Showing 24001 words to 27000 words out of 44930 words

Chapter 9 - Yar Talakawa Complete Hausa Novels by Afrah.txt

Advertisement

29 Sep 2025

3408

tsaya cak ta kasa juyowa, prince ya mike ya kusanto ta sosai.
Neena gabadaya taji lumfashin ta na neman ya tsaya, toh mai hakan yake nufi?
Bata idasa tunanin da take yi ba, taji prince ya juyo da ita, ta fada a faffadan, kirjin sa, ta ware ido a tsorace...
Saukar ajiyar zuciyar shi , gabadaya gabobin ta, suka kasa yunkurin kwace kanta daga kirjin sa, ta shaki kamshin sa, ta lumshe idon ta, take taji kamar an dasa mata wani masifaffen sonsa.


YayaB ce tazo wurin window din dakin ta, neena ta manta bata kullo min windows dinnan ba yau.....
Hango su prince tayi, da yake akwai , wutar lantarki ta wajajen, ta haska su.
Ta kura musu ido tana kallo, taji mamaki kwarai, ashe akwai ranar da prince su wata banda nateefa, ta kullo windon ta dawo ta zauna bakin gadon ta tana tunanin wannan al'amari.


Sai da sukayi minti sha biyar a haka,sannan prince yasa hannu yadan matsar da ita, yayi tafiyarsa zai shige cikin gidan, neena tabi bayan sa da kallo, har yakai kofar shiga ya tsaya, ya juyo, shi take kallo, ya sakar mata murmushin da tunda take dashi bata taba ganin yayi saba.
Neena mutuwar tsaye tayi , bata san lokacin da kumatun ta da lips din ta, suka bayyanar da murmushi ba, prince ya juya ya shige ciki.

Yana zuwa dakinsa, ya dafe kirjinsa, sai bugawa yakeyi da sauri da sauri, ya runtse idanunsa, koda yayi soyayya da lateefa, bai taba jin wannan yanayin ba, ya dafe kansa, noo prince u cant fall inlove wit dat small gal, gata _YAR TALAKAWA_ yarinyar da bata waye ba, yarinyar dake matsayin mai rainon danka, yaja tsaki da yaji zuciyarsa ta fara zafi, ya mike ya dauko drugs dinsa ya sha, sannan ya kwanta, wani barci mai dadi ya dauke shi mai tattare da mafalkai masu annashuwa.

Neena ma daki ta koma bayan ta duba amir yayi barci, ta haye saman gadon ta, tana murmushi kamar bakin ta zai yage, ta mike ta zauna tsakiyar gadon, ta dafa kirjin ta, ta runste ido, ta shiga tunano duk wani moments da sukayi da prince.
Can kuma tadan tsaya da murmushinta, mai yasa toh ya rungume ta, kodai tausayin ta kawai yaji, ba sonta yake ba, ta buga uban tagumi tace....
Ya za'ayi kuwa ya prince yaso ta, _YAR TALAKAWA_ da ita, wadda a karatu ma ajin ta uku ta tsaya, ta sauke ajiyar zuciya, shi dake da mata kamar ikram ai bazai taba son mace irin taba ( ni kuwa afrah nace, kedai duba mirror _NEENA_)
Tadan buga goshin ta da tafin hannun ta, neena ki dawo daga duniyar tunanin ki.


ikram kuwa neena na wucewa , ta kira mummy dinta, ta fada mata komai tace, mummy ba inda zani da wannan karuwar yarinyar, gara ma kusan abunyi kafin gobe eheen.
Mummy tace, haba ai koni bazan yarda ki tafi da itan ba, zan kira mum dinshi, zamuyi maganar, ba inda yarinyar nan zata biku.
Ikram tace, ni mummy har amir din ma, bana so ya bimu, da rainon shi zanji ko da cin amarcina ( kuji fa mutum yana magana da uwarsa amma kamar yana yi da kawar sa zamani kam ya canza).

Mummy tace, hakane gaskiya bari na kira mum dinshi muyi maganar, ikram tace toh mummy , sukayi sallama.

Moha dake zaune kusa da mummy yace, mummy mai ya faru ne da ita ikram dinnan, uwar shaida.
Mummy ta fada masa, ikram na zargin prince da mai rainon amir.
Moha yaja tsaki, dama ashe akwai abunda ke tsakanin su, shiyasa ranar ya bata min show, mummy tace kasan suna tare kenan, moha yace eh mana mummy ranar family dinner, ya ganni tare da ita, shine yazo ya wani kora ni, ashe dama shike nemanta, mummy taja tsaki , kai kuwa mai zakayi da wannan aljanar yarinyar, ga yan'matan a gari, moha yayi murmushi, mummy Allah yarinyar ce akwai kyau, mummy tace ,kadai bi ahankali idan abban ku ya san da wannan banzan halin naka , bazakaji da dadi ba ( pls iyaye mata a kiyaye).

Mummy ta kira mum, suka maganar , mum bataji dadi ba ko kadan, tayiwa prince aure ne, dan amir ya samu wadda zai kira uwarsa, amma ba damuwa nan gaba sai yaje, dan maganar mummy tayi tasiri a zuciyar mum, da tace idan amir da neena sukaje, su ikram "bazasu sake da junan suba"


Washe gari da sassafe, aka taru family, a babban falon dad.

Abba yace wa mum, ita neenan ta shirya daiko? Ikram tayi saurin kallon mum, suka hada ido, mum tace ai bada su zasu tafi yanzu ba.

Dad yace kamar yaya? Mum tace wai da idan sunyi dan watan ni sai akai su amir din , abba yace hakan yayi, ikram tayi murmushi ta kallo prince...






Aka°•○sultana
[8/9, 8:30 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→8⃣1⃣→8⃣5⃣









Prince ya dauke kai, yayaB ta gyara murya, toh idan dai bazata bi su na'im ba, nizan tafi da ita.
Duka falon aka kallo ta, tace ku kalle ni dakyau, ta kalli abba , yau zamuje ka kaini gidan su, nayi magana da umman ta, ta bani rikon ta, nasakata makaranta tayi karatu itama.
Dad yace , yayaB ai ko anan dinma zamu saka ta, amma raba neena da amir zaiyi wahala.
Abba yace kwarai kuwa, kada ki damu indai karatu ne zamu saka ta tayi inshaAllah.
YayaB tace toh shikenan, dan dai bana son amir yayi rashinta ne kawai zan barta anan.
Abba ya kalli faruk dake zaune suna magana kasa kasa da zarah, yace kai faruk, makarantar nan dakayi service, kaje ka nemawa neena, dad yace kaje ka tambaye ta inda ta tsaya.
Faruk yace toh dad, yaci gaba da maganar su da zarah, yayaB ta kai masa duka, kaji ja'irin yaron nan, an maka magana amma ko tashi bakayi ba, faruk yace, haba yayaB zan tashi mana, yayaB tace ai fah, an zama ango har an fara rashin kunya, nan da jiyane ana fada zaka mike, saura ka zama mijin hajiya...
Aka kwashe da dariya, amma banda prince, mikewa yayi ma zai fita, yayaB tace su oh oh kuma, sai bakin rai, ana so ana kaiwa kasuwa...
Ikram tayi wani fari da ido, prince yace ehh din ina ruwanki, yayi ficewarsa.
Mum tace, ikram muje ki dauko jakar ki , flight din 8 zaku bi, mami ta mike tana cewa, bara na daukowa na'im danbum naman sa.

Prince ya fito da jakar shi, ya bawa faruk yakai masa mota, dakin amir ya nufa dan yi masa sallama.

A zaune ya iske su, suna wasan *X* and *O* a ipad din zuby.
Sai dariyarsu sukeyi, ya tsaya yana kallon su, amir yace anty neena banda cheating fah, neena tace little master, kaima fa dazun kayi , amir ya amshe ipad din ya haye gado yana cewa, toh dukkan mu winners ne, neena ta fara binsa yana guduwa, tace ban yarda ba, dawo mu sake wani...
Suna cikin wasan su, basu ma lura da prince dake tsaye bakin kofar ba...
Sai da zarah tazo wurin tana cewa, ya prince ka fito inji su mum...sai sannan neena ta juyo ta ganshi a tsaye, tayi saurin tsayawa daga wasan da suke, amir yayi wurin papa dinsa, prince ya shafa kansa, ya riko hannun sa, suka fita.
Neena tabi bayan su itama.

A waje faruk ne zai kaisu, mum, mami , zarah, zuby duka ana wajen, yayaB taki fitowa , wai barcin ta zata koma.
Mum ta rike ikram, tace ki kula da kanki dear, ikram tace toh mum, zuby da zarah sukayi hugging dinta, sukace ki kula mana da yayan mu, ikram tayi murmushi, mami tace shiga ikram kada kuyi latti, ikram ta shiga, prince ya fito da amir, yace takecare my boy, amir yace I will papa, prince yazo yayi side hugging mum, tace Allah yayi maka albarka , ka kula da matarka da kanka pls, prince yace ok mum, yaje yayiwa mami, ta mika masa wata leda, ga danbum naman, prince yace a'a mami ki barshi, mami tace aikuwa sai ka tafi dashi, wahalar neena bazata tafi a banza ba...
Ikram najin ance neena, ta kallo neena dake rike da amir ta balla mata harara, neenan ma bata san tanayi ba.

Prince ya juya yakalli neena, bata san lokacin da tayi masa murmushi dole ba, dan wani daci takeji a zuciyarta, yanzu idan ya tafi bazata gansa gobe ba, hakama jibi, wasu hawaye suka sulalo mata.

Prince ya amsa ledar yace nagoda mamina..
ikram ta duba jakarta dan dauko chewing gum, taga ba dayar wayarta data bari a dakin mum dataje dauko gyelen ta, tace laah! na manta wayana a dakin ki mum,mum ta kwalawa neenah kira, jeki daukowa ikram wayarta a dakina yi maza.

Neena ta saki hannun amir tace toh, ta shige cikin gidan.
Prince na ganin ta shiga yace oops nima na manta drugs dina, mum tace yi maza kaje ka dauko, prince ya juya shima ya shige cikin gidan, ikram ta tabe baki kadai gama yangar , sai ka dawo cikin tafin hannun nan nawa.


Neena ta dauko wayar ta fito, a lungun da zai fitar da ita zuwa benen suka hadu da prince, tafiya kawai takeyi amma hankalin ta baya jikinta.
Prince ya kura mata ido tana tahowa tazo har zata wuce sa, taji kamshin nan nasa dasauri ta tsaya ta kallo shi, prince ya kura mata ido shima ya sa hannunsa a kyakkyawar fuskarta, neena zata ja baya, yasa dayan hannun sa ya riko hannun ta, ta kalli fuskar sa da sauri..
Ya wani daure fuskar tana kallon shi ya karasa kai hannunsa kan kumatun ta, ya goge mata ziraren hawayen fuskar ta.

Neena ta kasa controlling kukan daya zo mata, ita wai meyasa ya prince yake mata hakane, ya kuwa san hakan da yake mata yake sa tana kara sonsa, shi tunda ba sonta yake ba ya daina tausayin ta mana....
Wani kuka yazo mata, ta saki kukan, gwanin tausayi, fuskar nan har ta fara yin ja, wani abu ya tsayawa prince a makoshi, kirjin sa na bugawa da sauri da sauri, shi ma kansa ya rasa mai yasa yake jin tausayin yarinyar, kwata kwata baya son yaganta cikin damuwa, ganin hawayen ta dazun shiyasa yayi karyan dauko magani dan kawai ya lallashe ta..
Neena ta janye daga rikon da yayi mata, taci gaba da tafiyarta, prince yayi saurin karasawa wurin ta, ya jawo hannun ta suka shige dakin zuby dake kusa da wurin..

Ya saki hannun neena ya juya mata baya, tayi tsaye tana share hawayen ta tana shashshekar kuka, prince yace da silent muryar sa, kee mai yasaki kuka uhm, neena tace ni ba kuka nake ba, prince ya juyo yace toh me kike? Neena tace ni hawaye nake, prince ya kalle ta mai ya saki hawayen? Neena tace wani abune ya shigar min ido na.

Prince yadan naushi hannun sa, yaso ace neena ta fada masa cewar danshi take kukan, shi baya son raini dan haka koda son ta yake ma, bazai taba fada mata ba.

Yayi dan tsaki yazo ya bude kofar ya fice, neena ta saki wani kukan, tayi saurin lallashin kanta ta goge hawayenta tayi waje da sauri.

A wajen ta iske shi zai shiga mota, ta mikawa mum wayar ikram, mum ta bawa ikram zuby tace wa neena, mai ya samu idon ki? neena tace wani abune ya shigar min, ta riko hannun amir suka shige ciki.
Prince ya shige mota shima, faruk yaja suka tafi, su mum nata musu bye bye



Edited by namecy♥afrah😘


[truncated by WhatsApp]
[8/9, 8:40 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→8⃣6⃣→9⃣0⃣







Neena dakinta ta shige, amir na kiran tama bataji shiba, ta haye saman gado , tana rusa kukan da baya da dalili, ita wacece da zatayi kuka dan ya prince ya tafi, ko amir baiyi ba sai ita, wata zuciyar ta bata amsa da , ke masoyiyar sace, kuma mai kaunar sa, neena ta daga hannun ta sama.

Ya Allah kaine ka halicci, dukkan bayi ka, Allah kai ka saka min son wannan bawan naka, Allah nasan bankai matsayin yin soyayya da wannan bawan naka ba, ya Allah ka zaba min abunda yafi alkhairi, ta sha a fuskar ta, sannan ta mike ta dauro alwala, tazo tayi nafila raka'a biyu, a take taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta.


Su prince sun sauka lagos lafiya, sojoji ne suka zo daukar su, ikram sai cika take tana batsewa, shi prince gaba daya ma ya kosa ya isa gida ya samu peace of mind, dan wani haushin ikram dayake ji, gaba daya bata burge shi.


Sun isa kantamemen gidan prince dake Victoria island, a lagos, gaba daya gidan sojoi ne, suna sauka a mota, duka sojojin dake wurin suka zo suka sara masa, ya daga musu hannu kawai ya shige ciki, ikram na biye dashi.

Dakin sa ya shige, ta biyo shi ciki, prince yace dakin ki na can a gaba, ikram zatayi magana ya shige toilet abunsa, ta sauke ajiyar zuciya, lallai sai tayi aiki wurin shawo kan prince dinta.

Da daddare ikram aka ki barci, sai jiran ango takeyi, amma har sha biyu shiru bata ko kyallin prince ba.

Ta naushi gadon ta, taja tsaki, ta mike ta fito zuwa nasa dakin, ta murda kofar taji ta a kulle, ta shuri kofar ta koma dakin ta.

Prince najin ta tana murda kofar, yayi tsaki, mayya kawai, sannan ya dauko ledar danbum naman da mami ta basa.

Ya bude, wani kamshi ya doki hancin sa, ya bude robar, yasa hannu ya dibo kadan ya saka baki, wani dadi yaji ya mamaye bakin sa, ya lumshe idonsa, take ya tuno dazun, daya juyo yaga hawaye a fuskar neena, ya bude idon sa , yayi dan tsaki, why do I care about ha?, yayi kansa tambaya, ba sonta kake ba , tausayinta kake, wata zuciyar ta basa amsar tambayar sa.

Ya mike ya koma kan gadonshi, ya jawo wayar sa, ya kai sunan mum, Ya sa kira.

Mum ta dauka, ya sanar mata sun iso lafiya, mum ta kara masa fada sannan sukayi sallama.
Ya mirgina , yana tuna lokacin daya rungume neena, ya sauke ajiyar zuciya, sannan runtse ido, a haka barci yayi awon gaba dashi.


Sati daya kenan da zuwan su prince lagos, amma ba abunda ya shiga tsakaninsu, kullum prince na busy wurin aikin sa, ikram abun duniya ya taru yayi mata yawa, gashi duk aikin gida ita keyi, duk da bata wani iya ba, shiyasa prince a waje hake siyo abincin sa.

Yau dai hakurin ta ya kare, kullum ta fada wa mummy sai tace, tayi amfani da hikimarta ta mata ta jawo ahi jikinta, taja tsaki ita mummy bata gane bane, ni ina ma ganin sa ne.

Wayarta tayi ringing, wata sharifa ce, kawarta ce dake zama a lagos, ta dauka sukayi fita kadan, shine take fadawa sharifat, din ko zata taimaka mata, dan sharifat, gogaggiyar yar duniya ce.

Sharifat ta fadawa ikram, gobe zata zo suje wurin wani, bayarrabe ya iya aiki sosai, ikram tayi murna sosai tace mata to sai tazo din.

Neena yanzu harta fara zuwa school, tana ss1 yanzu, idan ta dawo sai ta shiga kula da little master dinta, kullum zata kwanta sai ta tuna da ya prince.

Faruk kuwa, suna zaune lafiya da matarsa deeja, duk Fridays, sai ya kawo ta , yayaB ta koma itama, su zuby da zarah suna busy da makaranta, yanzu gidan kullum shiru, dad da abba sunyi tafiya hajji.


Sharifa tazo gidan ikram, Allah ya so su prince baya nan ma, ikram ta shirya, ta kwashi kudi sosai, cikin wadanda ta samu na biki, sukayi wurin bokan yarbawa.


Sunje wurin shi, tsoho ne mutumin, baki mummuna, ikram ta tsorata da farko sosai, sharifata ta fada masa bukatar su, yayi sundabaru yace, zasu kawo masa jinin ikram na hayla, sannan zasu biya kudin aikin aljani.

Ikram ta gwale ido, sharifat ta kara zurmiyar da ita, ikram tace ai yanzu ma tan _ON_ ne, bokan yarbawa ya bata wani kallo kallo, yace taje ta diga jinin a kai, ikram tayi yadda yace, sannan ta biya kudin aikin bakin aljanin da zasu turawa prince.

Komai an kammala, boka yace taje gida zata sha mamaki.


Duk wannan abun dare ya tsaya sosai, prince ya dawo bai iske ta a gidan ba, yaja tsaki ya koma nasa dakin, yayi sallah yadan kwanta yana rage gajiya.
Cikin barcin sa yayi mummunan mafarki, wai ga wata bakar mata nan tazo da wuka zata kashe shi, har tazo zata tsaka masa wukar, wata tazo cikin fararen kaya ta rike hannun bakar matar, bakar matar ta ture mai farin kayan sannan ta hadasu duka zata kashe, dai dai prince ya farka....

Yayi zufa sharkaf, da kyal ya iya furta, a'uzubillahi minal shaidanil rajim.
Dai dai nan ikram ta shigo dakin cikin isa, prince na ganin ta ya mike, yayi saurin zuwa ya rungume ta, yana sauke lumfashi, ikram tayi murmushin samun nasara, sannan ta shafa kan prince...






Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login