Showing 21001 words to 24000 words out of 44930 words
Chapter 8 - Yar Talakawa Complete Hausa Novels by Afrah.txt
zan mayar maka.
Prince yace wane kaya, neena ta mika masa ledar, prince yaja tsaki, ta haka ake mikawa mutum abu a kauyen ku? Neena ta girgiza kai, sannan ta rufe idon ta , ta juyo ta mika masa.
Prince ya tabe baki, sannan ya amsa ledar ya bude.
Kayan daya bata ne a family house, ya mika mata ledar, mai zanyi dasu, ko kin taba ganina nasa kayan matane? Neena ta girgiza kai, yadda ta rufe idon ta, gashin idon ta masu tsawo suka karawa fuskar ta kyau, prince yadan kura mata ido, ganin girar idon ta, yayi wadda ta fado a kumatun ta, yadan kara one step zuwa gab da ita.
Neena ta sake matse idon ta, tana cewa , wayyo kayi hakuri, ban taba ganiba, a zaton ta bugun ta zaiyi.
Ya mika hannun sa, zuwa fuskar ta, zai cire gashin, zuby ta banko kofar dakin ta shigo, tana cewa neena neena, kizo ga ya abubakar dinku ya kira.....
Neena dake kusa da kofar ta tafi zata fadi, dan bude kofar da zuby tayi, ya turo ta ita kuma.
Da sauri ta ware idonta dan naiman ma kanta madafa, sai kawai taji ta a jikin mutum.
Ta shaki kamshin sa, zuby ta ware ido tana kallon su, wani mamaki da tsoro ya lullube ta, miye haka yake faruwa?
Prince ya ture neena gefe, da kyal ya iya ma turen tan, da duka gabobin sa sunyi sanyi.
Neena tayi saurin juyawa ta kalli zuby, na'am anty zuby.
Zuby ta kalli prince, ya wani watso mata harara, yayi kan gadon ya kwanta, yace ku fice min pls!!!
Sukayi waje da sauri, har suna buge juna.
Zuby kasa tambayar neena tayi, sai dai tayi alkawarin yin investigation akan abunda idon ta ya gane mata.
Washe gari juma'a, 21 of November, misalin karfe biyu da rabi na rana, dubun nan jama'a suka halarci _DAURIN AUREN_ na'im prince da Ikram isma'il.sai faruk da Deeja Aliyu.
Bikin ya tara manyan manyan yan siyasa, da masu hannu da shuni, sojoji dayawa sunzo dan a reception din har pareti akayi.
Da karfe 6 na yamma aka kawo amaryar ya faruk, deeja, ta sauka a gidan abba.
Karfe 8 aka shigo da amaryar prince wato ikram.
Gidajen biyu sun cika sun batse, angwaye kuwa na family house da abokansu, sai washe gari zasu dawo gida ayi budar kai, sannan kowa ya dauki matarsa yakai, gidajen dasu dad da abba suka gina musu.
Umman neena tazo itama, amma basu hade da yayaB ba, dan ita tana family house wai dole ne yaran zamani asa musu ido, dan kada muyi barna.
Neena na kicin tana taimakawa inna ladi suna wanke wanke, bayan ta raka umman ta , tahau mota.
Zarah ta shigo kicin din, tace neena ga waya yayaB zatayi magana dake.
Neena ta goge hannayen ta, ta amsa wayar.
YayaB tace, niimatu kina ji ko, neena tace eh, ki hado min koko da tuwo , zan aiko a dauko minke, ina zan iya da abincin turawan nan duk maso sa basar ne, neena tayi dariya tace toh shikenan nan da awa daya zan kammala, yayaB tace toh kiyi dai sauri yunwa kamar ta zautar dani wlh.
Neena ta nemi taimakon inna ladi, da wata mata da tazo daga garin su dad, suna kwatanta mata har ta kammala duka ta saka a flask ta ruba a kwando.
YayaB na ajiye wayar, ta sauki dan samun wanda zata aika.
Samari ne su hudu a falon, tana saukowa suka gaishe ta, ta amsa, sannan tace musu, akwai wanda yasan gidan bikin cikin ku?, suka kalli juna , suka ce mama bamu kai ga zuwa can bama, yayaB tace hakane kusa baki ne, ina faruk ? Din ne? Sukace yaje siyo credit a waje, yayaB tayi dan tsaki ai shi dama yawo kamar yaci kafar kare.
Ta koma daki dan jiran faruk, amma inaa yunwa ta addabe ta.
Ta fito ta nufi dakin da prince yake.
A kwance ta iske shi, yana kallon sama, gaba daya baya cikin farin ciki, har kamar shi, za'a aura wa wannan yarinyar da ko kamun kai bata dashi.
Jin hannun yayaB yayi, ta riko kunnen shi, yayi yar kara yace, yayaB mai nayi maki, zaki cire min kunne .
YayaB ta zauna tace, tashi na aike ka gida, prince ya zauna yana cewa, ni na gaji ki aiki faruk mana, yayaB tace ni kai nake so kaje min aiken ai.
Sai da tayi ta rokon sa sannan ya yarda zaije.
Neena na nan a tsaye wajen gate, sai dube dube takeyi, amma shiru ba wanda taga yazo.
Can ta hango wata black benz ta nufu ta.
Akayi parking a gaban ta, ta karasa wurin driver din, prince ya sauke mirror, neena tana ganin shi taji gaban ta yadan buga, wani irin kyau yayi mata , tace kodan yau auren shi, shiyasa yayi kyau abunsa.
Ta mika masa basket , ga abincin , prince ya dauke kai yace, waye dan aiken ki???
Aka°•○sultana
[8/9, 8:30 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃
By→afrah
Episode→6⃣6⃣→7⃣0⃣
neena ta kalle shi, hankalinsa na wurin wayarsa, tace ban sanar wa mum ba, kuma zan kula da amir.
Prince ya juyo, ya wani watso mata idanunsa yace, nace kizo muje ne? Neena ta sadda kanta kasa, ita wallahi sometimes, prince dinnan na kule ta, kullum sai iya gwale mutum.
Prince ya tada motarsa, neena tayi saurin cewa, ga abincin nan fa bansa a motan ba, yayi banza da ita.
Taga alamun dai wucewarsa zaiyi, ta bude motar da sauri ta shiga tare da kwandon , sai sauke ajiyar zuciya takeyi, inaa zata kuskure ya tafi, ta bani da masifar yayaB.
Tunda suka hau hanya, bai ko kalle inda take ba, sai tafiya sukeyi kamar kurame, har suka iso, yana parking motar ya fice abunsa.
Neena ta fito, ta dauki kwandon, tabi bayan sa.
A falon suka iske faruk da frnds dinsa, suna shiga yayi sama abunsa.
Neena tayi tsaye dan bata san ina yayaB take ba.
Ta gaishe da faruk da sauran dake wajen, sai kallon ta sukeyi.
Faruk ya taso yazo wurin ta, yace wurin yayaB kika zone? Neena tace eh abinci na kawo mata.
Faruk yayi murmushi ya nuna mata dakin.
Tana shiga yayaB ta mike, yauwa , ta tari neena ta ajiye kwandon a table, neena ta zuba mata sannan ta samu wuri ta zauna.
YayaB na kwasar girki tace, kince ummanki zata zo? Neena tayi murmushi, eh tama zo dazun harta tafi.
YayaB ta kallo neena, shine baki fada min ba?, neena tace ai bakya gidan lokacin, amma tace a gaida ke, yayaB tace ina amsawa naso ai mu gaisa, dan na mata maganar rikon ki, kinsan zaman kadaici na ishe ni.
Neena ta kalle ta da sauri, tace riko? YayaB ta ajiye cukalin hannun ta, tace, ko bazaki bini ba? Neena ta girgiza kai dan mamaki take ji.
YayaB tace, dana daya a duniya, kuma yanzu bama tare da juna, akwai wadda nake nema, nasan idan har na ganta takaicina zai ragu.
Neena ta jinjina kai tace, ina danki ya tafi? YayaB tace yana kasashen nasara, neena ta gyara zaman ta, azuciyarta taji tausayin yayaB, (yayaB ta manyanta sosai, amma jikin ta na nan gwanin sha'awa , yayaB kanwar mahaifiyar su dad da abba ce, itace auta a wurin maman su dad wato kakar su prince kenan wadda ta zasu lokacin haihuwar faruk).
Neena ta mike tace, zan koma, nasan amir nacan na nemana, yayaB ta kurbi ruwa, toh shikenan , na'im zaya maidake, bari na kira shi, neena kamar ta fasa ihu, ita dama ko ya faruk ne.
Ya fito daga wanka kenan, yaga kiran yayaB, yaja tsaki, wannan tsohuwar yar rigima ce wallahi.
Ya dauki wayar yace, kuma ya akayi ? YayaB tace kazo ka mayar da niimatu gida, ta kashe wayar.
Sai daya bata kusan awa da rabi, har neena ta fara gyangyadi ita da yayaB, sanna ya shigo.
Sukayi saurin farkawa, yace muje kawai ya fita, neena tayiwa yayaB sai da safe ta fito.
Sun hau hanya, aka fara zuka ruwan sama.
Har suka isa ana kwara ruwa, neena ta bude kofa tana tsoron kada ruwan ya tabata, prince yadan kalle ta, ya juyar dakai abunsa.
Da kyal ta fito daga motar, dai dai lokacin wata kawar ikram ta fito da umbrella, da gani tafiya zatayi.
Prince sai kallon neena yake yaga ya zatayi da ruwan nan mai karfi, sai yaga tayi tsaye a bakin gate din .
Yaja tsaki wannan ita shes very slow at everything, ya juya seat din baya, ya dauko umbrella ya fito.
Yazo har wurin ta, neena sai binshi takeyi da kallon mamaki, ya mika mata umbrella din.
Kawar ikram ta kalle su, baki bude, ta shige motar ta.
Tana shiga ta kira ikram, ta kwashe gaskiya da karya ta fada mata.
Ikram ba karamin tashi hankalinta yayi ba, lallai kuwa sai ta gyarawa yarinyar nan zama....
Aka°•○sultana
[8/9, 8:30 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃
By→afrah
Episode→7⃣1⃣→7⃣5⃣
Washe gari akayi budar kai, amaren biyu duka sunsha gayu abunsu.
Neena kuwa ko fitowa bata samu yi ba.
General dinsu prince sai ranar ya samu zuwa.
A babban hotel aka saukar dashi, yazo har gida ya gaida su dad da abba, yana yaba irin gwazon prince a fanni aikin su.
Prince gaba daya ranar busy yake, sai da yamma sosai , ya shigo gidan, ya samu mum a daki ita da mami.
Sai daya gaishe su sannan ya samu wuri ya zauna.
Mum tace anya kuwa kaci abinci ma yau kuwa? Prince ya girgiza kai, yace ban samu lokaci ba wallahi, sai dana kai general waheed har airport sannan na samu dawowa gida.
Mum da mami sukace ai gaskiya mutumin nada kirki sosai, kalla fa kayan da ya kawo mana.
Prince yace haka yake, yana kyautatawa soldiers dinshi sosai.
Mum tace Allah ya kara masa budi, mami ta amsa da amin.
Prince ya mike yana cewa, ni na gaji ne over, let me go n hv a rest.
Mum tace sannanu, sai kaje kaci abinci ka huta dan kuna da tafiyar safe gobe.
Su ikram dinma na side din mamin ku.
Prince ya wani dauke kai abunsa.
Mum ta mika hannu ta dauki wayarta, bari na kira zuby ta fada wa neena ta kawo maka abinci.
Prince ya juya ya fita, kamar ya shake mum yakeji.
Yana shiga daki, ya shiga ya watsa ruwa, ya fito ya saka kana nan kaya, ya zauna bakin gadon yana amsa waya.
Neena tayi sallama ta shigo, amir na biye da ita dauke da cup.
Suna ajiye masa, sukayi kofa dan fita, prince ya ajiye wayar hannunsa, yace zoki zuba min.
Neena taji kamar ta ruga da gudu, dan tasan shi ba'a iya masa.
Ta dawo tazo, ta fara zuba masa, amir na gefen ta, yana wasa da dutsunan rigarta.
Tana zubawa tace wannan yayi?, prince yayi kamar baiji taba.
Neena ta kada kai, tace a zuciyarta, ai maza nata ci soaai, ya faruk ma idan yace na zuba masa, dayawa nake zubawa kuma ya cinye.
Ta dauki serving spoon, ta kara abinci, har sai daya yayi suro.
Tace na zuba, ta rike hannun amir zasu wuce.
Prince ya daka mata tsawa, ke dawo !
Neena ta dawo ta tsaya, prince ya nuna abincin yace, ni dawa zanci wannan?, neena tayi shiru, prince yace, kewai komai baki iya bane? Tayi shiru.
Ya kara kulewa, yace, toh sai ki zauna, idan naci wanda ya isheni, sai ki cinye sauran.
Neena ta ware ido, ni naci abinci dazu, prince ya jawo table ya faraci, amir yazo wurin sa yace, papa, anty neena taci nata ita, prince yace, sai ta kara wannan ai, amir yace papa, ya mata yawa, ita ba acici bane, prince yace sai ka taya ta kuci.
Suna nan tsaye, yadan tsakuri abincin, ya tura masa sauran, mai uban yawa.
Neena ta dauka, tace amir muje, prince ya rike hannun amir yace, ba inda zaku, a nan zaki zauna ki cinye shi.
Neena ta bata rai, ita da yanzun nan ta gama shan fura wurin yaya B ga cake din da su zarah suka bata, ko ita rumbu ce ai sai haka, toh ga kuma wannan uwar fried rice din.
Kamar zatayi kuka, ta samu wuri ta zauna, daga waje, mami tayi kiran Amir.
Yayi waje da gudu yana amsawa.
Prince ya haye gadon sa, wayarsa tayi ring.
Ya dauka bakuwar numba ce.
Hello,
Ikram daga dayan side din ta kashe murya, tace hello dear,
Prince yadan daure fuska, pls waye?
Ikram taji wani daci a ranta, mijin ta amma ko numbar ta baya da.
Ta dai yi murmushi tace, ikram ce.
Prince ya tabe baki, ohh toh ya kike.
Ikram ta amsa da lafiya, amma ina son ganin ka pls.
Prince yace a gajiye, ganina ? Me zan miki?
Ikram ta hade miyau da kyal, lallai ma, idan tana son ganinsa sai da dalili tab.
Ta kara tsuke murya, yau frnds dina zasu tafi, suna so kuyi bankwana.
Prince yace am really tired nw, bt zan duba dai.ya kashe wayar.
Neena dake zaune a kasan carpet, tana tsakurar abinci, taji yana ta waya , kuma taji yace ikram, bt bataji ya sukayi ba, dan shi maganar sa silent, ko wace albarka.
Hakanan taji wani abu a zuciyarta, ita dai idan tana tare da shi, she fills save.
Kodan ya taba taimakon tane oho.
Prince yace, kee! Ba tunani na ajiye ki, kimin ba.
Neena ta samu kanta da shagwabe fuska, tamkar yadda takewa, yaya habu, idan ya matsa mata taci abinci.
Ni na koshi☹, Allah cikina zai iya fashewa idan na cinye wannan.
Prince ya kura mata ido, hakanan yaji dama, taci gaba da maganar.
Ya mike ya nufi closet dinshi, ya dauko kudi bandir uku na dari biyar biyar.
Yazo gaban neena ya mika mata, ta ware ido, wannan kuma fa, ta furta a zuciyarta.
Yace amsa mana, ta amsa, yace kije side din mami ki basu.
Neena tace su wa? Prince yace ikram, sannan ya shige toilet.
Neena ta mike, ta kwashe kayan abincin, ta fita da kudin tayi side din mami.
A hanya suka hadu da zuby da zarah, sukayi barkwancinsu, tana zuwa taji firar yan mata, ta shiga da sallama.
Duka falon aka kallo ta, yan matane masu ji da kansu.
Ta rasa wa zata tambaya ina amaryar, tunda amaryar faruk an kaita dazun ita.
Ta nufi kicin ta tambaye inna ladi, dan tana side din tana wa frnda din amaren girki.
Tana shiga dakin, ta iske ikram tare da kawayen ta su biyu.
Tayi sallama, ta gaishe su, duk suna zaune a bisan gadon, daya na chat, daya na waya, ikram na duba wani book.
Suka watso mata kallon raini.
Ta karaso ciki ta mikawa ikram kudi.
Ikram ta harare ta, daya daga cikin kawayen tace, wannan ce fa yarinyar.
Ikram tace na gane ta ai, ta mike, neena tace gashi inji ya prince.
Ikram ta wani daure fuska, haushi kamar ya kasheta, wato bazai iya zuwa ba, sai na aiko wannan _YAR TALAKAWAN_
Kawarta tace , lallai ikram , kinyi sa'a mune anan, dakin bani da sharrin su teema.
Ikram taja tsaki, ta kalli neena sama da kasa, sannan ta nuna ta da yatsan ta dayaji karin akaifa da jan barce.
Ke kada na sake , na kara jin ko gani ki, tare da prince kinji ko, dama ko yan kauyen nan yaya _TALAKAWAN_ nan, aikin ku kenan snatching mazajen wasu.
Kawayen suka kwashe da dariya, neena ta dukar da kai kawai, ikram taja hannun ta, ta tura ta waje, get out , dayar kawar tace mutum kamar bunsuru, tana shigowa dakin yahau wari.
Neena na fita tayi garden da gudu, ta samu wuri ta zauna, wani kuka tari yazo mata, zamanta tare da family dinnan shekara daya kenan, (kenan shekarunta sha bakwai yanzu)
Ba wanda ke wulakanta ta, tasan ita ba yar kowa bace, tasan ita _YAR TALAKAWA_ ce, amma ai suma mutane ne.
Ta saki wani kukan, ita kam tasan ya prince , ba sonta yake ba, amma yanzu, itama kam ta fara kamuwa sa son sa, dan yadda yake taimakon ta.....
Aka°•○sultana
[8/9, 8:30 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃
By→afrah
Episode→7⃣6⃣→8⃣0⃣
Hannu taji a kafadarta an dafa ta, a tsorace ta juyo dan ganin waye.
Prince ta gani a bayanta, ta ware ido, tana goge su , wai ko gizo ne yake mata.
Prince ya zauna a kusa da ita, (ya kasa barci shine ya fito shan iska, Allah yasa ya hango fitowar ta sashen mami tana kuka).
Yana zama neena ta mike da sauri, zata fice.
Prince ya riko hannunta, ta