Showing 3001 words to 6000 words out of 44930 words

Chapter 2 - Yar Talakawa Complete Hausa Novels by Afrah.txt

29 Sep 2025

1469

β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:50 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah



Episode4⃣



Wani katon gida ne mansion, mai dauke da fulawoyi, ko ina , ga swimmingpool da garden babba , ko ina security ne, gidan kashi biyu ne duka iri daya ne , hawa bibbiyu, wasu motoci na hango manya manyan gaske, daga benz sai prado, cikin gidan nan suka nufa da jiniyar su.

Wasu matane su biyu naga sunyi saurin fitowa daga cikin gidan, sanye suke cikin kaya masu shegen tsada, sunci gayu kamar zasuje wani occasion, fuskar su dauke da murmushi, da gani cikin farin ciki suke.

Ana gama parking din motocin nan, wasu na gani da kayan sojoji sunyi saurin fitowa daga cikin daya daga hiking motocin nan, motar dake tsakiya naga sun nufa, bude kofar motar sukayi, sannan suka sara, (da gani dai ko waye a ciki soja ne shima)

wani kyakkyawan handsome ne ya fito daga cikin motar, sanye yake cikin wandon sojoji da farar top, yana da tsayi sosai, da ganin shi kaga jarumin namiji mai ji da kansa, fuskar shi ba alamun wasa, a daure take , idanun shi medium ne masu kyawun gaske, ya saka sun glasses, bakin sa dan karami, hancin sa nada tsayi mashaAllah, fuskar shi ba saje ko kadan da gani ya aske ne, dan akwai shaidar gashi a wurin,
(O.M.G ni kaina afrah sai dana kyasa wannan guy din)


Yan matan nan naga sunyi saurin zuwa wurin shi, daya mai haske kamar shi, sai daya mai dan duhu , a tare sukace you are welcome ya "PRINCE!!"


Glasses din idon shi ya cire, yadan kalle su kadan, fuskar nan a daure, ya galla musu harara yayi cikin gidan.

Mai duhun tace, zarah kinga wulakancin da kika ja mana ko!, kalla a gaban sojojin nan ya disga mu, mai hasken tayi dan murmushi, ta dafa dayar tace zuby kin cika surutu, ke kanki kin riga kin san halin ya"PRINCE" ai, muje pls na sake ganin cute face dinnan tasa, taja hannun zuby sukayi cikin gidan suma.


WAYE PRINCE ?????

Readers nasan kuma kuna son sanin waye shi, dan haka ku biyo afrah luv dan yanzu labarin YAR~TALAKAWA ya fara.....





β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:55 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah




+2347010902548
Episode 5⃣





Zuby da zarah na shiga suka iske ya prince a zaune falo,tare yake da mum da mami, zama sukayI suma suna kallon shi yana gaisawa da iyayen sa, amma fuskar sa ko gizo.

Mum ta kalli prince tace , my son kana kuwa cin abinci a lagos dinnan?, mami tayi murmushi tace gaskiya baka cin abinci sosai prince, prince ya mike yana kallon su yace, mum, mami let me fresh up , yanzu yunwa nake ji,bazan iya duguwar magana ba, zuby ta kalli zarah, zarah ma ta kalli zuby, suka rike baki, ashe har iyayensu yana wa wannan miskilancin.

Yayi one step kenan, wani kyakkyawan yaro, mai kimanin shekaru shidda,ya fito daga wani daki dake kusa da falon da gudun sa, PAPA! PAPA!, yake ta cewa, wata ce ta biyo sa , da gani dai mai aiki ce dan tana sanye da wasu uniform ne kalar baki da fari.

Yaron yazo ya rungume prince yana dariya, mum tace su AMEER anga daddy yau sai aci abincin kirki, amir ya dago ya kalle ta , grany yau zanci ko me kika bani, mami tayi dariya, zan maka pancakes kuma dole ka cinye su, amir yayi dariya qibin hakorin sa ya fito, yace zan cinye grany mami.

Su zuby da zarah suka kura ido suka ko prince zai wa amir smiling, ga mamakin su sai suka ga ya shafa kansa kawai, ya rike hannun sa sun haura sama.

Zuby tace zarah ya prince bai canza ba ko kadan, see fa ko little amir dake mutuwar son ganin Papa dinsa amma baiko yi wa poor boy din smiling ba, zarah da tayi tagumi tana kallon zuby tace, halin ya prince sai shi amma ni yana burge ni a hakan ma, zuby ta mike, tashi muje daki kafin ya same mu anan kema kinsan sauran.

Prince a kwance a saman katoton gadon shi, mai laushi, yana hutawa kafin su dad su dawo yaje ya gaisar dasu.

Amir ne ya shigo dakin da gudu ya haye saman bayan prince, yana dariya cike da fara'a yace , papa papa! Yau zamuje ka kaini nasha ice cream ko kai kuma kaci pizza??, prince ya kada masa kai kawai, amir ya mirgino ya kwanta yana kallon papa dinsa, yace papa kasan me, prince ya girgiza masa kai, yace jiya ko grany mami tayi wa anty zarah fada a falo, prince ya ware ido yana kallon amir, amir yace kasan me tayi , prince ya girgiza kai, amir yakai bakin sa kunnen prince yace, wai taje party din frnd dinta da daddare.

Prince ya mike ya zauna, ya kalli amir yace da anty zuby sukaje?, amir ya girgiza kai, sannan ya sake matsowa kusa da prince yace papa, kasan me anty zuby tayi yau da safe? Prince ya girgiza kai, amir yace, grany ta kama ta tana wa uncle fahad rashin kunya.
Prince yace good boy,ya shafa kansa, kai kuma mai kayi da bana nan, amir yayi saurin mikewa , yana zuwa bakin kofa yace papa, na samu 5/10 a math, yayi saurin gudu, dan yasan halin papa dinsa.
Prince yace zamu hadu dakai kaima.




β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:55 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah




+2347010902548
Episode 6⃣




Prince bai fito daga dakin sa ba sai da yamma, ya shirya cikin kananan kaya,ba karamin kyau da kwarjini yayi ba, fuskar nan a daure yazo wuce falo dan zuwa babban falon dad dinsu, zarah ce a kwance tana kallon vampires diaries,bata lura da shigowar ya prince ba, kwata kwata,tsawa taji kawai a kanta,Kee!! Zarah tayi saurin mikewa tace na na'am, prince ya galla mata harara,da kyal ya iya bude bakin sa yace,ki kira zuby kuje garden ina zuwa, zarah ta ware ido,tayi saurin cewa wayyo ya prince kayi hakuri.

Prince bai ko kalle ta ba yayi ficewar sa.zarah ta dafe kirjin ta yau mun shiga 10,dan 3 kadan ne.

Dad da abba ne zaune a falon, prince yayi sallama ya shiga.
Abba yace major an tuna damu kenan?, prince ya samu wuri a kasa ya zauna, dad ya kalle shi yace, kunzo wani aikin kenan nan abuja?, prince ya kada kai,dad ya kalli abba yace,na fada maka ai, abba yace, NA'IM ya kamata ka manta duk wani abu daya faru a baya, u most go on with your life,kowa ya maidaka kumurci, duk yaran nan da sunji zuwan ka hankalin su sai ya tashi , haba ! shekaru biyar kenan fa.
Dad yaja tsaki,kai ma dai Usman baka gajiya wlh,kullum sai ka maimaita masa wannan maganar,ni nama gaji da masa fadan nan, dan shi ba yaro bane yanzu,he should knw by now he have to go on in life,prince dai kansa na sunkuye yana sauraron su,sun yi fadan su na kullum , sun gaji,prince ya mike yace dad,abba, dama muna da meeting da general ne a abuja, nan da kwana hudu zan koma inshaAllah, dad yayi banza dashi, abba ne yace toh Allah ya kaimu.

Zarah a goje ta shiga dakin zuby,ta iske ta tana chat a wayan ta, zuby tace yauwa zarah zo kiga guy din nan da nake fada miki,he's darm handsome,wlh kamar ya prince.
Zarah tace kee its nt time for dat nw, tashi fa tamu ta kare, zuby ta kalle ta, meya faru? Zarah tayi saurin amshe wayar dake hannun zuby , ta ajiye a gadon tace, tashi muje garden, zuby ta kalli zarah tace me zamuyi acan din?, zarah tace ohhh har kin ma manta mai ke kaimu garden ko??, zuby ta ware ido ta dafe kirjin ta,tayi saurin mikewa, dnt tell ya prince....kafin ta idasa zarah tace, shine yace muje mu jirashi acan, zuby tace muje muje pls ban shirya tsallen kwado ba wlh.

Prince na barin falo wurin abba , direct garden ya nufa, as expected , ya iske su a tsaye cikin garden din suna jiran sa.

Prince ya zauna a wasu kayatattun kujeru dake tsakiyar garden din.
Da hannu yayi musu nuni dasuzo kusa, cikin rawar jiki suka karaso, prince yace wato idan kunga bana nan , sai ku riga duk abunda kuka ga dama ko!!!!!
Sudai sun sadda kai kasa kawai, prince ya daura kafar sa bisan table din dake gabansa yace, ke zarah, partyn dare, ya nuna zuby , ke kuma rashin kunya , ya daga murya yace Ko! Suka hada baki wurin cewa , bazamu sake ba ya prince.
Prince ya mike yace, basai na fada muku me zakuyi ba,am sure baku manta ba, yayi hanyar gidan abba, dake kusa da nasu,yana cewa zan turo Sargent ema ya duba min ku.

Yana shiga kayatatcen falon gidan abba,komai da komai irin nasu ne,colour ne kawai ya banbanta, ya iske Fahad tare da amir suna zaune a three seater , suna temple run, a wayar fahad din.
Prince na shiga ya samu kujera ya zauna, fahad yace, ya prince sannu da zuwa, dama yanzu nake shirin zuwa gaida kai.
Prince yace a takaice , ya service din? Fahad yace alhamdulillah,muna nan muna fama, prince yace Allah ya taimaka,fahad ya amsa da amin, prince ya kalli amir dake faman game dinsa yace , amir come here! Amir ya mikawa fahad wayarsa yace ok papa, har yazo kusa da prince sai ya tuna, da sauri ya koma bayan kujera yana cewa, am sorry papa, zanyi kokari next text dinmu na samu 10, prince ya mike ya nufi bayan kujeran, amir yayi saurin guduwa kicin yana kiran grany mami grany mami, mami ta rike hannun sa Zatayi magana prince ya shigo.
Tace prince pls ka daina dukan yaran nan , yayi karami dayin wadan nan punishments din naka, prince yace mami kyele ni dashi,ai yasan mai yayi, yasa hannu zai kamo amir, mami tace prince bar kicin nan, daga dawowar ka zaka takura yaro, prince ya juya ya fita,yana kiran fahad.

Ya dawo daga masallaci kenan yazo wuce dakin zuby dake kusa da nashi, yaji suna gulmar shi, tsayawa yayi yana sauraron su.
Zuby tace wai shin waye ya sanar wa ya prince ne,?, zarah tace kee mayb fa ya prince ya saka cameras a gidan nan, kinsan soja, zuby tace noo I dnt think yasa, zarah tace kodai ya fahad ne ya fada masa, zuby tace kila, amma ni wlh harna kosa ya koma wlh, zarah tace kedai bari mutum kullum fuska a daure,kamar an aiko masa da sakon mutuwa.

Prince yaja tsaki yayi shigewar shi daki.


Yau umman su niimatu ta tashi da ciwon kai, abu kamar wasa ciwo sai kara gaba yake yi, hankalin su ya tashi sosai, habu yace niimatu ina ganin mukai umma asibiti, niimatu data buga uban tagumi tace toh yaya, amma kudin fa?habu yace muje dai muji kome ke damun ta, akwai wasu kudi dana rantawa sanusi,sai na maso su, niimatu ta kada kai, sannan ta shiryawa umma sukayi asibitin.

Doctor ya duba umma, yace hawan jini ne ke damun ta , amma zai basu magungunan da zata ringa sha , inshaAllah zata samu sauki.

"Habu yaje ya amso kudin, suka biya komai suka dawo gida, ranar ko kasuwa basuje ba, suna nan tare da umman su suna kula da ita.



β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:55 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah




+2347010902548
Episode 7⃣





"Bayan kwana biyu jikin umman su niimatu yayi sauki.
,tunda sanyin safiya ya habu ya shigo gidan.
Niimatu na tsakar gida, tana juya kunu a wani yellow bucket ,tace yaya harka shirya?habu yace na shirya yau zamu kasuwa ,kije ki shirya kema so nake yau mu dan samu ko dari shidda ne sai mu sake siyowa umma maganinta,tunda dama na kwana biyu kawai muka siya; niimatu ta mike da kofin kunu a hannun ta,eh gara muje gsky dan, dan ragowar garin dake gidan ya kare ma, habu yace toh yi maza ki shirya mu tafi,niimatu tace toh ta shiga daki, a zaune ta iske umma,tace umma ga kukun ki,bari na shirya shaf shaf,yau zamu kasuwa, umma tace toh Allah yayi muku albarka,Allah ya kuma bada sa'a, niimatu na cire rigar jikin ta,tayi murmushi tace amin umman mu.

Suna shiga kasuwa,mutane sai tambayar yaya habu suke lafiya kwana biyu basu zo kasuwa ba?, habu ya fada musu rashin lafiyar umman su ne kwana kwana biyu , shiyasa ,sun tausayawa yaran kwarai,dan ba karamin kokari suke ba,dan kawai su ciyar da kansu.

Niimatu ranar ta kara dagewa tana ta advertising din kayan marmarin su,har yamma tayi,ya habu yace niina muje gida hakanan,kinga mun bar umma ita daya, tunda dai mun samu dari biyar sauran an biyo bashi a clinic din, niimatu tace toh, suka kulle rumfar su sukayi hanyar gida.

Suna cikin tafiya,niimatu ta hango wani mai naman tsire daga tsallaken hanyar da suke ,tace yaya mu saya wa umma dan tsire kona dari ne mana, tadan ji maiko maiko, ya habu yace tsire kuma?kinsan kofa kudin maganin basu cika ba, niina a bar tsiren nan,tunda dai ba sanin mu mai tsoren yayi ba, balle ya bamu bashi, niimatu tayi murmushin ta tace bari dai ka gani yaya, ina zuwa,tayi saurin tsallakawa titin,ya habu na kiran ta amma bata tanka ba,sai saurin take bugawa, tana zuwa wurin mai tsiren tayi masa murmushin ta mai sanyi ,sannan tace malam dan Allah ka bani tsiren nan sadaka, umma na zan kai wa bata da lafiya, mai tsire da farko bai so bata ba, mai ma so tanka mata ba, amma ganin innocent face dinta da kuma cute smile dinta, sai yace toh yan'mata,ya dauko tsinke daya yana washe baki, kamar gonat auduga, ya saka mata a takarda, yace gashi, ta amsa tana murya sosai, Allah ya zunduma maka albarka nagode sosai, mai tsire ya washe hakoran shi yace ba komai yan'mata, amma ina ne gidan.........

Kafin ya karasa tayi hanyar tsallake titi, da gudu ta tasar wa titin, cike da murna, bata ko tsaya kallon ko akwai motoci maso zuwa ba, sai smiling take tana kallon ya habu dake tsallake,tana daga masa takardar naman,dan ya gani.

Ya habu ya hango wata mota ta taho cikin speed sosai, ya kwala wa niimatu kira, yana nuna mata motar,dan ta koma baya , amma me kafin ta ankara motar ta kwashe ta kiiiiiiiiiiiiii.......



Toh readers waye ya buge niimatu?
waye wannan prince din
Yana da mata kuwa?toh kuma gashi harda yaro?
Miye ya faru shekaru biyar da suka wucen da prince ya kasa mantawa?
Mai zai faru da niimatu yanzu?

Ku kasance tare da afrah dan sanin amsar wadan nan tambayoyin.

Anan zan dan tsagaita muku da labarin YARβ™‘TALAKAWA, sai kuma Allah ya kaimu bayan sallah,inshaAllah zan ciga ba da sanbado muku ci gaban lbrn.
godiya mai tarin yawa ga masoyan yar'talakawa, idan nayi wani kuskure a rashin sani a yafe ni.



β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:55 PM] .: πŸ˜˜β™‘

🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘ TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳





By ~ afrah




+2347010902548
Episode 8⃣




Mutuwar tsaye yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login