Showing 27001 words to 30000 words out of 44930 words

Chapter 10 - Yar Talakawa Complete Hausa Novels by Afrah.txt

29 Sep 2025

1466

Aka°•○sultana
[8/9, 8:44 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→9⃣1⃣





Cikin kwana biyu, ikram ta maida prince bawan ta, komai tace yayi sai yayi shi yake samun sukuni, gaba daya yanzu baya da aiki sai nata, dan ma zuwa aikin shi ya zama dolene, mummy ta kirata taji ko abu ya daidaita, ikram tayi dariya tace lafiya lau mummy nayi yadda kika ce , komai ya daidaita yanzu, ta mikawa prince wayar, hannunsa na rawa ya amsa, ya gaida mummy.

Mum suna falo tare da mami, sai zuby da zarah suna kallo, a dinning kuma su neena ne suna assignment dinsu.
Kiran mummy ya shigo, mum ta dauka suka gaisa, sai mummy take fada mata ai su prince sun daidaita kansu, mum murna sosai tayi .

Mami ta kalli mum, ya naga kina jin dadi, wani abun farin ciki ne ya faru? Mum tace kedai bari danki ya sauko, sun daidaita da amaryarsa, mami tayi hamdala, kice shiyasa bai kiramu ba kwana biyu, toh madallah. Zarah tayi dariya, su ya prince an shiga layi, zuby dake waya kasa kasa , tadan jefawa zarah littafin dake kusa da ita, pls rage muryan mana, zarah tayi dan tsaki, ku bakwa gajiya da wayane, Allah sai na tonaki, zarah tace, mum....zuby tayi super ta rufe wa zarah baki, mami tace Allah dai ya shirye ku, ku kam.

Neena dake assignment dinta, duk maganar su mum tanaji, wani daci taji a zuciyarta, ita kam tana tausayin kanta, soyayya da wanda tasan bazata taba samu ba.tayi tagumi, amir yace anty neena, kalla, neena ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa book din amir din.




*Bayan shekara daya*


Dad da abba tare da mum da mami a falo, dad yace ni kam na kasa gane abunda yaron nan yake nufi, abba yashafa gemun shi, ni kaina wannan al'amari ya dame ni, ka duba ka gani, ko da dayake cikin damuwa yana zuwa weekend ko wani aiki ya kawo shi, mum data buga uban tagumi tace, ni amir kawai nake tausayi, gashi ko ikram din bata kira , mami tace gaskiya ya kamata a je aga ko lafiya, suna cikin maganar, wayar mum tayi ringing. .mum tayi saurin dauka dan ganin numbar prince...
Sun gaisa tace wai kuwa lafiya?, prince yace lafiya lau, amma zasuyi tafiya zuwa Australia, zasuyi watan ni shida, mum ta sauke ajiyar zuciya sannan ta masa fada na rashin kiran su da baiyi ba.

Hankalin iyaye yadan kwanta, matar faruk deeja yanzu har tana da tsohon ciki, faruk shike kula da harkokin su dad yanzu.

Su neena yan makaranta yanzu an waye an kara kyau, su zarah da zuby na kula da ita sosai kamar kanwarsu, amir kuwa yanzu sun zama jini da hanta, yana son neena sosai, hakama ita.

Yau Saturday, neena ta gama shiryawa dan zuwa gaida ummanta, ta shirya amir dan tare zasu tafi.

Dakin zuby ta shiga dan mata sallama, ta iske zuby tasha gayun ta da wani lace , tayi kyau sosai, tana ganin neena tace, ki jirani muje tare, neena tace toh, taga zuby ta yafa babban mayafi, sai mamaki take, zuby zataje gaida umma, shine sai tayi wannan gayun?

Zuby tace wa neena, nayi kyau ko? neena tayi murmushi kinyi masifar yin kyau ma , zuby tayi dariya nagode, wayarta tayi ringing, ta dauka tana murmushi, tace sadeeq, kai koh, sai yanzu ka tuna dani? Sai wayarta takeyi cikin nishadi, ta miko wa neena wayar, gashi ku gaisa, bari naje dakin mum na sanyo turare.

Neena ta amsa, tayi sallama tace ina kwana?, muryar yaya habu taji yana mata dariya, ta ware ido😳, tace yaya habu?, yayi dariya, kwana biyu bamu gaisa ba, zubaida tace kina zuwa lesson ko?, neena tace wai yaya tsaya badai anty zuby kake....yaya habu ya kwashe da dariya, ko batayi bane?, neena tace tayi mana sosai, suka sha fira, daga bisani suka yi sallama, neena tayi farin ciki sosai, dan tana son zuby sosai.


Sunje gidan umman, tayi farin ciki sosai da gani su, sai kallon zuby takeyi, dan yaya habu ya kirata ya sanar mata da zuwan zubaida gaishe ta, yarinyar tayi mata sosai, dan yadda neena ke bata labarin ta.

Amir na jikin umma, dan ya saba da ita, zuby tayi mamakin ganin umma, kyakkyawa ce sosai, kamar su daya da neena, da sadeeq, dandai shi bai kaisu haske ba, sunsha fura , sunyi fira sai da yamma, suka mata sallama suka tafi.


Tun wayar da prince yayi wa mum, bai kara kiran su ba, har wata shidda ya wuce, ana neman wata takwas.

Dad da abba suka kira faruk a falo, lokacin kwana biyu kenan da haihuwar deeja, dad yacewa faruk ka shirya gobe kaje min lagos, ko hauka na'im yakeyi ni na fi shi.....











Aka°•○sultana
[8/9, 8:44 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→9⃣2⃣→9⃣3⃣






Faruk ya mike, toh dad, zanje yanzu nayi booking flight, abba yace toh madallah.
Faruk na fitowa ya iske mum a tsaye ta jingine da bango, ya karasa wurin ta ya dafa ta, mum ki daina tunanin nan pls, inshaAllah komai lafiya, nasan aiki ne ya rike shi.

Mum ta kalli faruk da idonta ya ciko da kwallah, faruk ina ji a jikina na'im na cikin matsala, faruk ya girgiza kansa, mum ba komai kada ki damu zanje na duba su yau dinnan, mum ta rike hannun faruk, ka taimaka kayi booking flight dani faruk.

Faruk yace no mum, ki bari naje ni kadai pls, ki kwantar da hankalinki, mum tace ka taimaka faruk, wallahi kullum sai nayi mafarki da na'im.

Faruk yace toh ba damuwa , amma na yamma ne zan samu, mum tace ba damuwa, zanwa dad dinku magana.

Mum tayiwa dad maganar bin faruk lagos, da farko yaki yarda, sai da mami da abba suka saka baki sannan ya yarda taje.
Faruk ma ya shiga sashen mami wurin deeja, dan tunda ta haihu ya maido ta nan, sunyi bankwana. Su neena, zuby da zarah na wurin ta, kullum a nan suke wuni.



*Lagos*

Faruk da mum sun isa da daddare, suka samu mai taxi driver, ya kawo su har victory island.

A gaban gate ya ajiye su, suka kwankwasa, soja ya bude musu, faruk ya masa bayanin, cewa shi brother din prince ne, sannan wannan , mahaifiyarsa ce, sojan nan yace yauwa, am glad I meet oga's family, ya kalli faruk yace, oga yana cikin damuwa kwarai kwarai, yau 2days kenan bama ganin oga, mum tambayi madam, tace wai miye namu ciki, sojan ya kalli mum, I think oga de sick Ma.

Faruk ya kalli mum, mum ta kalli faruk, hankalinsu a tashe , sojan yace su shiga, mum jikinta na rawa ta shige ciki.

Tun a bakin kofa, suke jin tashin music kamar gidan zai tsage, faruk ya shiga buga kofar amma inaaa ba'a zo an bude ba.
Sojan nan ya karaso wurinsu, ma she no go hear wuna woo, kawai ku bude ku shiga ne, faruk ya murza kofar ta bude, mum ta shige da sauri, faruk na biye da ita.


Ikram suka gani, tare da kawayen ta , yan duniya ne na karshe, ga maza nan suma, an cakude ana ta kwasar rawa, ana zukar sugari, falon ya cika da hayaki kamar ana gobara.

Mum ta saki baki da ido, faruk ya tsaya cak yana kallon ikon Allah, mum ta kasa hakuri dan ganin ikram bata masan sun shigo ba.

Mum tace , *IKRAM*!!!!!!!!!
Da tsawa, har sai da gidan yadan amsa.
Da sauri ikram ta juyo, sukayi ido hudu da mum...
Ta ware ido tana kallon mum, ta karaso cikin rawar jiki, mum tace a fusace ina Dana yake????
Ikram ta nuna mata sama, mum da faruk sukayi saurin saurawa saman, ikram tajaa tsaki, sannan ta sallami duka kawayen shashan cinta.


Mum na shiga dakin, taga dakin duhu, ta kunna wuta, can suka hango prince, a kwance yana lumfashi dakyal dakyal, mum tayi saurin karasawa wurin sa, faruk yazo ya rike hannun prince, yayi baki ya rame, mum ta saki wani irin kukaa, ikram ta shigo dakin, mum ta mike a fusace, ta shiga wanka mata mari..., ihun da ikram tayi , yasa prince mikewa da kyal, yacewa mum, kada ki kara marin mum, da sauri mum ta juyo tana kallon shi, tace na'im ba hankalin ka daya ba, prince ya daddafa ya mike, yayi wurin ikram ya rike ta, sai kukan shagwaba takeyi, faruk yace ya prince, ciwon kane ya dawo?, Prince ya wani harare shi, ya nuna musu kofa, ku koma gida, zan zo...
Mum ta kasa cewa komai, sai kallon prince takeyi.

Faruk ya rike hannun ta, yaja ta suka fita..

Wurin sojan suka dawo, yace ai nasan madam ba mutumin kirki bane, faruk yace wa mum, ya prince ba hankalin sa daya ba, kuma ciwon sa ya dawo, dan yadda naga yana lumfashi, sojan nan yace, eh mana an taba kai oga hospital yayi collapse, hankalin su ya kara tashi, mum sai kuka takeyi, faruk yace, muje nayi miki booking flight, ki koma gida ki sanar dasu dad komai, ni zan tsaya nan.
Mum ta kada kai kawai.


Mum ta isa da daddare sosai, ta iska yayaB tazo dan lokacin an kusa babbar sallah.
Hankalin kowa sai daya tashi ganin yadda mum ta dawo, ta kwashe komai ta fada musu, kowa hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, neena dake labe itama tana komai, wani hawaye taji yazo mata, ba karamin tausayin prince tayi ba.

YayaB tace , wannan al'amari harda sihiri, amma na'im bazai taba aikata haka ba, abba yace gaskiya wannan al'amari abun a duba ne, dad yace aikuwa dani ake zancen, ya ciro wayarsa , ya kira numbar wani malami, daya koyar dasu prince din islamiyya.

Suna nan zaune jugum a falo, ya iso, malam ya zauna aka fada masa komai, yace toh su bashi dan da gobe da safe.

Da sassafe malam barau, bayan kowa yazo ana jiran bayanin sa, yayi gyaran murya yace, gaskiya, wannan al'amari bayyi dadi ba, wato na'im dai _SIHIRI_ akai masa....

Gaba daya falon suka hada baki wurin cewa sihiri....






Aka°•○sultana
[8/9, 8:44 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→9⃣4⃣→9⃣6⃣







YayaB tace, bana fada muku ba, wannan aikin sihiri ne.
Abba yace , yanzu yaza'yi kenan malam?
Malam barau yace, bakin sihiri ne akai masa, dan haka dole ne sai an kawo sa nan.
Dad yace, yanzu ya zamuyi mu kawo na'im nan?, mum tace gaskiya zaiyi wahala dan na'im zai iya hallaka wani dan ikram.
yayaB tace, ku kira min faruk dai ku gani, mami ta saka kiran faruk ta mikawa yayaB.

YayaB tayi masa bayani, kamar yadda malam yayi musu, faruk yace da wuya ikram tabar ya prince ya biyo ni, yayaB tace , kace mata mahaifiyarta ba lafiya, idan kun iso airport, ka make shegiya ka taho mana da na'im kaji!!? Faruk abun dariya yama bashi, yayaB taja tsaki,dadi nadai tsoro wlh, duka nawa take, faruk zai magana, yayaB tace kai kayi maza da Allah, malam nada abunyi, ta kashe wayar.

Neena ranar gaba daya tana daki, sai karatun alqur'ani takeyi, tana wa prince addu'a.

Kamar yadda yayaB tace wa faruk yayi, haka kuwa yayi, da wayar soja John suka kira ikram, sukayi mata karya, kamar dai likita ne ya kirata mahaifiyarta na asibiti, hankalinta yayi mugun tashi, kuma Allah ya taimaka, duk numbars din data kira basa shiga, da yake da sassafe ne, lokacin mummy ma basu kai ga tashi ba.

A take tayi booking flight, tare da prince, dake jin jiki, kokari kawai yakeyi yana binta.

Faruk ma ya bisu, a jirgi daya suke, amma faruk bai yarda sun ganshi ba.

Suna isowa abuja, dama an turo driver, ikram na rike da hannun prince, daya koma kamar wawa sai binta yake kamar bindi, sukazo neman mai taxi, a inda suke tsaye, motar su faruk ta tsaya, fitowa faruk yayi, ya fisge hannun prince daga na ikram, yayi saurin turasa cikin motar duk da prince din na fisge wa, ikram ta shiga kuka, tana bin motar, amma inaa su faruk sun mata nisa.

Suna isa gida, faruk ya riko prince, prince na sauko da kafarsa, yaji kan sa ya sara masa, ya dafe kan, faruk na masa sannu, har suka karasa cikin falon, duka family suke mike , sun tausayawa prince mutuka, mace ta kusan hallaka shi.

Mum kuwa hawaye kawai take, dan ita taja masa, tunda dama bason auren yake yi ba, duk ita taja wa danta wannan wahalai.

Faruk ya zaunar da prince gaban malam, malam ya kurawa prince ido, ya taso yazo ya dafa kansa, yayi masa addu'a , sannan ya basa ruwan addu'ar , da kyal aka samu yasha, aka shafa masa a fuska, take prince ya fara yi kamar zaiyi amai.

Malam yasa zarah ta kawo ruba, ai kuwa prince ya shiga kwara aman wani irin bakin abu, yana gamawa ya fadi sai barci kuma.
Malam yace ku kaishi daki, idan ya farka inshaAllah zai dawo daidai.
Dad yayi masa godiya sosai, abba yace wa faruk, ya kira driver su kama sukai shi dakin.
YayaB tace, malam ba wani maganin da zaka basa ne, mami dake zaune shiru tace, eh malam ko ruwan addu'a babu?
Malam barau yace, zan aiko a kawo masa anjima, akwai su duka, amma sai nan da yamma InshaAllah.

Sukayi wa malam godiya, akasa faruk ya maida sa gida.


Ikram kuwa hankalinta ya tashi, tasan dole ne iyayen prince suyi masa magani,tasan kashinta ya bushe, gidan su ta nufa, kamar mahaukaciya, ta shigo falon, mummy, moha, fuad duka da abban su , suna dinning suna breakfast.

Tana shigowa ta zube a kasa, sai shure shure takeyi, mummy tayi kanta tana tambayar ta hankali tashe, tace, lafiya ikram da sassafen nan?, ikram tayi dariya, sai sushe sushen kai takeyi, ta fara zaiyana duk wani asiri da tayiwa prince.

Abbansu ya fusata sosai, mummy kuwa zaman dirshan tayi, moha ya kasa dauke ido daga kallon ikram, mamaki yakeyi, yauwa ikram tayi wayo da har tasan tayiwa wani asiri, abbansu yahau dukanta kamar jaka.
Mummy ta tashi tana basa hakuri, ya ture ta yana fada kamar zai cinye su, duk laifin mummy ne kawai yake cewa, bata bawa yayan ta tarbiyya ba, ranar ikram duka har sai da abban ya gaji ya ya fice cikin konar rai, nan kuma ta fara hauka, hankalin mummy in yayi dubu ya tashi, tasa moha ya kamata ya kai daki suka kulle ta, suka fita dauko likita.


Mami da mum kitchen suka shiga, suka shiga hadawa prince girki kala kala, hankalin su kwance, sai godewa Allah sukeyi.

Zarah da zuby tare da faruk su, aka bari dakin prince su kula dashi.
Neena da amir , kuwa turasu akayi wurin deeja, dan kada kadaici ya dame ta.

Hankalin neena ya kasa kwanciya, ita kawai burinta shine, taga halin da prince yake ciki, deeja tace, neena kodai bakya jin dadi ne, yau ba ko fira, baby ma tayi missing din daukarta da kike.

Neena tayi murmushi, lafiya lau anty deeja, kawai dai tunanin waec dinnan zamuyi nakeyi, deeja tayi dariya, ba wani wahala gareta ba, indai kinyi karatu.
Neena tayi murmuahi, ta mike tazo ta dauki babyn, tana cewa, bari ya faruk yazo, sunana za'a sawa babynah.




Aka°•○sultana
[8/9, 8:44 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→9⃣7⃣→1⃣0⃣0⃣






A hankali prince ya bude idonsa da sukayi masa nauyi, zarah tace ya faruk, ta nuna masa prince, faruk yayi saurin kama hannun prince, ya prince sannu, baka jin komai ko, prince ya motsa bakinsa, a hankali, dauko min drugs dina, faruk yace wa zuby, duba acan ki dauki drugs dinda abba ya kawo dazun.

Zuby ta kawo, zarah ta fita ta kawo masa ruwa, tare ta shigo dasu mum.
Sai sannu suke masa, mum tace na'im badai inda ke maka ciwo ko?, prince yace a hankali, zuciyata nadan zafi, amma nasan idan nasha magani zai bari, kada ku damu.
Mami tace sannu dana, kai faruk taimaka masa yayi wanka.ku kuma muje ku dauko abincinsa.

Prince yayi wanka, ya saka kana nan kayansa, su zuby suka zuba masa abinci, yaci bana wasa ba, sai mamakin shi sukeyi, dan bai cika cin abinci haka dayawa ba.

Su neena kuwa suna sashen mami, tadan sake suna fira da deeja.
Faruk ne ya shigo dakin da sallama.
Deeja tace sannu , ya jikin yaya prince din, faruk na neman zama gadon yace, da sauki yama tashi yaci abinci, kinsan abun ya hadu da miskili, sai a hankali.
Neena dake jinshi, taji wani sanyi a zuciyarta.
Faruk yace, su neena yan waec ana dai karatu ko? deeja tayi dariya, tana nan tana tunanin exams dinma, faruk yace kiyi karatu ba wani wahala garai bane, neena tace karatu kam muna tayi, sai dai yaya ku taya mu da addu'a , faruk yace inshaAllah, yauwa munyi waya da sadeeq, yace gobe zai dawo daga Jordan.
Neena tayi murmushin jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login