa ne na rike baki nuna alamar
mimaki na ce lallai baba Se buwa tana ji da ita. Anti ta rike baki ta
ce ai kanwar baba Sabuvar ne ta haifeta a hannunta kuma ta girma
don tarc aka kawoe ta y1 nata zaman daki data girma tä aurar da
ila ta baiwa kaninta abokin wasansu shi ne ta haifi Nuwaira na ce to
yanzu tana ina? Ta ce Allah sark ai tn nahuwar Nuwairan ta rasu
tausayi ya kamani na kara jin mamakin shakiyancin Gali na ce wato
dai Gali so ya y1 ya tsokano sama da tsinke da vake cewa ba zai aur
Nuwaira ba Anti ta ce rabu dashi ja'ir washegari a wurın liyafar

42

kuwa komai ya tsaru ango da amarya sai kyalli ske yi kana shiga wurin zaka gane irin ta'adin da aka yiwa turare kafin azo ina zaune gefen Muktar muma mun sha kwalliya anko muka yi. Hari tana kusa dani Major Amadu yana can gefenta don tunda ya zo daurin aure bai tafi ba. flari ta rada min a kunne ta ce kai wannan amarya akwai ta da kyau, dubi yanda ta zama cikin kawayen nata tamkar wata a Cikin taurarı, na yi murmushi na ce kin ganta ko? Ta yi.saurin amsawa e, na ce to kema dai sheda ce makaranciyar alkur'ani ce tunda a gabanki aka yi mata sauka, ta ce kwarai, na ce bayan haka tana da diploma a Home Management daga kaduna Polytechnic, ta ce eyc, na ce to auren dolc aka yiwa Gali ta rike baki nuna alamar yin mamaki, na ce amam fa nima fin karfin Muktar aka yi aka bashi ni, ta kyalkyale da dariya ta cc ke kice abotar tasu ta yi matukar daccwa na ce uh kwarai kuwa, ta ce to amma fa babu laiti suna da biyayyar iyaye na ce c to da wannan kam, kawar amaryace ta mike take karanto tarihin amaryar lokacin da na ji wata irin masokiya ta sokc sai da na ce wayyo Allah na saurin abin Muktar ne kawai ya ji cikin hanzari ya juyo gareni menene Badi'atu? Na ce bana jin dadin zaman kujerar ta matseni dubi duk matan da suke wurin nan Muktar ni kadaice mai katon ciki dukansu kwalliyarsu gwanin sha'awa da sauri ya ce min wa ya ce miki kwalliyarsu tafi taki kyau? Katon cikinki abin takamarki ne, don kema kowa ya ganki ya san mijinki yana sonki. Ni in kika kyalcni ma sai in ce miki dukan su sha'awarki suke ji, na dai yi murmushi kawai na hakura, an gama ciye-ciye da tande-tande an kuma gama jawa bai har an karbi kyaututtuka ni kam ban iya tashi bayar da kyautar ma ba saboda yanda cikina ya dun kule wuri daya sai Muktar ne ya bayar mana da namu, taro ya kusa tashi Muktar ya mike yana
Karanta jawabin godiya yana gamawa aka rufc taron da addu'a, muka dawo gida wajen sha biyu Muktar ya dawo gida don ya tsaya raka ango dakin amaryarshi da asuba muna idar da sallah Muktar ya shiga kinisa wuri cikin shirin tafiya sammako zamu yi don mun kwana bamu yi barci ba saboda ciwon bayan daya addabeni ina can Cikin dakin Muktar ina fama da cikina wanda ya dunkule wuri daya naji shigowar Gali falon Muktar din lafiya ka zo mana gida yanzu? Gali ya yi tsaki daidai lokacin da na ji zamanshi kan kujera, to yaya zan yi? Mata sun cika min gida? Ya sake wani tsakin, yarinyar nan bata barni na yi barci ba kwana ta yi tana kuka, to kai me ya kaika wurinta? In ji Muktar, Gali ya sake jan wani tsakin wai daga naji zan mata sai da safe kar ace an bani amana ban rikc da kyau ba sai kuma na kasa fitowa daga dakin. Muktar ya fita tsakar gida ba tare da ya yi magana ba ya sake shigowa Gali ya ce yarinyar nan fa budurwace sai da naji faduwar gaba jin maganar Gali shi kuwa Muktar tsaki ya yi ya ce haba Gali ka ja bakinka ka yi shiru kar mutane su ji wannan abin kunya da ka yi su yi maka dariya, ya ce Allah ina jin da addu'o'in da Umma ta tofa mata shi yasa dana ganta na kasa hakuri ai ba jiyan na soma ganinta ba ko zaka tura Badí'atu ta gaisheta? Ya ce to ya leko dakin ya ce Badi'atu yi kokari ki je ki yiwa su nna sallama yanzu zan zo mu tali, na ce to na fito da kyar nake iya daga kala katuwar rigace a jikina ina rikc da gyalcna a hannu na ce ina kwana Gali? Fara'ar dake fuskarshi ita tafi komai bani mamakı ya amsa yana tambayar ko dai asibiti zamu kaita Muktar.
Ya ce a'a gidanmu zmau tafi in Allah ya yarda sai mun isa ta haihu na shiga wurin Innar su Wasila tana falonta ta bini da kallo anya wannan tatiyar kuwa zata yiwu? Na yi murmushi kawai na zauna na gaishcta. Muktar ya shigo cikin ladabi ya gaisheta ya kuma yi mata sallama sai ta ce-mishi ka bar Badi'atu anan in ta haihu ta yi wanka sai a kawota ya ce to ya fita har na dan ji dadi don kuwa ni kadai na san abinda nake ji sai ga Naff'u da sauri shima shirin tafiya yake yi ya zo ya zauna cikin ladabı ya ce Inna wal Badi'atu ta fito su tafi in ji Baba babba, ta ce to tashi ku je, na tashi na yi mata sallama ko wurin Antina ban shiga ba, a kofar gida bab babba yana tsaye ya sha manyan kaya tamkar wani mai mulki saboda kwarjini shi kuwa Muktar yana jikin motarshi ku je gida Badt'atu Allah ya kaiku lafiya, na cc amin na je na shiga mota na zauna na ji Muktar yana cewa buba Babba idan abokina ya kawo matarshi yimu uku sallama a hadosu da goggo Uwale su zo, ya ce to In Allah ya yarda zasu zo, wata inin tafiya mai matukar wahala na yi sai dai cikin yardar Ubangiji mun isa lafiya mun isa kuwa kayan haihuwa kawai Muktar ya dauka ya nufi asibiti dani mun yi sa'a Dr Lami tana nan ita ta karbeni, ta gama dubani ta cewa Muktar in yana da abin da zai lya tafiya don kuwa ko zan haihu zan kai wajen magariba, na kalli agogon dake dakin naga lokaci a zuciyata na ce wato kusan awa takwas kenan daga yanzu lallai kuwa za a taba jifa-jifa Muktar kan dawo ya dubani na rinka ganin awa takwas din nan da likita ta diba tamkar ba za su taba zuwa ba saboda wahalar da nake ciki sannu a hankali sai gashi sun cika ban halhuwa ba suka fara wucewa azaba ta gallabeni na shiga wani hali na gajiyar da azabar da nake ciki na rasa inda zan tsoma rayuwata in ji dadi, tun bayan sallar isha'i nake tare da Muktar a dakin haihuwa har wajen hudun asuba na kalieshi lokacın da yake ta aikin goge min gumi na ce Muktar a kira min Antina kawai ina ganin mutuwa zan yi cikin sauri ya ce stop it Badi' atu ya kankameni yana min magana a kunne yana kara karfala min gwiwa kar ki ji tsoro kar ki karaya haka iyayenmu suka wahala kafin suka haifemu shi yasa ya zama tilas mu yi musu biyayya muryata tana rawa na cc Muktar zan mutu ya kara kankamcni daina Badi'atu daina fadin haka ba zaki mutu ki barni ba na riko Ubangiji in har zan rayu to ya rayani tare da ke ne ki yi hakuri ki yi hakuri kin ji? Yi nishi Badi'atu umarnin da likita ta bani kenan Muktar yana rike dani don kara min karfi yana min magana daure ki yi nishi Badi'atu ko ma samu Allah ya taimakemu ki huta da wannan wahalar da iya karfina na kc nishin na ji tahowar wani abu na ji tamkar kokarin rabani biyu yake yi jikina sai bari yake y na kidine saboda azabar da nake ciki na saki komai na koma kiran Ubangji ina cewa "Hasbuneliahu wa ni'imal wakil a haka na haihuwa, Muktar yana gopge mii gimı da gcien rigarshi yana fadin Alhamdu lillahi kin haifi daya saura daya, duba mana ka gani Muktar ko Shine mai hannu ukun abinda na fara gaya mishi kenan da sauri ya nufi gun likita wacce ka gwade nauyin jaririn ya karbeshi ya zo dashi wurina hannu biyunc dashi' Badiatu kin ganshi? Dogone Sambalcle kyakkyawa kaleshi ki gaya min dawa kika ga ya yi Kama? Duk da ban gama wartsakewa ba sai da na yi murmushi ya Bama tofeshi da addu'o'i ya mikawa nurse din da tazo karbarshi, su Hari da Goggo Uwale suka aiko min da gaisuwa na ee ina amsawa a gajiye kwarai na haifi daya yaron don kuwa shima na wabala kafin in haifeshi cikin matsananciyar murna Muktar ya shaida min shima hannu biyu ne dashi Badi' atu kin ganshi komai nashi irin na dan uwanshi ne har nauyinsu, sa mnusu shaida don mu ganc na farko da na biyu ya umarci nurse din likita ta ciro min mahaifa ta kuma shi latsa cikina a kokarın da taek yi na gano hannun da suka ce sun gani, mawa kadan sai ta cewWa Muktar akwai sauran da acikin an na in numfashi flasbunallahu wani imal wakil, in ji Muktar ni kam kidimewa na yi na shiga halin targaba saboda tsoron wahalar da zan sake shiga shi kuwa yana ta gaya min kalmomin karfafa gwiwa ciwo ya taso na ji tamkar ya zarce duk wanda na yi a baya tunda yanzu kam jina ya yi tsami duk idna aka taba min sai in ji tamkar famani akayi na rasa inda zan sa kaina Hafsa ma'aunin likita kin yarda na yi a dora min shi a cikin rarrashina Muktar yake yi yana bani hakuri yi nishi Badi'atu in ji Likita ta fadi hakan ya fi sau ashirin shima Muktar ya yi iyakar taimakonshi na kasa, Badi'atu zaki kashe yaron fa gashi ya sauko ki yi nishi ta fito mana Dr. Lami take gaya min a firgice, hankalın Muktar ya kai matuka wajen tashi ya yi duk abinda zai yi na kasa nishı ji yake. yi tamkar shi ya yi min nishin babu hałi, yana rike dani sai bari jikinshi yake yi yi kokari Badi'atu a hankali na dago idona na kalleshi da kyar na iya buda bakina na cc mishi ka yi hakuri Muktar karfina ya kare ji nake tamkar numlashina zai tsaya ka yale min laifutfukan da na yi maka na sake lumshe idona saboda jinn dake dibana da gwiwoyinshi biyu ya durkusa a kasa ya kifa fuskarshi akan tawa yana sissika tamkar mai yin kuka yana fadin ya Allah abinda na saui kawai shi ne na ji lokacin da Dr. 1Lami ta ke kokarin tura min injun din da zai taimaka musu Ciro yaron da aka cc ya saura a cikina na dawo cikin nayyacina, na ganni cikin wani dakin na daban Muktar yana zaunce Kan kujera yana rike da hannuna da ake min karın ruwa ta jikinsn Antina kuwa tana tsayC sai faman lyacc majina take yi Innalila Wa inna ilaihir raji'un abinda na fara fada kenan Muktar da An Kamar rigc-rigcn kiran sunana suke yi sannu Badi'atu na kallcshiu a hankali shima ya yi muzai-muzai kamar tare muka yi nakudar na ce Sun Cire yaron ko har yanzu tana cikina? Cikin sauri ya ce sun cire Badi'atu mace muka samu sai dai itama kamar ke ta wahala da yawa dukansu suna dakın renon jarirai wasu hawaye da ban san dalilınsu ba suka gangaro min Antina ta matso kusa dani kar ki yi kuka Badi'atu ki yiwa Allah godiya ya yi miki kyautar da bai yiwa dubban mata ba, 'ya'ya uku kika haifa lokaci daya na zuba mata ido ina kallonta ta sake kusantoni yau ke da Muktar 'ya'yanku uku kuyi farin ciki ku yiwa Allah godiya na ce to Anti kafin yamma asibitin ya cika kwarai da jama'a masu taya mu murnar samun yan uku. Dr Lami ta shigo tana auna jinina bata da wata matsala sai na karfin jiki ina ganin tunda kuna son ta koma gida sai ku tafin kawai, nurse din da kace in samo maka akwai kanwata ta gama karatunta na nursing bata samu aiki ba sai ta zo ta kula maka dasu Muktar ya ce na gode, Dr Allah ya saka da alheri ta yi murmushi ta kalleni to Badi'atu sai na zo gida ganinki da yaran ko? Na ce to Dr mun gode, mun iso gida Antina tana rikc dani saboda rashin karfin jiki su I lari suna rungume da yawan muna isa hanyar da ta raba sashina dana kicin ma hango Nuwaira a ciki tana ta aikin girkin abincin dare tamkar ita ce matar gidan. Anti tana gyara min kwanciya Nuwaira ta shigo tana murmushi na ce amarya ce da aiki haka kace-kace? Ta ce to amarya ta samu 'ya'ya uku ras ina ta ga ta zama, gaba daya aka yi dariya, na cc ke da wa kika zo? Ta yi wani irin lallausan murmushi da nake zaton in a gaban Cali ta yi kila sai ya kusa shidewa, don dadi ta ce ni da ango saukeni ya yi ya shiga kasuwa, wai zai yiwa babin da ya buya musu nata sayayyar me zan kawo miki1? Na ce Nuwaira da masu aiki a gidan nan kar ki wahalar da kanki ta kalleni la ce ni fa mijina ya cc in na zo gidan Muktar in maida gidan tamkar nashi na yi dariya na ce gaskiya ya gaya miki Nuwaira to kafin in ci komai ina so in yi wanka, cikin sauri ta je ta juyc min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login